← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 117

Sashe 31

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta riƙo hannun Reina dake lulluɓe cikin baƙi da jan lallen da ya dace da hasken fatar ta ya fito yayi kyau duk da ta caɓa zanen jan, baƙin kuma bata bar shi ya gama bushewa ba ta wanke.

"Mai sunan kina addu'ar da nace kiyi ta yi?"

"Ina yi fa Ummi, ina yi har da wasu ma, nayi istigfari nayi ma Annabi salati, har duk wasu addu'a da na sani duk nayi Ummi" tace hawaye na sake ɓalle mata.

Sai Ummi ta rufe hannun da ta riƙe cikin tafukan ta jin yanda yayi sanyi. "Dukkan tsanani yana tare da sauƙi, alƙawarin Allah ne Hafsah, kuma in sha Allah naki sauƙin ne yazo"

"Ya Allah ka tausaya min" ta kife kanta a kan cinyar Ummi tana ɗaurawa a kan kukan tunda yanzu ta huta, kuma daga gobe shikkenan hala ta daina zubar da hawaye sai dai jini daga idanun ta, idan tana raye kenan ma.

Shafa kanta Ummi take yi tana jin kaman ba zata iya jurewa a ƙarasa shirin nan da ita ba, ta amince ne saboda Yaseer da ta yarda an zalunce shi. Domin da Alaji Abdou yazo mata da zancen Tahir na raye hankalin ta bai fara ɗaukan zancen ba har sai da ya nuna mata hoton shi da suka ɗauka kwanan nan, shine a bidirin graduation ɗin Yaseer.

Lokacin ce mata yayi "Kinga dai wannan yarinyar dake tsaye ta nan gefen har parlon nan na shigo da ita, wannan kuma matata ce ƙanwar mahaifiyar ta mai rasuwa da kuma sauran yara na, sai shi yaron da abun ya ritsa dashi da iyayen shi. Hoton nan bai kai ko sati biyu da ɗauka ba, ga kuma Tahir a cikin ta kin gan shi"

Dalili kenan da ta amince take bin shirinsu shiyasa ma bata yi wani gayyata ta wurin ta ba domin ta san auren manufa ne, amma halin da Reina ta shiga ciki yana karya mata zuciya.

.....

Dariyar da ya ƙwace ma Yaseer ya saka tea ɗin da ya kurɓa ya biyo bakin shi zai zuba yayi saurin saka tissue ya tare.

"Dubu ɗari biyu dai kace Daddy?! Amma wannan an yi matsiyatan mutane" yaci gaba da murmushin dake fitowa daga ƙasan zuciyar shi yana jin wani ni'imtaccen daɗi. Ai Reina ma bata ga komai ba tukunna.
Ya ɗaura da "Mahaifin ƙawar ta safina ma yace wai sun ce lefe ma sai an ɗaura aure zasu kai mata gidan ta, sai naji kaman ma na haɗa musu a kai musu tunda dukiyar da suka satan basu iya cinta."

Alaji Abdou ya murmusa, da gaske shima ƙarancin da suka nuna ya bashi dariya, ko tsaban don sun raina ma Hafsatun hankali ne oho, tunda ga mara gata.
Harta invitation basu wani tura sosai ba, ba wai bikin bane basu son azo musu sai don suna kunyar gwada Jamal a matsayin angon kuma ɗan su. Basu ma san yaya zasu yi da tatoos ɗin shi ba idan ace babban riga da hula zasu ɓoye illar da ƙwayoyi suka yi ma jikin shi. Amma Yaseer har biyan platforms yayi aka ɗaura katin auren, gidan radiyo har ma da gidan talabijin wanda basu ji ba su ji wanda ba'a gayyace su ba su zo ayi dasu.

Suhail dake shigowa balcony ɗin yace "kamata yayi muyi convoy goben nan ayi hiring body guards da zasu take mana baya, motocin gidan na ayi all out da su muje mu kankaro mutunci."

