Sashe 102
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nuni yayi mata ta kai nata hannun tana taɓawa sannan ta ciro shi ta ajiye a gaban teburin. Sai tayi ɗan murmushin yaƙe tana godiya ta ɗauki mug ɗin Black coffee da tayi order daga baya ta kai baki.
"Muyi hira to, ki bani labarin kan ki sai in baki nawa"
Cire mug ɗin tayi daga bakinta tana tambayan "Ni ina da wani labari ne?. Iyaye na ƴan Niger ne nima haka, kasuwanci da zumunci ya kawo mu Nigeria. Amma kace mahaifiyar ka tana auren Sarkin Damagaram, kai kuma ga ka a Bold family, ta yaya? Jadda ba kakar ka bace?"
"Kaka ta ce, ita ta haifi mahaifina wanda Allah yayi masa rasuwa shekaru 18 da suka wuce tare da ƙanne na biyu masu shekaru goma da sha biyar a hatsarin jirgin sama lokacin tana da Cikin ƙanwata Asal, ni kuma shekaru na 17 a lokacin."
Kallon tausayi ta bishi da shi tana mayar da mug ɗin saman table ta ajiye "Allah yayi musu rahama, I'm very sorry for asking"
"No it's okay, kina da damar sani" yace cikin sakin fuska kaman labari mai daɗi yake bata. Kana ya ɗaura da. "A lokacin ta shiga tashin hankali sosai don sai feɗe ta aka yi aka ciro Asal kuma ko shayar da ita da kanta bata iya ba, hakan yasa familyn mahaifina suka haƙura suka barta ta koma Niamey hannun Auntyn ta da ta taso a wurinta don ta samu nutsuwa idan tayi nisa da abinda zai cigaba da tuna mata su. Babu daɗewa ta buƙaci nima in koma hannun ta har tayi aure a Damagaram ina tare da ita. Shekaru na 27 kuma Allah ya haɗa ni da matar da na aura a Nigeria, saidai zaman namu ba mai tsawo bane itama a haihuwa Allah ya karɓi abun shi. Yarinyar da kika gani tare da Jadda ƴata ce. Sunan ta Najma shekarun ta shida da rabi kenan."
Aicha ko motsin kirki bata yi, idanunta ke kyallin ruwan hawaye a kan shi zuciyar ta kuma tana harsaso irin yanayin da ya shiga da wannan manyan rashi ba ɗaya ba biyu ba kuma ba uku ba, tana haɗa ciwon da raɗadin da ita da ta rasa guda ɗaya mafi girma, amma ta sani raɗaɗin nashi ya zarce nata tunda ita ga nata mahaifin ya samo mata wata uwa mai ƙaunar ta amma tashi mahaifiyar duk da yunƙurin ta haka dole ya dawo wurin dangin mahaifin sa.
"Akwai wani abun da kike son ki sani bayan wannan?"
Ta ja dogon numfashi tana fifita idanunta da hannunta kada ta zubar da hawaye a gaban shi gobe ya faɗa mata wani abun tazo tana nadama.
Ta gyara zama tare da girgiza kai.
"Ni kuma akwai abinda nake son sani." Yace da ita.
Ta ɗan kalle shi sannan ta amsa da "ina jin ka"
Tambayar da ya san bata yi tsammanin jin shi ba ya jefa mata "Kina da burin irin namijin da kike son aure?"
Yaseer. Da son shi ta girma ta zama irin macen da zai yi sha'awar rayuwa da ita, Saboda bata taɓa tunanin wani qualities ne a wurin shi take so da zata iya samu a wurin wani namijin ba, shi ɗin ɗungurungum take so amma sai ya kasance abinda ta zamo saboda shi yana burge shi ne ba jan ra'ayin shi ba. Yana son ya ga mace mai ƙarfin zuciya, jajirtacciya kuma ta tsaya da ƙafafuwanta, yana birge shi. amma sai wanda duniyarta ta kusan ruftawa da ita ta ɗauki hankali da zuciyar shi.
"Aysh." Ya kira ganin kaman ya jefa ta wata duniyar.
Ta dube shi da idanu a cikin zuciyarta tana ayyana 'kusan haka shima yake kira na, don Allah ka bari'. Amma kwarjinin shi ya saka ba zata iya furta mishi ba.
"Okay bari na gyara tambayan. Idan nace ina son ki zaki amince da ni?"
Ta ware ido kaman wanda ya rikiɗe ya canza suffa a gabanta. Suka tsaya kallon-kallo na tsawon mintuna kafin can ta fashe da dariya tana kare bakinta da hannu.
"Ban san ashe kana da abin dariya ba na ɗauka aiki kawai ka iya, yauwa sai gwada izza da ƙasaita, although shi na rayuwan gidan sarauta ne"
"So kike yi ki kira ni da agola?"
girgiza hannu tayi tace "lala, ba gashi ka dawo gida ba?"
"Then ba da wasa nake yi ba, ko dan in baki dariya, ina son in san ra'ayin ki game da ni"
Ta sake shiru tana nutsa zancen shi a zuciyar ta, ba don babu kalolin mazan da suke bayyana suna ra'ayinta ba sai dai duk cikin su babu ɗan rainin hankali kaman wannan, ya tsaya mata a wuya kaman ƙaya sannan yanzu kuma yazo mata da zancen soyayya.
"Shekaran jiya fa muka fara haɗuwa" ta tuna mishi, ga haɗuwan ma ba mai daɗi ba, basu yi zaman lafiya ba sai yau shima da tursasawa.
