← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 117

Sashe 25

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata rufe baki ba aka miƙo musu wasu jibga jibgan laidodi mai tambarin wurin a jiki. Hannayen su yayi amfani da shock ɗin da suke ciki ya karɓa musu, aka sake miƙa ma Reina kwalin cake ɗin da nauyin shi ya saka ta kusan sake shi a ƙasa.

"It's all from the gentleman" matar ta washe musu baki kafin su kai ga tambaya, ba zallan mamaki ba har tsoro yanzu ya rufe su. Gentleman ko crazy man? Wannan uban kaya ina zasu da shi?.

Reina ta ajiye duk kayan hannun ta a saman wurin ta buɗe cake ɗin tana kallo ya sha frosting na chocolate spread da cream cheese, ta haɗiyi miyau. Ita daga nan gidan Hajiya Hauwa zata koma, da wani baki zata yi mata bayani idan taje da wannan niƙi-niƙin kaya? Daman da ƙyar ta barta zuwa gidan su Safinan ma a yau don sai da mummynta ta kira ta roƙe ta kafin nan.

"Na hannun ta kawai ya ishe mu, kuyi kyauta da wannan ɗin" ta juya zata bar wurin, receptionist namijin ya sha gaban ta ya haɗa hannu yana roƙo.

"Ma'am please, idan baki tafi dashi ba zamu iya rasa aikin mu"

A garin roƙo Reina na tirjewa har aka yi abinda bata so ɗin ba, hankalin mutane ya fara dawowa kan su.

"Ta ina zan iya zuwa gida da wannan abun Feenah?!" Ta dubi Safina kaman zata yi kuka.

Safina tayi murmushin samo mafita, "Kin san me? Ba birthday kika zo ba dama?"

Reina ta gyaɗa kayi "wallahi ta ganni da wannan kayan sai tace satowa nayi, ko zan kwana ina rantsuwa kuma ba yarda zata yi ba"

Safina tace "ku rubuta Happy Birthday Safina a jiki sai ku raba gida biyu kuyi packaging"

Ma Reina kawai aka ce su bayar amma idan har zasu tafin da shi gwamma su raba musu.

Ta buɗe laidan Reina ta cire komai bibbiyu ta mayar cikin nata laidan, Aka kawo rabin cake ɗin ma kowannen su suka karɓa. "Idan sun tambaye ki sai kice kayan birthday ne aka raba Saboda nayi hosting small party, ni kuma zan raba sauran kayan ma almajirai saboda idan naje gida dashi da yawa haka nima za'a min faɗa sosai".

Shawarar yayi ma Reina, da haka suka bar restaurant ɗin Safina ta fara saka ta a napep ta biya kuɗin ta kama hanyar fadaman mada kirjin ta na bugun uku-uku.

......
*Yaseer*

Da isar su suka samu Aicha a gidan ita kadai Saboda Umma da Abbah sun je jama'are yin kwana biyu suyi musu sallama domin da sun dawo zasu wuce Niger daga can kuma Yaseer zai koma makaranta.

Itama bata daɗe da dawowa ba ta shiga kitchen samawa kanta abu mai sauƙi.

Oats ta haɗa ta zuba inabi, cashew nuts da madaran ruwa a ciki ta dawo parlour yanda Irfan da Sabir suka yi jingum-jingum ga tvn dake ɓaɓatun banza.

"Bro"

Sabir ya juyo ya dube ta "Darling ina wuni, yaya aiki"

"Lafiya lau, ina Yayan mu? Ya fara shirin tafiya kuwa?"

"Ban sani ba, yana ɗakin shi ki duba shi" yayi mata nuni da hanyar ɗakin don bayi son dogon surutu.

"Lafiya kuwa? Wani abu ne ya faru? Yaya fa?"

Ƙaramin tsakin takaici ne ya suɓuce ma Sabir. "Babu komai, shima Yayan yana ɗakin shi ki duba shi"

Bata yarda ba amma ta rabu da shi, ɓacin ran da yake ciki a bayyane yake, shi da duk gidan Yaseer kawai yafi shi rashin matsala amma yau harda su tsaki.

