Sashe 108
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"ɗoki ne ya saka na ɗauka bayan shekaru bakwai salon bai barni ba, shine na samu reality check" ya mayar mata shima yana murmusawa, tare da zaran tissue a kwalin tsakiyar table ɗin ya saka a cikin hannunta da yake riƙe da shi "Aicha ina son ki, ina ƙaunar ki kuma zan riƙe amanar ki saboda Allah. I hope zaki buɗe mun zuciyar ki ko kaɗan ne ni kuma zan koya miki yanda zaki so ni cikin ƙanƙanin lokaci" ya ƙarasa yana sakin hannun ta samu ta kai shi fuskarta ta share sauran hawayenta.
Gyaɗa kai tayi tana murmushi "In sha Allah" da daɗi jin cewa itama wani yayi dakon sonta da gaskiya kaman yanda tayi na Yaseer koda bai kai shi tsawo ba, amma ya saka taji kaman itama tana da muhimmanci kuma akwai wata duniyar bayan wanda take ganin yana kewaye ne da Yaseer, zata iya farin ciki ko bayi tare da ita.
"Okay finish your coffee sai mu fita mu karya, you must be hungry"
"Coffee mai sanyi?" Ta tambaya tana taɓa jikin mug ɗin taji yanda ya huce, sannan ta kai shi bakinta.
Ya gyaɗa kai "Yeah, nima na san nayi magana da yawa."
Ta cire mug ɗin daga bakinta tana lashe laɓɓen ta kana tace "Har na kusa tambayan ka a ina ka samo wannan, ya cika min kunne"
Dariya mai sauti yayi tunawa da maganan da ya fara haɗa su kenan, daman ya san zai yi nasaran hana ta mantawa da shi. Wayan shi ya shiga ringing kafin ya sake magana.
"YK" yace lokacin da yaga sunan dake yawo a saman screen ɗin.
Miƙewa Aicha tayi tana faɗin "Bari naje na ɗauko mayafi na" bata kuma dawo wurin ba saida ya gama wayan ya fito parlor ya same ta zaune a gaban TV da ake gwada labarai a tashar aljazeerah. Ta saka mayafi harda takalmi mai kyau da tsini tana zaune ƙafarta ɗaya kan ɗaya ta fito kaman wata babban baƙuwa a taron manyan mata sai ɗaukan idanun shi take yi.
"Muje?" Ta tambaya tana duban shi, ya gyaɗa kai sau ɗaya.
Miƙewa tayi ya kashe TVn suka bar gidan a cikin motar shi.
Saboda su sha iska yasa ya zaɓi wuri mai ɗan nisa daga gidan su. Suna tafe yana ƙoƙarin yanda ba zai gundure ta da shiru ba, sai yake ƙara sanar da ita wasu abubuwan da bata tambaya ba yana kuma ƙoƙarin amsa mata wanda ta kai ga tambaya.
"..Yanzu kana nufin su Jadda sun san ni wacece lokacin da naje wurin ka?"
Gyaɗa kai Rafeeq yayi yanayin da yake ciki bayyane a saman fuskar shi.
"Shiyasa ashe za'a shigar da ni in sada zumunci, ashe kowa ya riga ya san ni nine ban san kowa ba. Ni kada ma suyi tunanin biyo ka nayi, amma ka yi musu bayanin abinda ya kawo ni ko?"
Ya ɗan juyo yana duban yanda duk ta shiga damuwa. "Ki kwantar da hankalin ki basu da matsala. Kuma sun yi farin cikin ganin ki yanda baki tsammani."
"Hmm, ba dole ba tunda ka zauna musu 6 years babu mata?"
Juyawa ya sake yi ya dube ta da murmushin da ya bayyana fararen haƙwaran shi, ya girgiza kai ganin kaman zancen zucin ta ne ya fito fili domin wani gefen daban take kallo ba shi ba.
