← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 117

Sashe 97

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta juya wurin Safnah dake tsaye a gefe.

"Yaya baku kawo mata ruwa ba Safnah, haba ku kuwa kun kyauta ma Rafeek kenan?!" Jadda ta tambaya cikin faɗa-faɗa sai Safnah kawai ta juya dukda ta san Asal zata yi Abinda ya dace.

Daɗin ambatan sunan wanda tazo domin shi Aicha taji don har ta fara tunanin yanda zata shiga yiwa Jadda bayanin ɓatan kai tayi ba wurinta ta zo ba.

Glass tray suka dire a gabanta har guda biyu sannan ƴammatan suka shiga tsiyaya mata lemu da ruwa a cup, yarinyar kuwa ta dawo jikinta ta shige sai wangale mata giɓin bakinta take yi.

"Jadda an gama shirya teburin." Cewar ɗaya daga cikin masu aikin sannan ta juya tayi tafiyar ta.

"Yauwa sha sai muje ki karya ƴar nan, daga ganin ki babu komai a cikin ki."

Ita yanda suka tsareta da idanuwa ma ta ina zata iya karyawa?.
"Umm.. Jadda, Mr Rafeeq ɗin ya yarda zai gana da ni?"

"Dolen shi ma!" Jadda ta amsa, sannan ta dubi ɗaya daga cikin ƴammatan tace "kaita ɓangaren Uncle ɗin ku saima ta karya a can"

Ta waro ido, a cikin kanta tana faɗin lallai wa'innan sun kwankwaɗi madarar boko.

Tsugul yarinya mai giɓin nan ta miƙe. "Jadda zan kaita Please"

"A'a, baki zuwa ki dame shi da safiyar nan ya ƙare wunin shi yana mana kurmanci da shan ƙamshi"

Aicha ta taɓe baki, ashe abun shin har gida.

Ta miƙe zata bi bayan ƴammatan da taga ta fara tafiya sai jadda ta kirata ta juyo.

"Idan ta fito zaku shiga da ita gidan Mamman ku da na Mamman Asif, sai kuje ku kaita gidan Ali Omar ta gaida Nooriyya da Kalimullahi, ina Hidaya ma? Hidaya ƴar albarka dole na haɗa ku ƙawance" ta ƙarashe tana riƙo hannun Aicha da take kokwanton lafiyan Jadda kada cutan mantuwa da kuma ruɗu suka fara kama ta. (Makarantan My Lifeline da Tangled Hearts na san kun riga da kun fahimci wani family ne wannan😉)

Haka dai ta bi ƴammatan nan har part ɗin da suka samu babban parlon babu kowa shiru kaman ma ba a cikin gidan yake ba. Sai taga sun cigaba da shiga har wani ƙaramin parlo dake haɗe da corridor da zaka iya ganin ƙofofin ɗakuna daga wurin sannan ta bata wuri ta zauna tace bari ta je ta dawo. Aicha kuma sai ta yarda zata dawo ɗin tunda sai ta zo ta sanar da shi yana da baƙuwa.

Shiru-shiru minti 10, 15, 20. Tana zaune babu shi babu ƴar aike.

Sai ga kiran Yaseer ya shigo wayanta kuma ta san tambayar ta zai yi ko ta samu ta gana da shi, haka bata so ba tayi picking tunda ba iya share kiran zata yi ba.

"Yayanmu ina kwana" ta gaida shi.

"Lafiya, kin samu ganin shi kin bashi haƙuri?"

"To gani nan dai ina zaman jiran bayyanar Mahadi" tace lokacin da taji ƙaran rufewar ƙofa sannan ƙamshin turaren da take da tabbacin nashi ne ya shiga hancin ta.

Ya ilahal alameen, ita kam dai ita kam dai!.

Saurin katse kiran tayi ba tare da tayi sallama ma Yaseer ba ta miƙe tsugul tana ɗaura fararen idanunta a cikin nashi.

