← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 117

Sashe 21

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanda zuciyar Aicha ya buga ya saka taci gaba da zuba ma kan ta stir fry ɗin nan don kada ta ɗago labarin zuciyar ta ya bayyana a kan fuskar ta Amma tana matsanancin son taga reaction ɗin Yaseer, taga yaya zuciyar shi ta amshi zancen.

Sai kuwa ya sauƙaƙa mata ta hanyar mayar wa Irfan amsar. "Daɗi na da kai baka da hankali"

"Da dai kun taimaka ma ƴan media don na lura sun fiku matsuwa"

Ya ɗaga ido ya harari Suhail, sai yayi saurin toshe bakin shi da wainar ƙoyin da ya yanko da fork ya ɗauke duban shi daga na Yaseer dake da kaifin da zasu iya masa rauni.

A kaikaice Saudat ta dubi Aicha, lokaci ɗaya duk ta shiga wani yanayi.
Saudatu a daɗe da fahimtar tana son ɗan ta amma shi ogan bayi ra'ayi, bata cusa mishi ita bane don kada ta lalata shaƙuwa da zumunci dake tsakanin su.

Haka ba wanda ya sake cewa komai suka fara cin abinci cikin shiru sai ƙaran karon cokali da plate lokacin da wayan Yaseer ya shiga vibration.

Ya kurɓi ruwa kana ya ɗaga da sallama.
"Yallaɓai abun ya samu, daman an bawa wani wanda bai cancanta bane amma mun yi bincike mun karɓo, har ma mun kira shi ya zo ya bada bayanan shi a tura masa"

Murmushi ya sake haɗe da numfashi "godiya nake, Allah ya saka da alkhairi "

"Haba yallaɓai, ka cancanci fiye da haka, abinda yafi haka wahala ma zamu yi maka in dai zamu iya"

Ya sake musu godiya yace zasu ji shi kafin ya katse wayar.

Miƙewa yayi yana Faɗin "fita ya kama ni, Darling I'll meet you in the office"

"Yayan mu 8 fa har ya wuce" ta faɗa tana duba agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannun ta.

"Wani abun gaggawa ne ya taso, I need to..."

Sallamar Muhammad ya katse shi, sai ya nuna ta da yatsa tare da nuna Muhammad.
"You and P.A can go ahead, zan tarar da ku in 30 minutes in Allah ya yarda"

"Muje tare kawai, in kai ka daga nan sai mu wuce, a kan ƙafa ta nake" ya faɗa yana wuce Yaseer ya tsuguna ya gaida Alhaji Kamal da Hajiya Saudat.

"Da dai ka bar shi ya tafin ka karya"

Muhammad ya girgiza kai yana murmushi. "A'a yanzu na karya kafin na fito Hajiya, Nagode"

Har kaman Yaseer zai ce Aicha ta turawa mutumin nan kuɗi sai ya fasa, duk abinda ya shafi Reina bayi son wani daga cikin familyn sa yana shiga ciki, kuma handling finances ɗin shi ba hurumin ta bane ba ma.

Yayi musu sallama suka bishi da addu'an tsari da nasara.

Key ɗin motar da ya karɓa a hannun drivern shi ya cilla ma Muhammad, sannan ya buɗe seat ɗin baya zai shiga.

"Alhajin Allah ba'a ɗauke ni aikin tuƙi ba don haka dawo gaba" cewar Muhammad.

Banza Yaseer yayi mishi ya matse a owners corner, daman gulma ne yasa yace zai bishi ɗin ma, tunda yana saka mishi ido a kan duk motsin shi.

Yayi ƙwafa ya rufe mishi marfin motar sannan ya zaga ya shiga mazaunin driver.

"Ina muka nufa?"

"Can gidan" ya amsa a taƙaice.

Muhammad ya gane don haka suka ɗauki hanya har fadaman mada gidan Hajiya Hauwa.
Daga tsallake suka yi parking a ɗan gefe, ya ciro MacBook pro ɗin shi yana ɗan rage wasu abun har motar Uncle B ya ƙaraso aka buɗe mishi gate ya shiga gidan, cann sai gashi ya fito babu jimawa, sannan bayan ƴan mintuna ta tako ta Fito.

Ta tako tare da zuciyar shi wanda ke bugawa da yanayin tafiyar ta.
Tana tafe hannun ta na fuska tana risgan kuka kaman ranta zai fita.

Sai ya ji bai kyauta ba.
Kaman ya dawo mata da abin da take kukan rashin sa.

Ya ɗauke kai don bayi son ganin kukan ta, yaci gaba da danne-danne a MacBook ɗin shi amma zuciyar shi yaƙi take yi dashi ya ɗago ya cigaba da kallon ta koma yaje ya rarrashe ta.

"Yanzu kaji daɗi da ka raba ta dashi?" Cewar Muhammad dake zaune a mazaunin driver yana kallon Yaseer dake seat ɗin baya ta cikin mirror.

"Kai baka ga ɓata mata rayuwa yake niman yi ba?"

"Ɓata mata rayuwa kamar yaya? Tun lokacin da muka fara bin su ko ka saka a bi maka bayan su ka taɓa ganin ya kai ta wani wurin da bai kamata ba?"

Ya rufe MacBook ɗin "wai kai ina ruwan ka ne? Dalla fita ka sama mata abun hawa kaga muna da abun yi a gaban mu" Muhammad ya girgiza kai, Yaseer yana da tunani da fahimta a kan dukkan lamari amma banda wanda ya shafi yarinyar nan, shi yanzu har ya daina bashi mamaki ma.

~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

56

~~~~~~~~~~
_You're born reaching for your mother's hands_
_Victim of your father's plans to rule the world_
~~~~~~~~~~

Gaba Muhammad yayi kafin ya saka hannu ma wani napep ya tsaya. "Yauwa barka dai, idan na baka 10k zaka iya kai wancan yarinyar Gubi Campus?"

