Sashe 8
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kai tsaye yayi gaba abinshi suke rufa mishi baya, ya sama ma kanshi mazauni yana sauƙe numfashin gajiya kana suka shiga gaisawa suna mishi yaya hanya.
Sanin shi ba mai yawan surutu bane Hajiya Hauwa ta gabatar mishi da abinci.
"No I ate on the plane, zan fi so in fara Sallah tukunna" yace yana duban agogon wayan shi lokacin la'asar har ya shiga.
Sake duba saƙon da ya tura ma Meesha tun sauƙar shi a airport ɗin Lagos yayi amma har yanzu bata yi reply ba, ga wanda ya tura mata watanni biyu da suka wuce wanda ke ɗauke da hoton doctor Fahad da duk wani bayanin shi har tsayin shi da size ɗin takalmin da yake sakawa sai da ya tura mata.
Yana mai sanar da Ita zai tura shi ma iyayenta Saboda sun dace da juna shima ɗan babban gida ne.
Shima bata yi reply ba har yau da bikin sauran sati ɗaya.
Ya miƙe ganin Hajiya Hauwa tayi mishi tsaye a kai tana jiran ta gwada mishi masauƙin shi. Idan yayi sallan sai ya kira mahaifiyarta ta haɗa su, yau kam yana buƙatar magana da ita.
A bakin kofa Hajiya Hauwa ta tsaya bayan ta buɗe mishi "Idan kana buƙatar wani abu kawai ka kira ni"
"Thanks" yace ya turo ƙofar ya rufe.
Ya fara da ajiye wayar shi da agogon hannun shi a kan chest of drawers dake kusa da toilet hankalin shi bai kai kan Reina dake kwance mashe-mashe a saman gadon ɗakin ba, ya buɗe ƙofar toilet ɗin zai shiga warin bleach ɗin da ya daki hancin shi ya tseratar dashi daga taka tsantsin wurin, har yana ganin yanda zai timu a ƙasa a cikin kanshi.
A hankali ya maido da ƙafar shi na hagu ya juya zai bar ɗakin dogon minsharin da ta ja ya saka shi saurin juyawa idanun shi suka sauka a kanta.
~~~~~
Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.
*Seemahwrites ✨*
46
.
.
"...Bata jin magana bata gaida mai jin sa" ta ƙarashe tana duddungure ma Reina dake kan guiwowin ta kayi. Ita kuwa tayi baya ta zauna da kyau idan ta gama zungurin ta sai ta faɗa mata taci gaba da kneel down ɗin.
"Kuttt, uban wa yace ki zauna?" Ta zuba mata dundun da ya saka ta sakin ƙara ta miƙe bayan ta da kyau, "kaga abinda nake faɗa maka ko?" Ta gwada bakin Reina da ta turo shi gaba tana mumbling Allah ya Isa a ƙasan maƙoshi. Sai a lokacin Uncle B ya ɗago ya kalli yanda take kumbure-kumbure kaman ita aka yiwa laifin, taɓe baki yayi ya maida hankalin shi kan wayan shi.
Lokacin da ya sameta tana barci a ɗakin, zagawa yayi ta ɓangaren da take kwance ya kalli fuskarta yaga wata hamshaƙiyar ce?.
Hannu ya kai ya bubbugata amma a maimakon ta buɗe Ido sai ta ƙara gyara kwanciya ta nannaɗe jikinta taci gaba da minshari harda tanɗe baki.
Ɗan murmushi yayi, koma wacece yanda take jin daɗin barcin nan bai kyauta ba idan ya tashe ta. ya juya ya bar ɗakin.
"Uncle B" Zahra ta kira lokacin da taga ya fito daga ɗakin kaman yana niman wani abu, kuma tana tsoron tambayar shi ta ɓata mishi rai.
"Kawo min buta inyi alwala a waje". Yace da ita.
"A waje kuma?" Ta waro ido.
"Kurmanta ya fara kama ki?"
