← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 117

Sashe 17

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon shi tayi da mamaki ta karɓi envelope ɗin ta buɗe ta zaro takardun ciki tana dubawa, ga sunan ta a jiki har da hoton ta.

Yau ake saka ran za'a fara sake admission ɗin gaba ɗaya amma shine za'a ce har anyi mata registration? Kuma ma ba last week aka gama kokwanton wani ɓangare ne guda ɗaya zasu biya mata kuɗin makaranta ba?

Su Alhaji Salisu sun ce su Ummu in dai suna son taci gaba da karatu sai dai su cigaba da biya mata, duk cikin su ƴan uwa biyar Saboda lalacewa.

Shine suma su Ummin suka ce ai tunda su suka karɓi riƙon ta don haka hakki na kan wuyan su, amma sun saka a ransu admission ya fito suka ga su Hajiya Hauwa basu da niyyan biya zasu biya, tunda na Maama ma ba gazawa suka yi ba.

Toh wannan kuma daga ina?.

~~~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

53

~~~~~~~~
_I don't blame you_
_but I can't change you_
~~~~~~~~~~

A hannun ta suka bata envelope ɗinnan suka tafi, tana shiga ɗaki ta samu baƙon da bayi fashi sai gaggawa ko jinkiri ya iso don haka kawai ta faɗa wanka ta kimtsa kanta ta fito kitchen ɗaura abincin mai gidan domin yanzu ita take dafawa.
Tayi ma Hajiya Hauwa sannu da gida taƙi amsawa ita kuwa ta cigaba da harƙan gaban ta domin a halayen ta babu baƙon Reina.

Ranta a mugun ɓace yake, taso tace ta bar aikin gabaki ɗaya ta ɓace mata da gani amma kuma yana da yawa ba zata iya haɗawa ita kaɗai ba ga su Zaheera sun tafi birthday ɗin wata ƙawar Zahra da tun last week ta dame Reina ko zata je? Tace ita a suwa ɗanwake a Zaranda hotel? Toh ko da suna nan ma basu ayyana wani abun arziƙi sai dai kowa ta ƙule a ɗaki sai an kira su cin abincin.

Ta gama haɗa komai ta jere mata su a kan dining sannan ta ɗibi nata a ɗan bowl tayi mata sai da safe ta wuce ɗaki. Washe gari tana shiryawa ko karyawa bata yi ba ta wuce Islamiyya don ta lura Hajiya Hauwa ƙiris take nima ta huce haushin ta a kan lafiyar jikinta, don ta jiyo su jiya tana yiwa su Zahra Ihu sun yi dare a waje, a karo na farko, domin kusan duk wata kaman bashi Zahra sai ta je birthday party, wataran ma sai kowa yayi barci a bar Hajiya Hauwa a parlour tana jiran dawowar ta.

Daga can kuma ta wuce gidan Ummi, zata bata kwana biyu ta huce kafin ta koma.

"Ko su ɗin ne suka biya?" Ummi ta tambaya tana tsefe mata kitson kanta.

"Anya kuwa Ummi? Kin ji baƙaƙen maganar da matar nan ta dinga faɗa min a kai? Ni dai ban tanka ta ba"

Ummi ta buge mata baki "matar wan uban ki ne matar nan?"

Reina ta turo baki. Daga nan duk tambayar da Ummi zata yi mata tana ji tana shiru ita ala dole ranta ya baci.

A tsakanin gidan Ummi da Hajiya Hauwa Reina sai da tayi addu'ar Allah yasa ayi a fara zuwa makaranta yafi ƙafa ɗari musamman da suka sauƙe a Islamiyya Hajiya Hauwa bata bari ta fita ko nan da can wai zata koyi gantali, haka zata wuni tana ɗaurawa tana sauƙewa, Alhaji Salisu har ya fara jin daɗin girkin ta fiye da na matar shi.

