← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 117

Sashe 79

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kai matsa can, ba kai kace idan aka yaɗa hotunan yaron nan zamu kai shi ƙasa ya rasa komai abubuwa su zo ƙarshe ba?. Toh gashi ma hala kai kayi mishi dalilin Aure kaga yanzu zasu haɗa ƙarfi da ƙarfe kenan "

Alhaji Salisu ya nuna Hajiya Hauwa "ga mai ƙaramin tunanin da ta bada wannan shawarar ba ni ba. Ai nikam wannan mata ta zamo min annoba, wallahi ɗana da kuɗaɗe na suna fitowa duk tsufan ki sai kin koma gidan uban ki don na gaji da asara nikam."

Tuna ranar da ƙawarta ta kawo mata gulman da taji a napep Hajiya Hauwa tayi, tace saboda motar ta ya ɓaci mata a hanya makanike yana dubawa shi ne ta shiga napep ta gangaro gidan, kuma taji sunan amaryar irin na yarinyar da ta riƙe amma bata ga fuskar ta ba.

A lokacin ƙaryatawa tayi ta dangana zancen da son gulma irin na matar, ashe kuwa Reina da Yaseer ɗin da ta sani ne.

......

*Reina*

Da kiran ya shiga mishi katsewa ya fara yi sannan yayi calling ɗinta back a take.

"Assalamu alaikum. Umry?"

"Yaya Yaseer baka yi barci ba?"

"Ke zan tambaya Umry, me kike yi har wannan lokacin baki yi barci ba?"

Ɗaga ido tayi ta kalli agogon ɗakin ta ja gauron numfashi ganin har ɗaya ta wuce. Ita dai ta san tabbas dare yayi sosai Amma bata yi tsammanin kamar haka ne ba.

"Ashe lokaci ya tafi har haka? Na ɗauka fa bai wuce ƙarfe 11 ba, baƙin Dass ne suka sauƙa shine fa ake ta hira ni kuma na bar wayan a nan yayi caji, ashe ba don Baba ba sai dai muji ana kiran sallan asuba don shi ya shigo ya watsa taron."

"Lallai kam, yayi kyau. Ni da naga kiran ki har na fara tsoron ko ba lafiya ba"

"Lafiya ƙalau missed call ɗinka na gani na biyo"

Tana jin sauƙan numfashin shi wanda ke haɗe da gajiya Sannan ya amsa da "Oh, I thought kinyi barci ne shiyasa ban sake kira ba"

"Amma kai ma muryar ka bai yi kama da na mai barci ba. Ko aikin kake kan yi babu hutawa? Ramewa kake so kayi a hotunan bikin mu?"

Ya saki murmushi mai sauti yana jin gajiyan ma a hankali yana rabuwa da shi. "I have severe Insomnia, ko kwanciya nayi ba zan iya barci ba, yawancin lokuta sai na sha maganin barci, yanzu kuma abubuwa sun sha min kai ya ƙare na manta ban yi refilling ba."

"Yanzu barci ne sai da magani?"

"Kiyi haƙuri na so in sanar da ke tun wuri na manta, Allah yasa bai isa dalili da zaki haƙura dani ba. Ban ɓoye miki da gangan ba believe me"

Cike da tausayin shi da ya gwada a cikin muryarta tace "mai kake faɗa haka. Akwai wani abu da zai raba ni da kai a yanzu bayan ikon Allah?"

Yayi murmushi mai sauti jin da iya gaskiyar ta tayi maganan "Nagode Umry and zan gwada sake zuwa therapy bayan auren mu in gani ko zan iya rabuwa da shi saboda ke tunda na gagara a karan kaina"

"Amma ai naga kana barci idan muna tare a study Room" ta faɗa don har yanzu mamakin abinda ya sanar da ita bai barta ba.

"Ina ganin saboda ke ne, saboda kina kusa dani, shiyasa yanzu ma nake son ganin ko jinya zai karɓe ni idan kina tare dani."

"Toh wani sati sai muje in raka ka ko?"

"Oh ashe fa wani satin iwar haka kin zama tawa."

Ta rufe ido da hannu tana faɗin "bari na wanke baki na kwanta yaya Yaseer. Kaima ka gwada kwanciya kayi addu'a in sha Allah zaka samu barci yazo. Kayi ta nanata "
اللَّهُمَّ غَارَتِ النُّجُومُ، وَهَدَأَتِ الْعُيُونُ، وَأَنْتَ حَيٌّ قَيُّومٌ، لَا تَأْخُذُكَ سِنَةٌ وَلَا نَوْمٌ، يَا حَيُّ يَا قَيُّومُ أَنِمْ عَيْنَيَّ وَأَرِحْ لَيْلِي".

(Allahumma gaaratil nujoum, wa hada'atil uyoun, wa anta hayyin qayyoum, la ta'akhudhuka sinatun wala naum, ya hayyu ya ƙayyoum anim aynayya wa arih laylee.)

Da A'uzhu bi kalimatillahi tammati min ghadabihi wa iƙabihi, wa sharri ibadihi, wa min hamazatit shayaɗini wa an yahduru ni."

"In sha Allah Umry, jazakillah. Sweet dreams"

Da "same to you" ta katse kiran tayi shirin kwanciya tana ƙirgen daga gobe sauran kwana biyar kacal, lallai abu ya zo in ji mai tsoron wanka.

.....

"Mai kake so in yi?"

Uncle B ya kalli Aicha da ta toshe da baƙin gilashi ya saki murmushi kana ya dire mata Containern magani a gaban ta.

"So nake yi ki canza ma Reina maganin ta da wannan.

"Saboda?"

"Theophylline ne a ciki, zan san yanda zan yi in ƙara mata dosage. So nake yi ya ɗaga ciwon ta."

