← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 117

Sashe 28

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙarfe 11 da rabi na dare Uncle B ya kira ta, bai yi tsammanin bata yi barci ba a wannan lokacin amma ba zai iya sake kwana suna fushi da juna ba. Reina itace da laifi ita kanta ta sani, amma a yanzu a shirye yake ya sauƙar da kai a samu daidaito a tsakanin su, domin bai san yana tsananin sonta ba sai da yayi kusan kwana biyu yana kwokwanton yanayin da take ciki da lafiyar ta. Ya sani abu mai sauƙi ne a wurinta ta wuni ta kwana tana kuka, a yanayin lalurar da take fama da shi kuma yawan kuka zai iya zama barazana ga rayuwar ta gaba ɗaya.

Kallon wayar dake saman gado take yi har ya gama ruri a karo na farko ya sake bata da ƙarfin ƙarasawa balle ta ɗauka. Sai a karo na huɗu da wayan bai fasa ringing ba taga kuka ba zai mata maganin komai ba amma Uncle Bilal zai iya wani abu a kan yanayin da take ciki don haka ta rarrafa har jikin gadon ta ƙara wayar a kunne tare da saka mishi wani kukan bayan ya ɗauka.

"Doll...." Ya kira yana jan numfashi don a tunanin shi shine dalili.
"Hafsah na, I'm sorry, na tuba ba zan sake ba, ki bar kukan haka Please"

"Un...cle Bilal... Un.."

"Ya isa Hafsah, ki sha maganinki ki kwanta gobe zan karanto miki laifuka na in nemi yafiyan su kinji?. Kinji Second mummyn Mufid?"

Ta bangaren shi ya kaste kiran bayan ƙoƙarin shi na lallashin ta da kalamai masu taushi, ita kuwa ajiyar zuciyar niman bakin magana take sauƙewa shiyasa yayi tunanin ko ta haƙura ne.

Yunwa, gajiya da ciwon kai su suka yi mata dalilin zuwan barci bayan ta haɗiyi maganin ba tare da ruwa ba ma, domin idan na huɗun su ya haɗu mata toh tabbas ba zata wayi gari lafiya ba.

......

Farin hoodie ne ƙarr a jikin shi, gashin kan shi na rufe a cikin hular rigan ya ƙaraso jikin dining ɗin da Aicha da iyayen ta ke zaune, tare da ƙannen shi da nata ƙannen, su Abban shi ne kawai suka koma Maradi da safiyar nan su ƙarƙare komai cikin kwanaki biyu yanda zasu koma gida Nigeria su cigaba da rayuwa cikin ƴan uwa domin wanda suka gudo a dalilin shi ma a shirye yake ya koma.

Gaisawa suka shiga yi suna mishi ban gajiya yana mayar musu banda Aicha da kanta ke sunne a ƙasa tana wasa da abincin gaban ta cikin tsananin kunya.
Ta sani bata yi daidai ba, tun kafin ta aikata ta sani amma hanyar da kawai take tunanin zai ɓulle mata kenan.
Ko shi ya gane nufin ta ko iyayen shi da nata suyi ƙoƙarin haɗa zumunci ita kowanne a cikin su yayi mata in dai zata mallaki Yaseer.

Kallon ta kawai yayi ya nemi wuri ya zauna ya fara cin abinci a nufin shi sai su biyun su zai yi mata magana amma ya manta bai gargaɗi masu kai da kunnuwan nan ba.

"Yayan mu yau na amsa kiran mutane har naji ba daɗi, har da masu min mitar auren gatan matasa guda ban gayyace su ba" Suhail ya fara magana.

"Ni na kashe wayan ma" cewar Sabir. "In banda shiga uku mutum da ƴar uwar shi don kawai sun yi hoto tare?"

