Sashe 105
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fitowan Aicha ya saka ya ɗago ya dubeta, idanunta luhu-luhu ta wuce kitchen ba tare da tace dashi komai ba, abu mai sauƙi suka haɗa ta koma ɗakin yin sallan Isha don haka ya saka a mayar da Asal gida, a lokacin ya kasance su biyu ne kawai a cikin gidan.
Jin ƙaran tashin mota ya saka da ta fito tayi tunanin ko shine ya tafi don haka ta shiga duba Asal amma bata ji ɗuriyar ta ba, sai gashi ya turo ƙofa ya dawo daga masallaci.
"Ina Asal tazo mu ci abinci?" Ta tambaya.
"Ta tafi gida" ya bata amsa.
Ɗan buɗe idanunta da suka sauya kala suka yi mata nauyi tayi tace "gida kuma? Yaushe kenan zata dawo? Ko nima gidan Jaddan zaka kai ni in kwana?" Tayi masa tambayoyin a jejjere zuciyar ta na fara dokawa. Ita daman ta sani tayi kuskure tun daga farko, tayi wauta da rashin hankalin biyo Rafeeq gidan da ya buɗe baki ya faɗa mata babu wata mace a ciki.
"Muci abinci muyi magana tukunna" yace yana wucewa ciki.
Ta ji kaman ta arci na kare daga wurin tunda ƙofar ba a garƙame yake ba turawa kawai yayi amma bata da tabbacin gate ma haka ne.
"Aysh" ta sake jiyo muryar shi don haka ta haɗiyi miyau ta juya ta same shi ya samawa kan shi matsuguni a kujeran dining.
Abincin ta fara saka mishi hannunta na rawa. Ya san fargaban me take yi, kuma nan da minti talatin yake da niyyan warware mata komai amma yafi son taci abinci tukunna domin dole hankalin ta zai tashi.
"Zauna" yace da ita, ya tura mata abincin da ta zuba masa gabanta kaman ranar haɗuwar su na biyu.
Bai ko kalleta ba har ya gama zuba ma kan shi abincin ya fara ci, hankalin shi na kan wayar shi abinda bai saba ba.
kada fargaban yayi mata yawa ga kuma yunwan da take ji yasa itama ta fara kai abincin bakinta.
Gidan yayi shiru kaman babu wasu masu rai a cikin sa sai ƙaran cokula dake karo da plate kaɗan-kaɗan.
Taci fiye da rabi lokacin da wayan hannun shi ya fara ringing, kaman wanda yake jira yayi saurin ɗauka yana sakin fuska ya tsayar da wayan a saitin fuskar shi sannan yayi sallama, hakan yasa ta gane video call ne.
Muryar da ya amsa masa sallaman kuma ya bata mamaki domin sakk na mahaifin ta. Hakan ya tunasar da ita komawa ɗaki ta ɗauki nata wayan ta kira Daddy domin Allah ne kaɗai zai iya fitar da ita a cikin wannan ramin da ta faɗa da gangan.
"Daddy barka da dare an wuni lafiya" cike da girmamawa yake gaida wanda yake cikin wayan, ganin hankalin shi ya tafi ya saka ta miƙe zata saɓule jiki ta Shiga ɗakin ta garƙame ta kira daddynta ta jira har zuwa lokacin da taimako zai iso.
Wucewar da zata yi sai taji Rafeeq ya riƙo hannunta. Ƙirjin ta yayi mugun bugu ta sanƙare kawai a wurin. Saida ta ɗauki sakwanni wurin 5 kafin ta iya juyowa ta dube shi, har Yanzu hankalin shi na ga fuskar wayar shi.
"Toh Daddy gata nan" yace yana ɗagowa ya dube ta Finally. Sai taga ya miƙe ya dawo da ita kujerar da ya tashi ya zaunar da ita, sannan ya saka wayan a hannun ta, "gashi Daddy na son magana da ke" yace cikin ƙasa da murya hakan ya saka ta dubi screen ɗin sai ga idanun mahaifinta cikin nata.
"Darling. Kina lafiya"
Daman daddynta ya san Rafeeq?. Sauƙe ajiyan zuciya tayi, tashin hankalin da ta shiga yana yayewa, murmushi ya wadaci fuskarta sannan ta gaida shi.
"Ina Maami? Kace nayi kewar ta da my sisters"
"Idan mun gama magana in kina so sai in haɗa ku ku gaisa" juyawan da zata yi taga Rafeeq har ya shige master bedroom ɗin da ya bata ya rufo ƙofa.
Magana kuma? Kada dai a kan zaman gidan Rafeeq da take yi ne ya samu labari ta wani wuri shiyasa har ya samo contact ɗin shi ya kira shi? Tabbas tayi wauta.
Ɗan murmushi Alaji Abdou yayi ganin yanda ta tsargu yace "Tunanin me kike yi? Ba abinda kike tunani bane, duk abinda kike yi a Abuja da sani na kuma ba laifi kika yi ba sai dai rashin sani"
"Toh maganar menene Daddy?" Yanda muryar ta ya fito da sanyi sai ta bashi tausayi.
"Aicha, kin yarda duk duniya babu wanda ya kai ni son ki?" Yanzu cikinta ne ya shiga ƙugi saboda sunanta da ya kira kai tsaye da ba zata iya tuna yaushe ne na ƙarshe ba.
A hankali ta gyaɗa kai sannan Alaji Abdou ya cigaba da cewa "kuma kin yarda ba zan taɓa cutar da ke ba?"
