Sashe 38
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Mutum ɗan uwanka musulmi har zai koma ga Allah ka ƙi ka sada zumuncin ka na ƙarshe a gareshi saboda wani banzan ra'ayi? Ko me yayi maka ba Allah ya karɓi abun shi ba dai Yanzu? Sai me ya rage kuma? Ashe mutuwar shi ba ishara bane a gareka da komai na duniyar nan ƙayyadadde ne kuma mai wucewa? Toh wallahi idan baka je ka raka shi har makwancin shi ba zaka ga ɓacin rai na, mummunan ɓacin rai nake faɗa maka"
Ko wurin kwana bayi da shi a Garin Bauchi amma haka ya yanke shawarar ya zauna, a massalacin da yayi sallan isha ya zauna har ƙarfe tara, idan ba kulle masallacin zasu yi ba sai ya kwana a can.
Ƙarfe 10 kiran Alaji Abdou ya shigo wayan shi, yayi mamakin yanda ya samu numbern shi da yayi masa bayanin kan shi, sannan yayi masa maganganun da ya gagara musawa lokacin da ya buƙaci ganin shi.
Ya tambayi Kamal a ina yake lokacin da yaji cewa yana cikin garin ma, bayan mintuna kaman 17 sai ga mota ya zo ɗaukan shi. Haka ya shiga suka kama hanya sai gashi a gidan Alhaji Tahir, wanda a yanzu ya daina ɗaukan idanu kaman da, ga gini nan har gini babu abinda ya same shi amma gyara babu, fentin gidan har ɓaɓɓakewa yayi, hasken da ya wadaci ko ina ma a yanzu sai kaɗan.
Har ɗakin da gawar Alhaji Tahir yake kwance aka shigar da shi, ya samu Alhaji Abdou riƙe da tasbaha yana masa addu'a.
"Ka gani halin da yake ciki. Duk wani abinda yake taƙama dashi ka ga ƙarshen sa? Ya riga mu tafiya don ya riga mu amsar hisabin sa ba don ya riga mu gaggawa ba ko dan mun yi jinkiri"
Kamal ya kalli makaran da aka rufe da zani, wai Alhaji Tahir dake yawo cikin fantsama fantsaman motoci ne kwance a nan.
"Idan da hali ku yafe mishi, kuyi mishi taimakon haɗuwa da Ubangiji ba tare da nauyin hakkin ku ba. Nayi kuskuren barin shi da halin shi, aboki na gari kamata yayi ya gyara maka kuskuren ka koda baka so ba, amma bani da shaidar da zan yi hakan sai yau da ya bayyana min komai, ya yanke hukuncin bayyana ma hukuma ma amma kwanan ya ƙare, sai dai ni zan tsaya na gyara komai alƙawari ne nayi maka zan fitar da Yaseer in wanke shi."
Shiru Kamal yayi yana kallon gawar. Shikkenan duk wannan ɗagawar, duk wannan ɗaukakar, duk wannan dukiyar! Shima ƙasa za'a tona a bisine shi kaman kowa.
"Allah ya yafe man..." Dakatawa yayi ganin kaman gawan ya motsa, to ko dai gizo idanun shi suke mishi?.
~~~~~~
Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.
*Seemahwrites ✨*
69
Ɗagowa yayi zai yi nuni ma Alaji Abdou amma shima idanun shi yana wurin, kuma daga yanayin fuskar shi ya gane shima yaga Abinda ya gani.
Kamal ya buɗe baki zai yi magana Alaji Abdou ya saka yatsa a baki alamar yayi shiru yana girgiza masa kai.
Ya ƙarasa a hankali ya buɗe ƙofa ya leƙa don tabbatar da babu kowa a kusa kafin ya dawo ciki ya ɗaga waya ya shiga niman yanda zasu yi.