"Allah umma ta ganka a waje dukana zata yi"
Ya sauƙe numfashi, "ina toilet ɗinki?"
Tana son tambayar shi mai ya samu nashi toilet din amma tana tsoro, gashi ɗakin ta babu gyara tarkace ne barbaje a ko ina, Umma tayi mata magana ta gyara har ta gaji, don haka sai ta shiga dashi ɗakin su Zaheera.
A parlour ya dawo ta shimfiɗa mishi darduma ya tada Sallah. Sai a lokacin Hajiya Hauwa ta shigo ɗauke da tray mai jug ɗin zoɓo da na kunun aya, Zaheera na biye da ita da wani tray ɗin mai ɗauke da ruwa da kofuna.
Reina guduwa tayi suna tsaka da aiki, ita taso sakawa ta kawo wannan, gashi ko ƙyallin ta bata sake gani ba tun wanke banɗakin ɗazu.
Sakare tayi tana kallon Uncle B dake Sallah a parlour, toh ko ɗakin da aka bashin bai yi masa bane?.
A lokacin ya sallame tunda ƙasaru yayi, yana ɗan zikirori Hajiya Hauwa da ba zata iya haƙuri ya kammala ba tace "Bilal ko zaka koma ɓangaren Abban su?"
Bai kulata ba saida ya shafa ya juyo. "Can ɗin ma yayi, zuwa anjima zan tafi kada ki takura kanki"
neman wuri tayi ta ajiye kayan hannun ta a gaban shi sannan ta shiga tsiyaya mishi.
"Kayi haƙuri a baka wani ɗakin idan wancan bai yi ba"
"No, na riga nayi booking hotel, zan fi sakewa a can" daga yanda ya fito mata a mutum ta san ya riga da ya gama magana amma bata daddara ba, wannan kusancin dake tsakanin su da Maryam itama sai ta samu, kada idan komai ya kankama ta dawo ƴar kallo.
Ta buɗe baki zata sake cewa wani abu Ƙofar ɗakin ya buɗe Reina ta tako tana tangaɗin barcin da bai gama sakinta ba ta fito. Gabaki ɗaya hankalin su na kanta ba'a maganan Hajiya Hauwa da mamaki ya bushar da ita.
Hamma tayi tare da miƙa tana mommoƙada jikin ta saboda yanayin kwanciyar ta ya saka mata tsamin jiki, ta kai hannu kan cikin ta dake kukan yunwa tana saake wani hamman, a gaskiya sai taci abinci ma kafin tayi Sallah wannan.
Juyowar da zata yi idanun ta ya sauƙa cikin na Hajiya Hauwa biyu, na Zahra biyu, na Zaheera biyu da kuma ɓakon idanuwan da taji nashi kallon har hanji, ya ɗaga kofin zoɓo zuwa bakin shi sannan ya ɗauke ganin shi daga kanta.
Rasa abun cewa ya saka Hajiya Hauwa tafa hannuwa "Hafsatu!" Kada ace ita tayi dalilin da Bilal ya fito yin Sallah a falo, yaranta ma saida ta ja musu kunnen su kama kansu balle wannan abun da ba kan gado gareta ba.
"Barci ne ya ɗauke ni wallahi, kuma yunwa nake ji yanzu, ina cin abinci zan koma in ƙarasa kafin inyi Sallah ma" ta sani tabbas sai ta daku amma idan za'a bata abincin a dake ta da sauƙi.
Miƙewa Hajiya Hauwa tayi ta tunkare ta gadan-gadan, a tsorace Reina ta kame jikinta a jikin garu ta saka hannunta biyu ta kare kanta sanin a wurin zata fara kai mata duka ta saka mata ciwon kai. A maimakon tayi mata wani abun sai ta wuce ta faɗa ɗakin jin wai zata ƙarasa, zata karasa mene kenan?.
