← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 117

Sashe 65

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Okay ina zuwa" Safinan tace sannan ta koma jin motsi da magana sama-sama sai can muryar Safinan ya dawo "ina jin ki, na dawo parlour babu kowa"

"Yauwa, kin san me?"

"Sai kin faɗa" Safina ta amsa cikin ƙaguwa tana jin kaman ta jawo Abinda Reinan zata faɗa.

"Feenah wai yaya Yaseer ne yake son aure na can you imagine?"

"Yessss!!! Au Alhamdulillah!" Sai ta shiga murna kaman ance mata gobe ne biki.

"Kin ji Abinda nace kuwa?"

"Ƙwarai kuwa! Allah ya kawo ƙarshen Uncle ɗin su Zaheera, wasshagare walle yaushe zan ciro ashobe?"

"Ba fa ce miki nayi muna soyayya ba"

Tayi nasarar dakatar da ita daga rawan murnar da take yi "Soyayyar yaci uban sa da uban ƴan gidan su! Allah kada ki saka in dawo ba'a yi suna ba in zo mu kwashi ƴan kallo. Shi Uncle ɗin su Zaheeran ance miki son sa kike yi ne? Kin san ma menene soyayya Reina? Kin san daɗin ta? Kin san kwanciyar hankalin da ake samu a cikin ta? Amma tun da Allah ya haɗa ki da mutumin nan kike a firgice kuma kullum ƙara firgicewa kike don haka ki raba ni"

Sai ta ajiye wayan bayan ta kashe ta ƙurawa ceiling idanu ta ma rasa tunanin me zata yi. Ta sake ɗaukan wayan zata cire a DND sai ga saƙon message daga YK.

Janyowa tayi ta duba ba don tana da niyyar replying ba don bata san yaya wani magana zai sake haɗa su a yanzu ba.

"Nayi miki ba dai-dai ba Reina kiyi haƙuri please. Idan na samu dama I can explain myself Amma son ki babu shakka ina yi, ina son ki da dukkan zuciya ta. kuma ina da burin mallakan ki a matsayin matata ta aure. Hafsat I'm not here to lose."

Tabbas taji abinda ake cewa yana tsirga wa mutum tun daga yatsar ƙafa har zuwa kai ɗinnan, don ta samu kanta da sake karanta saƙon nan a karo na biyu da na uku.

Sai ta danna kan numbern tana jin kaman ta kira shi yayi mata bayanin da yace yanzu ko zuciyar ta zata fahimce shi.
Sai dai lambobi guda goma bayan +234 da ya ke haɗa ta da Yaseer a kowani lokaci shi ya ɗauki hankalin ta.

Wannan numbern ne.

Numbern cikin diaryn Aunty.

Numbern da ta haddace shi fiye da yanda ta haddace abubuwa da dama masu muhimmanci a rayuwar ta.

Babu shiri ta samu kanta da danna shi, kaman mai jira Yaseer ya ɗaga dan ita bata ji kaman yayi ringing ba ma.

"Reina" ya kira ta cikin wata murya dake a dake amma kaman da rauni.

"Yaya Yaseer mai yake faruwa please? Ina ta ƙoƙari Amma na kasa ganewa"

Shiru yayi kafin ya furta "I'm sorry. Yau nake shirin faɗa miki idan na dawo daga wurin goggo"

"Ka faɗa min mene yaya Yaseer? Cewa zaka aure ni?"

"No. Toh tell you that I love you. In faɗa miki Yaseer yana son Hafsatu Reina adadin soyayyar da ba zai iya misaltawa ba. Ina son in cika rayuwar ki da farin ciki, jin daɗi da kwanciyar hankali, ina son in kasance a cikin rayuwar ki har ƙarshen rayuwata, I want you to be my other half Reina, I want you to be my future. Ga ƙoƙon bara na ki taimaka don Allah"

ita kanta ta sani Yaseer ya cancanta har ya wuce, koda ace ba son ta yake ba idan suka yi Aure yankan naman jikin ta zai dinga yi kullum ya cancanci ta so shi ta zaɓe shi idan ya buƙaci hakan. sai dai ita ne bata kai ba, zata yi kishin sa taji zafin ƴammatan da suka baibaye shi Amma bata isa ta fara kwatanta kanta a matsayin su ba ma.
Yaya Yaseer ba tsaran ta bane, zaren ba kalan yadin bane.

Jin tayi shiru yace "ba zan takura ki ba, take your time while thinking it over Amma ko dama ɗaya ce ki bani, nayi alƙawarin ba zan yi wasa da shi ba. Sweet dreams my dearest" yace yana katse kiran gudun jin Abinda bai shirya masa ba, yanzu ma yayi ƙoƙari da ya buɗe ajjiyar da yayi shekara da shekaru a rufe.

Adashen soyayya da ya fara zubawa tun shekaru biyar da suka wuce bayan ya kwashe na tsananin tsana da ƙiƙayya na shekaru uku toh sai yau aka bashi damar ɗauka kuma idan bai yi da gaske ba zai iya asarar shi a lokaci daya.