Yaseer yana shirin gwale shi Alaji Abdou yace "duk abinda kuke so kuyi, kun daɗe kuna rayuwa a ɓoye ba tare da kun yi laifin komai ba, lokaci yayi da kuma zaku futo"

Wani ihu Suhail ya saka da faffoti ya koma inda ya fito yaje ya shelanta ma sauran ƴan uwan shi yana faɗin "akwai celebration gobe"

"Daddy baka san yaran nan bane yanzu sai suyi abinda zasu bawa kowa mamaki".

"Na gobe ne kawai, ka bari su yi making grand entrance "

Ya girgiza kai yana ƙaramin murmushi. "Allah ya kaimu goben da rai da lafiya".

.....

*Toh muma Allah ya kaimu goben da rai da lafiya. Gnyt*

*Seemahwrites ✨*

64

*Washegari*

Da ƙyar ta iya miƙewa tayi sallar asuba ba wai don ta samu barci ba, sai don yanda ciwon da take ji a zuciyar ta ya kama ko wani gaɓa na jikin ta saboda abun yayi mishi yawa shi kaɗai.

A yanda tayi sallah a wurin rana ya fito ya same ta, bakin ta ne kawai bai gaji da motsi ba yatsar ta maƙale da counter, amma idanu da numfashi sun yi mata barazana sun gaji.

Yanda zaka san suma niman kai suke yi da ita ko irin girke-girken biki da ake farawa tun asuba, wasu ma tun kafin asuban suke tashi basu ɗaura ba, babu ma wanda ya tashi har yara kowa ya yada kafaɗa yana barci har ƙarfe 7 kafin kukan masu jarirai ya ɗaga su, sai a sannan suka fara niman abinda zasu karya dashi.

Ƙarfe 8 Aunty Zeenat ta tura ƙofar ta shigo ɗauke da bokitin plastic mai ruwan zafi. Sai da ta ajiye a banɗakin Ummi kafin ta dawo ta dubi Safina da Maama dake yashe a gado kowa ta ɗuƙunƙune cikin hijabi. Har ta nufi gadon ta hango wacce take nima a ƙasa ta ƙarasa wurinta ta durƙusa.

"My daughter" Aunty Zeenat ta bubbuga ta murmushin fuskar ta yana gagara ɓoyuwa, basu yarda sun shiga hidimar nan ba saida Ummi ta bayyana musu halin da ake ciki, domin sun so mata tijara daga farko, tace su kwantar da hankalin su in sha Allah alkhairi ne.

Kamo kafaɗar ta tayi ta zaunar da ita sai ta zube mata lakatar a jiki. Da gaske ta bawa Aunty Zeenat dariya ganin yanda tabi duk ta ɗaga hankalin ta, amma kuma suma da ace basu san gaskiyar ba tada jijiyoyin wuyan da zasu yi ba kaɗan, ayi auren dole ma yaran kowa amma banda na Fauziyyar su, ƴar uwar su Fauziyya da babu kamar ta.

"Ki tashi kiyi wanka ko zaki ji daɗin jikin ki, kinga ƙarfe 11 za'a ɗaura,"

"Da mutuwa nayi da yafi mun ko mummy Zee"

"In sha Allah sai kin yi rayuwa abin kwatance, zaki yi farinciki ɗiya ta"

Ita ta miƙar da ita tsaye ta taya ta rage kayan jikin ta, sannan ta tura ta toilet ta rufo mata ƙofa tayi kan su Safina suma su tashi su taimaka mata da wani abun.

Ƙarfe 9 da rabi lokacin gidan ya ɗan daɗa cika sai ga mota daga gidan Hajiya Hauwa wai an zo ɗaukan amarya.

"An zo ɗaukan amarya a kaita ina? Su jira a ɗaura auren mana idan sama jannati ne ma sai su tafi da ita!" Aunty Sajeedah autar Ummi ta hau sababi.