Shima saida ta ɗau lokaci kafin ta gyaɗa kai, tana taraddadin abinda zai faɗa a gaba "toh Darling nayi duba da wa'innan hujjoji guda biyu ne wurin sauƙe amanar ki da Allah ya damƙa a hannuna. Na baki ci da sha, sutura da ilimi iyakan iyawa ta sannan kuma yanzu da kika kawo gaɓar girma na zaɓa miki abokin rayuwa na gari wanda ya cika sharuɗa na addini in sha Allah..."
Auren haɗi kenan Daddy yake so yayi mata. Da Rafeeq hala tunda gashi kaman Daddy ya san da alaƙar su.
Ya ci-gaba da cewa "Nayi amfani da ikon da Allah ya bani na ɗaura miki Aure da Rafeeq sati biyu da suka gabata, halin rashin lafiya da kika samu kan ki a ciki ya hana ni sanar da ke tun da wuri. ina fatan ban yi miki katsalanda a cikin rayuwar ki ba"
Cikin matsanancin tashin hankali take kallon shi, bakinta a buɗe amma ta gagara cewa komai sai hawaye da suka fara bin kuncinta.
Dalili kenan, dalilin da ya saka Yaseer ya tafi ya barta da Rafeeq ba tare da wata damuwa ba. Dalilin da ya saka Rafeeq ya dabaibaye rayuwar ta lokaci guda, dalilin da ya saka ya ɗauko ta ya kawo ta gidan shi sabo, saboda itace matar gidan. Saboda mijinta ne shi.
"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun" ta samu bakinta ya furta kaman raɗa hawaye na wanke mata fuska.
"Zaki mun biyayya ko ƴata? Zaki saka Daddyn ki alfahari?"
Gyaɗa kai tayi kuka na daɗa cin ƙarfinta tace "In Sha Allah Daddy"
"Alhamdulillah. Daman na san ban haifi ƴar da zata baɗa min ƙasa a idanu ba. Allah ya baku zaman lafiya ya sanya ƙaunar juna a tsakanin ku"
Laɓɓen bakin ta suka furta ameen Amma sauti ya gagara fitowa.
"Kuma duk abinda kike so ki sanar dani kada ki ji nauyi kin ji? Duk fafutuka na saboda ku ne, ina alfahari da Allah ya azurta ni da ku, Allah yayi muku albarka" yayi mata murmushi sannan ya katse kiran.
Itama kifa wayan tayi a kan dining ɗin ta kifa kanta tana ƙara sautin kukan ta.
Fitowa Rafeeq yayi ya tsaya a bakin ƙofa yana kallonta. Ba haka yaso ba, amma bayi da zaɓin da ya wuce hakan wurin karkato da hankalin Aicha daga kan Yaseer ta fuskanci aurenta.
Ya tako inda take ya saka hannu ya ɗago kanta daga kan table ɗin ya juyo da ita, sai ta rungume ƙunkumin shi tana ƙara ƙarfin kukan ta don ko san kallon fuskar shi bata yi.
Rasa wani kalma zai yi amfani dashi ya rarrasheta ya saka ya shiga buga bayanta a hankali har ta ci kukanta ta ƙoshi yana tsaye a jikin ta.
"Zuciya na zafi Rafeeq ka taimaka min"
yayi saurin ɗaga ta daga jikin shi yana riƙe da kafadunta ya rage tsayin shi a kan kujeran gefenta yana fuskantar ta "Baby I'm here for you, Ni zan baki duk abinda kika cancanta, I'll treat you right nayi alƙawari"
Ganin yanda tayi sukuku ya matsa kusa ya bata daman faɗowa jikin shi bayan ya sake ta, ta ɗaura kanta a saman kafaɗar shi tana sheshsheƙa, shi kuma a hankali yaci gaba da shafa bayanta cikin sigar lallashi.
"Rafeeq don Allah ka koya min son ka, ka bani daman saka wa mutumin da ban taɓa niman wani abu a wurin shi na rasa ba. Ina so in so ka Rafeeq don Allah"
Zagaye ta yayi da hannun shi da ƙaramin murmushi a kan fuskar shi. "Nayi alƙawari, You'll fall head over heels for me"
.....
*11:48pm*
*JW Marriott hotel*
"Gufranak" Yaseer ya furta lokacin da ya fito daga ban ɗakin yana jawo ƙofar shi a bayan sa sannan ya fara takowa cikin ɗakin sanye da dogon wandon barcin da ya shiga da shi ya saka bayan yayi wanka.
Kallon Reina ya tsaya yi da roban ice cream a gabanta tana ta haƙar shi da cokali. Sai ta ɗago ta dube shi tana sakin murmushin rashin gaskiya.
"Zaƙi da sanyi duk kika haɗa kike sha a wannan lokacin? Ni da na ɗauka zan fito in samu kin yi barci?" Ya tambaya fuska ba yabo ba fallasa amma ita da ta saba ganin murmushin sa a kwana biyu sai taga kaman haɗe rai yayi.
Ƙara faɗin murmushinta tayi, tayi saurin riƙe cokalin a baki ta saka hannu biyu ta mayar da murfin roban ta rufe ta ajiye shi a gefe. Ta cire cokalin a bakin ta Sannan ta amsa dalilin rashin barcin ta "story ɗinka na IG nake gani. Ashe har kirari ka iya bae?" Tace tana shafa zoben ta, Ya samu ya lallaɓata ta cire bracelet ɗin da zata yi shirin barci.
"Ina auren sarauniya dole in koya" ya amsa yana sakin fuska tare da ƙarasawa ya ɗauki tub ɗin ice cream ɗin ya mayar fridge.