Shiyasa aka ce komai zaka yi ka yi shi saffa-saffa, da ace bai tsananta ƙiƴayyar Reina a cikin zuciyar shi ba, ya san da lokacin da zuciyar ta fara warkewa ba ta rikiɗa kiyayyar nan zuwa soyayya sannan tayi amfani da shi a matsayin maganin ta ba.

~~~~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

88

*Saturday*

Ƙarfe bakwai na Safiya ya samu Yaseer a kitchen, fatan shi kuma Reina ce mutum na biyu da zata shigo.
Ya kasance mai bin komai a sannu sai dai tunda lissafi ya riga ya ƙwace masa sai yaji kaman kawai ya kira Reina ya ji ra'ayin ta game da shi a daren jiya.

Shi kuma barci yana kauracewa wa'inda suka saba yinsa isasshe ne Amma a daren jiya Yaseer ɗawafi ya sha ba tare da ya je ɗakin Allah ba.
Duk bayan Sa'a kuwa sai yayi yunƙurin kiran layinta sai ya tuna dare fa ya raba.

Yanzu So yake yi ya ga yanayin da zata shigo da shi ta fuskance shi tunda ance juma'ar da zata yi kyau tun daga laraba ake gane ta, sai ya sani idan zai cigaba da jira da fata ne ko kuma ya sauya salo, domin da gaske yake he's not here to lose. babu yanda za'a yi ya bar Reina ma wani a yanzu balle Bilal da bai san me yake yi ba.

Yana jikin Fridge ya ji motsin takowa, ya ɗago daga jiki ya zuba ma ƙofar shigowa idanu, sai ga Suhail ya shigo yana hamma.

Ƙaramin tsaki Yaseer ya ja ya cigaba da duba abinda yake nima.

"Yayanmu ina kwana. Jiya ashe wai ku kuka fita da wannan Reina ɗin Umma ta ɗaga mana hankali tayi ta Kuka, baka ganmu muna karaɗa garin Bauchi niman ta ba, sauran kaɗan a saka police ma a ciki Allah ya taimaka sai ga kiran ku. Ai na so in dawo in ɗan kwakkwaɗe ta gobe ma ta ƙara Allah dai ya taimaketa Abbah ya aike mu da nisa kuma ta shiga ciki kafin mu dawo"

Yaseer ya haɗa ƙofofin fridge ɗin guda biyu ya rufe ya zuba ma Suhail Ido har ya dasa aya.

"Wa kake cewa wannan ɗin? Sannan wa zaka kwaɗe?"

Suhail ya cigaba da faɗin "Hmm baka ga yanda ta wahalar da mu bane yayanmu, ina faɗa maka ko rasuwar baban Ummah ban ga tayi irin kukan da tayi jiya ba wallahi"

Ƙwafa kawai Yaseer yayi ganin Abbah da kan shi ya shigo kitchen ɗin. sai ya miƙe ya juya jikin sink ɗauke da abinda ya ciro daga Fridge ya fara wankewa.

Suhail ya haɗa wa Abbah coffee ya karɓa ya fice daga kitchen ɗin ba tare da yace masa komai ba, magana ne dai ya riga da ya gama ta jiya kuma sati biyu na cikawa ko kwana ɗaya ba zai ƙara masa ba, idan yayi wasa ma saidai kawai ya je ya tarar da amarya a shimfiɗar sa.

Su uku suka fara haɗin abin kari bayan Sabir ya shigo don Irfan wai fushi yake, sai da suka fi rabi Umma ta zo ta saka musu hannu aka ƙarasa da ita Amma har aka gama haɗuwa a dining bai ga ƙyallin Reina ba.

Ummah da kanta taje kiranta ganin babu wata mace a gidan da zata tura, sai ta same ta a ƙudundune cikin bargo wai bata jin daɗi. Ta kai hannu kan goshinta taji sanyi ƙalau amma sai ta bita da Allah ya sawaƙe ta koma ta haɗo abincin ta a dan ƙaramin tray ta kawo mata ɗakin sanin yanda zata haɗa ido da wasu daga cikin mutanen gidan ne ya dameta.

Umman tana fita kuwa ta sauƙo ta taɓa abincin kafin ya gama yin sanyi, bata yi nisa ba saƙon Yaseer ya shigo wayanta, tayi saurin ajiye fork ɗin hannunta tana dubawa daman shi take jira tun ɗazu, ta ga yace da wasa yake yi koma ya fasa tunda saƙon jiya da ta kwana tana karantawa ya tabbatar mata ba mafarki tayi ba.

Amma me? Good morning message ta gani irin wanda masoyi yake turawa masoyiyar sa. Saƙon bayi da tsayi Amma kalaman da aka yi amfani da su yayi tasirin da dogon surutun su da Uncle B bayi da shi.

Sai ta ji abincin ya ishe ta ma, a lokacin kuma kiran Uncle B ya shigo kaman haɗin baki don su dagula mata lissafi.

Ɗauka tayi ta saka a kunne ba tare da tace komai ba tunda ta san complain ne zata sha a kan rashin ɗaukan wayan shi jiya, idan ta saurare shi ma ya isa.

"Good morning doll" muryar shi ta fito da annashuwan da bata yi tsammani ba.

Sai ta samu kanta da gaida shi itama cikin sanyin murya "Ina kwana Uncle Bilal"

"Lafiya ƙalau Auntyn Mufid, kin tashi Lafiya?" Tunda ya san ta gane cewa original mummyn Mufid ɗin tana nan a matsayin ta shi kuma ya mayar da ita matsayin Aunty.

"Alhamdulillah, sorry I couldn't return your call jiya, wayan bayi kusa da ni ne" ta samu kanta da ƙin masa bayanin ainihin Abinda ya faru don idan ya tsananta tambaya zasu Iya gangarowa har kan Yaseer da baƙon lamarin da yazo da shi.

"Ayyah, ni kuma na ɗauka ba lafiya ba gashi har mun kamo hanya"

Ta ware idanu "hanyan ina?" bata san meyasa yake son yanke hukuncin da ya shafe ta ba tare da ya sanar da ita ba.

"Ina kike tunani?" Shine amsar shi, ita yanzu da wa ɗaya zata ji?.

"Daddy na fah yana asibiti Uncle Bilal, idan ta nawa ne da ka bari sai next week Please, kuma ma exams muke shirin farawa"

"Mu juya kenan doll?"

"Ba haka nake nufi ba"
Chapter 65 · 0% Book details