Lokacin suna tsaka da waya Alhaji Tahir ya gamu da hatsarin shiyasa bai yi jinkirin tasowa daga Niger ba bayan katsewar wayan da isowar shi sai ya samu labarin wai shi da drivern shi duk sun cika, amma kasancewar yammaci sai yayi kwanan keso, kuma cikin ƴan uwan shi aka rasa wanda zai iya kwana dashi, bayi raba ɗayan biyu da saka hannun su a abinda ya same shi, domin ya feɗe masa biri har wutsiya tsakanin shi da Alhaji Salisu, har da kalolin barazanar da yake mishi.
"Shikkenan! Shikkenan zasu kashe ni, innalillahi wa inna ilaihirrajiun.... " Shine kalaman Alhaji Tahir na ƙarshe sai ƙaran karon mota Alaji Abdou yaji sai kuma wayar ta tsinke.
Likita amintacce ya fara kira, ya tabbatar musu akwai rai a jikin Alhaji Tahir dogon suma yayi amma yana cikin mayuwacin hali, dole a san yanda za'a yi a fitar da shi daga gidan cikin daren zuwa asibiti don bashi taimakon gaggawa.
Haka cikin taletainin dare bayan kowa ya yada kafaɗa suka fita samo wani gawan da za'a musanya da Alhaji Tahir ɗin a mortuary.
Sun kwatanta samun wanda ƙirar su ya kusan zama ɗaya, shima hatsari yayi kuma ba'a samu ƴan uwan shi ba, cikin hukuncin Ubangiji kawai suka samu damar sauya gawan nan ba tare da kowa ya lura ba, dukda ma Alhaji Tahir ɗin kaman mara gata, babu wasu na jikin sa a kusa da shi.
Kamal da likita su suka tafi da Alhaji Tahir clinic ɗin likitan don bai isa kai shi babban asibiti ayi aikin a sirrance ba, yanzu ma kasada kawai yayi.
Da taimakon tsirarun nurses suka samu suka tsayar da internal bleeding ga fractures da ya samu har bayan asuba suna kan shi.
Kamal ya bar shi a wurin ya koma wurin alaji Abdou domin suyi gaggawar wanka ma wancan gawar su naɗe ta kafin a fahimci halin da ake ciki.
Babu wanda ya zargi komai aka sallaci gawa aka kai shi makwanci kafin suka koma wurin Alhaji Tahir suka samu an gama masa abinda zasu iya Amma yana buƙatar a duba shi a babban asibiti domin akwai buguwa a kan shi sosai da yake buƙatar ayi CT koma MRI scan a duba ko yana buƙatar aiki a ƙwaƙwalwa.
Ganin kwana biyu ta wuce Alhaji Tahir bai farka ba Alaji Abdou ya buƙaci Kamal ya biyo shi su fitar da shi waje ayi mishi jinya shi kuma zai dinga biyan shi ko nawa yace har ya warke, domin a yanzu da shi kaɗai ya yarda.
Girgiza kai Kamal yayi bayan yaji bayanin Alaji Abdou, "a gaskiya albarkacin daraja ta rai da musulunci ya saka har aka kawo wannan gaɓar da ni, amma nima fama da kaina nake yanzu, ina da iyalai wanda suka dogara dani sai in tsallake su in tafi jinyar wanda bai san darajata ba bani da ƙima a idanun shi. Yanzu haka ma Wallahi kun takura ni, amma batun in bar Bauchi ga Yaseer na garƙame a nan zancen banza ne."
Amsar da ya bawa Alaji Abdou kenan.
Alƙawuran da ya ɗauka mishi a lokacin Musamman a kan ingancin rayuwar Yaseer da sauran ƴan uwan shi ya saka zuwa maghriba sai gasu a ƙofar gidan goggo Halime sun kawo Alhaji Tahir zasu ɓoye shi a nan har Alaji Abdou ya gama musu shirin tafiya baki ɗayan su bayan an fito da Yaseer.
