← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 117

Sashe 41

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai tsaya sauraron ta ba ya ƙaraso ya riƙo ƙasan hajibin ta dole ta biyo shi a baya idanun su Aicha suka musu rakiya.
.
.
Amsa waya yake tun da suka ɗauki hanya, ta mayar da nata hankalin a kan hanya da take ganin garin yayi mata daban, ko dan tana kallon shi a mahanga ta daban ne a yau din?.
Yau ba saurin ta koma ta kama aiki take yi ba, ko taraddadin komawa ta haɗu da bala'in Hajiya Hauwa, babu wani tunani a kanta shiyasa take ƙarewa wa gidaje, motoci da mutane kallo.

"Kina jina?"

Juyowa tayi ta dube shi "Na'am"

Idanun shi a kan hanya kaman ba da ita yake magana ba yace "nace yaushe zaku fara exams?"

"Ba'a cire time table ba amma sauran wata ɗaya a calendar"

"Shine kuma kike zaman ki a gida har na sati biyu ko?"

Zura mishi idanu tayi bata ce komai ba tunawa da bala'in da ta shiga a sati biyun ina take tunanin wani makaranta? Da yau fa shikkenan za'a rakata ɗakin Jamal?! Kai Allah ya sawwaƙe mugun tunani ma. Ta girgiza kai kaman zata jijjige tunanin ne daga kanta ta hakan.

"Bani da lafiya ne shiyasa" ta sauƙe murya tana murza zoben Aunty dake hannunta.

"Ko dai baki son karatu ba? Nikuma gashi bani shiri da mai ƙin karatu"

Tayi saurin cewa "wallahi ina so"

"Zamu gani ai, idan na lura wasa ne a ran ki ni da kaina zan maida ke inda aka ɗauko ki"

"Gidan Umman Zahra?!" Ta tambaya tana mai dafe ƙirji.

"Koma Waye ne ke kika sani, can ɗin zan maida ki"

Zata fara rantse-rantse ya ɗaga mata hannu. "Ki saurare ni da kyau"

Haɗiye maganar ta tayi tana kallon shi idanun ta wuri-wuri.
"Idan kika bari naji kin yi ma wani rashin kunya, zaki koma inda kika fito. naji kin yi sa'insa da wani ko faɗa bare dambe kaman yanda kika saba innalillahi" da babban yatsar shi yayi mata nuni da baya, bayan ya dunƙule sauran yatsun shi huɗu alamun zata koma inda ta fito.
"Haka idan na lura kina wasa da karatun ki ko kika bari iyayen mu suka koka dake Hafsatu Reina you'll go back to where you came from!."

Ba ɗazu ya gama cewa bai san ta ba? Ita da akewa faɗa murmushi ne ya suɓuce mata.

"Oh dariya ma na baki?" sai a lokacin ya juya ya fuskance ta fuska a tamke.
Da sauri ta haɗiye murmushin tana girgiza kai "A'a naji zan kiyaye in sha Allah"

"Better for you" yace yana kutsa hancin motan cikin gidan da aka wangale masa gate.

Sai da yayi parking yace "fita min a mota"

Ta ɓalle marfin motan ta fita da sauri shima ya fito. Har ta saka kai zata yi gaba yace "waye yaron ki da zai biyo ki da kayan?"

Juyowa tayi ta dawo yanda ya buɗe Booth ya fara ɗauko laidojin kayan yana jibga mata har saida tsayin jeren ya fara rushewa kafin yace taje ta ajiye ta dawo ta ɗebi sauran, ya bar mata booth ɗin a buɗe yayi gaba abin shi.

A daidai entrance na gidan ya ci karo da wata yarinya dake fitowa da gudu, har tayi baya zata faɗi ya riƙo ta. Murmushi yarinyan tayi ganin shine tace "Uncle oyoyo" tana mai rungume shi.

Ɗaukan ta yayi a hannun shi yana jan kumatun ta. "Meesha 2 ina Meesha 1?"

