← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 117

Sashe 117

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai ya sauƙo daga kujeran da takalmin ya durƙusa a gaban yarinyar zai saka mata kafin Aicha ta kaiga fitowa ta samu bai gama ba ya ƙara wani laifin.

Ƙwafa tayi lokacin da ta fito ta wuce ciki ta saka mayafi sannan ta fito ta dauki key ɗin motarta ta riƙo hannun yarinyar zasu fita.

"Hajjaju ikon Allah ai da kin bari na gama na ajiye ta"

Taɓe baki kawai tayi ta juya janye da hannun Najma dake faman yiwa Daddyn ta bye-bye suka fita daga gidan.

Yau kuma tashi ta same shi.

.....

A cikin yanayin uncertainty na aikin yaya Yaseer na fahimci cewa idan kuka cilla wani wurin to kuma sai randa Allah yayi. Wannan ciki na jiki na dai ya sha yawo tunda a tsakanin yawon ma aka same shi, yanzu haka Watan mu biyu a Niger daga tafiyan sati biyu bayan mun yi hutun makaranta amma wannan zangon kan na san First class ɗinnan da na hau dirowa dole don karatu a study room ba yiyuwa yake ba, koda mun bi tsarin da muka yi a baya mun yi nesa da juna don muyi abinda ke gaban mu toh fa da na riƙe littafi sai barci, sannan yaya Yaseer bayi iya takura mun. Haka dai na lallaɓa na rubuta jarabawar sannan muka kara gaba toh sai yau Allah yayi muka dawo har fargaban haihuwa a wani ƙasar ya kama ni don na kusa shiga cikin watan haihuwa na.

Muna fitowa daga cikin airport yaya Yaseer na tura trolley ɗin mu muna ɗan zantawa naga wucewar su.
"Uncle Bilal?!" Ban san lokacin da baki na ya furta sunan shi ba domin gani nayi kaman ba shi ɗin bane.

Sai naga sun tsaya harda sojojin da suke biye da shi sannan ya juyo, matar dake gefen shi riƙe da hannun yaranta ma ta juyo.

"Reina kece? Yaya kike" Ya ambata mamakin yanda na mayar da uban ƙiba ya kama shi, idanun shi na sauƙa kan cikin da nake tallafe da shi, sannan ya mayar da shi kan Yaseer dake tsaye da hannun shi a baya na fuska ba yabo ba fallasa.

Uncle B ne da uniform ɗin soja? Military doctor kenan ya zama? Ikon Allah.
"Lafiya ƙalau" sai na ɗaga ma Mufid hannu shima ya ɗaga mun da kyakkyawan murmushin shi ɗinnan sannan na gaishe da Afifa matar shi ta amsa kadaran kadahan.

Basu yi magana da yaya Yaseer ba yayi mun sallama ya juya kuma shima sai na fahimci ɗan sauyawan yanayi game da shi. wani ɓari na zuciyata yana gwada min rashin kyautawa na amma wani ɓarin na son gwada mun Uncle Bilal ya cancanci gaisuwa daga gare ni koda sau ɗaya ne amma wannan shine na ƙarshe, bani fatan Allah ya sake haɗa mu koda a hanya indai har ran mijina zai ɓaci saboda shi.

Kwana ashirin daga nan muka tashi da labarin Aicha ta haihu ta samu ɗanta santalele namiji bayan tariyar ta da wata bakwai. Mamakin da wasu mutanen suka shiga bai hana su murna ba, aka nema ma su Umma jirgin Abuja ba'a samu wanda zai tashi a ranar ba, zata bi mota kuma su Jadda suka hana don zuwanta ba zai ƙare su da komai ba babu abinda ba za'a mata ba daga can. Ashe Allah ne yayi hukuncin sa don zuwa yammaci nima na fara laushi, tun ina kuka da hawaye har ya kafe gashi sun zo sun gwada sun ce da saura ina 4cm har yanzu. Na dai tabbatar na jajjada ma Yaya Yaseer daga wannan babu ƙari na gama.

Kafin a fito daga sallan Isha cikin ikon Allah sai ga ƴata ta fito duniya. Da aka ɗaura mun abu na a ƙirji na saida na zubar da hawaye, I can't believe wai jini na ne wannan, ƴata da yaya Yaseer kai duniya mai juyi-juyi.

Labari na yaɗa dangi nan celebration ya dawo double, ganin yanda jama'a ke tuttuɗowa yasa aka rubuta mana sallama muka wuce gidan Umma aka fara bamu kula yanda ya kamata.
.
.
.

Riƙe yake da jaririyar shi ya ƙura mata ido kaman idan ya juya zata ɓace ne, ina tunanin hala har ni da nake wurin ya manta dani ita kawai yake gani "Bae baban baby" nace ina sakawa ya ɗago ya dube ni da fara'a a fuskar shi ƙauna mai zurfi a cikin idanun shi.

"Na'am Umry Maman Fauzy."

Ido a waje na dube shi ina riƙe hannun shi "Sunan Aunty na ka mayar bae?"

Gyaɗa kai yayi. "Auntyn mu dai, Allah yayi mata rahama yasa kyawawan halayenta yabi namu Fauziyyan"

Ƙara karfin riƙon da nayi ma hannun shi nayi hawaye na kawowa a idanuna, shi da yace bayi da ra'ayin takwara ma kowa amma gashi ya bani mamaki.