Bai kalli yarinyar da ake faɗa mutum ce ko aljan ba yace "Da gudu ma!"

"A'a ku dai tafi a hankali. Kuma idan kun isa ka sama mata abun hawan makaranta a kai ta har gaban ajin da zata zana jarabawa" Ya ƙarasa yana miƙa mishi kuɗin da ya ƙirgo daga cikin wallet ɗin shi.

Hannu bibbiyu mai napep ya saka ya amsa yana faɗin "an gama oga, idan jarabawar ma kake so in rubuta mata zan ƙoƙarta"

Anya Idan ya bar Reina da wannan ɗan rawan kan zasu shirya da Yaseer?.

Ya harare shi, "kayi abinda aka saka ka kawai".

"Toh oga"

"Bani numbern wayan ka"

Ya karanto mishi Muhammad ya ɗauka, sannan ya matsa baya ya ɗauki numbern jikin abun hawan.
"Har ku isa kada ka kuskura kayi mata magana, kuma Idan wani abu ya same ta hukuma ne zata raba mu."

A kan dubu goma dai duk wannan mai sauƙi ne don haka ya gyaɗa kai. "Ba za'a samu matsala ba oga"

Muhammad yayi mishi nuni da Reina da ta ɗan yi nisa da tafiya bata fasa kukan ba, ya tada napep ɗin ya ƙarasa wurin ta.

"Hajiya shiga mu tafi" mai napep yace da ita, amma ɗamarar tafiyar kilomita 16 da rabi da taci yasa ta cigaba da tafiyan ta.

Da sassarfa Muhammad ya ƙarasa ya sha gaban ta "Ki shiga Please, idan ba haka ba zaki yi missing exams" hannun ta sauƙe ta zuba mishi idanun ta da suka yi luhu-luhu.

"Shit!" Yaseer ya furta daga yanda yake kallon su, tare da dunƙule hannu cikin ɓacin rai yana jin kaman ya ɓalle marfin motar ya fita ya janye Muhammad daga gaban ta.

Bata yi musu wa Muhammad ba ta shiga cikin napep ɗin ganin yau aljanin dake bibiyar ta ya ƙare ya bayyana kan shi.

Sai da yaga sun bar wurin kafin ya tsallako ya dawo wurin da motar su yake ya shiga. Ya sani abinda yayi dole sai Yaseer yayi magana, kuma bai bashi kunya ba ya fara magana cikin kwantacciyar murya amma kana ji ka san ran shi a ɓace yake.

"What the hell is wrong with you? Yaya zaka gwada mata fuskar ka? Daman ka biyo ni ne ka warware min aiki?"

"Ko da naji, ashe taurin kan ku iri ɗaya. Idan taga fuska ta ma ta san ni ne? Ko baka ga muna niman rasa lokacin abubuwa masu muhimmanci bane saboda ita?" Da faɗar haka ya tada motar suka kama hanya.

Yaseer bai sake cewa komai ba amma idan duba Reina ne daga yau ya daina zuwa da Muhammad na farkon ma ya rasa yanda zai yi ne, lokacin bayi kusa kuma bayi da wasu amintattu a Nigeria shiyasa ya ɗaura shi a kan lamarin ta.

.....

"Kin ga Allah yayi mana maganin munafuka, da ikon shi kuma kafin Bilal ya dawo zan san yanda zan yi da ita, ba zai dawo ya same ta a cikin gidan nan ba"

"Ni banda zubar da girma irin na Uncle Bilal ma mai zai yi da wannan abun? Yarinya tana tafe kamar one sai tsayi kaman daren Sallah"

Hajiya Hauwa ta taɓe baki "jaraba irin na ɗa namiji fah? Wani ko sarauniyar kyau na duniya ya ajiye a gidan shi sai ya zaga wurin baiwar ta, amma wanda ya rabu da balarabiyar usuli ko baƙar fata yake son Aure sai ya ƙare a jikin wannan ƴar tsanar?"

Zahra ta cigaba da duba hotunan shafin Yaseer wanda yawanci na kayan sayarwa ne sai wanda yake ma designer brands tallen tufafi, kama daga Babban riga, kaftani, huluna, Suits da takalma har da ƙananun kaya da kayan training. Duk wanda taga kuɗin shi a caption kuwa sai ta ja dogon numfashi, don hulan da ta gani mai arha wai ana sale an fitar dashi 30% off shine na dubu ɗari biyar. Wani ɗan banzan sweat shirt da wandon shi ma miliyan har da rabi sai dai yanda ya zauna a jikin Yaseer yayi wani ɗanyen kyau idan ace tana da kuɗin tsaff zata cire ta siya.

Shiga comment section tayi bata damu da daɗewa da ɗaura hoton da aka yi ba, cikin harshen turanci ta rubuta 'Duk tsadar kayan basu kai mai ita haɗuwa ba' har da jan heart a ƙarshe sai taga ta bada kanta da yawa ta goge heart ɗin kana ta tayi posting comment ɗin sannan ta ɗago ta dubi mahaifiyar ta da itama nata wayar take dannawa tana sanar da Alhaji Salisu tafiyar Uncle B ta saƙo.
"Kin san makira ce yarinyar nan umma kina kallon ta. Idan tafi haka Allah kaɗai ya san mai zata yi kuma"

Hajiya Hauwa ta ajiye wayan bayan saƙon ya tafi ta gyara zama "Ai shiyasa da kin samu wani ya fito zan lallaɓa abban ku a samu wani a jona masa ita kafin zaman gida na ma ta hana ni tunda yanzu ta shiga tsakani na da uba na"
Chapter 21 · 0% Book details