Ga Tahir nan a jama'are, jama'aren nan da yake musa kasancewar shi tushen sa yana ganin kaman wani ƙasƙanci ne, gashi da ya gama yawo yaga duniya jama'aren ne ta amshe shi.
Da safe Kamal ya koma ya ziyarci Yaseer ya sanar dashi halin da ake ciki, amma bai faɗa mishi maganar fitar da shi da sauran alƙawuran Alaji Abdou ba gudun kada ya saka rai abu kuma yazo bai yiwu ba.
A can bangaren kuma sun yi shirin dafe dukiya tunda giwa ta faɗi, aka tada rikici a kan riƙon yaran Tahir ɗin yanda zasu kwashe abinda aka bar musu na gado. Tashi ɗaya masu bin shi bashi suka fara fitowa, daga bankuna har mutanen da ya ranci kuɗi a hannun su kuma kowa gashi ya zo da shaida.
Aka yi gwanjon shares ɗin shi na Tk Kingdom aka biya su, still su Alhaji Kalabu basu haƙura da sauran Abinda ya rage ba, ga kuma properties da suke da tabbacin yana da su bila adadin.
sai dai fitowan mutanen Alhaji Salisu masu kuɗin ruwan nan ya rusa komai, sannan har shi takardan da Alhaji Tahir ya saka hannu ba shi suka kawo ba, Alhaji Salisu ya ƙara a kai da sunan shi shiyasa ya yanke shawarar raba shi da duniya domin bai san ta ina zai fara biyan kuɗin ba sai dai ya ƙare rayuwar shi a kurkuku, amma Idan Tahir bayi raye dole nauyi ya hau kan shi.
Haka suka zo suka ƙwace komai har gidan da yayi rayuwa da iyalinsa aka saka a kasuwa ko rabin kuɗi bai kai ba. Cikin kwanaki bakwai mai dukiyan da bai san yawan shi ba ya dawo bayi da komai bayan takardun kadarorin da ya siya ma Reina da riban da mayaudaran nan suka fara bashi har ya danƙa amanar shi a hannun Alaji Abdou amma ya watsa mishi takardun cikin fushi yayi tafiyar sa.
Alhaji Tahir bai yi zuciya ba a lokacin, haka ya haɗa kan takardun ya tura ma Alaji Abdou har Nijar.
A kwana na takwas ne bayan taro ya watse suka zauna muhawaran waye zai riƙe Reina, tunda ita Maama su Ummi sun karɓe ta kuma da kunya yanzu su maida musu da ita bayan watsewar a suka yi a kan riƙon yaran, har ƙaddara ta ƙayyade mata zaman gidan Hauwa da Salisu na tsawon shekaru 7.
A ɓangaren Yaseer bayan zuwan da Kamal ya sake yi ya kai mishi ɗan abubuwa har yayi suɓutan bakin tambayar jikin Alhaji Tahir, washegari Sai kawai gani yayi an zo an kira shi daga cell room ɗin su, sannan aka ce mishi ya tafi anyi belin shi.
A waje yaci karo da mahaifin shi, Alaji Abdou
Sai kuma lawyern da ya shige musu gaba.
Kamal sai kuka yake yi a hanya Amma Yaseer hanya yake bi da idanu har suka isa jama'are yanda mutane suka yi dandazo ana jiran isowar su.
An sha kuka kam kada Saudat ma taji labari domin saida aka yi ta sheƙa mata inhaler, Amma idanun shi a bushe ƙarau sai ya koma mai rarrashi kawai. Ya gagara gaskata cewa wai shine yau yake yawo a waje a matsayin mai ƴanci ba a keji ba, ga abinci lafiyayye mai daɗi da rabon shi da cin irin shi har ya manta, bai daɗa ƙaryata lamarin ba har sai da ya hau gado, barci yace mishi ɗauke ni a hankali, duk yanda ya juya ya mirgina haka asuba ta iso ta same shi bai rintsa ko nan da can ba.
Gari yana wayewa kuma aka fara shirin tafiya.