Sashe 2
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin Sa'a wayar alhaji kalabu ya shiga ruri. Ɗan shi ne na biyu yake kira amma sai yayi saurin miƙewa tare da amsa kiran ya kara a kunne yana faɗin "Barka dai yallabai"
har da wani duƙar da kai cikin girmamawa sannan ya saluɓe jiki ya bar parlourn. Ya rage sauran su uku, Hajiya Jummai da Alhaji Salisu sai kuma Reina. Hajiya Farida daman ko zuwa bata yi ba, ta kashe wayoyinta ta yanke duk wani hanyar samun ta don bata son damuwa, idan ma tazo sai dai tayi ta musu dariya kawai.
Ganin ɗaya bayan ɗaya suna barin Babban parlorn yasa Hajiya Hauwa shigowa a tunanin ta sun gama zaman nasu ne.
Kallon Hajiya Jummai tayi, dake shirin guduwa itama tana faɗin.
"Kaga Salisu dangin miji na ba mutunci garesu ba daman, kuɗin da nake taƙama da shi ina jerawa dasu ma kaga yanzu ba sosai ba. Idan na tafi da yarinyar nan daga ni har ita wallahi zaman ba daɗi zai yi mata ba, so kai ɗin dai ka kai zuciya nesa domin mai iyawa da yarinyar nan sai Allah"
Ya buɗe baki zai musa, har da saka hannu zai janyo mayafinta ta dawo Hajiya Hauwa ta katse shi da "babu matsala, zata zauna a nan ɗin, ai ɗa na kowa ne"
Kallon mamaki ya bita da shi ta girgiza mishi kai kar ya musa, har saida ta ɗan taka ma Hajiya Jummai ita kuwa sai godiya take zuba mata domin riƙe Reina jihadi ne, kafin ta dawo cikin parlorn.
"Kije ɗakin Zaheera ki huta kafin a shirya miki ɓangaren ki" tace da Reina a ƙagauce, amma dake bata tare da nutsuwar ta sai ta mayar mata da tambayar "iye?"
A hasale Hajiya Hauwa ta maimaita kafin Reina ta fahimta, ta miƙe cikin sanyin jikin da ba yanayin ta bane a da kwata-kwata. Tana tafiyan kaman ana tura ta har sai da ta bar ɗakin baki ɗaya kafin Hajiya Hauwa ta dubi Alhaji Salisu.
"Wato da bari zakayi su ɗauke ta? Idan taje tayi suɓutar baki ta bankaɗa mana sirri fa kaman yanda ta faɗa ma Tahir! Ka san har yanzu zancen nan ba wai mutuwa yayi ba ko? Kuma koda babu wanda zai iya ɗaukan wani mataki a yanzu amma zata ɓata maka suna "
Tunanin hakan bai zo mishi ba kwata-kwata, tabbas idan Reina ta sanar ma ƴan uwan shi gaskiyar abinda ya faru bayan duk ƙokarin da suka yi wajen ganin sun birne shi sun aza babban dutse a kai, to duk wahalar shi na shekaru zai tashi a banza, kuma ƙaddarar shi zai iya ƙarewa kaman na Tahir ɗin, ya wayi gari bayi da komai sai tarin bashi.
........
ganin Yaseer yana shigowa Kamal ya miƙe da ɗan murmushin yaƙe a kan fuskar shi.
"Yayan mu" ya miƙa mishi hannu yana faɗaɗa murmushin shi zuwa na ganin ɗan nashi tare da shi a inuwa ɗaya.
Shima Yaseer ɗin miƙa mishi hannu yayi suka yi musabiha, fuska ba yabo ba fallasa ya gaida shi "Ina wuni Abbah, ka zo lafiya"
Zama suka yi a koɗaɗɗun bencinan suna fuskantar juna kana Kamal ya amsa da "Lafiya alhamdulillah. Kana cikin ƙoshin lafiya dai Yaseer" don tafiya lokaci ya tafi amma yana ganin kaman har yanzu Yaseer ɗin bai saba da zaman wurin ba, ko dayake ba wuri ne da za'a saba ba, ba'a taɓa sabo da wahala don haka tambayar shi a kan hanya yake.
Gyaɗa kai kawai Yaseer yayi Saboda a yanzun kalaman bakin sa a ƙayyade suka, ƙur'ani ne kawai take samun damar fitowa cikin sauƙi ba tare da abinda ke tokare da maƙoshin sa tsawon shekaru uku na ƙoƙarin maƙure shi har ƙarshe ba.
"Yaya umm.."
"Tana lafiya ƙalau, tace in gaishe ka sosai, in faɗa maka kana zuciyar ta da adduo'in ta a ko yaushe. Su Goggo da ƙannen ka ma sunce a gaida ka"
"Jikin...."
Kamal ya sake katse shi da
"Jikin ta da sauƙi sosai kuma bata wasa da inhaler, Sabir da Irfan suna kula da ita ko ni da Suhail bamu kusa.
Ya sake jinjina kai, shi karan kanshi ya fahimci tambayar shi a kullum ɗaya ne tunda har Abban ya tanadi amsoshin bashi tun kafin ya kammala su.
Shiru ne ya ɗan ratsa tsakanin su kowa da abinda yake tunani a ran shi.
Yaseer kunyar abban ne sosai ya lulluɓe shi ganin shi ya kamata ace ya zamo abin alfaharin su a wa'innan shekarun da yake dashi yana kula da su amma a maimakon haka sai ya zamo abin takaicin da ko shi da kan shi a gaba ba zai so tunawa ba. Ya zamo musu dalilin da zasu dinga sauke kan su ƙasa a kunyace idan suka haɗu da mutane saboda kowa kallon abinda ya faru da shi zai dinga musu.
