← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 117

Sashe 75

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin tana niman haukacewa ta so gudawa daga asibitin rashin passport ya saka ta haƙura. Haka ba yanda ta iya ta bishi ta cigaba da rainon abinda ta haifa, gashi can ba nan bane da maƙwafta zasu ke shiga maka balle su fahimci ba Lafiya ba, da suka ga basu ganin fitowar ta ko wucewar ta ma sai suka ɗauka bata nan ne. Haka dai bayan tsawon shekarun da Bilal ya mayar mata da gidan aure kurkuku sai gashi emergency surgery ya taso mishi ya fita ya manta bai rufe ɗakin shi ba ta shiga ta ɗauki passport ɗinta da na yaran ta da spare key na gidan da kuɗi ko kaya bata haɗa musu ba ta tattare su suka gudu.

Sai gashi bayan ta samu ta isa ƙasar su iyayen ta ko gidan basu bari ta shiga ba suka kora ta, har ƴan uwa da dangi kowa yaƙi karɓan su saboda guduwa yayi da ita suka je suka yi auren a masallaci ba tare da sanin kowa ba. don haka bata da zaɓin da ya wuce ta dawo gare shi shine da abun ya ishe ta kuma tayi-tayi ya sake ta yaƙi ta kai shi ƙara. Ganin zai iya rasa aikin sa da kuma daman zama a ƙasar da ya samu idan ya ja magana ya saketa da sharaɗin zata bar masa babban ɗan su, ta yarda saboda itama ƙarin ɗawainiya ne a kanta kuma ba ƙwaƙƙwaran abin yi take da shi ko mai kula da ita ba. Shine ya dawo da yaron Nigeria ita kuma ta nemi aiki tana kula da yarinyar amma wahala da ƙalubalen rayuwa yasa ƙarshe bata da zaɓin da ya wuce ta yarda ta dawo zama da shi gashi har ta haifa mishi ƴa ta uku."

Hannun Reina daii ya gagara barin bakin ta ga zuciyar ta dake dukan ashirin-ashirin.

"Ai baki riƙe baki ba tukuna, ba don Allah ya tsare mun tsananta bincike ba da yanzu kema idan kun tafi sai kin yi jikoki ki dawo ganin kaburburan mu. Kuma ni na bawa Daddyn Darling shawara idan kika yi taurin kai ya barki kije ki ɗanɗana don Allah, ashe dai da sauran lissafin ki.

_"Doll ni ke nake so zallan ke ba tare da komai ba. Afifa surkuwan general ce wanda zai nunata ma duniya saboda cimma wata manufar shi a duniyar Daula da siyasa, zama na da ita hoto ne kawai na ruɗan duniya amma kece matata mai ɗaki na, zan sirrinta ki a duniyata babu ruwan general ko Aunty Hauwa ko mummy M ko Ameesha ko Afifa dake domin bata ma san ki ba kuma ba zata sani ba!. ni kaɗai keda ke, zuciyata taki ce doll dan Allah kada ki bari a rusa kyakkyawan tanadin da nayi mana."_ ta shiga tunano Abinda ya faɗa mata a haɗuwar su na ƙarshe.

Wato ta tsallake rijiya ne da baya bata sani ba. Da yanzu ita ne zata kasance Afifa na biyu.

