Sashe 54
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Toh shikkenan, kayi barci mai daɗi..." ta saka tafin hannu ta kare Idanun ta a dole kunya take ji sannan cikin raɗa tace "..Na amince da tayin ka, Allah ya daidaita tsakanin mu. I love you" ba zata bari ta sake wasa da daman ta ba.
Da sauri Yaseer ya sauƙe wayan daga kunnen shi ya datse kiran. Amma sai ya kawo speakern wayan bakin shi cikin salo kaman wanda bayi son kowa yaji abinda zai faɗa ɗinnan yace "I love you too Ma chérie"
Ganin ya gama wayan Reina tayi saurin juyawa zata koma inda ta fito kafin ya lura da ita, ta jiyo muryar shi ya kira sunanta.
"Reina" ya kira ba tare da ya waiwaya ba, kenan ya san da ita a wurin yaci gaba da soyewa da budurwan shi Amma ita idan ya kama ta tana yi shikkenan ya fara share ta.
"Na'am" ta amsa cikin kasashshiyar murya.
"Ina zaki je da daren nan?. zo nan."
Sai a lokacin ta ƙaraso cikin parlon.
Ta zuba mishi idanunta dake kyallin hawaye. "Zan je shan Iska ne"
"Iska a daren nan?" Ya kalli agogo ƙarfe 12:49. "Duk na cikin gidan da ɗakin ki bai ishe ki ba?"
"Kuka nake so in yi kuma su Safina sunce na dame su, toilet kuma ina tsoron jinnu su raɓe ni shine zan je in yi a wajen" ta yanke shawarar gaya mishi gaskiya.
Rasa na cewa yayi ya tsaya kallon ta. Ya lumshe idon shi a kanta ya buɗe su sannan yayi mata tambayar da take jira ta samu zayyane masa matsalar ta koma ya iya nimo mata mafita.
"Me zai saka ki kuka da daren nan a maimakon barci?"
Sake hawayen idanu ɗaya tayi ya sauƙa kan kuncin ta sannan ta shiga mayar masa da matsalar ta, kuma bayan saƙon nan har yanzu tana kiran Uncle B wayan shi a kashe.
A wannan lokaci, duk yanda zuciyar shi ya kai da bushewa bayi jin ciwo ko bugu sai da mashin kalaman ta da Abinda ya gani a idanun ta ya soke shi a yanda ya ji zafi sosai.
Sai yayi murmushi mai ciwo yayi mata nuni da kujerar dake kallon nashi ta je ta zauna.
Soyayya Idan kana kayan ka kai kaɗai ita da hauka duk ɗaya ne, don addu'ar Allah ya kawo sauƙi zai iya maka amfani.
"Amma wani abu ya taɓa shiga tsakanin ku irin haka?" Ya tambaya.
Ta girgiza kai. Tana sakawa ranta daina ɗaukan wayar ta da yayi kwanaki ba ɗaya bane da wannan.
"Okay, sai ki kwantar da hankalin ki for now ki kwanta kiyi barci gobe idan ya kunna wayan sai ki buƙaci ya sanar da ke kuskuren ki sai ki amsa ki bashi haƙuri "
Gyaɗa kai tayi tana share hawayen ta, ta fara jin dama-dama tunda ta samu mai sauraren ta kuma ya fahimci damuwar ta.
"Toh Yaya Yaseer, Nagode"
Yayi ƙaramin murmushi, bayi jin ko ya haƙura da ita sunan shi a bakin ta zai daina mishi daɗi. Kuma daga yanzu a cikin wannan daren zai fara roƙon Allah ya cire mishi son Hafsatu Reina cikin ran shi, wanda a yanzun ne ya yarda ya amince da abinda yake ji a kanta soyayya ce kuma a yanzun yake fatan rabuwa da shi saboda irin wannan son cuta ne.
"Ki tabbata kin bashi haƙuri, ba wai idan ya sake miki kawai ki ɗauka komai ya wuce ba, kika cigaba da jeren tudun laifi wata rana rikitowa dake zai yi"
Ta gyaɗa kai cikin ƙwarin guiwa "In sha Allah Yayanmu, na gode sosai, "sai da safe" ta wuce tana ɗaga mishi hannu.
"Allah ya tashe mu Lafiya" ya bi bayan ta da kallon Abinda ran shi ke muradi na karshe. Daga gobe zai fara kallon ta kaman Aicha da Maama. ba zai takurata ta so shi dole ba, don bayi jin zai taɓa auren macen da bata son shi, koda wata daban balle wanda bayi da tabbacin lokacin da zuciyar shi ta mace a kanta, Idan Bilal shi yafi zama mata alkhairi Allah ya tabbatar ya kuma daidaita tsakanin su.
.....
Tana idar da sallan asuba ayatul kursiyy kawai ta samu tayi ta ɗaga waya ta sake kiran Uncle B, ta kuwa ci Sa'a ya ɗauka a kiran farko.
"Uncle Bilal" ta kira da wani murya mai sanyi don ta azabtu cikin daren nan barci rabi da rabi tayi.
"Na'am doll Good morning" sai taji shima muryar shi da sanyi ba kaman yanda ta tsammata ba.
"Ina kwana" ta mayar mishi da gaisuwan ya amsa sannan tace "Uncle Bilal nayi maka wani abu ne Please?"
Shiru yayi kaɗan kafin ya amsa da "Gaskiya l wasn't happy with you these days doll. Kin sani ni mutum ne mai son kula kuma bani juran shariya Amma haka kike bari na in yi ta faman yanda zan samu in yi magana da ke na wasu ƴan mintuna. Idan kuɗi kike so ki faɗa mun ko nawa ne doll zan baki, amma ba zan ɗauki wani rainin hankali da sunan sana'a ko makamancin sa ba you hear me?"