Bai tanka ba taci gaba da cewa "Har da Asal ma?! Kace mata ido na idon ta tunda za'a haɗa baki da ita a yaudare ni"
"Ta ce in baki haƙuri"
"Ba wanin nan, ba zan haƙura ba, ido na idonta kawai"
Yanzu ma murmushi yayi mata kawai yana nima musu wurin parking.
Kashe motan yayi ya cire seatbelt yana gyara zama a cikin seat ɗin shi ya dube ta, tare da ɗan rankwafowa kaman da wanda wani ya kasa kunne yake son jin abinda zai faɗa mata kafin cikin ƙasa da murya yace "Kin ɗaga komawan ki daga yau ina?"
Ɗan goge laɓɓen ta na ƙasa tayi da babban yatsar ta cikin rashin son kallon cikin idanu shi tana kallon man leɓɓen da ya shafu a yatsarta don ta fara hango inda ya nufa kuma ba zai yiwu ba. "Nayi missing ɗin jirgin yau sai daren talata wani zai tashi, jibi kenan"
"Ba zaki bari in gama aikin gaba na in ɗauki hutu mu tafi tare ba sai ayi bikin mu ɗiyanin, nima ina son ganin ki cikin shigan amare,"
Ɗage gira ɗaya tayi tana kallon ikon Allah, "Daman sir Rafeeq ana biki ne don a rako amarya ɗaki, kuma na riga da nazo da kaina babu amfani kenan."
"Still za'a rako ki, me zai hana? Amma muna buƙatar mu zauna tare kafin nan mu fahimci juna sosai." Ya riƙo hannun da ta sake kaiwa baki zata cigaba da share man leɓenta. "Ki bari yayi miki kyau."
"Aiki na fa, na riga da naci sati biyu a cikin hutu na, kuma ina son zuwa Niger kafin ya ƙare"
"Kin dawo Bold family Yanzu, YK su san nayi. So maganan tafiya Niger shima ba matsala bane" ya ɗauka bai iya ja'inja ba amma sai dai idan ba zasu yi dogon magana da Aicha ba.
"To..." Numfashin ta ne ya ɗauke idanunta suka ware kaman zasu faɗo ƙasa amma kalaman dake bakinta sun gagara fitowa saboda na Rafeeq dake kan su, hannun shi na zagawa zuwa bayan wuyanta domin ya ƙarawa kan shi ƙaimi har saida yayi nasarar sanya ta mayar da idanun ta lumshe tunda sun gagara faɗi ƙasa kafin a hankali ya janye fuskar shi daga nata idanun shi a kan lips ɗinta da kaman bai taɓa samun lip oil ba, tass ya shanye. ya jinjina kai "Cherry flavour, tasty"
Shikkenan ita kuma first kiss ɗinta a parking lot ɗin restaurant!. Buɗe idanunta tayi da ƙyar ta zuba masa tana ajiyan numfashi Amma kaman ba shi ba, ko dan shi ya riga da yabi masa jiki ne tunda wannan ba shine mishi karo na farko ba?.
"Idan muka je gida zamu ƙarasa maganan" yace yana gyara zaman shi ya buɗe ƙofar motar ya fita domin ya zaga ya buɗe mata. Ganin tana zaune kaman ta gagara motsawa har yanzu yace "ko muyi ordering to go?"
Sau ɗaya shima ta gyaɗa mishi kai ya rufe mata ƙofar motar ya juya ciki cike da nishaɗi, idanunta suna mishi rakiya.
.......
*Yaseer*
Waya ne maƙale a kunnen shi, Hannun shi a jikin zip ɗin bayan gown ɗin Reina dake zaune a gaban vanity table yana zuge mata ba tare da ya hana yatsar shi manuniya shafa gadon bayan a yayinda yake jan zip ɗin sama ba, ita kuwa sai noƙewa take yi domin tayar mata da tsikar jiki yake yi, kuma bata son tayi magana muryarta ya shiga cikin wayan shi mai muhimmanci.
