Sashe 110
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Saida maman Meesha ta bari Hajiya Hauwa ta gama narkan Zahra kafin tayo kan su wai zata raba. "Haba ke kuwa Hauwa! Ai idan rai ya ɓaci hankali bayi gushewa ko? Wannan ai Sai kiyi mata wani illan bayan wanda tayi ma kanta" ta janye Zahra da fasasshen baki.
Zata wuce da ita ɗaki Hajiya Hauwa ta fauci jakarta ta zazzage a ƙasa, Kuɗi ne bundle ɗin ƴan dubu-dubu guda biyu da na ɗari biyar wanda bai cika ba, Ga anti-biotics nan da aka bata harda takardan scan din da taso jefarwa tun a asibitin ta manta.
"Tsaya ki saka min finger print dan uban ki" tace tana miƙa mata wayar da ta ɗaga daga cikin kayan jakan. Saida ta buɗe mata har WhatsApp sannan ta durƙusa a gabanta tana roƙonta don Allah kada ta faɗa ma abban su ba zata sake ba. Hajiya Hauwa ta saka ƙafan ta tokare ta tana shiga chats ɗin da tayi archiving don kada idanu ya kai kansu ta shiga bubbuɗewa amma ko na uku bata kai ba jiri ya ɗibe ta, maman Meesha da Zahran suka yi kokarin taro ta amma sun makare sai gata sharaf a dandamalin ƙasa.
....
*Edition hotel, Reykjavik*
*Reina*
Gashin kanta mai yawan cika ta tufke cikin ribbon, yau da ta samu lokacin kanta tayi zaman tsefe shi tayi wanka kuma gobe take so ta yi amfani da gift card da aka basu na salon ɗin hotel ɗin taje a kwantar mata da hankalin shi kafin ya cigaba da damun ta.
Ta juya a gaban madubin ban ɗakin tana ƙara kallon jan rigan barcin jikinta da wanda ya kira shi da babu ma bai yi laifi ba. Anya zata iya?.
Jan dogon numfashi tayi ta furzar ta ƙara turaren ta na turkey ta juya ma madubin baya ba tare da ta sake duban sa ba domin zai iya sakawa ta fasa, ta fita daga bathroom ɗin su zuwa cikin ɗakin inda ta baro Yaseer.
Yana zaune a kujera mai ɗan bouncing yana motsawa gaba da baya a hankali, hannun shi da tab yana ƙarasa duba investment request da zai bawa mutanen da zasu sake haɗuwa gobe.
Ɗakin da ƙarancin haske domin ya riga yayi shirin kwanciya, tunda Hajiyar shi tana off.
Ƙaran buɗe ƙofar ya saka ya ɗaga idanun shi daga abinda yake yi ya ɗaura a kanta ga hasken da yake fitowa daga bathroom ɗin ya bashi daman hango ta da kyau.
Da sauri ya ajiye tab a saman cinyar shi yana miƙewa zaune da kyau a yayin da Reina ke takowa ɗaya bayan ɗaya zuwa gare shi. "Damn!!" yace faffaɗan murmushi yana suɓuce mishi ya tsare ta da idanu tun daga yatsar ƙafarta dake da cikin lallausan slipper mai gashi ga zanen lallenta da kalan shi ya fara dishashewa har zuwa gashin kanta dake warware babu kitson da ya barta da shi da safe.
Ta ƙaraso a kunyace bata daina jin kaman ta juya ta zura a guje ba har ta iso gare shi ta ɗaga tab ɗin dake cinyar shi ta kashe ta ajiye a gefe sannan ta maye gurbin shi tana saka hannu cikin salo ta zagaye shi.
"What a surprise wifey. What a pleasing surprise" yace yana tallafo fuskarta ta kalli cikin idanun shi wanda yake ganin kaman nata har walwali suke yi.
Juya idanun tayi tana karya kai tace "hira na zo muyi, ka bani labarin yanda ranan ka ya kasance"
"It's boring, you don't want to hear"
"I do" ta faɗa cikin wata murya kaman wanda aka sirka ruwa da ƙanƙara.
Ya shiga bata labarin mutanen da ya haɗu da su da kuma abinda suka tattauna tun fitan shi.
Jin tayi shiru yace "barci kike yi ko?"
"No, no" ta murmusa tana ƙaramin hamma.
"So congratulations in advance, don ina da yaƙinin zaku samu da ikon Allah"
"Allahumma ameen" ya amsa yana daɗa rungume ta a jikin shi.
"Amma nima ina da wani gift da nake so in baka" tace tana daɗa narkewa a jikin shi.
Dirin sautin dariyan shi ta ji. Kana yace "Bayan gift ɗin dake hannuna wanda buɗewa kawai ya rage min akwai wani?"
"Yeah. Amma sai ka amince in iya bayarwa"
"Okay, sai muji"
Ta haɗiyi miyau ta ƙara sanyanta murya kafin ta fara magana "idan zaka yi min izini ina son in tsaya a gaban kotu in bada shaidar da zai wanke Yaya Yaseer, in ƙaryata kaina a gaban wanda na ƙaryata shi a gaban su. Don Allah mijina kada kace A'a"
Bai ce A'an ba kuwa don babu kalmar da ta sake fitowa daga bakin shi daga nan. Da ta ishe shi da magiya ma sai ya miƙe da ita a hannun shi yayi mata masauƙi a saman gado ya rufa mata baya. Idan magiya take son yi zai saka ta mai dalili.
Washegari da ya tashi sai ya fita tare da ita, suka je kuma cikin Sa'a aka amince da investment request ɗin shi suka yi sealing deal, har kaman ta fishi murna kuwa. Ya kai su wani halal restaurant ya siya mata cake suka yi celebrating su biyun su a can ya ɗaɗɗauke ta hotuna da wayan shi, don haka saida suka koma masauƙin su bayan maghriba ta ciro wayan ta take ganin missed calls har uku daga baƙon number na Nigeria.
