Sashe 13
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Na'am mai sunan" Ummi ta amsa tana shafa kanta, bata ganin kowa a jikin yaran nan bayan Fauziyyar ta.
"Ummi nima in dawo nan mana ina zama da ku? Bani son zama a gidan umman Zahra wallahi, ina shan wahala Ummi" hawayen idanun ta suka ɗigo cikin plate ɗin abincin dake gabanta.
Rage volume ɗin news ɗin da yake ji mahaifin Fauziyya yayi kafin ya dawo da hankalin shi garesu.
"Akwai wani abinda ake miki a can ne?" Shima da ganta yaga lalacewar ta.
Ta ɗago idanunta dake zuban hawaye ta gyaɗa musu kai. "Umman Zahra tana dukana, bata bani abinci sai nayi mata aiki, kuma idan aka kawo abin daɗi gidan ba za'a bani ba saidai Zaheera ta sammin, bata bani komai in tafi dashi makaranta, ni bani jin daɗi ko kaɗan bani so in koma"
Ummi da baba suka kalli juna. Daman basu so aka bada ɗaya daga cikin yaran ba, ƴan uwan Tahir su suka matsa harda tada tarzoma, shiyasa suka ga gwamma ita Reinan da tafi wayo kuma take da baki ta tafi, ba kaman Maama ba don ita saidai su dafa ta su cinye babu wanda zai sani.
"Shikkenan ba zaki koma ba, kici abincin ki"
Hannun riganta ta saka ta share hawayenta tana washe haƙwara, "dan Allah ummi?"
"In sha Allah mai sunan" tayi ƙoƙarin mayar mata da murmushi.
.....
*Uncle B*
Receiving kiran barrister da ya shigo wayan shi yayi, sannan ya maƙala airpod a kunnen shi saboda driving da yake yi.
Sallama yayi mishi ta ɗaya ɓangaren tare da tambayar shi yana ina ne?
"Wa'alaikumus salam, gani na bar cikin Bauchi yanzu. Zanje Kd in amsa kiran general ne, idan ya samu zan dawo kafin in wuce"
Abinda barrister ya faɗa mishi ya saka shi cin wawan birki da baiyi niyya ba a tsakiyar hanya, cikin Sa'a babu kowa a bayan shi.
"Mai kace ya samu yaron?"
Abinda ya faɗa mishi ɗazun shi barrister ya maimaita, sai kawai ya tada motar ya juya kanta ya mayar dashi yanda ya fito, bai ga na tafiya ba tukunna.
Ya ɗauke shi kusan minti arba'in kafin ya isa gidan su Dr Fahad da ake wunin biki ya kira Hajiya Hauwa a waya.
Ita dai taga masifar da ba'a saka masa rana, kaman ta sani tana isowa jikin motar shi da yake jingine cikin ƙosawa tambayar da ya fara fitowa daga bakin shi shine "Ina Reina?"
50
~~~~~~~~~~
_You're born bluer than a butterfly_
_Beautiful and so deprived of oxygen_
~~~~~~~~~~
"Uncle Bilal ina zamu je?" Reina ta tambaya cikin ɗoki tana cire hijabin wuyanta, daman ba a son ranta Ummi ta matsa mata ta saka ba.
Ya juyo ya kalleta, yau ba laifi kayan jikin ta a wanke a goge, ta shafa powder bakinta na ƙyallin wet lips ga goshinta sabon kitsonta ya fito dashi.
Sai a yau yaga tayi masa fasalin masu shekarunta.
"Wani wuri" kawai ya bata amsa ya maida hankalin shi kan hanya yana kokwanton ko ya tsame hannun shi daga lamarin nan ne tunda har ya kai haka? Amma sai yanzu tausayin Reina yake daɗa kama shi, tayi yarinta ma kalolin shafukan ƙaɗɗarar da rayuwa yake buɗe mata.
Ya fara biyawa ya sauke Zahra da tayi mishi rakiya ya ɗauko Reina, tana ta zumɓuro baki domin ta ɗau wani wurin jin daɗi zai kaita.
Suna tafiya tana masa nuni tare da bashi labarin duk wani wurin da mahaifinta ya taɓa kawo ta har suka zo wuce wani modern bakery, tayi saurin wawuran hannun shi "innalillahi ka kalli shagon cake ɗinnan? A wurin daddyna yake siya min cake idan Aunty tace ba zata bani ba"
A maimakon yayi mata masifa na jawo hannun shi dake kan sitiyari suna kan hanya da tayi sai ya samu kansa da yin parking. "Muje in siya miki"
Ta ware idanu cikin al'ajabi da wargajejen murmushi a fuskar ta. "Dan Allah? Babba sosai wanda zamu ci da Maama ya rage?"
Ya gyaɗa mata kai, da hanzari ta ɓalle marfin motan ta fita, ta ma riga shi shiga ciki.
Da niƙi-niƙin kaya suka fito don duk abinda ta gwada tana so saida Uncle B ya siya mata, kuma yaji daɗin da ta fara ci a take, yana da yaƙinin idan suka shiga prison suka fito ba lallai ta iya saka wani abu a bakinta ba hala sai ta koma gida.
Kaman yanda yayi tsammani aman da ta fara kelayawa ya saka suka fito ba tare da ya gama shigar da ita yanda yaso ba. Yanzun ma he has to pull some strings, har matsayin general saida yayi amfani dashi kafin ya samu permit ɗin da ba'a bawa kowa.
Ruwa ya bata a gora ta ɗauraye bakinta yace "mu tafi?"
Ta gyaɗa kai idanunta na ƙyallin hawaye, sai ya taimaka mata ta miƙe ya saka ta a mota ya shiga suka bar wurin.