"Sir ina kwana" ta gaida shi da hausa cikin rawan murya dan kunyan yin faransanci take ji a gaban shi.

Wuce ta yayi ya ɗauki hanyar barin parlon yana cewa "wato ke ba zaki iya zama shiru a wuri ba kuma sai kin zage ni"

Da sauri tabi bayan shi ta shiga roƙon shi. "Sir I'm very sorry it was a mistake, I swear didn't mean anything I said"

Birkin da ya ja tare da juyowa lokaci ɗaya ba tare da tayi tsammanin zai tsaya ɗin ba ya saka sauran kaɗan tayi tuntuɓe da ƙafarta ta faɗa jikin shi.

"Mistake shine har sau biyu? Kuskuren da aka maimata shi ba kuskure bane, ganganci ne"

~~~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

107

Shiru tayi ba don ta rasa abin faɗa ba sai don yanda ya tsare ta da idanuwa. "Oya ki kare kan ki, ko har surutun ya ƙare ne?" Yace yana sakin ƙaramin murmushi sannan ya juya ya cigaba da takawa a hankali itama taci gaba da bin sawun shi a sannu.

"Sir I promise ba zaka yi nadaman sake tunani ba, sannan duk wani asara da kake tunanin za'a iya samu zamu ɗauki responsibility ɗari bisa ɗari"

"Oh nine ma nake tunanin asaran?" Yace yana sake juyowa.

Ta shiga girgiza kai da hannu da sauri a dalilin haka gyalen kafaɗan ta ya zame ya faɗi a ƙasa. Tayi saurin durƙusawa ta ɗauka, a tunaninta kafin ta miƙe zata ga ya sake juyawa har yayi mata nisa amma dago kai da zata yi taga Idanun shi a kanta.

Ta ɗan haɗe fuska tana fara kare ƙirjinta da mayafin kana ta zaga da shi ta rufe bayanta, sannan ta miƙe idanunta a kan wani farin decoration table daga gefen mashigar karamin parlon a ƙoƙarinta na kada idanunta su sake shiga cikin nashi "ba abinda nake nufi ba kenan."

"Okay then, explain me kike nufi" yace yana juyawa ya fita zuwa babban parlon don ya bata damar sake buɗe bakinta taci gaba da magana, domin a tsakanin sauraron muryarta da kuma kallon fuskarta bai san wanne ya fi so ba. Maganan kowa Hayaniya yake jin shi amma banda nata.

Kallon yanda suke tafe kaman ba zasu je ba ya saka a cikin zuciyar ta tace "yau kuma ina sandar Ikon?" Hala idan yana dogarawa da ita zai fi sauri.

Amma sai jiyo muryar shi tayi yana faɗin "sanda bata da amfani a cikin gida tunda ba ƙoƙarin ɓoye wa family na halin da nake ciki nake yi ba, sannan ba na iko bane rauni naji a ƙafa"

A fili kenan tayi magana? Lallai idan tarayyar su babu alkhairi zata haƙura su lallaɓa su samu wasu a madadin shi kokuma tayi switch off ɗin ƙwaƙwalwar ta da dage sai taga bayanta ta tona ƙasa ta bisine ta kafin su rabu da mutumin nan.

Tayi ɗan murmushin yaƙe duk da a yanzu bai juyo ba cikin muryar alhini tace. "Ayyah Allah ya sawaƙe, garin yaya?" Sai yanzu ta lura da ɗan ɗingishin da yake yi Amma yanayin tafiyar tashi ya saka ko ba sandar idan ba ka ƙura ma ƙafar shi idanu ba ba zaka gani ba.

Sosai yaji daɗin da ta tambaya, koda ace ita politeness na business ne kawai a ɓangaren ta "Gardama doki yayi min last week"

"Doki kuma? In this day and age Wa ke hawa doki?"

"Ƴan gidan sarauta.."

Tayi saurin amsawa da "no wonder. Ƙasaitar a jini yake"

