Sashe 49
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Toh Umma " ta amsa sannan Saudat ta juya ta koma ciki, itama Reina ɗakin su ta shiga ta samu Maama ta fito daga banɗaki kenan, bata bi ta kanta ba ta mayar da hijabinta ta tada Sallah.
Itama banɗakin ta shiga, tayi uzurinta ta ɗauro alwala sannan ta gabatar da Abinda ya samu kafin ketowar al-fijr ta yi raka'atanil fijr da sallan asuba sannan ta zauna yin azkhar ɗin safiya lokacin da ta jiyo muryoyi kaɗan-kaɗan suna tashi cikin ƙira'a mai daɗi.
Kaman zata share amma daɗin ƙira'ar na ratsa ƙirjin ta don haka ta fito ta leƙa.
Duk suna wurin daga kan Abbah har zuwa Irfan suna tilawa. Sai ta samu kanta da komawa ta ɗauko al-ƙurani ganin haka Maama ma ta biyo ta suka zo gefen Saudat suka zauna ana yi da su.
Sai da gari ya waye sosai Yaseer ya rufe da addu'a suna ameen, sannan Abbah ya bada sadakan 5-5k ma kowa aka watse haɗa abincin kari.
Yau kam tare suka yi aiki da Irfan suka gama, kuma Sabir ya buƙaci taimakon ta da wasu abun kasancewar Aicha bata nan Maama ne ta kama aikin ta na wanke-wanke.
Amma dai Yaseer da Suhail basu kula ta ba har ta gama dukda ba wai ta damu da shariyar Suhail bane sai dai fushin Yaseer ya dame ta matuƙa, tana ta kokarin fayyace abinda tayi mishi yayi fushi haka, rashin ɗaga wayar ne ko kuma akwai wani abu?.
Da hantsi Uncle B ya turo mata da kati na 10k da data 30gb sannan ya mata tunin fitan su na yammacin don haka ta samu Umma da maganar.
"Ki tambayi Daddyn ki zan tambaya miki Abban ku amma Maama ta ajiye zuwa islamiyyar yamma ta raka ku in dai sai kin je"
Ƙarfe biyar saura sai ga Maama ta coge a kwana Ɗaya da roban ice cream a gaban ta tana kumbure-kumbure domin ta so bayar da hadda yau Amma saboda kawai Reina tana son ta fita yawo aka hana ta.
"Ƙanwa ta, a canza miki wani flavour ne idan baki son wannan?"
Uncle B dake zaune a gefen Reina ya tambaya.
"A'a wannan ma yayi" ta amsa fuska ba yabo ba fallasa.
"To ai naga kin bari yana ta melting ne, idan kuma baki son nan wurin ne sai mu je inda kike so."
Girgiza kai tayi ta luma cokalin Ice cream ɗin ta fara kaiwa baki, daɗin shi ya saka ta zage ta cigaba da sha amma ta saka a ranta sai ta kai ƙarar Reina ma Ummi ko Umma koma ma yaya Yaseer yanda ta wani zauna daff da namijin da ba muharramin ta ba har jikin su na gogan juna idan suka motsa, ita gashi ta girma zata fara ketare iyakokin Allah ko?!
Ƙwafa tayi tana ta recording ɗin abinda suke yi da abinda suke cewa a kanta duka. Sai da shida ta gifta Reina ta ɗaga hankalin su koma gida don taje ta shirya ma karatun yau kada shima ta ƙara wani laifin a wurin yaya Yaseer.
Yayi musu takeway sosai ga siyayyan da yayi mata tun daga UK, sannan da ya ajiye su ya basu kuɗi masu yawa ita da Maaman duk suka ƙi karɓa sai da ya gwada ɓacin ran shi Sannan Reina ta karɓa tayi mishi godiya don shima bata son ɓacin ran nashi gwamma a barta taji da abu guda ɗaya.
Lokacin da ta shigo study room ɗin Maama ce zaune a kujerar gaban teburin Yaseer tana mayar masa yanda aka yi.
Kunne ya saka sosai yana sauraren ta, kuma ganin Reinan bai saka ta fasa ba, haka tana tsaye tana jinta ta fayyace masa komai har zuwa lokacin da suka dawo gidan.
"Nagode Maama za'a yi mata faɗa in sha Allah" shine abinda yace. Amma ko da Maaman ta fice bai cewa Reina ƙala ba ya shiga aikin gaban shi, ga fuskar nan ya haɗe gabas da yamma babu halin tunkarar shi ma.
Da ƙyar can bayan wani lokaci ta iya zuwa gaban teburin tace "na gama yaya Yaseer"
"Yayi kyau, sai da safe"
"Toh questions ɗin fa?"
"I'm busy sai gobe"
Haka ta juya cikin sanyin jiki ta tafi domin bata ga fuskar gardama ba.
°°°°°°°°°°°°°
_The Bleeding Rose is now available on arewabooks 🌹🔥_
*The story of Prince Namir and His Rooh Farah*
The love story between a mighty warrior and his damsel in distress.
If you're looking for a scorching hot romance, this is it!
If you're interested in historical fiction, This is it!
If you're interested in anything royalty, you'll love this!
~~~~~~~~
Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.