Ya mayar da duban shi kan babyn yana cewa "kinga don kin ɗauko kamannin ta ban yarda ban amince ba ki ɗauko mun yawan kukan nan"

Sai na ɗan taba shi "ka daina ɓata ni a wurinta ba haka nake ba" nace ina mayar da hawaye na.

"Gwamma ki dai gyara"

"Kuma da gaske tana kama da ni?" Na tambaya ina leƙa ɗan ƙaramin fuskar ta a hannun shi.

"Baki ga farin fuskar da jan bakin tsotson ba. Banbancin kawai Allah ya rufa mata asiri ta ɗauko hanci na ta huta da gorin jama'a"

Inaga a lokacin ne, kaddara ta fara rubuta labarin Fauzah Yar Reina. Ita kuma Hafsatu ta yanke shawarar rubuta Reina's diary ko wata rana Fauziyya jikar Fauziyya zata karanta ta amfana. Idan ba ita ba ma ko wani mai buƙatar darasi daga cikin ƙaddarorinta.

Sannan muma da muka gan shi a zahiri mun ɗauki darasi a cikin kuskure da kuma nagartan iyayen mu wurin tarbiyyantar da tamu ƴar.

Sai gashi Uncle B rana ɗaya ya haɗa daddy da likitan kashin da yake magana a kai kuma ya amince zai yi mishi jinya. Yayi hakan da fatan Allah zai yafe mishi tashin hankalin da yaso jefa marainiyar Allah don kawai ya mallake ta.

Sannan ya haɗa Zahra da wani yaron shi kurtun soja amma ya ɗan manyanta don har yana da yara ma kafin ya nemi aikin sojan. Zaheera kuma police ɗin da ya taɓa kama ta tayi sata shi ya fito yace yana so haka babu yanda Hajiya Hauwa ta iya ta bashi ko zata ji da kanta ita kaɗai tunda masu kuɗi sun saka an rufe Alhaji Salisu har zuwa ranar da zai biya su kuɗin su Jamal kuma an yanke mishi hukuncin ɗaurin rai da rai.

Safina kuma ta ƙaraci zille-zillenta ta auri Yaya Suhail gashi har muna shirin gama makaranta haihuwa yau ko gobe.

Maama ta samo wani young Ustaz ɗan wani babban Malami gashi miskili irinta an haɗu da an dace kuma yana da rufin asirin shi alhamdulillah.

Ganin haka goggo Halime ta haɗa daddy da wata bazawara a jama'are tunda lafiya ya fara samuwa kuma tace ko yaji ya bari tayi ita da shi.

Bayan shekaru biyu da rabi Allah ya sake azurta mu da ƴan biyun da mutane suke ta mun fata da addu'a da bakin su, mace da namiji. Shikkenan daga nan a hankali muka cigaba da tara zuri'a. Na so amsar kaddarar ƙiba ta in yi ta zuba shi Amma Yaseer yace bai san zancen ba sai gani wai ina gyming.

Ban koma siririya ba amma ƙiba na yayi kyau tunda ana regulating din shi nayi ƴar duma-duma tabarakallah masha Allah, a duk sanda na samu lokaci kuma ina zuwa Reina modern bakery da aka buɗe mun nima in gwada sana'ar ko zai karɓe ni tunda ance an ga alamun ba iya zaman office zan yi ba, haka nake murza ƴar mota ta inje ran da naga dama.

ga kyawawan yara da ni da mahaifin su muka yi tsayin daka a kan su wurin ganin sun san addini da koyi da ita da dabi'u masu kyau.
A duk lokacin da yake musu karatun Addini nima na kan zauna ayi da ni, kuma muna nishaɗantuwa da ƙissosi ta tahirin annabawa da manzanni Musamman na Annabi mu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

A rayuwar yau da gobe kuma muna samun saɓani da yaya Yaseer a kan abubuwa da dama. Yana ɓata mun nima ina ɓata masa amma mun horar da kan mu da amsar laifi idan kaine mai ita sannan ka nemi afuwan wanda kayi wa, shi kuma wanda aka bashi hakuri ya haƙura ya yafe albarkacin ingantacciyar ƙauna da soyayyar da muke fatan ta tabbata har abada.

Tarbiyya ba abu ne mai sauƙi ba kuma zaka gama ƙoƙarin ka Idan Allah ya so ya jarabce ka a kan yaro Amma buƙatar shine kada ka zamo wanda yaranka zasu koka da kai a nan gaba suyi nadaman amanar su da Allah ya bayar a hannun ka, sannan kaima idan ka tsaya a gaban shi ranan gobe ka tabbatar ka sauke wannan amana da iyakan iyawar ka.

Allah ya bar mu da masoyan mu na gaskiya.

TAMMAT BI HAMDILLAH.

_Dumɓin Godiya da jinjina ga duk mabiyan labarai na a duk inda kuke. Ina fatan yanda Labarin Reina yake da matsayi a zuciya ta yana da kwatankwacin shi a zuciyoyin ku._

_abinda muka rubuta daidai Allah ya haɗa mu a ladan ya yafe mana kuraran mu_

_Gaisuwa ga women of words writers association da zaƙaƙuran marubutan ta_

_Ina ƙara miƙo wata jinjinan ga ƴan Reina conversation room. Gudumawar ku ya kawo mu wannan gaɓar ina godiya sosai da sosai Allah ya bar ƙauna da kulawa._

_Taku Saliha Ahmad Na'ibi wacce kuka fi sani da Seemahwrites ✨_

For any enquiry contact me via 08021689184.
Chapter 117 · 0% Book details