← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 117

Sashe 87

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi kuwa ganin da gaske idan ya tsaya kallon ruwa kwaɗo ne zai yi mishi ƙafa ya saka bai bari sai gobe ba ya kwace damar zuwa gidan daga hannun Sabir domin ya san idan ya samu Reina ta shige masa gaba komai me sauƙi ne.

Da ya matsa Yaseer kuma ya dage bayi tashi sai Reina ta tashi ita tace su shiga kitchen suyi magana.

Tura ƙofar kitchen ɗin yayi ya rufe shi kada iska ya dauke maganan su ya kai kunnen Yaseer kafin ya juyo ya fuskanci Reina "Auntyn mu don Allah ki taimaka min. Ni bani shiga yanda ba'a yi da ni amma wannan karon kam wallahi ba zan iya haƙura ba"

Dariya ne ya ƙwace mata ganin yanda ya dirirce, ta kai hannu baki tana sassauta dariyar tace "Ina Maama ce?" Idan ita ce bai ga komai ba ma.

"Wata Maama? Ina zan kai wannan miskilar? Safina dai ƙawar ki, duk ta gama caza mun kai ta mayar dani abun Allah sarki."

Dariyar ta ya ɗauke ta waro idanu cikin kaɗuwa "Safina dai?! Taɓɗijam" ta jinjina kai tana girmama ƙokari irin na Suhail.