Murmushi ya sake mata ta cikin mirror bayan ya gama ya juya yana faɗin "kusan komai ya gama shiryuwa Abbah, sannan abubuwa sun daidaita, zamu iya farawa yanzu a hankali kuma sai mu ƙarasa haɗa shaidu, amma ko a haka muka tsaya ma zamu yi Nasara in sha Allah".
Juyowa yayi ya dubi Reina dake rolling ɗin baƙin gyale a kanta bayan Abban ya faɗi wani abu sannan ya juya yana ƙara tafiya nesa da ita zuwa inda ya ajiye agogon shi, ya sauƙe murya yana amsawa da "Na haƙura Abbah, idan sai ita ce zata bada shaida Wallahi na haƙura. kawai zamu nemi wata hanyar koda ba zai yi mana sauri ba, daman ba gaggawa muke ba tunda kasuwar mu da ya taɓu ma har mun fara ƙoƙarin farfaɗo dashi. Daga nan ma wani deal ɗin zan je mu ƙara ƙullawa idan Allah ya saka da rabon mu." Ya ƙarasa yana ɗora baƙin agogon fata a hannun shi.
Magana kaɗan suka ƙara suka yi Sallama da Abbah ya feshe jikin shi da turare kana ya dawo jikin mirror yanda ya samu Reina ta gama da gyale tana mayar da bracelet ɗinta.
Gashi silver color ya dace da kayan jikinta, yau baƙin English gown ne a jikinta mai faɗi da dogon hannu, ta dauki takalmi da jaka duk baƙake, sai ta saka baƙin sunglasses. har suka isa kocatape mosque kafin ta cire gilashin daga idonta ta ɗaga shi zuwa saman kanta Yaseer ma ya cire nashi ya mayar cikin aljihun baƙin wandon suit ɗin shi wanda ya hada da baƙin button down shirt. Kafin suka shiga Masallacin mai ɗumbin Tarihi, musulman cikin wanda suka zo a ranar suka gabatar da nafila, su Reina ma aka kai su ɓangaren mata sauran suka cigaba da ɗaukan hotuna har suka idar suka fito sannan Yaseer ya riƙo hannunta suka cigaba da zagawa haraban Masallacin. Saida suka gabatar da sallan azahar suka bar wurin zuwa bakin teku dake can ƙasa, dalilin saka sunglasses ɗin kenan domin rana ke baza hasken ta a sararin samaniya amma yanayin wurin da sanyi.
Idanunta a kan sauran mutanen dake shawagin su a wurin, ya kawo inabi bakinta yana faɗin "Haa" sai ta juyo ta kalli inabin sannan ta dube shi. "Na ƙoshi wlh, mun ci abinci da yawa"
"Na sani, wannan fruit ne, ance you need it idan kuna yi"
Dariya tayi tace "idan muna mene wai?"
"Period" ya bata amsa.
"Wa yace?"
"Google, Research nayi" ya ƙarasa yana daga mata gira.
Sai ta murmusa ta buɗe bakinta tana karɓa, sannan ta gwada mishi wasu iyaye da suka zo da yaran su mata guda biyu tace "kalle su abin sha'awa bae, kaman Aunty da Daddy da ni da Maama, Allah sarki."
Matsowa jikinta yayi yana saƙalo hannun shi daga ta baya ya zagayeta suna kallon familyn dake nishaɗin su "Idan Allah yayi watarana sai kiga mun dawo da yaran mu"
"Ba biyu ba amma, ina son yaran mu su samu ƴan uwa kaman ku, bani son su taso da kaɗaici koda bayan bamu tare da su" tace tana juyawa domin suyi ido huɗu.
Ya ɗan tsaya yana kallonta sannan a tsanake yace "yara nawa kike so then?"
"Ko nawa, amma biyu yayi kaɗan, ina son inga da zuri'a mai girma a tsakanin mu yanda labarin soyayyar mu zai daɗe a doron duniya."