Tabbas saƙon jiya nata ne, tunda gashi ya maimaita mata wani ɓangare na cikin sa.
"Toh Amma shine zaka kashe waya? Gashi naga missed calls ɗinka da yawa duk hankali na ya tashi."
Saida ya furzar da numfashi ya daidaita yanayin shi kafin ya saki murmushi yace "Albishirin ki"
"Goro"
ya sake sakin wani murmushin kana yace "Yau zamu kawo tambaya da sadaki in sha Allah"
Cike da rashin fahimta tace "yau kuma?" Ita tama manta da sati biyu da suka wuce suka yi maganan, kuma kaman ya faɗa mata ance ya dakata da sadaki tukunna, toh ko sun amice masa ne?.
"Yes, albishir ɗin da na kira in yi miki kenan but I called you 5 times doll please, dan Allah kada mu sake irin haka da ke"
"Ba zamu sake ba kayi haƙuri dan Allah"
"Yauwa good girl, nayi ai amarya bata laifi"
Ɗan murmushi tayi amma tana mamakin yanda bata yi murnan hakan sosai ba, ko dan hidima ya sha kanta ne? Sai take ganin kaman yayi mata sauri.
Kaɗan suka ƙara magana suka yi Sallama tunda da tafiya a gaban Uncle B. Itama da sauran cake da zasu ƙarasa amma babu yawa 200 ne zuwa azahar ko bayan shi za su gama.
Dukkan su uku harda Safina suka shiga kitchen aka haɗa abin karyawa suka karya kana suka fara aikin su.
Yau ma kaman jiya an taya su, kuma kaman jiyan Yaseer bayi nan, sammakon fita yayi duk da yayi complain din tashi da ciwon kai ma Ummah, amma gwamma ya fitan, yayi nesa da ita na wani lokaci ko zai ji dama-dama.
Suna gama aikin ta gudu gidan Ummi da sunan kai cake kafin su Uncle B su zo. Kuma ko tambayar ta aka yi a kan sadakin da zasu kawo cewa zata yi bata san komai ba, don itama ba shawartan ta yayi ba, sanar da ita kawai yayi.
.
.
Ba sojojin da aka jere tun daga bakin gate har cikin parlon da suke zaune bane ya dame su, ba kayan bidi'a da aka jere kaman kayan lefe ko na biki ba, sai dai rashin sanin da zuwan su a yau din baki ɗaya.
Shi kuma Uncle B a nashi lissafin ya fadawa Reina ne ta sanar da su tunda wancan auren shin a tsakanin shi da Amaryar shi ƴar Egypt suka tsara komai, so yanzu ma ya ɗauka hakan ne zasu yi da ƴar arewacin Najeriya.
Gashi ganin girman shekarun general kafin azo ga matsayi ya saka sun gagara mishi musun karɓan tambayan tunda dai Uncle B sun faɗa mishi ya dakata da komai ba yanzu ba tukunna. Sai dai a kan sadaki sun so suyi gardama tunda bincike wannan mai zurfi basu yi a kan Bilal ba.
General yayi gyaran murya "Idan ma auren za'a ɗaura a yanzu mu a shirye muke in yaso duk wani biki sai ayi shi daga baya. Ayi komai cikin sauƙi kaman yafi"
Habawa, sai kace wata ƴar tsana, Cewar Alhaji Tahir cikin ran shi. "Sauƙi na da daɗi a kowani lamari amma hidiman aure shi bayi son gaggawa. Yanzu ita yarinya daga ni sai kakanninta na fannin uwa take dashi kun ga shiri ba zai zo mana da sauƙi ba domin ni ɗin ma babu cikakkiyar lafiya, to kuma bani son saka gaggawa a cikin lamarin ya haifar mana da ɗa mara ido tunda Aure lamari ne Babba"
Uncle B bai yi zaton idan suka musu haka za su ƙi ba, shiyasa yayi duk abinda general ɗin yace har da wanda bayi so saboda ya samu ya yarda ya zo da kan shi amma a banza.
Sai bayan maghriba Reina da Maama suka dawo suka riski tilin kaya a parlo, ganin huhunan goro da kwalayen minti a cikin su ya saka ta fahimci na menene don haka tun da ta shige ɗaki ko daddynta bai sake sanya ta a idanu ba kuma bai nime ta ba shima, haka ma Uncle B bai kira ta ba shi ala dole laifin ta yake gani itama fargaban yanda zata fuskanci iyayen ta ya saka bata nime shi ba.
Har washegari ta tashi ta samu an kwashe kayan daga parlour sannan babu wanda yace mata komai har suka karya ta wuce gidan Ummi.
.....
Monday.
9:34am.
Sosai hayaniya ya kaure a class ɗin lokacin da aka manna list ɗin wanda registration ɗin su yayi, sauran kuma class rep zai maida musu kuɗin su.
"Habawa! Ta yaya za'a ce a cikin mutane fiye da ɗari da hamsin mutane 21 kawai aka ɗauka, sannan a maimakon ayi balancing maza su fi yawa sai aka ɗibe mu daidai har da ɗorin mace ɗaya a kai, su da a ƙarƙashin wani zasu zauna ya kula da su? Gamu masu buƙata shuwagabannin al'umma amma an zaɓi ayi asaran slot da a bawa wanda zai amfana da gaske" ɗaya daga cikin wanda ya fi sauran masu mita murya kenan.