Yaci gaba da cewa "Wallahi ko saurara na bata yi balle in yi fafutukar kafa gwamnati na, Aunty Reina ke kaɗai nake da, ki taimaki bawan Allah, ki faɗa mata da gaske nake yi auren ta zan yi kuma ko yanzu a shirye nake"

~~~~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

101

Reina ta sauƙe dogon ajiyan zuciya, itama ba iyawa take da Safina ba a yanzu.
"Abun da kamar wuya Amma zan gwada yaya Suhail"

Ya girgiza kai "Ki sauƙe yayan nan dan Allah daga yau ni ƙanin ki ne, kiyi min ƙoƙari Aunty na, kuma bani son jin A'a dan Allah. Ni kuma ko me kike so zan yi miki, zan iya zama ɗan aikan ki ma in dai yayanmu bayi nan kawai ki kira ni."

Dariya da tausayi ya bata a lokaci guda, tace "ba sai an yi haka ba ma, zan yi iya ƙoƙari na in sha Allah tunda dai na samu kana kula ni yanzu".

Kunya ya ɗan kama shi don shima yayi wannan tunanin, kowa ya san baya yi da ita bayan suna gida ɗaya tsawon watanni amma ba kunya da tashi buƙatar ya tashi ya zo gareta.

"Kiyi haƙuri aunty Reina, ban kyauta ba na sani Amma duk wanda ya san abubuwan da ya faru da Yayanmu da iyayen mu dole amsar sabon yayayin nan yayi masa wahala, saidai tunda aka ɗaura muku aure na fahimci ƙaddarar ku ne ta zo a haka kuma na manta da komai. kiyi haƙuri kada ki hana ni Safina"

"Nima kayi haƙuri da abubuwan da suka faru, ba a son raina bane. Kuma zan yi maka ƙoƙari in sha Allah, duk yanda ake ciki zan sanar da kai"

"Toh ai ko number na ma baki dashi Auntynmu"

Tayi dan murmushi "ina dashi mana, sai dai idan kai ne baka da nawa."

"A'a na karɓa a wurin Yayanmu fa tun kafin biki, zan miki magana a Whatsapp"

Ta gyaɗa kai lokacin da Yaseer ya turo ƙofar ya shigo. "Kai yaya ne zaka zo ka ɗauke min amarya na tsawon lokaci? Ka zo ka tafi gida mun gode"

Ya dube shi da mamaki "Ko minti 10 fa bamu kai ba"

Ya ƙaraso ya riƙo hannun Reina yana jan ta zasu bar masa kitchen ɗin don bai ga dalili ba. "idan ka gama ai ka san hanyar fita, ka rufe mana ƙofa"

Suka fita parlor ya ɗauki babban basket ɗin ta ɗauki ƙarami suka haura kitchen ɗin sama da su.

Plates da cokula da aka jere mata ta ɗauko ta sake ɗaurayewa tare da cups ta jere a kan tray ta saka juice ɗin kwali da goran ruwa a kai sannan ta fitar da shi dining area ɗinta. Tana cikin serving ɗin su Yaseer ya dawo daga part ɗin shi ɗauke da ƙaramin a tray hannu ɗaya mai ɗauke da mugs guda biyu wanda ya haɗa musu tea ɗaya hannun kuma akwatin tea ɗin ya ɗauko sai da ya ajiye tray ɗin ya kai akwatin kitchen ɗinta ya ajiye a cikin cabinet.

Ya dawo lokacin ta gama haɗa komai a plate ɗaya zata haɗa na biyun ya dakatar da ita.
"Zaki tara mana wanke-wanke, muci idan bamu ƙoshi ba sai mu ƙara."

Ance babu musu don haka ta amsa da toh ta zauna ta dauki cokali suka fara ci daga plate ɗaya.

"Ai da ma mun tsayar da su mun karya tare don hala basu karya ba suka fito"

Ya kalleta kawai, sai ya zaunar da wani ƙato a gidan shi yana karyawa tare da amaryan shi kenan?.
ya ɗauki mug ɗin tea ɗin shi ya kai baki ya kurɓa yaji babu zafi sosai sannan ya kai bakin ta.
Ta ɗauka zai tanka yanda zata lallaɓa shi ta samu ta ɗauki waya ta kira Suhail su dawo don tana da tabbacin basu yi nisa ba.

Baki ta saka a jikin cup ɗin idanunta a kan shi ta dan kurɓa kaɗan ta ɗaga kai. "Ba sugar" duk da ya sha ya ji yayi masa daidai amma sai da ya sake kurɓa yaji. "A hakan ne ba sugar? Cube ɗaya fa na saka"

"Ni uku nake sakawa"

Yayi mata kallon da gaske? ɗinnan. Sai kuma ya tuna rainon cake ne dole.

A drawern console ɗin dining ɗin yace ta ɗauko Jar ɗin zuma babu nauyin jiki kuma ta miƙe ta kawo ya saka mata tea spoon ɗaya ya rufe sannan ya gauraya ya kawo bakin ta.

"Har yanzu bai ji ba fah" tace tana kwaɓe fuska.

Ya ajiye mug ɗin ya dagota ta dawo cinyar shi sannan ya sake kai mata cup ɗin bakinta "oya sha"

