Sashe 77
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Uhmm hmm" Aunty Zeenat ta kasa kunne ta ji kanun labarai.
"Sai nayi mishi yaya hanya sai muka yi taɗi"
"Shi taɗin me kuka ce?"
Sai tayi kaman tana tunani kana tace "Na manta"
"Allah ya shirye ki" ta miƙe ta barta a wurin.
Babu jimawa ta dawo rike da kofi mai ɗauke da markaɗaɗɗen ruwan karas wanda aka sakawa ɗanyen citta, lemun zaƙi da na tsami kaɗan, aka markaɗa aka tace mata tana sha.
Dake akwai daɗi babu musu ta karɓa ta sha, Aunty Zeenat tana jaddada mata idan dai zata dinga haɗawa a kai a kai tana sha sau biyu zuwa uku a rana nan da sati biyu zata ga yanda fatar ta zai murje ya ƙara sheƙi, sannan kada tayi wasa da cin cucumber haɗe da dabino shima.
Hankalin ta na kan saƙon Yaseer da yake sanar da ita ya isa gida tare da godiyan tarban da ya samu ta amsa mata da toh, Aunty Zeenat ta girgiza kai kawai ta bar mata ɗakin don tayi shirin komawa gidan ta.
.
.
Shirin biki ya kankama a duka ɓangarorin, ba zaka ce ga na amarya ga na ango ba don ko ta ina ƙoƙarin gwangwaje duka biyun suke.
Kama daga kan Uban gayyan Yaseer wanda ke cikin hali na tsaka mai wuya don raɗe-raɗi mai kama da gaskiya dake yawo a kan shi ya taɓa kasuwancin shi sosai har ya jawo musu asaran da basu yi tsammani ba. Sannan mutane da yawa da suke aiki tare sun janye daga gare su gudun kada suma asaran ta shafe su bayan an ci riba tare.
Yayi imani cewa Allah mai azurtawa da hanawa zai iya karɓe duk abinda ya bashi lokaci ɗaya idan yaso kuma zai kasance mai godiya a koda yaushe tunda ba tsimi da dabarar shi bane suka bashi amma Tsoron shi ɗaya tawaya ya samu Dukiyar Reina da Alhaji Tahir. Yana tsoron ya gagara riƙe amanar da Alaji Abdou ya tsallake kowa ya ɗauka ya bashi.
Ya dai samu ya lallaɓa Aicha ta koma bakin aiki amma har yanzu bai bata gamsashshiyar amsa a kan kuɗirin ta ba, zai fi ya bari a ɗaura auren shi da Reina tukkunna. Dukda bai san ta ina zai fara tunkarar iyayen shi da nata da maganan ba, bayan a da an kawo mishi zancen firr yaƙi, kuma suka yarda suka bashi muradin shi, yanzu sai ya sake komawa?.
Saboda ya samu sauƙi ta wani wajen Abbah ya tsaya masa wajen ganin an kammala ginin shi, daman an riga da anyi har plaster da marbling kaɗan ya rage. Ummah kuma ita da Mariama ke siyayyan haɗaɗɗun kayan ɗaki ma Reina da haɗa lefe na gani na faɗa ma Yaseer sai kuma shirin yanda biki zai kasance wanda mutanen Jama'are suka shiga ciki dumu-dumu kuma sun ɗauke musu nauyi da yawa.
Alaji Abdou da Alhaji Tahir kuma sun mayar da hankali kan case ɗin da ake kan Shari'a na masu kuɗin nan. Zasu ja abun ne su samu har sai an bayyana komai a idanun duniya an yayata Jamal ya karɓi hukunci Musamman yanzu da wasu ke niman ɓata ma Yaseer suna a karo na biyu kafin su bari a kama Alhaji Salisu.
.....
A kan teburin sakatariyar Yaseer ta zuba takardun hannunta tana fitar da guntun numfashi tare da duban lokaci. "Gashi ki kaima yayanmu ki sanar da shi na tashi a aiki"
Sakatariyar ta miƙe tana mata bankawana tare da ɗiban takardun ta shigar masa a take.
Aicha kuma ta juya tana jin wani iri sanin cewa kusan kowa overtime yake aiki yanzu Saboda farfaɗo da darajar kamfanin koda ba zasu samu ƙarin biya a dalilin hakan ba.
Amma biyar ta wuce, lokacin da tayi alƙawarin kasancewa a tare da su ya cika sai gobe kuma don haka gida zata tafi ta huta ma ranta kada asaran yayi mata yawa.
Ta juya ta fita daga bulding ɗin zuwa wurin da ta ajiye motar ta tana luma hannu a cikin jakarta don ta ɗauko key sai ta fito da wayanta da ya ɗauki ruri a maimakon haka.
Har ga Allah ta ɗauka yaseer ne yake kiranta don ya lura kwana biyu bata zuwa office ɗin shi kai tsaye kuma tana gujewa duk wani abu da zai haɗa su amma sai taga baƙon number.
Kaman zata ajiye ta dai ɗauka tunda ta riga da ta ciro wayan, tayi picking ta maƙala a kunne ta cigaba da lalumen key ɗin mota.
"Aicha Abdou speaking" tace jin wanda ta kira ko ya kira basu da niyyar magana idan kuma suka bari ta samu abinda take nima kashewa zata yi.
"Bilal ne. Kina lafiya?"
Ta yamutsa fuska "wani Bilal?" Tana buɗe ƙofar motar ta wurga jakar ta a kujeran mai zaman banza sannan ta shiga ta kunna.