"Amma fa duk wanda bai san zahirin lamarin ba dole yayi musu gurguwan fahimta, tunda har shafukan da bayi ɗora wani abu da ya shafi rayuwar shi sai da ya ɗora hoton, kuma nasu su kaɗai mu munyi kwantai, ga caption Alhamdulillah kawai ya rubuta, kaga dole su yi mishi kallon Aure"

Irfan da ya cika bakin shi da dankali yana dariya yace "ai sun yi kyau ne, kaman amarya da ango"

Murmushi ne ya suɓuce ma Aicha kafin Yaseer ya gwale irfan. "Yi mana shiru ɗan secondary kawai" ya kuwa shaƙa ya hau fushi.

Alaji Abdou da Mariama dai basu ce komai ba suna sauraron yanda hiran tasu zai kasance. Zasu yi kwaɗayin haɗa zumunci da nagartaccen yaro kaman Yaseer amma basu son su gwada wata alama da zai saka iyayen shi suyi ƙoƙarin tilasta mishi ya auri ƴar su Idan bayi son ta. Idan sun haɗe kansu zasu fi kowa farin ciki idan basu ra'ayin juna kuma Allah ya haɗa kowa da rabon sa.

Sai da aka kammala karyawa kowa ya miƙe, ganin Yaseer bai tashi ba ya saka itama Aicha ta zauna tana jiran ta amshi laifin ta.

"je suis vraiment désolé (I'm really sorry), ba zan sake ba"

Ya sani Aicha tana son shi, shi ba wawa bane ya daɗe da sani. Amma bayi jin komai a kanta bayan irin abinda yake ji a kan su mai haƙuri, shiyasa a maimakon ya gwada ya fahimci halin da take ciki amma bayi ra'ayi ta muzanta ya gwammace yayi pretending bai gane ba har yanzu.

"Me kika yi kike bani haƙuri?" Ya tambaya muryar nan Calm Amma bai kai ya ɓoye ɓacin ran shi ba.

"Na ɗaura pictures ɗin mu a platform ɗin da basu kamata ba" tayi admitting cikin sanyin murya.

"Lallai kin yi Babban laifi ƴar ƙanwa ta..."

Haka kalmar 'ƴar ƙanwar' nan ya rikiɗa ya zamo kifiyoyi kafin ya watsu mata a kan zuciya ya ɓula shi ta ko wani angle, yau ko darling ɗin ma babu.

"...kina so ki kashe min kasuwa ne ƴar budurwar da nake ƙoƙarin lallaɓawa tayi tunanin fasawa nayi?"

Sai ta zuba mishi idanun da hawayen takaicin shi yake bin su.
"Ni kada ki ɓare min baki, jeki na haƙura, zan sauƙe in wayar musu da kai ba abinda suke tunani bane"

Da ace zuciyar ta ba ƴar abu kazan uba bane da a yanzu yaci ace ta haƙura da Yaseer kafin ya gama ƙarasa ta. haka ta miƙe tana riƙe ƙirji ta taka a sannu ta bar wurin, zuciyar ta bindiga zata yi idan taci gaba da kallon fuskar shi.

Ya bita da kallon tausayi, da ace ana cusa soyayya dole a zuciya da yayi ƙoƙarin cusa na Aicha ma tashi busashshiyar zuciyar, domin ta cancanci a sota ta kowani ɓangare. bata da makusa bata da aibu, amma ba haka abun yake ba.

Tun kafin gari ya waye kuma ya hau ya goge hotunan tare da sauya su da wanda suka yi baki ɗayan su, ya rubuta cikakken bayanin bidirin da suka yi har da cake ɗin da aka rubuta mishi 'congratulations on your graduation' sai da ya ɗaura. Kuma ya canza passwords ɗin shi duka, Aicha tayi haƙuri amma ba zai sake bata wani damar ba.

.....

"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Wallahi yayi aure. Sun yi aure da yarinyar nan umma"

"Waye?!" Salatin da Zahra tayi ya saka Hajiya Hauwa rikicewa amma sai ta juyo mata fuskar wayan ta yana nuna hoton yaron nan da ta dame ta dashi tun da ta fara following ɗin shi.