"Darling kin san da wa muka haɗu yau? Har yaya da yayanmu suka yi faɗa a kan ta?"

Haka kawai taji gaban ta ya yanke ya faɗi, taƙi jinin taji an ambaci wata mace an danganta ta da Yaseer.

"Irfan!" Sabir yayi mishi ido. Sun san sai ya faɗa mata shiyasa suka gargaɗe shi tun a mota.

Yanda sunan Hafsatu balle Reina ya zamo haramtacciyar kalma a gidan haka zasu cigaba, abinda suka shaida a yau bai isa ya canza komai ba.

"Auta faɗa min, ba zai maka komai ba" Aicha ta tambaya ta samu zuciyar ta ya rage lugude ko ya ƙara.

"Kin san Reina?"

Tushsh... Ta saki bowl ɗin hannun ta a kasan wurin.

"Irfan!!" Yaseer ya kira cikin ƙaraji dukkan su suka ɗaga ido suka dube shi.

......

"Shine ko gayyata na baki yi ba ko Reina?" Zaheera ta kwaɓe fuska tana kallon kayan da aka baje a wurin Hajiya Hauwa tana musu raba dai-dai harda ita kanta, zata iya cewa karo na farko kenan da aka kusa yin rabon adalci a kan wani abu a gidan, saboda ita ta kawo.

~~~~~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

59