Ranar da taje ta karɓo ƴan kuɗin da ƴan uwan aunty suka haɗa mata na hidimar makarantar da zata fara tafiya gobe, ko awa biyu bata yi a gidan ba Hajiya Hauwa ta kira Ummi wai ace ta dawo yanzu-yanzun nan.
Bata san abin da gaske bane sai da ta fito niman adaidaita taga drivern gidan yana nufo ta.

Tsoro ya kama ta haka dai ta shiga motar tana mai sadaƙarwa tare da yiwa gidan Ummi kallo na ƙarshe don ita kam nata ya ƙare mata.

Da sallama ta shiga parlon tana rakuɓe-rakuɓe a jikin labule lokacin da baƙo kuma sananniyar fuska ya sake mata murmushi.

"Daddy?"

"Na'am sarauniyar Daddy?"

Sake labulen tayi ta ƙarasa wurin shi da azama kaman zata faɗa jikin shi ta rungume shi amma sai ta samu kanta da zuba a kan guiwowin ta tace "Daddy ina wuni" cikin wani murya mai cike da kewa "Daddy yaushe kazo?"

"Lafiya sarauniyar Daddyn ta, bamu daɗe da shigowa ba nace sai na zo na duba ƴata tukunna mu wuce masauƙi." Ya juya wurin budurwar dake zaune a gefen shi ta zuba ma Reina dake riƙe da kafar Alaji Abdou idanu.
"Aicha ki gaisa da ƴar uwar ki" yace da ita cikin harshen faransanci.

Sai a lokacin Reina ta ɗago ta kalli Aicha zuciyar ta ya buga saboda karama da kwarjinin da taga budurwar tayi mata. Babu kwalliya a fuskar ta tana sanye da sutura mai sauƙin yanayi Amma irin matan nan ne sai dai su suyi ma kwalliya kyau ba shi yayi musu ba.

Babu yabo babu fallasa tace "Yaya kike?"

A cikin idanun ta Reina take hango wutar wani abu da ta kasa gane menene, jin kamar wutan na niman ƙona ta gashi ta gagara ɗauke idanun ta a kan Aicha yasa bakin ta ya nimo kalmar "Lafiya ƙalau" kamar mai koyon magana ta fitar dashi.
Cikin Sa'a ta samu Aicha ta ɗaga idanun ta daga kan ta.

"Yanzu za'a fara zuwa makaranta ko sarauniyar daddyn ta?" Alaji Abdou yayi nasarar dawo da hankalin ta gare shi.

Ta saki murmushi kawai.
"Allah ya taimaka, mummyn ku da yayyen ku suna hanya gobe, sai tazo aje a siya miki abin buƙata"

"Daddy!" Aicha ta ɗan ware ido tana kallon Alaji Abdou a tsorace.

Sai ya basar da wancan maganar ya koma tambayar Reina wani course ta samu?.

"Amma daddy mai yasa baka taɓa zuwa duba ni ba? Har na kusan mantawa da fuskar ka"

Ya shafa kanta dake cikin hijab "kiyi haƙuri ƴata, manyan uzururrika suka shiga gaba na tun rabuwa na da mahaifin ki ban sake saka ƙafa na a Nigeria ba sai yau."

Hawaye suka shiga zarya a idanun ta "Daddy ai da nima ka ɗauke ni ka tafi dani"

Ya murmusa yana shafa fuskar ta "kiyi haƙuri, nayi miki laifi" tabbas da ace yana da damar tafiya da ita tun wancan lokacin duk abinda za'ayi da dangin Tahir sai dai ayi ba zai bar Nigeria ba saida Hafsah, amma ba zai iya haɗa taura biyu a baki ba.

"Yanzu idan kin gama makaranta sai ki dawo rayuwa tare damu ko?"

"Har sai na gama makaranta?"

"Idan kina so sai in dawo da ƴar uwar ki kusa dake, zata jira ki idan kin gama makarantar sai ku koma tare" ya faɗa da iyakar gaskiyar shi yana nuna Aicha.