"Kinga wurin da muka shiga ɗazu? A wurin Yaseer yake, kullum kina kwana kina tashi a kan gado amma shi kinga wurin da yake kwanciya ai, abinda ya saka ki amai kuma shine abinda yake ci"
"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun, innalillahi wa inna ilaihirrajiun " ta shiga maimaitawa cikin gunjin kuka tana ɗaurawa da "Na shiga uku Uncle Bilal ka maida ni wurin shi dan Allah, ka kaini in ganshi in bashi haƙuri"
"Meyasa zaki bashi haƙuri? Ai masu laifi kawai ake kawowa nan shima mai laifi ne"
Sai ta shiga girgiza kai amma kuka ya hana ta cewa komai. Barinta yayi tayi mai isar ta, numfashinta ya fara sama-sama tana riƙe ƙirji. Saurin parking yayi a gefen hanya ya juya back seat ya zazzage brownies ɗin da suka siya ya miƙa mata paper bag ɗin yace ta saka a hancinta tayi numfashi da baki a ciki. Sannan ya fita ya buɗe bangaren ta yana mata fifita da wani folder har numfashin ta ya daidaita.
Ba zai ƙara mata wani damuwan a kan wanda ke lulluɓe da ita ba tare da ta sani ba, don haka a nan zai ajiye wannan maganar yayi abinda ya shafe shi kawai, wannan ba hurumin shi bane.
Ya koma cikin jakar aikin shi ya dawo da wani goran magani ya zazzago guda ɗaya ya bata babu musu ta karɓa ta haɗiye.
"Wani likita kike gani Idan yayi miki haka?"
Saida ta kora maganin da ruwa ta amsa da "babu"
"I'll arrange one for you kafin in tafi" kaman da kanshi yayi maganar ya rufe mata ƙofar ya zaga suka bar wurin domin a ɗan kwai mutane a arean.
Shirun da tayi daga nan shiru ne na yaƙi da tsoron ta, ƙoƙarin balle kejin tsoron da Jamal, mahaifiyar shi, harma da Daddynta Alhaji Tahir suka rufeta a ciki take yi.
Shima gargaɗi yayi mata kada ta faɗa ma kowa, sannan tun daga ranan ya canza daga daddynta da ta sani zuwa wani mutum da bata saba dashi ba, yayi nisa da kanshi yayi nisa dasu, sai gidan da suke rayuwa a ciki yayi mata faɗi sosai.
"Ba Yaseer bane.
Yaya Yaseer bai yi min komai ba.
j...j...jamal ne.
Wallahi sharri nayi ma yaya Yaseer.
Naji tsoro ne...."
Yayi ƙoƙari wajen ganin bai sake tsayar da motar ba, kada ya gwada mata yanda kalamanta suke girgiza shi ta gagara ƙarasawa, tiryan-tiryan ta shiga mayar masa yanda komai ya faru a lokacin, ta samu kejin ya buɗe ta fara takowa a hankali daga ciki tana fitowa. Numfashi yaso yayi mata gardama amma sai yau ta samu wanda ya saurareta bai dakatar da ita ba bai gargaɗeta ba, don haka ta riƙo shi sosai tayi ƙoƙarin lallaɓar shi ya barta ta tsere.
"Uncle Bilal"
Ya juyo ya kalleta bayan yayi parking, idanunshi sun kaɗa sunyi jaa.
"Ka kaini wurin yaya Yaseer dan Allah, ina son in gan shi" ta roƙa tana riƙo hannun shi.
"Ki shiga gida idan na sake dawowa zan kai ki"
Ta gyaɗa kai sannan ta ja jikin ta da ya gama mata nauyi ga zazzaɓi dake ƙoƙarin lulluɓeta ta fita a motar, har zata tura ƙofar dake jikin gate ɗin gidan Ummi ya kira sunanta ta juyo. Sannan ya fito da containern maganin ɗazu ya ya buɗe seat ɗin baya ya tattaro tarukucen da suka saya ya haɗa ya miƙa mata, "guda ɗaya kawai zaki na sha, kada kina ajiye shi da nisa"
"Uncle Bilal kayi haƙuri"
"Babu komai jeki"
"Ka bawa yaya Yaseer ma haƙuri"
"Zan bashi"
"Nagode"
Yana kallo ta shiga kafin ya koma cikin mota ya kifa kan shi a kan sitiyari, lallai da yau zaiga Jamal sai dai Hauwa ta haifi wani. Shiyasa ashe da suka ce zasu tura shi karatu yace a kawo shi wurin shi taƙi ta tura shi wani wurin, saboda tasan Abinda ɗanta ya zama kuma ta bashi goyon baya.
Miƙewa yayi ya zauna da kyau ya ɗauki waya ya danna kira tare da yin sallama bayan an ɗauka kafin ya tada motar ya bar ƙofar gidan.
......
"Yanzu ace ma yaranki mata aka yi wa abinda kuka yi ma yarinyar nan, yaya zaki yi?"
Sai ga Hajiya Hauwa na ƙoƙarin sauƙa saman guiwar ta a gaban Uncle B.
"Bilal dan girman Allah..."
"Ke da guiwowin ki kike amfani wajen tarbiyyantar da yaran ki? Gatan da kike musu shine rufe laifin su ki ɗaura alhakin kan wanda bai ji ba bai gani ba?"
"Akasi aka samu wallahi, Allah ne ya ƙaddara zai shiga ciki lamari ta juye dashi amma bamu bishi har gida mun ɗaura mishi ba, shi ya kawo kan shi har yanda muke."