Ta ware idanu cike da tsoro, tunawa da bayi ganin idanunta ta zare gilashin tana daɗa ware masa su.

"Kashe ta kake son yi?"

"Ta yaya za'a yi in kashe wanda nake so? Na ƙanƙanin lokaci zan bari yayi aiki kafin su nime ni idan sun gagara kamo bakin zaren tunda ni na fara mata prescribing maganin dama, idan ma basu nime ni ba zan zo da kaina daga nan in ɗauke ta daga Asibitin. kinga idan mutane suka taru babu amarya dole a haƙura da aure, idan na dawo da ita daga baya kuma dole a aura min ita tunda basu da wani zaɓi?"

"So kidnapping ɗinta kake so kayi kuma ni Aichatou kake son in taimaka maka?" Ta tambaya tana gwada kanta da yatsa.

"Ba zaki kira shi da kidnapping ba tunda babu kuɗin fansa sai nine ma zan basu sadaki. And nayi miki alƙawarin ba zan cutar da ita ba, ko ƙuda ba zai taɓa ta ba har in dawo da ita"

Ta mayar da gilashinta ta miƙe tana daukan jakar ta "soyayya ai ba hauka bane. Idan kai Reina ba zata iya auren ka ba bayan tayi aure ni Yaseer zai iya aure na"

"Toh baki tsaya kin ji plan B ba, ai bani da tabbacin wannan zai yi aiki dama"

Bata saurare shi ba ta fice a wurin yayi murmushi don ya san zata dawo, kawai dai kada ta bari lokaci ya ƙure musu.

.....

Zuwa yanzu gidan Ummi da gidan Umma ya cika ya tumbatsa, don gobe Alhamis amarya zata fara events ɗin ta.
Sun shirya zata yi Qur'anic picnic sai walima shi kuma ango dangi da abokai sun haɗa mishi dinner babu yanda ya iya.

Reina kuwa tayi ruwa tayi tsaki a kan yanda take son komai ya kasance, Ga event planners ga Safina da ƴan uwan mahaifiyar ta suna bakin ƙokarin su amma ita take ta hidimomin ta da kanta.

Yanzun ma Safina ta saka a gaba ta karɓo mata gown ɗin da zata saka a wurin walima ba sai gobe kai ya ƙara zafi ba, shine tana shigowa da shi mutane suka yayyameta zasu gani Reina ta fakaice su ta wafce laidan ta zura a guje tayi ɗakin Ummi ta rufo ƙofa.

Tana jiyo su suna ta maganganu da buga ƙofa wai bata da kunya bata kula su ba ta shiga gwada rigan tana ganin kanta a madubi.

Can suka gaji suka bar bugun ƙofar kaman zasu ɓalla shi kafin ta fara jin knocking ɗin masu hankali don haka ta ƙarasa jikin ƙofar tana tambayar "wanene?"

"Dalla nine idan ba zaki buɗe ba in ƙara gaba bani son iskanci"

Tayi saurin buɗe ƙofar Safina ta shigo tana kumburi kafin ta mayar da ƙofar ta rufe.

"In banda iskanci kin san awa na nawa ina zaune a gaban tela shago duk maza? Amma ko godiya ai ba zaki iya yi ba kin fauci kaya kinyi gaba. Ko nace miki dama barinsu su gani zan yi?"

Ta riƙo hannunta "sorry my Feenah, a sirace kinji babban ƙawar amarya?"

Tayi ƙwafa "a sirace ma kike cemin? Idan na tafi zan ga uban da zai biye ma fidda ficen ki. tunda ga kayan nan sizes ɗin ki available muyi order kika dage sai wanda babu size ɗin ki saboda kin samu Feenar banza.
Ni da na ɗauka shagali zamu yi a biki duk nayi baƙi harda rama ke kuwa kaman an canza ki, Allah ya kawo nawa bikin Wallahi ko yara gare ki sai kin rama min"

"In sha Allah ramako dole. Ai ko yaya Yaseer saida yace ayi miki Godiya da jinjina"

Ta ɗan murmusa tana mayar da hankalin ta jikin kayan da Reina ta saka. "Gashi kuma ya zauna miki ɗass babu wanda zai ce ba haka yake ba."

Tayi juyi a gabanta ta jin daɗin ta take ciki ya bayyana a yanayin ta, sai Safina ma taji a ranta bata yi zaman banza ba.
"Kin duba snall veil ɗin da za'a yi miki rolling da babban gyalen, yadin ɗankwalin ma yayi?"

Sai Reina ta rungume ta. "Nagode miki sosai Feenah, Allah ya baki mai miki kema"

Tayi dariya "gaki nan Allah ya riga ya bani"
.
.
.
Washegari da safe aka zizara mata lalle baƙi da ja kuma ta mayar da hankali ganin a wannan karon bai dagule ba ko kaɗan sannan tayi haƙurin zama har ya fito rass kafin ta wanke.
Yaseer ya turo Muhammad ya kai su gidan kwalliya sannan da aka gama ya koma ya ɗauke su zuwa wurin da za'a yi Qur'anic picnic wanda ya ɗauko mata ƙwararrun masu decorations tun daga nesa.

Wuri yayi kyau anci an sha an kuma sha madarar Al-qur'ani. Abin mamaki sai ga Zahra da Zaheera da sauran cousins ɗin Reina ta ɓangaren mahaifinta sun zo sun ware aka yi komai da su har taro ya watse lafiya.

~~~~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

97

Da farar safiya dangin Alhaji Tahir suka yi sammakon zuwa gidan Ummi da niƙi-niƙin kayayyaki kama daga abinci har zuwa ƙayan tsaraba, tun da ba'a kai bikin wurin su ba ai gashi su sun zo.
Chapter 79 · 0% Book details