Sashe 112
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta sake dubanta lokacin da ta miƙe tana amsawa da "ba komai" ta fita, ta rufo mata ƙofa sannan ta nufi ɗakin da suka sauƙe Jadda. Ta same ta zaune ta saka masu haɗa kayan tsaraba a gaba sai yanda tace ake yi, Safnah na yi mata danna, suna taɓa hira.
Zama tayi a kusa da ita tayi mata sannu sannan ta matso kusa da kunnen ta cikin ƙasa da murya tace "Jadda, nake ganin kaman amaryar nan shigan ciki take da shi, alamu duk sun nuna"
Jadda ta juyo ta dubi yanayin ta mai kama da damuwa tace "kin saka ni a gaba to in je in tambayo miki Rafeek ɗin yanda aka yi ne ko yaya? Ko daman kun bashi ita ne ya saka ta a gaba yana kallo kaman talabijin? Ko ba ke kika zaunar da ni kina kuka wiwi ya gagara auruwa ba ƴan bayan shi suna ta tara zuri'a kuma yanzu wani munafurci ne wannan?"
Ta girgiza kai, "ba damuwar ba kenan jadda kada muje muna ƙoƙarin mata gata ne mu bata abinda zai cutar da abin cikinta"
Jadda ta jinjina kai cikin gamsuwa "Haka ne kuma. Ni ina ganinta ma cikin na fara hangowa amma ki saka shi ya kaita a gwada a tabbatar"
"Allah yasa muji labari mai daɗi" Safnah ta faɗa da murmushi.
Itama murmushin ne a kan fuskarta ta amsa da "Ameen Mammyn Hidaya" ta miƙe don ta kira Rafeeq ɗin tabi ta sake duba Aicha.
*Niamey, Niger Republic*
Da sauƙar su motar da Alaji Abdou ya turo ya ɗauke su zuwa katafaren gidan shi inda ake ta shirye-shiryen biki.
Yaseer ne ya fara fitowa daga bayan motan bayan sun isa idanun shi suka sauƙa a kan mahaifiyar shi da ƴan uwan shi da aka fito tarban shi. Tsadadden murmushi ya sake musu daga nesa, mayar masa da kwatankwacin shi suka yi amma suna dai tsaye ganinshi shi kaɗai, daman ya faɗa ba zai zo da Reina ba Bauchi zata wuce, da gaske yake yi kenan.
Zagawa ta ɗaya bangaren yayi ya buɗe ma Reina ƙofa ya karɓi jakan hannunta tare da taimaka mata ta fito. Sai a lokacin hayaniya ya kaure aka fara musu oyoyo, Maama da kanwar Aicha suka ƙaraso da sassarfa suka rungume ta. Mai haƙuri da Suhail ma suka rungume ɗan uwan su bayan sun karɓi babban jakan hannun shi da na baya, Suhail ya miƙa hannu zai karɓi jakan Reina dake hannun Yaseer ya watsa mishi mugun kallo, sai ya waske yana juyawa wurinta "sannu Da dawowa Umrah Aunty Reina"
Murmushi tayi tana duban shi "Yauwa My in-law" sai yayi murmushi yana shafa ƙeya.
"Ni banga akwatin tsaraba na bane ba ma" cewar irfan yana kallonta a kaikaice. "Duk lokacin da za'a sayi wani abu sai na tabbatar an cire sunan ka" Yaseer ya amshe.
Irfan ya dube shi da tashin hankali sanin cewa zai iya ɗin. Reina tace "kada ka damu auta, babban jaka sai ka gama zaɓa kafin kowa ya ɗauka"
"Toh ku basu hanya su wuce" cewar Maihakuri.
Yaseer ya daura da "shine ai zasu ƙara ma matata ciwon ƙafa da surutun su, har Maama ma sun fara koya miki"
Maama tayi murmushi mai faɗi don murnan ganin ƴar uwarta duk ya cika ta, daman ance baka kewar naka sai yayi nesa da kai, gashi tayi wasu saɓa-saɓan kumatu kaman ba ita ba jiki duk hutu. Ta riƙe hannunta ta jata har gaban Umma, Reina zata rage tsayi tayi mata gaisuwa Umma tayi saurin tarota ta rungume ta. "Mu shiga ciki, kun sha hanya" suka juya umma tana riƙe da ita a jikin ta inda ƴan biki da ƴan uwan masu gidan aka fara tuttuɗowa kallon matar Yaseer, harda baƙin biki ma kowa na son kallon YK gatan matasa da matar shi a zahiri.
A parlor suka yada zango Umma da Reina suna zaune a two seater Yaseer na zaune a one seater dake fuskantar su idanun shi na haska mishi mata guda biyu da suka fi masa komai a duniya, matan da suka zamo jin daɗin shi na duniya da lahira suna zaune a wuri guda sai yaji kaman babu wani wanda ya kai shi Sa'a a duniya.
Aka sake sabon gaisuwa har da su Jadda da suka fito aka taɓa hira da dariya kaɗan sannan aka ce za'a kai matafiya su huta suci abinci don haka aka wuce da su ɓangaren Alaji abdou domin har part ɗin Maami da baƙi.
Basu samu faragar cin abinci su biyu ba, saboda su ma sun yi kewar ci a cikin ƴan uwan su sai kawai aka haɗu kaman yanda aka saba a gida, ana yi ana nishaɗi suna tambayan Reina Labarin ɗakin Allah tana basu cike da shauƙi, dawowar su kenan amma ji take yi kaman su koma, wa'inda suka je ma shauƙin komawa ya kama su, Maama da bata taɓa zuwa da wayon ta ba kuma fatan Allah ya kirata take yi.
