← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 117

Sashe 95

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannu take ɗaga mishi kaman hannun zai tsinke sai ta tuna mishi da haka take bye-bye a yarintar ta, ya saki murmushi shima yana ɗaga mata na masu hankali. Sai ta kai hannunta baki tayi kissing ɗin shi ta huro mishi.

"Iye yayanmu ana shan love" cewar Irfan yana dariya.

Abbah da mai haƙuri dake zaune a gefe-gefen shi suka dungure mishi kai a tare. Mai haƙuri ya ƙara da tambayar "wa yake koya maka manyance ne auta?" Yana ƙoƙarin ɓoye dariyar shi.
Shima Abban ƙoƙarin danne nashi fara'ar yake yi, soyayya ko yarinta da shirme? Amma dai koma menene yaji daɗi da ya shaida cewa lokacin farin ciki da kwanciyar hankalin Yaseer ya zo, yana godiya ma Allah da ya gwada mishi da rai da lafiyar shi kuma yana musu fatan hakan ya ɗore har ƙarshen rayuwar su.

Amsar kiss ɗin yayi ya manna a ƙirjin shi kafin a fakaice yayi mata nuni da motan dake bayan shi yana furta sunan Abbah ba tare da sauti ba.

Saida ya maimaita sau uku kafin ta gane mai yake nufi, ai kuwa ta gane jeep ɗin na gidan su ne. Tayi saurin durƙusawa a wurin bata ɗago ba har Yaseer ya ƙarasa ya shiga gaban Jeep ɗin da Suhail ke zaune a mazaunin driver yana murmushi da rera waƙan soyayya. Ya ja suka bar gidan sannan Reina ta iya komawa ciki a dudduƙe ta faɗa a kan gado da fuskarta wanda take jin bata son ta sake ɗaga shi Saboda kunya.

Yaseer yana dawowa suka shiga haɗa kayan da zasu tafi da shi, suna yi yana tsokanar ta da abinda ya faru ɗazu, harda bata saƙon Abbah yace a gaishe ta sosai.

Ta so ta haɗa musu da kanta amma bata san yanayin wurin da zasu je ba ko kuma tsawon lokacin da zasu ɗauka.

Madaidaitan akwatuna Yaseer ya ɗauka musu kuma yace kada ta damu da saka kayan gargajiya da yawa kawai ta tanadi abinda zata buƙata na wani lokaci.

Washegari jirgin su ya ɗaga zuwa Abuja, bata lura da suna tare da Aicha da Muhammad ba saida suka zo sauka daga jirgin. Haka ma ɗakunan su da suka sauƙa a hotel duk a floor ɗaya suke, sai dai a ɗan kwai tazara a tsakanin su.
Ita da ta ɗauka yawon jin daɗi zasu tafi?.

Da Yaseer ya lura da canzawar yanayinta ne ya shiga mata bayanin akwai aikin da zasu yi mai muhimmanci ne na ƴan kwanaki zuwa sati daga nan zasu raba jiha da Aicha kafin ta samu hankalin ta ya ɗan kwanta.
.
.
.
3:41pm

".... Sir, we'll make sure that you don't suffer any loss or damages, we assure you, no I give you my word that this will pan out like it always had, but please reconsider your decision."

Yamutsa fuska mutumin yayi tare da saka karamin yatsan shi na hagu a cikin kunne ya ɗan yi kaman ya sosa sannan ya fito da shi ya kawo baki ya hure. Bakin shi ya cigaba da motsi yana jan tally counter mai kaman tasbaha dake yatsan shi na dama.

Yana hakimce a kan kujerar dake fuskantar na Aicha amma idanun shi suna kan Yaseer har ta ƙare zuban ta bai tanka ko ya ɗaga ido ya kalle ta ba, domin shi ya riga da ya yanke shawara sune dai basu sani ba har suka ɓata ma kansu lokacin biyo shi.

"A ina ka samo wannan kai kuma? Ta cika min kunne." Yace da Yaseer cikin harshen faransanci.

"Excuse me sir, I can understand french" Aicha ta amshe a ɗan hasale da turanci.

Sai a lokacin ya ɗago yayi mata kallon sama da ƙasa sau ɗaya ya watsar "umm congratulations" Shima ya mayar mata da turancin, lokacin da wayan shi dake ajiye a saman table ɗin ya shiga kiran Salla na shigan lokacin la'asar, ya ɗaga yana mayar da wayan cikin aljihu tare da miƙewa tsaye.

"I have places to be amma zan yi tunani" yace cikin mix din Turanci da Faransanci. Sannan ya ɗauki sandar shi wanda ta kasance ba na dogarawan wata nakasa bane sai na cikar izza da isa, ya juya bodyguard ɗin shi ya buɗe mishi ƙofa yana takawa cike da gadara ya fita.

Saida Aicha ta bari sun rufo kofan kirif sannan ta juyo wurin Yaseer da yanayin takaici a kan fuskar ta "unbelievable!" Tace tana scoffing, sannan ta sauya harshen ta zuwa faransanci "wannan me ya ɗauki kan shi ne? Ka ga Saboda iskanci da wulaƙanci ko kallon mutane bayi iyawa? Na rantse ba don kai ba yaya Yaseer wannan ko kallon inda yabi ba zan yi ba duk Abinda yake taƙama da shi kuwa balle in nemi wani abu a wurin shi"

Shi kuma bai ga abun bacin rai ba domin ya sha karo da wanda suka fi shi ma, kuma ma ya ga ƙoƙarin shi da suka biyo shi ba tare da sanin shi ba kuma ya yarda ya saurare su.