Ya ƙara da "... Sabbin angwaye, ƴan wasan tseren doki da ƙwallon doki"

"Oh haka Ashe, na manta according to statistics na duniya maza sun fi mata ƙokarin halaka kan su ta hanyar ganganci"

Murmushi yayi mai sauti yana jan kujeran jikin dining guda ɗaya ya zauna tukunna ya ɗago ya dube ta. "Wai me ma ya kawo ki?"

Lallai kam mai ya kawota ta ɓige da shiga uku. Gyaran murya tayi ta gyara tsayuwar ta "Firstly I'm terribly sorry sir, abinda kaji na faɗa ba daga zuciya na ya fito ba, kuma ina niman afuwan ka if I hurt your feelings"

"Abinda ya kawo ki kenan?"

Saurin ƙarasawa ta amshi warmer da yake ƙokarin buɗewa tayi ta buɗe mishi, ta ɗauki serving spoon da bowl ta zuba mishi farfesun kifi da yake ciki ta ajiye a gaban shi tana ɗan murmushin da bai kai zuci ba, kana ta dauki plate ta buɗe warmer na gaba.
"Secondly Idan ka fasa janye investment ɗin ku zamu ƙara 5% a profit ɗin ku" ta tura plate din gaban shi bayan ta gama haɗa komai zuciyar ta na luguden jiran jin amsar shi.

Shiru ya ɗan yi idanun shi a kan abincin da ta gabatar mishi bakin shi na motsi, babu counter a hannun shi don haka da gaɓoɓin yatsun shi yake amfani.

"Zamu kai shi 7%" ita tace ma Yaseer ba sai sun ƙara musu komai ba amma gashi har ta yi mishi tayin percentage ɗin da ta hana Yaseer ɗin ƙarawa.

Har yanzu bai tanka ba, ya saka cokali ya ɗibo romon kifin da take jin ƙamshin sa yana dukan hancin ta daga yanda take tsaye amma ta jingina hakan da yunwar da ta fara ji Saboda lokacin karyawar ta yayi.

"What about 7.5% sir?"

Sai ya ɗan murmusa yana kai cokalin bakin shi.

Ganin haka sai ta sare, cikin muryar da babu karsashi tace "8% is the highest we can go, shima gaban kaina nayi tunda ni na ɓata maka"

"Amma kin san it's impolite ki tsaya ma mutum a kai yana cin abinci" yace yana tsiyaya ruwa a glass cup, shi kam bata hana shi ba domin ya kai maƙura wurin ƙunsa mata takaici.

"Idan ka bani amsa zan tafi"

"Zauna" yace yana nuna mata kujeran dake kallon nashi.

Bata yi ƙasa a guiwa ba tayi saurin daga jakarta da ta ajiye a kujeran lokacin da zata zuba mishi abinci ta mayar na gefen shi kana ta jawo ta zauna.

Plate da bowl ɗin da ta zuba masa abinci ya maida gaban ta harda kofin ruwan da ya fara sha, ya shiga saka ma kan shi wani. Bai ce komai ba har saida ya gama sannan ya ɗago ya dube ta.

"Ina da sharaɗi, idan kin amince we can do 5%"

Cike da zumuɗi tace "faɗi muji, zamu kiyaye in sha Allah"

"No ba sai kun yi mun taron dangi ba, ke kaɗai ma zaki iya, tunda ke kika ɓata min" ya mayar mata da zancen ta.

Sai ta fakaici idanun shi ta yatsina baki. samm namiji mai riƙo bai yi ba, gashi kaman wani babban mutum amma ba hali.

Tayi saurin kai hannun ta baki kada yanzu ma a bayyane tayi magana.

"Kin zage ni a zuciyan ki ko?" Ya tambaya ganin yanayin ta.

Sai ta sauƙe hannun da sauri tana girgiza kai, ta yi saurin kai farfesun kifin bakin ta tana hamdala a cikin zuciyar ta da bai ji ba.

Shi kuwa daɗi yaji ganin cokalin da yayi amfani da shi ta saka a bakin ta.
Chapter 97 · 0% Book details