~~~~~~~~~~
_But they could say the same bout me_
_I sleep bout 3 hours each night_
_means only 21 a week now_
~~~~~~~~~~~

"Ai ba ni bace mai gayya Safina ce, kuma naga ba shiri kuke yi ba" Reina ta mayar mata domin mitar Zaheera ya fara damun ta.

"Amma dai idan kin tafi da ƴar uwan ki laifi ne? Ko akwai wanda zai ce meyasa? Itama ba haka naga take zuwa dake ba? Dake kin yi gadon baƙin hali?!" Hajiya Hauwa ta dungura mata containern da aka cire spring rolls da aka saka mata nata kason a ciki.

Kallon shi tayi rabin samosa, rabin spring rolls, rabin meat pie, filled donut da glazed donut duk rabi-rabi kuma an kwashe ɗan kayan daɗin dake jiki, sai abinda yafi damun ta cake ɗin da aka gutsura mata kaman ta roƙa, duk girman shin nan, akwai milk cake ma da Zahra ta ɗauka ta gudu da shi ɗakin ta kuma ya tafi kenan.

Rau-rau tayi da idanu don abun yayi mata zafi tace "ku ƙara mun cake ɗin dan Allah."

Hajiya Hauwa ta kalle ta sheƙeƙe "Hafsatu! Dan yau kawai zamu ci arziƙin ki? Nace dai shekaru ɗaɗɗaya har shida mu ke ciyar da ke..."

"Wallahi Idan baki ƙara min ba zan faɗa ma Uncle Bilal" a kan cake ɗin nan dai yau ba haƙura zata yi ba.

"Iye!" Hajiya Hauwa ta riƙe baki kawai al'ajabi ya daskarar da ita.

Cake ɗin Zaheera da yayi girman nata biyu ta miƙo mata. "Karɓa wannan ni bani ci, I'm on a diet"

Ko kallon ta bata yi ba idanun ta na kan Hajiya Hauwa ta kafe ta da su, halan sun manta wacece Reina ne, amma yanzu da take da madafa idan matar nan bata kama kanta ba ta kusa fara mata rashin kunya.

"Sai ki ɗauka duka ai mara ta ido" Hajiya Hauwa taso naɗe tabarmar kunya da hauka Amma da mamakin ta sai ganin Reina suka yi ta miƙe ta sunkuci kwalin sauran cake ɗin ta kuma haɗa da wanda suka bata da gutsurarrun abubuwan ta wuce ɗakin ta da su, tana jin tafin hannuwan Hajiya Hauwa da salatin da take nanatawa.

Haka taci kayan ta Lafiya tana bawa Uncle B labarin yanda suka yi, dariya kaman cikin shi zai yi ciwo. "That's my Doll" yace cikin jin daɗin abinda tayin "duk wanda yace cutan ki zai yi ki barni dashi kawai, zan yi miki maganin shi"

Bata dai sanar da shi kan cewa wani ne ya siya musu cake ɗin ba, shima ta bar shi a kan na birthday ɗin Zaheera ne.

"Baka ga yanda taji tsoro ba da na kira sunan ka, yanda tace 'Iye' ɗin har nima ta kusa tsorata ni amma na dake"

Ya sake darawa sosai yace "I love you my Doll, komai naki daban ne"

Kunyan mayar masa ya saka ta kifuwa a kan gadon ta birne fuskar ta cikin katifa farin ciki na niman halaka ta.

"Ba zaki ce mun I love you too ba ko?" Muryar shi mai sanyi ta shiga kunnen ta.

Buɗe baki tayi zata gwada amma kunya yaci karfin ta.

"Shikkenan, gobe jirgin mu zai tashi da safe. Zan tafi da raunin zuciyan rashin sanin matsayi na a zuciyar masoyiya ta..."

Rintse idanun ta gamm tayi kafin ta fisgo kalmomin "I love You too Uncle Bilal!"

Ta jiyo sautin murmushin shi. "Doll Allah ya dawo da ni gareki"

"Ameen, cikin lafiya da aminci" ta amsa.

....

Kallon Yaseer duk suka juyo suka yi.

Sakwan 1, 2, Aicha ta fasa Ihu, tare da zamewa daga kujerar ta zuba a ƙasa.

Da sassarfa Yaseer ya ƙaraso gareta, tare da sauran suka rufu a kanta suna tambayar ta ko lafiya, amma ganin yanda ta riƙe ƙafa ga oats ɗin da ya zuba mata ya saka Yaseer saurin kamo ƙafar ya zame safar jiki.

"Maihaƙuri ban ƙanƙara"

Irfan har ya riga shi tashi ya ɓallo goran ruwan da ya daskare a cikin freezer ya kawo.
Kanƙaran ya manna mata ta saki ƙara tana niman ƙwace kafan amma bata isa karawa da riƙon da yayi mata ba.

Sai ga hawaye zirr na bin idanun ta.

Ta san Reina ake tambayar ta? Ita kuwa ta san Reina.

'Yarinyar da ta lalata min rayuwa, ta wargaza min farin ciki, ta shafa min kashin kaji, ta mayar da zuciyar dake bugu a ƙirji na ya koma dutse, ta ɗaiɗaita mafarkaina, ta saka ni kukan zuci.

Amma kuma numfashin da na tsira da shi bai taɓa manta sunan ta ba daidai da daƙiƙa ɗaya, Hankalin da nayi yaƙin dawowar shi gareni bai mance kamannin ta ba tsawon shekaru... Itace Hafsatu Reina'

Kalaman Yaseer ɗinta kenan lokacin da ta tambaye shi wacece Reina, lokacin soyayyar shi tana jaririya a cikin zuciyar ta.
Rana kenan da ta fara sanin menene tashin hankalin dake hana barci da daddare.

Soyayyar shi na ƙara girma yana mamaye ta tana daɗa rasa nutsuwar ta game da kasancewar Reina, ga alaƙa na zumunci da ƙaddara da ya haɗa su babu yanda ta iya.

Saboda ta samu nutsuwa ta matsa ma daddynta ya kawo ta taga Reina, taga da me ta fi ta, amma ganin babu wani abu da take dashi na musamman sai ma ta daɗa susucewa.

"Sannu Darling" Irfan ya dawo da ita cikin nutsuwar ta kaman zai zubar mata da ƙolla.

"Yayan mu Please!" Tace hawayen ta na daɗa gudu.
Chapter 25 · 0% Book details