Baki sake kawai Aicha take kallon shi, meyasa kowa yafi son Reina ne?

Ta girgiza kai, tana zagaye da abun tsoro za'a ƙaro mata wani?. "Allah ya kaimu lokacin Daddy"

"Toh muje mu duba daya ƴar uwar ki"

Ta gane Maama yake nufi, ta amsa da "Toh" ta miƙe lokacin da su Hajiya Hauwa suka shiga jere musu abinci.

Basu so zama ba amma haka Hajiya Hauwa ta dinga roƙon su har Alhaji Salisu saida ya saka baki, tun isowar su ta ɗago shi daga office.
Alaji Abdou Ya taɓa kaɗan Aicha kam duk yanda aka kaɗa aka rawa taƙi kai ko loma ɗaya bakin ta.

Amma a gidan Ummi ta sake sosai basu bar can ba sai wurin 9 na dare bayan sunci sun sha, Reina sai a wurin ta kwana.

Siyayyan da Mariama tazo ta ɗauke ta suka yi bayan kwana uku ko mai komawa hostel albarka.
Sun siya mata suturu masu yawa, ganin irin zanin da suka zo suka samu a jikin ta. Takalma mayafai da hijabai har kayan abinci da kayan kusa da baka sun jibgo mata tare da Maama.

Sai tayi dabara da aka je sauƙe na Maama a gidan Ummi ta cire duk wani abun da ya shiga ranta ta bayar a ajiye mata suka juya da sauran gidan Hajiya Hauwa, ita da yaranta suka rufu a kanshi.

Bata sha wahala kaman sauran ɗalibai ba, sai da aka fara lectures kafin ta fara zuwa makaranta.
Kasancewar an maida faculty ɗin su parmanent site sai ta je awala take shiga bus ɗin makaranta amma duk yanda zata yi masu bus ɗinnan basu karɓan kuɗin ta daga zuwa har dawowa.

Kwana biyu ta basu idan ma wani abu ne a ran su zai fito fili sai gashi har anci wata biyu a cikin semsester basu fasa ba, har Safina ma ba karɓan nata suke yi ba tunda kullum a tare suke da Reina amma idan ta matsa ita suna karɓa, wataran har masu napep idan ta tsare su su kaita bus stop sai suce ta bar kuɗin ta su tafi.

"To ko dai akwai wani aljani ne da yake bibiyar ki mu bamu ganin shi yake tsorata su suna ɗaukan ki a kyauta?"

Reina ta ajiye laidan fulawar da ta yunƙura zata ɗauka ta miƙe tana kallon Safina a tsorace, tama rasa abin faɗa domin zuciyar ta na son gaskata hakan, idan ba hakan ba nothing can explain abinda yake faruwa da ita a tsawon shekara ɗayan nan.

"Ke wasa nake miki" Safina ta bugi kafaɗar ta tana dariya ganin yanda ta razana.

"Hajiya kuɗin ku dubu takwas da ɗari shida"

Haɗiyan miyau Reina tayi kafin ta tsoma hannu cikin side bag ɗinta ta ƙirgo kuɗin ta miƙa mishi. Suka ɗauki kayan da suka siya suka bar kasuwan, to shima napep ɗin da ya kaita gida bayan sun ajiye Safina bai karɓi kuɗi ba.

Ta cire canjin ɗari uku a cikin jakarta ta watsa mishi ta zari kayan cake ɗinta ta ɗiba ciki a guje har tana jin ƙwan cikin laidar suna karo da juna.

Sana'ar baking take son gwadawa itama shine suka tallata a makaranta wata ƴar final year tayi ordern guda hamsin, gobe idan zata je fara rubuta exams ɗin kammala aji ɗaya sai ta kai mata.

Idan yayi kyau tayi alƙawarin ita da kawayen ta zasu bada ordern na graduation ɗin su zuwa lokacin da za'a gama exams.
Chapter 17 · 0% Book details