Ikon Allah.

~~~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*
94

~~~~~~~~~~
_Tu me trouverais ennuyeux_
_(you'll find me boring)_
_si je t'aimais à ta manière_
_(if I loved you like you did)_
~~~~~~~~~~

shiyasa ashe bayi damuwa suke waya mai tsawo koda ace yana gida. Kuma lokacin da ta san cewa da mata a gidan taga rashin dacewar hakan tayi mishi magana sai ya gwada ɓacin ran shi, ita kuma soyayya a lokacin da kake yinta kai da makaho duk ɗaya shiyasa bata ko yi tunanin idan itace a matsayin Afifa yaya zata ji ba. Koda ace yanzu ance zaman kawai suke yi amma duk da haka matar shi ce hakan cin fuska ne a gare ta.

"Ke kuma ya same ki baki da gata ga sokonci da wauta na ban mamaki shine zai saka ki a kwana yayi ta brainwashing ɗin ki.
da kuma Allah ya dawo miki da abinda kika rasa shine yaso kafin mu farga yayi wuff ya ɗauke ki yaje yayi yanda yake so dake. Shiyasa gwamma mu haɗa ki da ɗan uwan ki kafin mu wayi gari mu samu kema ya gudu da ke" yanda mariama ke bayanin nan zaka ce itace ta yanke hukuncin nan da kanta ba labarin abinda yake faruwa itama take samu ba.

Reina tayi shiru, kwana biyu duk wani abu da ya shafi Uncle Bilal sai ya saka jikinta sanyi. Ta sani ta shaida da kanta Uncle Bilal mutumin kirki ne kuma ya taimake ta irin taimakon da ba don shi ba hala da bata kawo yanda take da cikakkiyar lafiya da hankalin ta ba amma ko ita da ba wani buri take da shi a rayuwa ba bata jin zata iya irin zaman da Afifa tayi da shi. Ko ina aure zai kaita zata je amma ba zata iya rabuwa da ƴan uwa da iyayenta ba, ga ƴar uwarta kwalli ɗaya da take da ita a duniya, bata jin zata iya jure rabin shekara bata ga Maama ba balle daddynta.

.....
Kanta a ƙasa take zane da yatsar ta a jikin carpet ɗin dake lailaye a tsakar parlon.

Yaseer ya dubi dogayen yatsun kafarta masu haske yana ayyana yanda lallen bikin su nan da wata sati uku zai yi mata kyau matuƙa. shikam ma ance duk abinda aka saka masa rana saurin zuwa yake da shi amma ya tabbata banda ranar aure don a cikin sati ɗayan da ya shuɗe tun bayan saka musu rana yaci ace an cire sati biyu .

Ta ɗago jin yayi shiru ta dube shi daga yanda yake zaune shima a saman carpet ya tanƙwashe ƙafa ɗaya ya miƙe ɗaya yana jingine da kujerar dake kallon nata ai kuwa karaf suka yi ido huɗu, tayi saurin sake sunne kai ƙasa tana murmushi tare da kare fuskar ta da tafin hannun ta.

"Umry (my Life) Gani nazo ƙafa da ƙafa don wancan saƙon ba mai isowa ta waya bane so Please ki maimaita min abinda kika ce jiya in ji da kunne na"

Matse bakinta tayi cikin matsanancin kunya murya ƙasa-ƙasa tace "na manta fa"

"In tuna miki kenan?"

Ta girgiza kai. "Ka sha ruwa tukunna"

"Kin saka maganin mantuwa ne a cikin ruwan ko? Yanda idan na sha zan manta da abinda ya kawo ni shiyasa kika min tunin sha har sau uku?"

Kokarin dakewa tayi tace "A'a na soyayya na saka shiyasa na damu ka sha"

Ya shiga darawa sosai itama ta ta kare fuska tana taya shi. Sai da ya lafa musu yace "toh ai ba zai yi aiki ba Mon bijou (my jewel) don kin riga da kin gama da ni babu abinda yayi saura kuma"

"Shikkenan ba zan yi asaran kuɗi na ba nima tunda haka ne" ƙoƙari take yi ta ja hirar sun kaman yanda Ummi, Safina da malaman da ta fara ɗaukan darasussukan rayuwar aure a wurinta suka hore ta, don kullum idan yazo fa shine mai hira ita sai dai a barta da sauraro da murmushi amma yau ko ita taji ɗaɗin hiran balle shi da hakan ya gwada a fuskar shi.

"Reina, ina son ki. Irin son da baki ba zai iya misalta miki yawan shi ba saboda ba'a ƙirkiri kalmar da zata ɗauki girman ta ba, Amma ina fatan ki fahimci hakan a cikin rayuwar da zamu yi a ƙarƙashin inuwa ɗaya, sai dai lokaci ba zai ishe mu ki gani har ƙarshen shi ba koda ace zamu ƙara shekaru ɗari nan gaba".

Idan tace bata fara zurfi a cikin soyayyar Yaseer ba ta san tayi ƙarya, kuma tana daɗa dulmiya Uncle Bilal yana ficewa a ranta. sannan yanzu soyayya take yi mai sanya nutsuwa da kwanciyar hankali, babu takura, fargaba ko sammatsi a tare da ita, sai ma ta fara dasa ayar tambaya a kan wanda tayi a baya don kaman ita ta tursasa zuciyarta ya amshi abinda tazo dashi ba kaman yanzu da zuciyar ne ke riƙe da linzamin ta ba, kuma janta take yi Wurin Yaseer kai tsaye.

"Nima ina son ka yaya Yaseer, sosai"
Ya dube ta da mamaki don bai yi tsammanin samun amsa daga gare ta ba. Sai zuciyar shi tayi mishi sanyi tayi mishi haske kaman babu sauran duhu a cikin ta.

Ta sake ɗagowa suka yi ido huɗu da shi da yake aika mata kallon mamaki amma a maimakon ta sunne kai ko ta rufe fuska kaman ɗazu sai ta sake masa murmushi mai sanyin da ya saka shi fara tasbihi ma Ubangiji a cikin ran shi.

"Ba zaka sha ruwan ba?" Ta tambaya ta katse shirun don yaƙi take yi da kunyar ta na ƙanƙanin lokaci kuma idan suka cigaba da zaman kuramen nan yana mata kallon da shima bai san yana yi ba zai sake dawowa.

"Dole na Reina. Dole na" yace yana ɗaukan glass ɗin da ta tsiyaya mishi ruwan ya kai baki, idanun ta zasu tafi tamɓele kallon Adam's apple ɗin shi tayi sauri kawar da su.

"Na jiya da kika faɗa ma haka yake kenan?"

Ta gyaɗa masa kai cike da tabbatarwa. Sai ya shaƙi iska ya sauƙe ajiyar zuciya. "Na ranan fa da kika tura min kika goge? Shi kuma suɓul da baka ne ko ince da hannu?"

Sai ta ɗan yamutsa fuska alaman tunani don bata fahimci kan zancen shin ba.

"Ranar da muka fara chat a WhatsApp"

"Oh" ta juya ido da ta tuna. Ashe duk lokacin nan yana riƙe da shi bai tashi magana bane sai yau?.

Shafa ma idanunta toka tayi tace "well... Lokacin zuciyata ne ta rubuto tunda idanu na sun makance, dake ban gaji da makanta ba shine na goge amma a yafe ni dan Allah"

Wannan karon Yaseer ne ya samu kan shi da kasa magana, itama kunya kaman ta tona ƙasa ta shige ciki wannan malamar zata jawo mutuncin ta ya zube baki ɗaya a idon yaya Yaseer. Kokwanto yake yi anya wannan kuwa wannan Hafsatu Reinan shi ce kokuwa an canza masa ita ne bayan tazo gidan Ummi?.

Yayi gyaran murya sannan ya sauya akalar zancen ganin yanda duk tabi ta damu harda juyawa ta fuskanci wani gefen.

"Waye ya buɗe miki social media handles? Safinah ne ko?"
Chapter 75 · 0% Book details