Shi kuwa Kamal kallon uniform ɗin jikin Yaseer ɗin yake yi, ba wai dauɗar dake jikin ta sanin tsafta da gayun ɗan shi yake gani ko ya dame shi ba. Kasancewar bayan uniform ɗin secondary, a maimakon ya saka wani uniform dake nuna matsayin shi, na police, soja, likita ko na wani ma'aikata, sai ya ƙare a uniform ɗin prison, ba don komai ba, sai don su sun gaza a matsayin su na iyaye.
Da ace ya ɗauki nauyin Yaseer yanda ya kamata kaman sauran iyaye, da ace bai bashi damar tunanin ta ina zai nemi kuɗi ba kaman Sauran yara, da ƙaddara bata kawo su wannan gaɓar ba.
Wannan littafin na kuɗi ne, ga mai buƙata zaku samu a kan Naira 1000 kacal ta wannan account 8021689184 saliha Ahmad Na'ibi opay, sai a turo shaidan biya ta wannan number 08021689184.
Ƴan Niger kuma zaku turo katin Airtel na 600fcfa.
*Seemahwrites ✨*
42
~~~~~~~~~~
_I thought we're the same, birds of a feather_
_Now I'm ashamed I told you a lie_
~~~~~~~~~~
Can Yaseer ya sake motsa bakin shi jin shirun yayi yawa kuma tunanin dake shiga kan shi a irin wannan yanayin yana damun shi.
"Yaya...."
Ya fara tambaya amma wannan karon dakatawa yayi a karan kan shi domin bayi jin zai iya ƙarasawa.
"Lafiya." Kamal ya amsa domin ya fahimce abinda yake nufi a wannan karon ma.
Sai ya jaa dogon numfashi, yana ƙoƙarin tare zuciyar shi dake ƙokarin karasowa kusa a fusace, bai ma san dalilin da yasa ya tambaya ba.
"Abbah, Please ka rage zuwa nan tunda kaga yanzu ba a kusa kake ba. Na kai shekarun da zan iya kula da kaina."
Ba ƙaramin yaƙi yayi ba ya samu Magana mai tsayin wannan ta fito ba amma zafi da bushewar da yanzu yake ji a maƙoshin shi kaman ya kwana biyu bai sha ruwa ba, don haka ya miƙe kafin ma su zo su fara ƙoƙarin wulaƙanci ma Kamal ɗin.
"Abbah ka kula da..." Yace a matsayin sallama.
Kamal ma ya mike da niyyar tafiya. "Zan kula da kaina da su duka." Sai ya miƙa mishi laidar hannun shi wanda aka gama cajewa ya ɗan miƙa musu wani abu kafin ya samu damar shigo da shi kaman ko yaushe.
Abinda Yaseer yake ji ya fara fin ƙarfin zuciyar shi amma ya san idan bai karɓa din ba zai yi ma Abban shi ciwo a zuciya don haka ya saka hannu ya karɓa laidar tare da yin godiyar da ƙarshen ta bata fito da kyau ba sai dai Kamal ya jita a zuciyar shi.
Yana kallon bayan Yaseer ɗin har ya fice jami'in tsaron da ya rako shi ya saka shi a gaba suka koma.
"Mai muka samu yau kuma Malam Yaseer?" Jami'in ya tambaya.
Kafin su koma wurin da aka kirawo shi suna aiki ya buɗe masa laidan ya bashi damar ɗaukan abinda yake so. Babu kunya kuwa ya zura hannu ya ciro ƙullin madara guda biyu a farin laida, wanda Kamal ɗin ya saka saudat ta karkasa a ƙananun fararen laida har gida biyar saboda daɗin bincike, ya luma su cikin aljihun wandon shi, ya ɗauki sugar ma ƙulli biyu ɗaya ya shiga aljihun rigan shi amma idan ya ƙara ɗayan aljihun zai taso sosai, don haka ya haƙura ya mayar mishi cikin laidan, bai fasa bincikawa ba ko akwai wani abun da yafi wanda ya ɗauka daraja.
Yaseer dai na tsaye riƙe da hannayen laidan yana jiran shi har zuwa lokacin da zai gama. Idan akwai abinda zaman gidan yari ya ƙara masa toh haƙuri ne, domin tun yana jiran wucewar lokaci a ƙagauce har ya fara samawa kanshi nutsuwa a cikin saiɓin ta.
Suka cigaba da tafiya bayan mutumin ya ƙara wani abun da bai tsaya tantance meye bane. Duk inmates ɗin da suka wuce sai an miƙo mishi gaisuwa, samaruka da tsofaffi, da kai yake amsawa fuska a ɗan sake har suka koma wurin wanki kafin jami'in ya koma aka garƙame duk wata ƙofa da suka biyo ta cikin ta.
"Malam Yaseer ai da ka tafi ka huta kawai zamu ƙarasa" wani dattijo ne yayi magana yana ɗauraya.
Sai Yaseer ya ɗan ƙara sakin fuska ganin shi ya kamata ace ya karɓa mishi yaje ya huta.
Tsugunawa yayi ya buɗe laidar da ya shigo da shi sannan ya ciro sauran ƙullin madara da sugar ɗaɗɗaya ya miƙa ma wani saurayi.
"Gashi gudumawar yaye"
Ƙabbara aka saka, saurayin sai washe haƙwara yake yi "Allah ya saka da alkhairi malam, Allah ya biya ka da gidan aljanna, ya kuɓutar da kai daga wannan ƙangin"
"Amin" ya furta a ƙasan maƙoshi, ya cigaba da rabo ma wa'inda suka samu sauƙe Qur'ani a wurin shi cikin satin, sai abu kaɗan ya tsira dashi wanda zai amfane shi a wunin ranan kawai.