"Doctor Bilal saurayin Doll. Hafsatu da ta raba ki da Yaseer. Idan kina ganin kina da buƙatar ganawa ki same ni a dass park, na sama mana mafita" daga haka ya katse kiran tabi numbern da mamakin yanda aka yi ya san tana son Yaseer kafin yanda aka yi ya samu numbern ta. Ko dayake yanda shi Yaseer ɗin yake gwada mata ne ya saka take tunanin a sirrance take kayanta ashe kowa kallonta kawai yake.
.....
Idan kaga Reina a yanzu zaka yi mamakin yanda ta koma idan shaida ta bai yi maka wahala ba kenan. Sosai Ummi ta gyarata ta wanke ta tayi tass, ta murje, ta ƙara haske, ta tada komaɗa na kulawa da kuma kwanciyar hankali da take ciki ga shauƙin ƙauna dake ɗiban ta.
Biki sauran sati biyu Amma har baƙin nesa sun fara hallara don tallafawa da sauran shirye-shirye. Amarya Hafsatu Reina babu alamun kewan gida ko fargabar al'amarin dake gabanta a tattare da ita, kana kallon ta zaka ga wanda take cikin farin ciki zallah sannan ta saki jiki ne ana ta hidindimu da ita. Hatta ashoben da Yaseer yayi order masu Safina wanda aka cire na ƙawaye ita ta kwashe sauran wai ba za'a bawa wanda bata so ba tunda ita safinan ce kawai ƙawar ta sai kuma wanda ake mutunci a makaranta da cousins haka amma an kawo kusan ankon mutane 15 shine ta tattare sauran ta bawa Safina guda shida kawai ta raba musu, sai bayan biki tayi kyauta da sauran.
Yanzu kuma shirin kawo lefe ake yi kada ta zauna tayi ta yi ma mutane iyayi ya saka Ummi ta tura ta gidan su Safina taje ta ƙaraci wunin ta a can tunda yau ba ranar zuwa gidan Malama bane, daman a yammacin laraba da Alhamis ake zuwa kuma tana karatu ne ma matan aure sai ƴammatan da aka sakawa rana, yau kuma ta kama asabar.
"Ashe ƙaramar mara kunya kike don na ɗauka ma ke zaki karɓi kayan ki da kanki a buɗe a gani da ke."
"Toh ai na riga da na san abinda yake ciki don yawanci Umma sai ta turo min na zaɓa kafin a siya"
Ta amsa tana danna kiran Yaseer amma kafin ya tafi sunan 'Uncle Bilal' ya riga bayyana a saman screen ɗinta.
Saida gaban ta ya faɗi don wallahi ta manta da shi. Garin yaya ma har yanzu bata goge numbern ba? Sannan idan ta ɗauka yanzu mai zata ce mishi?
.....
*Aicha*
Tana ƙarasowa jikin motar shi da niyyar ta samu wurin parking ta fito sai taga ya kunna motar ya cigaba da tafiya.
Tsaki ta ja na Allah wadai da zuciyar ta tunda ita ta jawo ta ta kawo ta ba don tana da niyyar zuwa ba. Mai zata samu daga wurin mutumin da shima ya rasa soyayyar shi kaman ita? Har gwara ma ita a kan shi da ya riga ya kafa gwamnatin shi amma a ƙarshe aka kada shi.
Sai dai zuciyar ta tana ƙwaɗaita mata sanin wani mafita yake tafe da shi, kuma ta ina zai amfane ta. domin haka taci gaba da bin shi a baya suka ɗan yi tafiya ba mai nisa sosai ba kana ya faka gefen wani hanya mai ƙarancin ababen hawa ya fito ya ƙaraso jikin motar ta lokacin da itama ta fito ɗin tana kallon shi.
"Amma dan Allah mai kika gani a jikin Yaseer?" Ya tambaya bayan ya ƙare mata kallon sama da ƙasa.
"Kai ma mai ka gani a jikin Reina?" Ta mayar masa da raddi.
Yayi murmushi sosai sannan yace "idan na faɗa miki ma ba zaki gane ba amma zan yi miki misali. Da ace Reina ce a gabana a yanzu ba zata iya kallon idanu na da dafin dake cikin naki idanun ba ko wani irin laifi nayi mata balle ke da babu abinda ya haɗa ni da ke.
Yarinta, wauta, genuine innocence da rashin sanin ƴancin kai, maza muna son haka"
"Yanzu na fahimci dalilin da ya saka ka rasa ta ashe" ta ja tsaki tana kama ƙofar motarta zata koma ciki tayi tafiyar ta, daman ta sani ɓata mata lokaci zai yi itama maganinta.
Kafin ta ida shigewa yace "Idan kika taimake ni raba su kawai zan yi in ɗauke ta ki same shi. amma idan kika barni nayi yanda nake so ba zan yi miki alƙawarin ba zan iya cutar da shi ba. Kin san idan mutum ya fara shiga jikin ƴan siyasa yana koyan dabaru da yawa, ko baki ji mahaifina yana shirin tsayawa takara ba?"
"Ina fatan ba kaine ka yaɗa hoton nan kake son tado da abinda muka yi aiki tuƙuru wajen ganin mun bisine shi mun warkar da raunin shi a cikin zuƙata da yawa ba!"
"Idan nine fa miss Aicha Hamissou?"
"Ƙaran ka zan yi wurin hukuma."
"Ai ba ƙazafi nayi mishi ba, gaskiya ne, babu wanda zai kama ni da laifi"
"Ita Reinan haka ta faɗa maka?"
"No, bata min ƙarya ai, na san gaskiyar komai. Haka dai duniya ta shaida"
"Toh zan faɗa mata sai in ga yanda za'a yi ka same ta"
"Ba barazana nake miki ba amma kema zaki rasa Yaseer. Idan ya aure ta ba zai kalle ki ba. Nima kuma ba zan bar shi ba"