*Seemahwrites ✨*
77
~~~~~~~~~~
_J'étais censē t'aimer mais j'ai vu l'averse_
_(I was ready to love you but I saw d storm)_
~~~~~~~~~~
Hutun ƙarshen mako ya ƙare, masu aiki sun koma bakin aikin su haka ma ƴan makaranta. Yanzu tsakanin Reina da Yaseer gaisuwa ne kawai idan tayi mishi zai amsa sai kuma ya bata pocket money idan zata tafi makaranta. ba zata sake saka shi a ido ba wani lokaci sai washegari daman saboda ita yake dawowa gidan da wuri Yanzu kuwa sai ya ƙara daɗewa a kan daɗewan da yake yi da, ya bubbuɗe sabbin projects ɗin da aka jinkirta su sai gaba idan sun rage wanda ke gaban su yanda idan aka yi magana zai ce aiki ne yayi masa yawa.
Duk yanda Aicha ta kai da son kasancewa tare da Yaseer sai gashi stress ya saka tayi wuji-wuji a ƙasa da sati guda har ɗan rama tayi don sammako yake buga musu ga dawowa wataran tun a mota take fara bacci, da ta yada kafaɗa kuma gari ya waye a sake shiri a fito.
Knocking Aicha tayi kana ta turo ƙofar ta shigo tana jan ƙafa bakin ta da Sallama.
"Gani Yayanmu" ta tsaya a gefen teburin shi.
Yaseer ya ɗago ya dube ta sau ɗaya sannan ya mayar da hankalin shi kan Abinda yake yi yana faɗin. "Ina takardun Youth empowerment programme ɗinnan? Ki kawo in saka hannu sai mu saka date ɗin da ya dace"
Jin bata amsa ba kuma bata motsa ba ya saka ya ɗago ya dubeta sosai.
"Yayanmu, kai inji ne?" Aicha ta tambaya cikin gajiyayyen murya.
Yamutsa fuska yayi yana mata kallon rashin fahimta taci gaba da cewa "baka gaji ba? Baka jin barci? Kalli agogo fa ƙarfe tara na dare, rana ta juma'a mun wuni a office kana niman saka mu kwana"
Shi karan kanshi ya ji gajiyan a jikin shi ƙwarai amma zuciyar shi ta huta, don banda yanzu da Aicha ta dawo da shi cikin hayyacin shi ya huta da tunanin Reina tare da Uncle B, domin sheɗan har ayyano masa kalar rayuwar da zasu yi bayan sun yi aure yake yi.
"Kada ki damu zamu biya ki overtime hours ɗin da kika yi"
"Idan kuɗi nake bi ko aiki nake son yi overtime sai in je in saka Daddy na ya sauƙa a matsayin shi in hau, amma kai na biyo ka sani, aiki nake son yi tare da kai ba mutuwa ba. Allah idan ban samu na wuni ina barci ba gobe, ranar Monday a gadon asibiti zai iske ni" ta ƙarashe tana kwaɓe fuska.
Ajiyar zuciya ya sauƙe yana motsa wuyan shi da yayi mishi tsami shi har sai da ya bada sautin ƙass, ya maida numfashi.
"Ki je driver na ko Muhammad ya sauƙe ki" yace cikin hamman da ya taso masa yake son dannewa.
Wayar hannunta ta kunna ta saka finger print sannan ta shiga contact "Allah Umma zan faɗawa" tace tana laluɓo number.
Fauce wayar yayi tare da miƙewa yana faɗin "fitinanniya muje." Ya ɗauki hular jamfan shi ya mayar kai, sannan ya shiga gaba tana bin shi a baya suka fice.
Yana gaba tare da driver ya bar mata bayan motan don haka ta ɗan kwanta ta rage wani abun kafin su isa.
Wayar shi ya ciro ya hau kan numbern Reina amma ya gagara danna kira, a tsawon satin kullum sai yayi fama da wannan kokwanton sai ya haƙura, amma yau sai ya yanke shawarar dannawa ya kirata ta zo karatu don ba zai iya barinta da halinta ba, tayi mishi abinda yafi wannan ma bai iya watsar da hidimar ta ba.
Sai dai lokacin da ya saka wayan a kunnen shi a maimakon ya ji sautin ringing sai na'urar da aka saita take sanar da shi ɗaya ɓangaren da ake ƙoƙarin kamowa tana amsa kira.
......
*Reina*
Sosai ta shiga damuwa da fushin Yaseer Musamman ma da Maama ta haɗa su yake yin mai dalili, gashi ya datse duk wata hanya da zai haɗa su, haka zata je study Room ta sha chatting da gyangyaɗin ta bai zo ba, wataran kuma tayi ma kanta faɗa tayi karatun gudun kada ya turke ta bata da Hanyar gudu.
Ta samu Uncle B a waya ta zayyane mishi yanda aka yi, Maama kuma ta so suyi kaca-kaca amma bata sake bin ta kanta ba itama daman miskilar kanta ce.
Uncle B bai gwada damuwar shi a kan abinda ta ɗaga hankalin ta a kan shin ba sai ma jaddada mata da yayi satin sama da zai shigo tare da wakilan shi ne da zasu kawo tambaya a saka musu rana dukda mahaifin ta yace ba zasu karɓi sadaki yanzu ba saboda cases ɗin dake gaban su amma gwamma ko yaya ne ya kama dahir.
Ita kuma bata yi azancin ko kiran Yaseer a waya ta bashi haƙuri ba tunda ta san zuba mata ido yayi shiyasa bai ce komai ba, idan ma yaƙi ɗauka ko text da sai ta yi mishi ko ta WhatsApp, amma shi da ya siya mata wayan ma ko HI bata taɓa ce masa ba, kuma tana ganin yana kallon status ɗinta idan ta saka.
Yau a gidan Ummi ta wuni, bayan isha Umma ta tura aka ɗauko ta Maama kuma zata kwana a can in yaso wani satin ita sai taje ta kwana saboda kar su bar jikin mahaifin su baki ɗaya.