Yaseer ya buɗe buɗe baki zai tanka kenan ƙofar ta sake buɗewa sai gashi ya shigo.

Har Yaseer saida mamaki ya kama shi balle Aicha da hanjin cikin ta suke kaɗawa, idanunta zuru-zuru kaman wanda aka yiwa ƙarya hannunta a kan baki take kallon shi har ya tako ya ɗauki counter ɗin shi da ya manta a kan table sannan ya dube ita cikin ido.
"For your information, nima ina jin faransanci. And ina ganin ƙarshen deal ɗin mu yazo kenan tunda babu abinda kike nima a wuri na" ya kashe mata murmushi ya juya ya barta kunya kaman ƙasa ya tsage ta shige ciki.

Shikkenan bakinta ya jawo musu.

"Umry..." Yaseer ya kira yana shigowa hotel Room ɗin dake da ƙarancin haske.

Cover shoes ɗin ƙafar shi ya cire daga bakin ƙofa ya gyara masa zama ya saka indoor shoes kana ya ƙarasa shigowa ciki yana haskawa da tocin wayan shi.
Saida ya samu ya mayar da hotel card ɗin da ta cire daga jikin switch ɗin wuta haske ya gauraye ko ina ya iya hango ta cikin lallausan farin duvet dake gadon, ƙarfin hasken ya sakata ta daɗa jawo shi tana ƙokarin rufe fuskar ta ya ƙaraso ya riƙe ya yaye ta sai ta saka hannu tana kare Idanunta tare da fitar da ƙananun gurnani.

Riƙe hannun yayi yana sake kiranta, ta samu ta zame ɗaya hannunta daga riƙon shi ta jawo pillow dake gefe ta ɗaura a saman fuskarta.

Riƙon gaskiya yayi mata wannan karon ya ɗago ta ya zaunar sai gashi ta buɗe idanu ta zuba masa, yana cikin baƙin suit ɗin da ya fita dasu a jikin shi, idanun shi sun gwada yanayin gajiya gashin kan shi ya ɗan cakuɗe don suna isowa ya sake shiri ya fita ko abinci ma ita kaɗai yayi wa ordern Room service taci tayi waya da su Umma sai ta koma tsakanin kallo da barci shine sai yanzu yake shigowa.

"I told you zamu fita idan na dawo amma kin kwanta ko dinner baki yi ba?"

"Sannu da dawowa " tace tana murza idanu, "ina kallo ne barci ya ɗauke ni" tace tana hamma kana ta shiga laluɓan wayanta da ya faɗa ta ƙasan pillown da tayi matashin kai da shi.

Shi ya ɗauko wayan ya miƙa mata ta kalli lokaci takwas har da kusan rabi.
"Kin yi sallan Isha?" Ya tambaya.

Girgiza kai tayi, ta fara ƙoƙarin sauƙa sai ya miƙe ya yaye mata duvet ɗin ya taimaka mata ta sauƙo. Ya tsayar da ita a kan ƙafarta ta saka takalmi sannan suka yi hanyar bathroom, ya tsaya daga waje bayan ta shiga ya jawo mata ƙofa.

Showering tayi da ruwa mai ɗumi ta wartsake kafin ta ɗauro alwala ta fito ta saka doguwar rigan da ta samu a kusa da hijabi ta gabatar da Isha.
Tana gaban mirror tana shafa lotion Yaseer ya fito ɗaure da towel a ƙugu, da wani ƙarami rataye a wuyan shi yana tafe yana tsane kan shi da gefe ɗaya. Ta bi ƙirjin shi da ido ta cikin madubin tana ayyanawa a ranta ɗaga ƙarfen da yake faman yi duk safiya bayi tashi a banza. sannan ta mayar da hankalinta kan face cream da take shafawa kafin ya kama ta tana kallon shi.

"Bae baka faɗa min ina zamu je ba, saboda in san kalan kayan da zan saka"

"Zaki yi ma duk Abinda kika saka kyau, I just hope you'll like where we'll be going"
Tana iya hango murmushin dake kan fuskar shi yayin da yake ɗaga wani button up shirt da coffee brown kaftan a jikin hanger yana ƙoƙarin tantance wanda ya kamata ya saka sai itama taji zumuɗin fitan ya kama ta.

Akwai wani sabon cream abaya mai adon coffee brown flowers a cikin kayan da ta zo da su don haka ta bashi shawaran ya saka kaftan ɗin yanda zasu yi matching.

Ƙarfe 10:02 na dare suka fito daga hotel room din cikin shirin su tsaff Yaseer ya jawo ƙofar. "Shall we?!" Yace yana mayar da key card ɗin su cikin wallet ɗin shi, sannan ya ɗago ya dube ta da murmushi a kan fuskar shi.

Gyaɗa kai tayi itama da nata murmushin, she can't wait ta gan su a inda zasu je. Ya zura hannun shi ta bayan ƙugunta suka fara takawa yana tambayar ta yau ba za'a bashi jakan ya riƙe bane?.

Ƙofar dake gefen nasu ma a lokacin ya buɗe wata mace ta fito, Reina da suka gifta ta tayi saurin juyowa da mamaki tana zargin baiwan da take da tunanin tana da shi na gane mutane ne yake son ya kaita ya baro ta.

"Zahra??" Ta kira don tabbatarwa.

Dake suna linzami sai gashi ta juyo. Yaseer ma ya juyo don ganin abinda ya ɗauki hankalin ta, amma kallo daya yayi ma wanda yaji ta kira da Zahran ya kawar da kan shi.
Chapter 95 · 0% Book details