Da ƴar yatsarta ta gwada cikin gidan tana masa surutu da turanci, sai ya wuce ciki ɗauke da ita Reina ta bishi da kallo ya iya ɗaukan yarinya amma ba zai iya taya ta ɗaukan kaya ba.

Tana tangal-tangal ta taka matakalar mashigar sai ji ta yi tayi karo da ƙofa, Lallai ma yaya Yaseer! Jan ƙofar kenan yayi ya rufe bayan ya ganta biye dashi ga niƙi-niƙin kaya?.

Saida ta zube kayan tass a ƙasa sannan ta murza handle ɗin ƙofar ya buɗe ta sake kinkiman wanda zata iya sauran sai ta je ta dawo, ta shiga da sallama.

Yaseer ne zaune a kujeran mutum ɗaya, annurin da bata gani a fuskar shi ba tun haɗuwar su shine yanzu a wadace, yana kallon wata kyakkyawar bafulatana fara sol dake zaune tare da Umman shi a kujera ɗaya ta tankwashe kafafun ta tana ta surutu, sai kuma Umman na riƙe da jariri a hannun ta.

Ƙarasawa wurin su Reina tayi ta rage tsayi tayi ma Umma sannu da gida sannan ta gaida baƙuwar fuskar.

"Lafiya lau" baƙuwar ta amsa tana murmushi. "Umman mu kin yi ƴammata ne?"

Gyaɗa kai Saudat tayi tana ɗan taɓe baki. Yaseer ya jijjiga kai sanin tabbas Meesha bata gane waye bane da ko kallon arziƙi Reina ba zata samu ba.

"Ke kin fara tara yara ma Amma ba zaki bar gulma ba ko? Kuma har doctor ya barki kika fito da ɗanyen jego yaro less than 40 days. Koma satan hanya kika yi nikam?"

Gaba Reina tayi ta nufi stairs da kayan hannunta, zuwa yanzu ita kam ta gane Meesha , ta gane itace ƴar uwan umman Zahra da take zuwa lokacin da yaya Yaseer yake musu lesson, kuma ta tuna ganin da tayi mata na ƙarshe lokacin rasuwar Aunty tun daga ranar bata sake zuwa gidan Umman Zahran ba a iya saninta.

tana jiyo Meesha ta amsa da. "Sauran 2 days ne fa mu cika 40 days ɗin ina wani bambanci? Ni tun jiya ma da labari ya iske ni naso zuwa na dai haƙura da ƙyar zuwa yau ɗin. ga ni ka shafa min inji yanda abu ta kasance, Amma na so da sai bayan anyi auren wallahi kuka je, ai zamu je ne ya gamu da muje mu, ni dai sun dace mun da juna"

A maimakon Yaseer ya tanka sai ya sauya akalar zancen yana gwada yarinyar ta dake wasa da hannun shi yace "kin ƙi koya ma yarinyar nan Hausa ko tsaban iyayi"

"Yarinyar doctor ce fa! Barmu zata koyi Hausa a society a bakin irin ku..." Kirif Reina ta rufo ƙofar ɗakin bayan ta shige, tana saka ma ranta ba zata koma ɗebo sauran kayan nan ba sai Meesha ta tafi ko idan sun tashi a parlorn.

~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

71

~~~~~~~~~
_On était tellement complices_
_(We were great partners)_
_On a brisé nos complexes_
_(we overcame our flaws)_
~~~~~~~~~~

Shiryawa tayi a cikin ɗaya daga cikin dogayen rigunan da suka siya jiya, ta naɗa gyale 2 in 1 kalan da ya dace da kayan ga sabon takalmi da side bag sai ta jita daban cikin annashuwa da farin ciki ta fito cikakkiyar mutum, sabon kaya akwai daɗi.