Kan gadon a wargaje kuma tana da tabbacin ba Bilal bane ya hau kuma da hannunta ta gyara shi, gashi turaren wutan da tace idan ta gama wanke banɗakin ta saka ma bata saka ba. Tazo wuce toilet ɗin da ƙofar shi yake a ɗan buɗe warin bleach ɗin da ya shiga hancin ta ya saka ta ta tura ƙofar ta buɗe. Ko rabin shi Reina bata wanke ba, ga bokitin ruwan kumfa har ya dawo farin ruwa kumfan yabi iska, soson ma a ƙasan wurin ta barshi, tsawon awanni fiye da biyu.
A mugun fusace ta fito. Reina na nan tsaye a yanda ta barta jikinta na rawar tsoro. Ai kuwa ta kama hannun da take kare kanta dashi ta sauƙe sannan ta taƙarƙare ta kafa mata ranƙwashi ta riƙo kunnenta ta jawota dashi har gaban Bilal dake zaune a kan kujera yanzu, ta sakata yin kneel down.
Ta san duk hukuncin da zata yi mata ba zai yi rabin wanda zai yi mata ba.
Su Zahra tuni suka saluɓe jiki suka bar wurin kada ya ritsa da su.
Haka Hajiya Hauwa taci gaba da zayyano mishi laifukan ta ɗaya bayan ɗaya yanda zaiyi mata mummunan hukunci.
Da ya gaji da sauraron ta sai ya danna wa Maman Meesha kira, bugu biyu ta ɗaga ya ƙara wayan a kunne tare da yin shiru. Ganin haka ta miƙe zata bashi wuri taje ta ƙarasa wankin toilet ɗin da kanta, da tazo wucewa ta bayan Reina sai saka kafa ta hankaɗa ta ko zata rage haushi.
Hantsilawa tayi ta gaba, bata faɗa ko ina ba sai kan kafar Uncle B da ya ɗaura su daya bisa ɗaya ta riƙo ƙafar wandon shi tana maida numfashi.
"...Ameesha tana kusa?" Ya tambaya tare da ɗan motsa ƙafan, Reina tayi saurin sake shi ta gyara kneel ɗown ɗinta tare da ɗaga hannu sama ta rufe idanu, shikkenan yau ta mutu laifi bayan laifi.
"Gata nan" ta saka ma Meesha wayan kawai a kunne don idan tace shi ne ba zata karɓa ba.
"Mummy waye?" Yana ji ta tambaya kana ta ƙara wayar a kunnenta cikin sanyin murya ta furta "Hello?"
"Meesha, kin manta da Uncle ɗinki ko?" Yace yana kallon Reina dake ƙifi-ƙifi da ido saboda yunwar dake ƙwaƙular cikinta, ita ya bata abinci taci sai ta cigaba da kneeldown ɗin.
Da ace wani Uncle B ɗinne ba wannan ba da kashe wayan zata yi amma ta san bata ma isa ta fara ba, don haka tayi shiru kawai bata amsa shi ba hawaye na taruwa a idanun ta.
"Fushi kike yi dani?"
Sai kawai ta fashe masa da kuka, ita bata da abinda zatace masa.
"Kin san ba zanyi miki zaɓin abinda zai cutar dake ba ko? Ba zan bari wani cutarwa ya ƙaraso kusa dake ba ma Ameesha saboda ke tawa ce"
Cikin kukan da a yanzu yayi tsanani taja hanci kana tace "Ni taka ce Uncle B Amma alƙawarin da kayi min a kan Yaseer fah? Shekaru uku kenan Uncle B! He's been rotting in that hell hole for three good years!"
Lumshe ido yayi ya daga su daga kan Reina kana ya buɗe su. Damuwanta kenan? Ga babban lamari a gabanta ita ta wani Yaseer take yi?.
"Dan zo in same ki a gida gobe"
"Kada kazo, I don't want to see you"
"Ni ɗin Ameesha?"
Sai ta gagara cewa komai.
"Shikkenan, take care" ya katse kiran, zai barta da rashin kunyar ta ya fito mata da Yaseer ɗin.