Tsaki Hajiya Hauwa ta ja na haushin Zahra da kuma ganin wayar Reina da ta ƙwace da safiyar bai daina ringing ba, Uncle B bai fasa kira ba. Tayi ragon azanci ne ma da tun da ta karɓe ya kamata ta kashe amma ta bari har kiran shi ya fara shigowa, yanzu yana jin wayar a kashe shima wani tashin hankali.

"Amarya ta ba zata karya bane ita" Jamal ya tambaya hankalin shi a kan cinyar kazar da yake yaga.

Cike da takaici Hajiya Hauwa ta dube shi, yanda ya mayar da kan shi kaman ƙaton bayahude.

"Yanzu fisabilillahi wa zai kalle ka yayi maka kallon mutumin arziƙi?"

Dage kafaɗa yayi "Ni ina ruwa na da kallon mutane? I'm just living my life, ina moran ƙuruciya na"

"Moran ƙuruciya. A hakan?" Zahra ta tambaya tana mishi kallon sama da ƙasa, jikin shi har abun ƙyama. Gashi a bushe ƙashi da rai, ga wasu munanan tatoos, ya ɓula kunne don ma Alhaji Salisu ya tilasta mishi cire ɗan kunnen da ya saka da wanda yake harshen shi, yanda kasan Lil wayne. Takaicin shi ya hana Abban karyawa a gida yau.

Wata mummunan ashar da yayi Hajiya Hauwa saida taji dirin shi ya lailayo ya lailaya ma Zahra, "ke zan ci kazan uwar ki shegiya algunguma ƴar kaza-kaza" Zaheera saida ta toshe kunnen ta.

Duka Hajiya Hauwa ta kai mishi ai kuwa sauran kaɗan ya rama Allah ya taimaka ya sauƙe hannun yana ƙwafa. "Na shiga uku na lalace" tace tana duban shi sai kawai yayi mata murmushi ya ɗauki kazar shi ya cigaba da gurgura.

Kiran Uncle B da ya shigo wayan Hajiya Hauwa a lokacin Jamal yayi saurin ɗauka.

"Hello Uncle " ya ambata yana washe baki.

Sai a lokacin Uncle B ya fahimci komai.

~~~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

62

~~~~~~~~~~
_Grew up famous too_
_Just a baby born Blue Now_
~~~~~~~~~~

"Jamal?!" Ya ambata cikin shakku da mamaki amma sai jin gayen yayi ya amsa da

"Na'am Uncle"

"Aunty hauwa muryar Jamal nake ji?"

Kasancewar wayar ba a speaker take ba ya amsa da "nine Uncle, jiya na dawo ai. Ga umman nan" da hannun shi mai danƙon romo ya cire wayar daga kunnen shi ya saka ma Hajiya Hauwa a nata kunnen.

Kafin tayi magana cikin ɗaga murya yace "Jamal ne nake jin muryar shi a parlon ki ba a cell yana ihu sojoji suna ci min uban shi ba? General da yace ki kawo shi ya san da zuwan sa?"

Miƙewa daga wurin tayi ta shige kitchen tunda shi yafi kusa tare da rufo ƙofa kafin cikin muryar roƙo tace "Dan Allah a bar maganar nan Bilal, ya riga da ya wuce"

Bayi jin idan surfa mata zagi yace zai yi zai amfane shi da wani abu balle musanyar yawu da ita don haka juyawa yayi daga ƙofar lab ɗin wanda har ya saka ID card ɗin shi ya buɗe, zai sauƙe wayar daga kunnen shi ya taryo muryar ta tana faɗin "ya sani, general ya sani" ta faɗa sanin cewa kiran general ɗin shine abu na gaba da zai yi. "Na je har Kaduna na amshi laifi na a gaban shi, na gurfanar da Jamal ma ya bashi haƙuri, shine ya yanke masa hukuncin auren Hafsatu tunda ance ya ɓata mata rayuwa"
Chapter 28 · 0% Book details