"Ita uwar angon ne tace akwai walimar da zasu yi da zaran an ɗaura ɗin, toh kada a ɓata ma manyan baƙin da ta tara lokaci shiyasa take son su shirya amarya tun yanzu." Cewar matar da aka turo da driver, kana ganinta kaga cikakkiyar yar bariki gashi sai taunar chewing gum take yi ƙas-ƙas.

Hayayyaƙo mata suka yi, bata ce ma kowa komai ba bin su kawai take yi da kallon hadarin kaji tana jiran wani ya ɗaura mata hannu ne a cikin su suga yanda ake yinta, shiyasa ma suka zaɓe ta sanin tafi kauri a hidiman rashin mutumci.

"Aina'u! Rufe min bakinki ki bani wuri." Cewar Ummi dake riƙe da mace fuskar ta rufe da mayafi, kukan da take yi ya saka Ummin rufe mata fuska domin tayi jaa kaman tumatiri.

Ƙarasawa jikin motar tayi suka bita da kallon mamaki har direba ya buɗe musu ƙofar baya ta zaunar da Reina, amma ta riƙo Ummi gamm duk yanda taso ƙwacewa ta gagara.

"Kada ki damu, komai ya kusa zuwa ƙarshe kin ji, ki daure saura kaɗan" shine abinda Ummi ta raɗa mata a kunne sai kuwa ta sake ta.

A wurin Hajiya Hauwa ƙasƙanci ne idan an ɗaura aure ta turo mutanen ta ɗaukan amarya irin wannan unguwan a wannan gidan, shiyasa gwamma magana ya tsaya a ita take riƙon ta, tuwo na mai na aka yi.

Ita Ummi hakan ma zai fi mata saboda draman da za'a baro gidan nan ya kasa masa, gwamma su ƙarata ta can idan an gama azo a bata labari.

Ta juya ta dube yanda suka yi cirko-cirko mamakin abinda tayi ya hana su magana "Aina da Zeenat ku shiga ku raka ta"

Da gudu Maama ta fito Safina na biye da ita ɗankwalin ta a hannu, tana ƙoƙarin yafa gyalen ta a kayi. Zagawa tayi ta shiga bayan motar ta ɗaya ɓangaren ta rungumo Reina, kada ma wani yace ta fita ko za'a raba su.

A ƙarshe su huɗu suka shiga bayan motar, Aunty Aina, ƙanwar ummi, Safina da amarya Reina, ita kuma matar da suka zo ta koma gaba.

Aunty Zeenat,Aunty Sajidah, Maama da wasu wanda suka dage ma tafiyan suka bisu a adaidaita har biyu.

Da ƙyar aka bar su Aunty Zeenat dake napep suka shiga gidan bayan an bar motar amarya ta wuce ciki. Da suka shiga gidan ma kutsa su ɗakin kwanan Reina aka yi dukkan su banda ita amaryan da suka ɗauke ta zasu sake mata shiga kuma ko ruwa babu wanda ya miƙo musu.

.....

10:55am.

"Bismillahi mun iso" cewar suhail yayin da suka tunkaro babban masallacin juma'a da za'a daura aure motocin hukumar NDLEA da siren ɗin su suna musu rakiya. Ya dubi Yaseer da ya toshe idanun shi da ɓakin shades yana sakin malalacin murmushi.
Sun yi a kan kowa motar shi daban zasu zo amma Suhail yana burin ganin reaction ɗin Yaseer ɗin.

Ya fito ya jingina da motar yayin da jami'an suka kutsa harabar masallacin da makaman su.

.....

Tun kafin Alaji Abdou ya ƙaraso aka wangale mishi gate, suka kutsa hancin motar su ciki. Shi ya fara fitowa ya tura a kira masa Hajiya Hauwa.

"Alhaji barka da zuwa, ashe kana tafe" ta tako cikin shigan ta na alfarma tana faɗin "kada ace har ka bi wurin ɗaurin auren ƴar taka, Ai abban su yaso kayi mata waliyyi amma yace kai da shi duk ɗaya ne, shi Jamal kawun shi ya karɓa masa tunda kai ɗin ba zaka samu dama ba."
Chapter 31 · 0% Book details