Sashe 88
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
So yake yi su zauna suyi spending time da juna suyi hira da sauran su yanda zasu daɗa fuskantar juna su kuma fayyace ra'ayoyin juna da yazo ɗaya da kuma wanda suka yi saɓani. Amma kafin ya kaiga tura e-mail ɗin suka sake jin ƙaran doorbell.
"Yanzu kuma waye Please?" Shi ya dauka an daina yayin sintirin zuwa gidan amarya washe garin biki ko a satin farko ma, wannan ai akwai ɗaukan hakki.
"Bari na duba" ta miƙe ta ɗauki mayafinta ta lulluba sannan ta sauƙa ƙasan ta buɗe ƙofa lokacin da tayi arba da Aunty Zeenat.
"Mummy zee" ta ƙarasa ta faɗa jikinta cike da jin daɗi tana jijjigata . Har saida ta gama murnan ta ɗago ta riƙo hannunta tana mata iso zuwa ciki, ita kuwa Aunty Zeenat kallo kawai take bin Reina dashi har ta bata wuri ta zauna ta juya wai zata je ɗauko mata ruwa.
Ruwan sanyi da juice ta kawo mata sai peppered gizzard da aka kawo musu tare da abinci.
"Wallahi ban yi tunanin zan ga kowa yau ba Mummy zee, naji daɗin ganin ki sosai" tace tana tsiyaya mata ruwan a cup sannan ta miƙo mata.
"Yaaaya na ganki garau?" Tace tana sake kallon ta sama da ƙasa babu wani alama da yake nuna tana cin wani baƙon yanayi.
Itama Reina sai ta kalli jikinta tana ƙoƙarin fayyace abinda Aunty Zeenat take kallo.
"Kada ace da wannan ƙatoton gyalen kike masa yawo a cikin gida"
"A'a fa, saboda zan buɗe ƙofa ne ban san ko namiji bane"
"Kin yi kyan kai. Amma kina lafiya ƙalau ko? Ummi ta damu ne ta turo ni don tayi ta kiran wayan ki bata samu"
"Ayyah wayan na wurin Maama ne, ɗazu suka kawo mun, kuma ina da niyyan kiranta zuwa anjima"
"Angon kin bayi gida ne?"
"A'a yana sama yanzu zaki ga ya fito" tace tana kallon stairs, sai gashi kuwa ya fito da fara'a a kan fuskar shi, sallama yayi ya ƙaraso ya samu wuri a saman carpet ya zauna kana ya shiga gaida Aunty Zeenat don kallonta yake kaman Hajiya Fauziyya, yayi mata sannu da godiyan ɗawainiyan biki sannan ya tashi ya koma inda ya fito ya basu wuri.
"Ke tashi muje ɗakin ki muyi magana" ta tasa ta a gaba har uwar ɗaka suka rufo ƙofa sannan ta dube ta.
"Allah dai yasa ba rowan kan ki kika yi mishi ba Reina, idan ba haka ba na kama jibgar ki a dakin nan ko shi bai iya ƙwatar ki."
Dariya maganan ma ya bata tace "A'a ni ban mishi rowan komai ba, zaki iya tambayan shi ma kiji"
"Kin tabbata in tambaye shi? Yace ba haka ba da Ummi zan haɗa ki ko daddyn ki ai kin san abinda suka faɗa miki kafin a kawo ki"
"Allah ki tambaye shi, na yarda"
Ta sauƙe ajiyan zuciya suka zauna a bakin gado sannan ta shiga lallaɓata da sake mata nasiha. Ita ta taimaka mata suka ciro sauran kayan sakawa da na amfanin ta dake akwati suka jera a wardrobe ɗin ɗakin sannan ta saka ta ɗebi wasu ta kai walk-in closet ɗin dake bedroom ɗin Yaseer. Bayan sun gama da wannan suka yi sallan azahar suka wuce kitchen suma suka fitar da abubuwan amfani da suka jera a ciki da saman cabinet suka shirya kan dining ma aka jera duk wani abun bukata irin su sugar, table salt, madara da jam da butter da sauran su, sauran su cereal kuma aka jera cikin drawers din console ɗin wurin.