Da ƙarasawar ta dining ta samu har kowa ya fara cin abinci don haka ta shiga gaishe su ɗaya bayan ɗaya, Suhail ganin tazo kan shi yayi saurin tura doya bakin shi saboda kada a tilasta shi ya amsa, irfan ma ba don ya so ba ya gaida ta.

Tsantsar soyayya da farin ciki take gani a idanun mahaifin ta, yanzu kam ta tabbatar a zahiri ne farin cikin ta ya dawo gareta ba mafarki ba tunda ta sake farkawa ta saka shi a idanun ta.

A yau tsarin zaman an bar mata ne ta ɓangaren dama maza ta ɓangaren hagu. Abbah ne a head table kaman ko yaushe, gefen shi na hagu Sabir ne sai Alhaji Tahir, Irfan,Suhail sai Yaseer ya samu kansa a head table ta ɗaya ɓangaren yana fuskantar Abbah. gefen shi Aicha ne of course sai Maama sai space da aka bar mata kafin Umma dake zaune a gefen mijinta.

Sai da ta zuba abincin ta kafin ta zauna ta fara ci a tsanake. Ƙoƙari take yi ta saki jiki dasu tunda alamu sun nuna zaman ta a gidan ba na ƙanƙanin lokaci bane, don haka zata nemi yafiyan su a aikace da kalaman baki a lokacin da ya dace kuma zata jira har sanda suka ga daman yafe mata.

Cikin shiru suka ƙarasa cin abincin, ko Aicha tsoron ta ɗauko taɗi Yaseer ya sake gwale ta a gaban jama'a take yi, don haka saida ta jira ya gama sannan suka miƙe a tare ta karɓi plate ɗin shi ta haɗa da nata zata kai kitchen yayi mata godiya.

"Ki jira ni in zo kafin ki wuce" cewar Yaseer.

Reina ta nuna kanta ganin ita yake kallo "Ni?" Ta tambaya cikin shakku.

Yaso ya mayar mata da ba'a Amma yaji nauyin idanun mahaifin ta sai yace "Eh ke, abu zan baki"

Ya juya zuwa ɗakin shi tayi mishi rakiyan idanu har ya ƙule ciki, ita yanzu menene ba'a bata ba da za'a ƙara mata? Miƙewa tayi ta ɗauki abinda ta ɓata tayi da shi kitchen kaman yanda taga kowa yana yi.

Aicha ne a gaban sink tana ɗauraye kwanukan, jin nauyin taje ta ajiye mata Reina ta miƙa hannu zata karbi soson "kawo na ƙarasa"

Cigaba da abinda take yi tayi ko kallo Reina bata isheta ba har saida ta sake maimaita tayin ta kafin Aicha ta dubeta.

"Kada ki damu zan iya, kin san kowa da matsayin shi a gidan nan ba sai kin wahalar da kanki kin cike gurbin wani ba, har nakin ma duk zamu iya wankewa" ta ƙarasa tana sakin ƴar dariyar da bai kai zuci ba yanda zai hana Reina nazarin kalamanta.

Taso ta juya kawai ta bar kitchen ɗin ba tare da tace komai ba amma tayi tunanin toh Idan tayi ma Yaseer da ƴan uwan shi laifi ita Aicha nata a wanne?.

"Nikam dan Allah nayi miki wani laifi ne ban sani ba ki faɗa min in baki haƙuri?"

Aicha ta cire gloves ɗin wanke-wanken dake hannunta sannan ta juyo ta dubi Reina.

"Wannan kuma kanki zaki tambaya zaki fi samun amsa. But I can see through you, tarr nake kallon ki in faɗa miki"

Ta jinjina kai domin sai yanzu ta fahimci inda ta dosa, ta rabu da Zaheera a can ne ta sake haɗuwa da wata Zaheeran a nan. Har ta fara ganin girman Aicha amma ƙyashi ya saka lokaci ɗaya ya zube.
"Ki sani ba ƙoƙarin cike gurbin wani nake yi ba, Musamman ma naki, babu Abinda ya haɗa ni dake"
Chapter 41 · 0% Book details