← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 117

Sashe 39

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaseer, Saudat da sauran yaran suka sauƙa a gidan Alaji Abdou dake Niamey shikuma da Kamal suka wuce jinyar Alhaji Tahir.

Daga farko haka Yaseer ya dawo wani shiru yana wahala kafin kaji maganar shi, ga zaman ɗaki kamar mace sai ya wuni bayan zuwa masallaci babu abinda yake fito dashi abinci ma sai dai a kai mishi can, don ganin ƴan uwan shi yake yi kaman baƙi, duk sun canza mishi kaman yanda suma suke ganin ya canza musu, Musamman Irfan mai ƙananun shekaru har ya fara mantawa da shi.

A wannan gaɓar ne Aicha ta shigo rayuwar shi, tun tana mishi cusa kai ba kwarjini har a dole ya fara kulata. Idan suka zauna ta saka shi a gaba da surutu sai kaga yana murmushin shirmenta kawai, wani lokaci har ka ji sautin dariyar shi ko ka ji yana mata faɗa in tayi ba daidai ba, suma sauran sai suka fara maƙalewa a bayan ta, idan suna so yayi abu ko ana so ya fito daga ɗaki ya ɗan sha iska sai su tura ta.

Sai dai ciwon ɓarin kai da ya saka shi a gaba Saboda rashin barci ya saka Mariama ta kai shi asibiti a nan ne aka fara bashi sleeping pills kuma ya fara zuwa therapy sessions.

Sannu a hankali komai ya fara daidaita, Yaseer ya fara dawowa Yaseer ɗin shi na da, shaƙuwar shi da Aicha ya ƙara ƙarfi, ya ɗauke ta kaman ƴar uwar shi ta jini itama haka, domin bata da burin da ya wuce samun ɗan uwa namiji sai gashi ta samu a sama.

Zaman gida kullum shine abinda ya fara damun Yaseer, don ko a prison yanzu ya saba da aikin hannu da aikin ƙarfi, ya koyi sana'o'i da yawa a zaman shi na can. Don haka ya fara fita yana zazzagawa duk Abinda ya samu idan za'a biya shi zai yi, ya kuma dawo ya shiga gidan da kallo ɗaya zaka yi masa ka tabbatar masu ita sun fi ƙarfin bukatar yau da gobe har da wani shekara ko a jikin sa, tunda ba gidan su bane.

Ya wuce shekarun da ya kamata ace ya fara niman na kansa ya taimaki kanshi da iyayen shi, ganin kaman nashi arziƙin ba a jikin boko yake ba don haka ya ajiye tunanin shi a gefe, yana wannan fafutukar har Alaji Abdou da Kamal suka dawo ƙasar bayan wata biyu, sun zo wucewa suka hango shi a wani construction site yana ta ɗiban kankare.

Basu dakatar dashi ba suka wuce gida dukda hankalin Kamal ya tashi sosai Alaji Abdou ya taushe shi da halalin shi yake nima, kuma lokaci yayi da zai daina yiwa Yaseer ɗin kallon yaro, su bar shi yayi gwagwarmaya ya samo manufar shi a rayuwa ba sai lokaci ya gama ƙurewa ba.

Aka zo aka yi zama a kan maganar makarantar yara, Alaji Abdou ya siya ma Kamal gida a Maradi, a can Alhaji Tahir zai zauna dasu idan an sallamo shi daga asibiti yaci gaba da jinya saboda hankalin shi bai kwanta da barin shi a Niamey ba gudun kada watarana wanda ya san shi ya gan shi.

Saudat zata fara tafiya da sauran yaran saboda a saka su a makaranta shi kuma Yaseer sai ya zaɓi jami'ar da yake so a kowani ƙasa ne in Allah yaso za'a sama masa.

Sai ya gwada shi a lokacin ba karatu yake so ba, domin ƙwaƙwalwar shi ta cunkushe kuma babu ƙaunar karatun a zuciyar shi, aron jari yake buƙata wanda zai saka Ideas ɗin kasuwanci da yake dashi da na sauran matasan da basu da aikin yi into action.

Alaji Abdou ya gwada mishi wasu figures gashi yayi signing yayi komai zai bashi har tsawon lokacin da yaga zai iya maidowa babu kuɗin ruwa babu komai, ganin yawan kuɗin sai da ya saka kan shi juyawa, ya fara tunanin ta inda zai iya sarrafa wannan maƙudan kuɗade.

"Wani hanzari ba gudu ba, dukiyar Hafsatu ce ƴar Tahir, kuma amanar shi nake son danƙawa a hannun ka"

Shiruu Yaseer yayi yana kallon yawan kuɗin, yana da dalilin da zai amince kuma yana da ƙwaƙwƙwaran dalilin da zai ƙi amicewa, amma idan yaƙi amincewan waye ya cutu? Asarar waye? Hakan ya saka ya sanar ma Alaji Abdou ya amince.

Alaji Abdou Shi ya haɗa shi da ƙwararru da amintattu wanda zasu ɗaura shi a kan hanya ya Kafa YK & CO.
A yanda ya samu taken gatan matasa kuma komawa da yayi duk wani wuri da ya taɓa aikin gini ne, dako ne, da sauran su ya ɗebi matasan da suke fafutuka saboda rashin aikin yi ya kawo su YK aka basu aiki dai-dai da matakin karatun su ko kaifin basirar su.