Saurin mayar da kiran tayi hankalin ta na niman tashi gudun kada wani abu ne ya faru da wani nata ake niman sanar da ita, duk da tayi tunanin da ace hakan ne idan ba'a same ta ba za'a kira Yaseer.
Ringing biyu aka ɗaga sannan muryar mace yayi mata sallama wanda kana ji ka san ba yarinya bace don haka da Reina ta amsa sallamar sai ta gaida ta. Matan ta amsa faran-faran tana tambayar ta yaya Turkey, sai ta amsa da alhamdulillah. Matar kuwa ta shiga kwatanta mata wuraren da ya kamata suje a Istanbul har tana bata shawaran kada ta kuskura Yaseer ya dawo da ita bai kaita ba, ta riƙe mishi wuya.
Koma waye wannan ta santa amma bata santa na sosai ba, tunda har bata san sun kwana biyu da barin Turkey ba kuma ba a Istanbul suka sauƙa ba. sai tace "kiyi haƙuri dan Allah, lambar sabuwa ce ban gane waye ba"
"Baki gane ba Reina?" Matar ta tambaya da mamaki. "To mummyn ki ne Zuwairah, tunda ke kin manta da iyayen ki, ni gashi na kira in ji lafiyar ki"
"Ayyah aunty kiyi haƙuri dan Allah."
"Hmm babu komai, ƴan uwan ki ne daman suka bani labarin aikin da suka samu a wurin mai gidan ki, nace to ai yaran albarka ni ko sanar da ni ba ku yi ba shine nace bari na kira in yi godiya."
"Mmm.." ta sauƙe idanunta a kan Yaseer da ya fito daga alwala. Tana mishi kallon roƙo yace wani abu da zai saka ta samu dalilin katse kiran.
"Tashi kiyi Sallah." Yace yana amsar wayan daga kunnenta ya datse kiran.
108
"A haka kike cewa zaki iya bada shaida a court? Da wannan tsoron?" Ya cigaba da magana hankalin shi a kan wayar yana duba numbern da aka kira ta dashi.
Miƙewa tsaye tayi jin yau ya tanka a kan zancen. Ta ƙarasa gaban shi ta riƙo ɗaya hannun shi dake da danshin ruwa "Wannan daban ne bae, zan iya"
Sai ya ɗago idanun shi ya zuba mata fuska a tamke yana ɗaga kai yace "Ta yaya?" Shiru tayi ganin yana niman fusata sai ta shiga raba idanu tsilli-tsilli, amma ta kasa cire su daga cikin nashi.
Ya sauƙe numfashi kawai yana mayar mata da wayan ta "Idan ta sake kira kada ki ɗauka, na hana"
"Toh" ta amsa tana karɓan wayar, ya juya ya ɗauko musu darduma zai shimfida suyi jam'i tunda babu masallaci a kusa, ita kuma ta wuce ta ɗauro alwala.
Zuwa Lokacin da suka idar da Sallah kuwa Hajiya Zuwairah ta ajiye mata missed calls har biyu, haka ta share ta koma ta kwanta a saman darduman ta, ta kunna WhatsApp. Yaseer kuma ya janyo na'urar shi ya kunna sannan ya mayar da kanta saman cinyar shi, gadan-gadan ya shiga aikin dake gaban su da cewar zai tabbatar ya tsara komai yanda zai tafi musu Lafiya ne cikin kwana biyu ya tura ma team ɗin dake Niger su fara aiki a kai.
"Ki gafarce ni ko Umry" yace tana jin yanda yake typing da sauri sai ƙaran keyboard kawai kake ji babu jinkiri.
Ta mayar da hankalin ta kan chat ɗinta, ga saƙon gaisuwa da Suhail bayi gajiya da ajiye mata idan dai yana da wata buƙatar sai kuma tambayan wani irin turare Safina take shafawa da kuma brand ɗin jaka ko takalmin da tafi so, zai yi mata gift ɗin birthday ne.
"Hmm in banda samun wuri har wani zaɓen brand take yi?" Tace tana rubuta mishi 'ka zaɓi masu kyau kawai ka turo min in tura mata ta zaɓa sai ince tsaraban da zan yi mata kenan'
A take yayi mata reply
'Sai dake Aunty na' tare da turo mata hotunan wanda ya fara zaɓa din.
Ta mayar mishi 'amma birthday ɗin Feenah sai nan da wata uku fah' da emoji ɗin ɗaga gira.
'Sai bayan Sallan azumi kenan?, toh hala ta manta ne tace mun nan da two weeks'.
Reina tayi dariya, so makahon abu, tayaya za'a yi ace mutum ya manta da ranar haihuwar shi idan ba dai bai kiyaye ba tun farko? Ta so ta tsegunta ma Yaseer amma bata son distracting ɗin shi don haka ta fita daga kan chat ɗin Suhail ta koma na Safina domin ta san me zata faɗa mishi.
'Ke wai kika cewa yaya Suhail birthday ɗin ki in 2 weeks?' ta saka da emoji ɗin mamaki.
Tana sending kafin tayi typing ɗin abu na gaba Safina ta turo mata da 'Ai ni kuma na shiga goma'
'wato zaki wanki gara ko?' Reina ta turo ƙarashin zancen ta na farko sannan ta ɗauki maganar da Safinan tayi ta mata reply da 'baki shiga ba tukunna sai Allah ya kama ki da hakkin wanda kike son raina wa hankali ya baki shi a matsayin miji tunda baki son shi amma ba zaki guji abun hannun shi ba'