Karfe uku suka gama Aunty Zeenat bata tafi ba saida ta saka Reina ta sake wanka ta taimaka mata ta shirya tayi kyau tana zuba ƙamshin khumran Bakhoor by Seemah sannan tayi mata sallama Yaseer ya saka driver ya maida ita har gida.
Sun yi tunanin shikkenan kuma yanzu zasu samu lokacin juna saidai yana dawowa a masallacin ƙofar gidan shi, bai samu shiga ciki ba sai ga motocin ƴan jama'are wai sun zo musu sallama za su wuce gobe da safe.
Suka shiga gidan yana biye da su kan kace mene hayaniya ya cika ko ina. Reina ta fito suka gaisa ta ɗauki basket ɗin abincin su da suka zo dashi daga gidan umma ta haura dashi sama sannan ta ɗebo musu kayan tsaraba su cincin da dublan wanda Aunty Zeenat ta gwada mata yanda aka ajiye, harda su pepper meat da su alkaki ta cika musu gaban su dashi ga juice ai kuwa suka samu wurin zama basu tashi tafiya ba sai da aka fara kiran sallan Isha.
Daɗin abun ma basu tafi ba saida suka tattara mata parlon tass har banɗakin da suka yi amfani dashi saida suka wanke mata don haka gyara zaman throw pillows ɗin kan kujeran kawai tayi ta kunna burner ta saka turaren cotton daga cikin VIP diamond package ɗinta don ya ɗauki idanunta sosai, ga khumran da tayi amfani dashi har yanzu tana jin ƙamshin sa a jikinta kaman yanzun ta shafa.
Kafin Yaseer ya dawo daga masallaci ƙamshi ya kaure ko ina. Itama tana idar da sallan ta fito ta saka musu abinci suka ci suka koma parlon shi bayan sun tattara wurin sun kashe wutan bangaren ta baki ɗaya, domin ya sanar da ita yau a can zasu kwana.
A parlour suka fara zama, suka kunna TV yana ɓaɓatu tana kwance a jikin shi suna hira har wuraren ƙarfe 11 idanunta suka fara mata nauyi, ganin ta fara gyangyaɗi ya kashe TVn da wutan ya sunkuce ta suka wuce uwar ɗaka.
a ƙofar bathroom ya ajiyeta ta shiga ta wanke baki sannan ya tsaya duba mata rigan barci a closet ɗin.
Ruwan da ta watsa ya saka ta wartsakewa. Ta rasa tsakanin bathrobe da towel wanne zata iya sakawa ta fita dashi tunda bata shigo da kayan da zata sake cikin toilet ɗin ba.
Ganin bathrobe ɗin ya ɗan fi tsayi da kuma rufe jiki da kyau ta saka shi ta fito, tana takowa kaman mara gaskiya.
Yana zaune a gadon hankalin shi na kan wayan shi ga ɓacin rai da ya lulluɓe shi na abinda yake gani. Wasu mutane ne suke comment a kan hotunan nan dake yawo har yanzu a ƙasan hotunan bikin shi, shine Muhammad ya kira ya sanar dashi yake dubawa.
Motsin ta da yaji ya saka shi ɗagowa idanun shi ya fara sauƙa a kan santala-santalan kafafuwan ta don bathrobe ɗin ko guiwa bai ƙarasa ba.
Lokaci ɗaya ya saki wata kasalalliyar murmushi bacin ran shi yana yayewa, ya kashe wayan ya ajiye ya naɗe hannun shi a bayan kai yana kallonta, sai taji kaman ta juya ta koma banɗakin.
Sai a lokacin idanunta suka sauƙa a kan baƙin nightwears dake shimfiɗe a bakin gadon ta ƙarasa ta ɗauka da sauri ta koma bathroom ɗin ta rufe ta tsaya kallon kayan kafin ta saka.