Shekaru uku yana aiki tuƙuru a YK Alaji Abdou yayi ta kawo masa investors ganin ba zai bashi kunya ba, kuma duk mutanen da suka yi aiki da Yaseer sai sun yaba gaskiya da riƙon amanar shi.

Saida Alaji Abdou yaga YK ta zauna da ƙafarta sannan ya sake bijiro masa da maganan makaranta, shekarun shi ashirin da takwas ya kamata ace ko takardan degree ya riƙe nashi, hakan ya saka ya zaɓi zuwa China domin lokacin kasuwan shi yana ci sosai a can.

Course ɗin da ya shafi Business and entrepreneurship ya zaɓa kuma yana ƙara gogewa a kasuwa yana daɗa rage yawan rashin aikin yi a tsakanin matasa.

Shaƙuwar shi da Aicha ya ƙara yawa ya koma mata kallon ƙanwar shi da suka fito ciki ɗaya ita kuwa a nata ɓangaren tafiyar ta daɗe da sauya zani domin ginin soyayyar Yaseer da take yi a zuciyar ta har da bene.

Yana zama suyi hirar abinda bayi iyawa da iyayen shi ko sauran ƴan uwan shi saboda zai saka su a damuwa ko ya jawo musu ɓacin rai, yakan zauna ya bata labarin zaman prison tayi kukan tausayin shi kaman me.
A hakane ta san Reina da Kuma ƙaddarar da ta gifta a tsakaninsu, sai dai tun Yaseer bai fahimci mai yake ji game da ita ba Aicha ta fara zargin yana da nasaba da irin abinda take ji a kan shi.

A hankali kuma Alaji Abdou ya fara binciken yunkurin kisan Alhaji Tahir kuma suka fara tara shaidu, shima Yaseer ya saka ido a kan Jamal da duk wani motsi nashi, sai gashi cikin Sa'a wai ya shiga harƙar safarar ƙwayoyi, shi taimakon shi ma yayi.

Yana aji biyu a jami'a ya yanke shawarar kafa wani branch na YK & Co a Nigeria, a can ma irin recruitment da yayi a Niger shi yayi, bai bada vacancy ma masu ƙarfi da masu iyaye a gindin murhu ba sai ya zaɓi masu ƙaramin ƙarfi da kuma wa'inda irin ƙaddarar shi ya afka musu suka yi zaman kurkuku ba tare da wani laifi ba yanzu sun fito basu da madogara.

Ya ɗauki Muhammad abokin shi a matsayin P.A ɗin shi saboda bayi manta amanar da yayi mishi lokacin da kowa ya guje shi, da kuma baban Safina kawar Reina yanda zai samu kusanci da ita ba tare da sanin kowa ba.

Wayan da ya siya mata lokacin da tayi Candy shine abinda ya fara shiga tsakanin su, sai kuma ya biya mata kuɗin makaranta lokacin da zata shiga jami'a, ba tare da ya ankara ba kuma ya fara bibiyar ta, in dai yana Nigeria to rana ɗaɗɗaya ne zai fita bai biya ya ganta ba sai dai idan bata fito ba baki ɗaya.

Haka zai biya mata kuɗin abun hawa kuma yana bin su har su isa inda zata je.
A irin haka ta kusan kama shi a makaranta lokacin da zasu rubuta final exams na first semsester aji biyu.

Damuwan da ta shiga a kan tafiyar Uncle B ya saka shi zuwa yana dubata a kai a kai, suka tsaya a jikin motar da suka yi parking a hanyar venue ɗin lectures ɗin su yana kallon ta cikin baƙaƙen glasses ɗin da ya toshe fuskar sa ga facing cap duk don kada ta gane shi.

Ita da Safina da wata course mate ɗinsu suka zo wucewa amma ƙamshin turaren shi ya saka ta tsayawa yayin da shima nashi numfashin ya tsaya.

Ta taɓa jin ƙamshin nan a wani wuri.
Har kaman zata basar ta wuce sai kuma ta juyo ta fuskance su. Wani about turn da Yaseer yayi sai ji kake yi ramm.. ya buge goshin shi da karan hanci a garin ɓuya, ya kuwa rintse idanu cikin azaba yana laluɓen hannun ƙofar motar ya buɗe ya koma ciki.

"Kai... Kai ne?!"

Muryar ta ya saka shi dakatawa, zafin ma ya daina ji.

Yana shirin juyowa tunda an kama shi yaji Muhammad na dariyar ƙarfin hali da faɗin "eh wallahi, nine, kina lafiya?"

Ta gane shine wanda ya tsara mata adaidaita a ranar da Uncle B ya tafi.

"Daman a school ɗinnan kake?" Ta sake jefa mishi tambaya.

Sai laccin Yaseer yake yi da ƙafa amma firr yaƙi juyowa ya amsa da "eh.. Eh a nan nake"

"Ayyah amma ba student bane ko?"

Yayi saurin cewa "Non-academic staff ne"

"Allah Sarki, shiyasa ban taɓa ganin ka ba ashe. Na gode sosai da wancan Ranar"

Sai a lokacin su Safina suka gaishe shi, tayi masa sallama suka ƙara gaba suna tambayar ta kanun labarai.

"Matsoraci ta tafi"

Yaseer ya ɗago yabi bayanta da kallo.
Har yanzu tana nan da yawan tambaya.

~~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.
Chapter 39 · 0% Book details