A wurin Suhail ya kira mata Safina video call, itama tayi murnan ganin Reina kuma kaman nadaman ƙin amsar tayin Suhail ta biyo su Niger na so ya kamata amma ta san tayi dai-dai tunda Aicha ba kowan ta bane, balle ace tana da dalili, ba ma shiri suke yi ba kuma itace mai taro.
Saida aka kira sallan maghriba Maami tazo ta watsa taron, ta sanar da Yaseer an shirya mishi ɗakin shi dake part ɗin su na samari, Reina kuma zata bata ɗaki a part ɗinta. Ba haka yaso ba, bai ma ga dalilin hakan ba tunda ɗakin shi zai wadace su Amma yaya ya iya, yana gani ta tafi da ita.
......
*Rafeeq*
Parking yayi a gefen hanya ya zuba ma Aicha dake faman matsar ƙwalla idanu. "Love" ya kira ta a nitse.
Amma kaman yace ta ƙara sautin kukan ta. Ya furzar da iska ta baki "baki son babyn ne ko menene kiyi min bayani Amma kukan ki ba zai fahimtar dani abinda ke cikin zuciyar ki ba"
Saida ta ɗan ƙara rero baiti na kuka sannan ta cire hannunta daga fuskarta da yayi Caɓa-Caɓa da hawaye ta dube shi. "Ni yanzu da wani ido kake so in je in kalle su dan girman Allah. Saida nace muyi amfani da protection"
"Protection alfasha muke aikatawa ne? Ko nace miki bani farin ciki da ƙaruwar da muka samu? Har Mummyn ma farin ciki da haka take Amour kina ɗaga hankalinki ne for nothing!"
Sai ta sake fashewa da kuka "innalillahi wa inna ilaihiraji'un, shikkenan yanzu itama ta san abinda muka yi a bayan idonta, na shiga uku"
Jingina kai Rafeeq yayi yana furzar da numfashi. "Ɗan sunna ne a cikin ki Darling, kowa da haka aka haife shi"
Ganin kaman zaginta yake ƙara yi ya saka ya ja bakin shi yayi shiru, Yana son ya sauƙe window su sha fresh air amma sautin kukan ta zai fita. Saida ya ga tayi mai isanta yace "toh muje in siya miki ice cream? Da kaza ko nama? Ko duka?"
"Kifi nake so" tace tana hararan shi.
Yayi murmushi yana mata kalamai masu daɗi da zuzuta ta har suka isa aka siya ice cream ɗin, tun a motan ma ta fara sha, shaff ta manta da halin da take ciki har saida suka tunkaro gidan su sannan ƙirjinta ya fara bugu.
Shima saida ya sha lallashi tunda shi ya jawo sannan ya ɗauka mata kifin ya shiga gaba tana bin shi a baya ta jawo wuyan hijabinta ta rufe fuskarta.
Mummy na ganin su haka ta san kwanan zancen. Harsashen su ya tabbata kenan, don haka bata ce musu komai ba sai tayin abinci tayi ma Rafeeq tace ma Aicha ta koma ɗaki ta huta. Ya miƙa mata laidan kifi da na ice-cream ɗinta ta karba ta wuce simi-simi yayi mata rakiyan idanu yana jin kaman ya watsa taron nan ya dauke ta kawai su koma gidan su su cigaba da rainon cikin su a tare.
Tana shiga ɗakin ta zuba a saman gado sai kuma tayi saurin tashi tana kai hannunta saman mararta kada tayi ma abun ciki illa. Murɗa ƙofan aka yi ta mayar da hankalin ta wurin kafin Reina ta shigo da sallama. Sai Aicha ta sauƙe numfashi don ta ɗauka Maami ne.
"Amarya sannu" cewar Reina tana shigowa ciki tare da mayar da ƙofa ta rufe.
"Yauwa, Kema sannu. Yaushe a gari?"
"Ɗazu muka sauƙa aka ce kun fita da ango har kuwa mun gaisa yanzu"
"Yayi kyau sannun ku da hanya" Tace tana ciro abubuwan dake cikin laidojin da ta shigo da shi.
"Uhm hmm, me da me za'a yi ne in sani tun yanzu? Kuma ashobe na yana wurin wa?"
"Wai yaushe muka zamo ƙawaye ne ban sani ba?" Tace tana buɗe foil takeaway da ƙatoton grilled cat fish yake kwance a ciki, Reina tayi saurin kai hannunta ta toshe hanci tana matsawa daga jikin Aicha.
"Yanzu zaki iya cin wannan kayan ƙarnin?"
"Bari ma ki gani" tace tana saka cokali mai yatsun da aka saka a ciki ta yanki babban tsoka ta tura a baki.
Reina ta miƙe zata bar mata dakin "idan kin gama sai in dawo muyi maganan" tace tana juyawa.
"Reina, ciki nake da shi" ta faɗa a fili ko zai yi kaman gaskiya a cikin nata kunnen.
Reina tayi saurin juyowa ta dafe ƙirji manyan idanunta kaman zasu faɗo ƙasa "mene? Ciki kika ce? Ciki dai na haihuwa ko na cin abinci?"
Cigaba da cin kifinta Aicha tayi tunda ai taji abinda tace kuma ta gane. Ƙafafun Reina suka matso da ita kusa da Aicha ba tare da ta ankara ba ta ranƙwafo sannan ta tambaye ta "na waye?"
"Na miji na mana" tace tana hararar ta.