Murmushi tayi "kaman wata baby yaya Yaseer?"

"Oh seriously baki yarda zan iya ɗuran ki ba ko?"

Ƙarshe dai shi ya haƙura ya ƙara mata zuman Saboda yanda ta narke mishi duk yanda yaso zama discipline master ba zai iya ba.
Abincin ma a baki suka ƙarasa ciyar da juna tana zaune a yanda ya sama mata matsuguni, hannun shi ɗaya ajiye a saman nata cinyar.

Tare suka tattare wurin da sai da tayi shirin wanke abinda suka ɓata taga ashe akwai dishwasher da yake mata zancen tara wanke-wanke, suka jera komai a ciki suka kunna suka yi timing suka bar kitchen ɗin tana laluɓar numbern Safina a wayanta.

"Amarya bakya laifi, amarya mai maganan sugar" tace da dariyar ƙeta bayan ta amsa kiran.

"Feenah amma bamu yi dake zaki zo yau ba?"

"Ke bani son iskanci, in zo in yi miki mene? Ba na gama da ke ba? Keda kike da yaya Yaseer a tare da ke ai zaki barni na ɗan huta ko?"

"Shikkenan, yaushe zaki zo yanzu?"

"Maama bata faɗa miki ba?"

"Kema kin san kin faɗa ne kawai sati biyu kam, tunda ni gashi har an kawo min ƙaran ki"

"Waye?" Ta tambaya cikin ƙosawa.

"Ƙanin miji na"

Shewa Safina tayi ta ajiye wayan tana tafa hannuwa kafin ta ɗauka ta mayar kunnenta "Iye su masu miji! Allahu akbar shikkenan an wuce level ɗin su Feenah ko? Muma zamu jona soon in sha Allah"

"Yaya da son ranki" Reina ta amsa tana kallon Yaseer dake zaune a kujeran dake kallon nata teburin aikin shi ya raba tsakanin su, e-mail yake rubutawa ya roƙi ta bashi minti talatin shiyasa taga bari tayi wayoyinta a lokacin.

"Toh kin share ainihin zancen, me yasa kike wulaƙanta mun ƙanin miji?"

Ta ja ƙaramin tsaki, "Ni kada ku ɓata min rai da safen nan, ki je ki samu angon ki kafin ki saka na baki saƙon ɓacin rai ki bashi yauwa. Kuma kice ya daina zagawa yana haɗa ni da mutane bani so" da haka ta katse wayan ta. Ita daman ta san Suhail ya haɗa ta da aiki ne kawai don gwamma ace ta tsara Maama sau biyar a kan Safina.

"Wai daman Safina ne yake so?" Yaseer ya tambaya idanun shi a kan screen din system ɗin gaban shi.

"Nima dai nayi mamaki."

"Shine abinda ba'a so naji ɗin? Kuma ya faɗa miki yana tsammanin ba zan sani ba?. Da alamu kuma Muhammad ya riga shi, don tun fara bikin nan nake ganin su tare"

"Amma matan shi bata zo ba ko?"

Ya ɗago ya dube ta da murmushin gefen baki "Umry dani zaki yi gulma?"

"Tambaya ne fa ba gulma ba" ta karya kai tana ɗan tura baki.

"Idan na faɗa miki me zaki bani?"

"Me kake so?"

"Ba zaki iya bani abinda nake so ba"

"Idan ina dashi me zai hana?"

Confidence ɗin tayi maganar ne ya bashi dariya, sai anjima ido ya raina fata. "Shikkenan bikin ƙanwar ta ake yi itama a garin su shine ta tafi."

Kwantowa tayi jikin teburin tana ƙasa da murya ta tambaye shi "Ƴar wata gari ne?"

"In kira miki shi ne ki tambaye shi?"

"Kaii Babe ba nima na faɗa maka yanda muka yi da yaya Suhail ba?" Tace tana miƙewa daga mazauninta ta zaga teburin ta isa gaban shi ta ɗan ɗofana a kan table ɗin tana kallon shi. "Ance tsakanin mata da miji babu ɓoye-ɓoye"

"Waye yace?" Ya tambaya yana rufe system ɗin.

Ta juya ido kafin ta amsa da "Su"

Sai taga ya miƙe, ai da sauri tayi ƙoƙarin dira daga kan table din ya riƙo ta, sai gashi ta fara wulli-wulli da ido.
Kallon fuskar ta yayi na ƴan second kana yace "Na gagara fayyace innocence ne yayi miki yawa ko kuma wayo, amma ba damuwa I'll figure it out soon" ya matsa baya tayi saurin sauƙa daga table din, hannunta a kan ƙirjin ta dake lugude don da ya sake mata irin na ɗazu ba zata sake biyo shi study room ɗinnan ba, itama saurin sakewa da sabo yake jawo mata.
Tunani take matsayin ta na amaryar kwana ɗaya ko haɗa ido da shi bai kamata ace tana iyawa ba.

Komawa yayi ya cigaba da aikin shi Saboda na emergency ne idan ba don haka ba ma babu abinda zai haɗa shi da abinda ya shafi office a yau.
Chapter 87 · 0% Book details