Na yau ma yana da dogon wando amma yadin wani yala-yala haka, tsaf za'a iya ganin undies ɗin mutum ta jiki idan ya saka kala mai haske, ga rigan hannun vest gare shi sai akwai wani mai dogon hannu kuma ya sauka har cinya da zata iya ɗaurawa a kai.
Sakawa tayi ta tsaya tana kallon kanta a madubi, ita yanzu sai ta fita gaban yaya Yaseer da wa'innan kayan? Ko dayake ba shi ya siya kuma ya zaɓo mata ta saka ba? Ita nata wanne a ciki? Amma dai abin da kunya wlh.
Ta cigaba da ayyana abubuwa a ranta har saida taji yayi knocking a ƙofar bathroom ɗin. "Umry, I need to wash up also" ya faɗa a jikin ƙofar.
Da ƙyar ta yi ƙoƙarin tattaro ƙwarin guiwarta ta fito, ya kalleta tun daga sama har ƙasa ya saki murmushi. "You look hot!" yace yana kashe mata ido ɗaya. "Kin yi kyau sosai wifey" bata iya amsawa ba ta bashi hanya ya shiga ta ƙarasa gaban madubi ta fara shirin kwanciya, kulecham ta shafa da sauran kayan ƙamshi sannan ta nemi hulan da zai tafi da kayan ta saka a kanta ta kwanta lokacin da Yaseer ya fito cikin dogon wando kawai.
Tayi saurin rintse idanu lokaci da idanunta suka sauƙa a kirjin shi da babu riga, tana fatan kafin ya ƙaraso barci yayi mata babban sata amma tana ji ya shafa su turare ya kashe wutan ɗakin kana ya nufo gadon shima ya kashe lamps tunda barcin ƙarya zata yi bayan ya kamata tana kallon shi.
.
.
2:24am
Bayan ta sha faransanci, larabci da chinanci daga ƙarshe dai ganin bata numfashi Yaseer ya samu harshen Hausa da turanci suka dawo mishi tunda ya kashe musu ƴa!. ya shiga bubbuga fuskar ta da kiran sunan ta na ainihi. "Hafsat... Hafsat.. Reina! Open your eyes please, ki buɗe idanun ki kalle ni...."
*Yaseer*
Idan ya kasance kana riƙe da gaba ɗaya duniyar ka a cikin tafin hannun ka, ɗaɗin ka samu ka mallake shi daga ƙarshe zaka ji ko kuma tsoron kai da kanka zaka iya zama sanadin da zaka rasa shi? A halin yanzu ya gagara fayyacewa.
Akwai abubuwa da yawa da zai iya mata a halin yanzu sai dai tunanin komai ya gagara kama kan shi. Kaman yanda yana da sani a kan cewa tana hyperventilating idan ta samu panic attack shiyasa yaso ɗaga mata ƙafa ya bita a hankali ba wai don hakan jiki da zuciyar shi suke so ba, amma a ƙarshe suka yi amfani da kusanci da suke da shi a yanzu da begenta da ya dulmuya a ciki suka mishi fin ƙarfi ya nemi tabbatar da soyayyar shi a gare ta.
".... Please Umry... Dan Allah" ya dagota ya rungume a jikin shi cikin matsanancin tashin hankali ya shiga kalle-kalle a cikin ɗakin mai ƙarancin haske wanda ya samu ƙari da na farin wata dake ratsowa ta ɓangaren da ya kasance na glass wanda bai gama zuge dark grey curtain ɗin shi ba, daga wurin kuma zaka iya hango yalwataccen garden dake ta bayan gidan.
Sai a lokacin hankalin shi ya sauƙa a kan wayan shi da ya ajiye a saman bedside drawer gefen lamp ɗin da ya kunna minti biyu da suka wuce amma bai lura da shi ba sai yanzu.