Yayi murmushi don ya san mai take tunani "Ke dai kika fara gani na shekaran jiya Amma mun haɗu a lokuta da dama"
Kafin ta kai ga tambayan shi 'A ina' kaman yanda yayi tsammani sai ya dubi agogon tsintsiyan hannun shi yana faɗin. "Lokaci ya tafi sosai, we should get going" ya haɗa kan takardun ya mayar cikin manilla envelope da suka fitar da shi sannan ya miƙe a kan dugadugan shi yana jiran itama ta miƙe su tafi.
Sun isa mashigar hotel ɗin lokaci karfe 11 da ashirin da 3.
"Sai da safe" tace zata fita, ba zata yi mishi godiya da maido ta da yayi lami lafiya ba tunda fitan nashi ne dama.
"Ki shiga ki haɗo kayan ki ina jira kizo mu tafi"
"Ina?" Ta sake kallon lokaci a fuskar wayanta bayan Ta tambaya.
"Ba zaki cigaba da zama a hotel ba, it's not safe"
"Ssoo?" Ta ja kalmar don ya jita da kyau.
"Zan kai ki inda zaki samu kariya kuma a kula da ke"
This man is so weird. Ta faɗa a ranta daman maganan shi da tayi a zuciyarta yau babu yawa, toh ta ƙara. "Okay ina zuwa" tace dashi tana saka ƙafarta zata fita daga motar, idan ta koma tayi kwanciyar ta ya gaji da jira zai tafi.
"Idan baki sauƙo ba zan haura ɗakin in same ki, and I'm serious" ko bai faɗa ba babu alamun wasa a fuskar shi.
"Ina dai ba gidan Jadda ba?" Ta fara sadakarwa.
Ya ɗan saki fuska yana faɗin "ba gidan Jadda ba, zan kai ki inda za'a fita kula da ke."
"Shikkenan, ka jira ni zan dawo"
Ta ɗauki lokaci tana haɗa kayan da ba wani yawa suke da shi ba, don ma dai ta san yanayi ne irin na business trip ko yaushe ƙarin kwana zai iya kama ka ko idan aka gagara daidaitawa, shiyasa take ɗiban extra na kaya a koda yaushe saboda haka.
Ta linke komai tass ta jera shi yanda ya dace sannan tayi checking out ta fito waje janye da akwatin. Jikinta ya bata ya tafi tunda duk lokacin da ta ɗauka ko sau ɗaya bai kira ta ba, amma yana ganin fitowar ta ya kunna mota ya ƙaraso inda take tsaye yayi parking ya fito ya karɓi akwatin ya saka mata a booth ita kuma ta koma gaban motar suka ɗau hanya.
Kaman wanda aka ɗinke wa baki haka ta gagara tambayan wurin wanen shi zai kaita? Tafiyan minti 20 ya kawo su gate ɗin wani gida , babu kowa a bakin gate amma yana registering plate numbern shi taga ya buɗe da kan shi don haka ta dube shi.
"Gidan waye wannan"
"Gida na ne" ya bata amsa yana kutsa kan motan ciki.
Ya tabbata mutumin nan ɗan iska ne.
Tunda cemata yayi matar shi ta rasu kuma bai ce mata ya ƙara aure ba balle tace wurin amaryar shi ya kawota, koda ace labari ne bai kawo su kan gaɓar ba ma ba zama zata yi ba balle mata ta samu daman mata rashin mutunci, ita ta ɗauka gidan wata Auntyn shi haka zai kaita shiyasa ta yarda ta biyo shi.
"Gaskiya ka maida n..." Maganar ta ya katse ganin Asal tana ɗaga musu hannu da faffaɗan murmushi a kan fuskar ta. Gyara parking yayi ya kashe motar sannan budurwar ta ƙaraso da sauri ta buɗe mata ƙofa, yanda take murnan ganinta kaman sun saba, daman ranan ma itace ta rungume ta toh yauma haka ne.
Tana rungume da Asal ta dubi Rafeeq da kallon ƙarin bayani. "Idan na kai ki estate za'a saka miki ido, gwamma nan, Asal zata na taya ki zama" yace sannan ya ƙarasa booth ya ciro akwatin ta yayi hanyar ciki don haka Asal ma ta ja hannunta suka rufa mishi baya tana ɗaga idanu ta ƙarewa gidan kallo.
Gidan ba wani babba bane amma ko ita da tayi yawon duniya taga gidaje da dama wannan yayi mata matuƙa har tana adana tsarin a ƙwaƙwalwar ta irin shi Yaseer zai gina mata.
"Dakata!" Yace a lokacin da zata taka ƙafarta a kan mashigar gidan.
Tsayawa tayi da kafan a iska bata haura ba bata sauƙe ba tana duban shi. Sai yace "kiyi addu'a kinga babu macen da ta taɓa shiga gidan sai yau"
Sai ta juya ta kalli Asal, ita ba mace bace? Kuma kaman daga cikin gidan taga ta fito.
Asal tayi saurin cewa "Eh wlh Aunty, ki shiga da kafar dama ma saboda kinga mutanen ɓoye sun fi son baƙi"
Ita bata taɓa jin wannan zancen ba amma sai ta sauƙe ƙafan ta mayar da na dama ta taka tana ambatan sunan Allah. Ta bayan idonta Rafeeq yayi wa Asal murmushi tare da mata jinjina da hannu ta kashe masa ido ɗaya suka bi bayan Aicha da ta mace a kallon gida Asal na dariya ƙasa-ƙasa.
Master bedroom ɗin shi ya shigar da akwatin ta bai wani ƙara daɗewa ba ya tafi ya barsu domin ta sake da kyau bayan ya sanar da su duk abinda ya taso ko wanda babu su kira shi.