← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 117

Sashe 92

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata daina jin hanjin cikinta suna hautsinawa ba a duk lokacin da yayi mata kallon da bayi halarta sai da ni'imar aure ko kuma idan ya kai hannun shi jikin ta. Sabon rayuwar da ta samu kanta a ciki ya gagara zame mata jiki duk da bayan wannan daren da ba zai taɓa gogewa a cikin tarihin rayuwar su ba Yaseer bai sake yunƙurin kusantar ta ba. Zasu kwanta a shimfida guda suna jin ɗumin juna, gabaki ɗaya kwanakin sun kasance tare da juna a kowani lokaci suna komai a tare saidai idan ɗayan su zai shiga wanka ko shi zai fita Masallaci, amma yanzu ko kissing ɗinta deep ya daina saidai ya ɗan yi pecking ɗinta a baki ko kunci ko a goshi kokuma ya rungume ta.

Hannu na rawa ta danna snap button hoton ya ɗauku ai kuwa suka fito duru-duru.

Dirin murmushin sa taji a bayanta dake manne da ƙirjin shi, hannun shi dake wuyanta ya ɗan zamo absentmindedly zuwa saman ƙirjinta lokacin da ya miƙa ɗayan hannun shi ya amshi wayan daga nata, sannan ya saita cameran a jikin mirror ya ɗauki na farko wanda suka fito da kyau. Hoton yayi adalci ma kwalliyar da suka ci kuwa, yana sanye da shadda fara ƙall sai ƙyalli take ga hulan kansa ya dace da zubin fuskarsa ita kuma straight gown ne na atamfa embellish a nata jikin, ta kafa ɗaurin ture da ya samu support din zama da kyau a kan parking ɗin da tayi da kalan scrunchie ɗin da ya shiga da kayan, sai kuma sauƙaƙƙiyar kwalliya a kan fuskarta.

"Bari in ƙara mana wani" ya faɗa ko zata gyara tsayuwanta ko ta canza styles amma hankalinta yafi raja'a a kan fuskar shi zuwa leɓɓen shi da take jin tayi kewar su.

Ya saita cameran, yana tambayan ta "you ready?" Ta share vibration ɗin da take ji a duk lokacin da yayi magana tayi ƙoƙarin mayar da hankali a kan camera sai kawai taji ɗumin numfashin sa a gefen wuyanta kafin ya sumbace ta a kunci lokacin da ya ɗauka, bata san ta lumshe ido ba saboda yanda sumbar ya ratsa ta, kwana biyu jikinta karɓan saƙonnin shi suke koda kuwa ba da niyyan saƙon ya tura mata ba.

"Wifey, are you okay?" Ya tambaya yana juyo da ita ta fuskace shi.

Ta buɗe idanunta suka sauka a cikin nashi dake bayyana yanayin damuwa, sannan ta mayar da duban ta kan lips ɗin shi, bata san me ya jata ba a lokacin tunda ba zata ce shaiɗan bane amma ta samu kanta da yin ɗagyalgyal dukda tana kan takalmi mai tsini kuma ya ɗan ranƙwafo kafin ta samu bakin ta ya kai saitin nashi ta lumshe ido a hankali sannan ta manne su sai kuma ta ja ta tsaya.

Second ɗaya..biyu..uku suka ɗauka a haka.

Wayanta dake hannun shi Yaseer ya ajiye a kan handrail ba tare da tunanin zai iya zamewa ya faɗi har floor ɗin ƙasa ba, ya saka hannu a kunkumin ta ya janyo ta jikin shi da kyau ɗaya hannun ya zaga bayan wuyan ta Sannan ya ɗaura mata karatun daga darasin da ta tsaya.

"Umry!" ya sake kira yana tallafo fuskar ta a cikin hannun shi, "Lafiya? Ko barci kike ji?"

Yanzu abun nata har ya kai ta fara mafarkin tsaye? Buɗe idanunta tayi amma ta kasa saka idanunta cikin nashi sai ƙirjin shi dake daidai da tsayinta take kallo, Ta hango wayar ta da ya ɗauki hoton a cikin aljihun gaban rigan shi, amma shine ƙwaƙwalwarta dake yana da raunin lissafi ya kasa hango mata idan ma suka shiga wani yanayin yana da aljihu, ko duk zaƙuwan ce haka? Duk da dai ba wai mu'amalar aure take son ya sake shiga tsakanin su ba samm, kusancin da ya fara sabar ma jiki da zuciyar ta shine take so.

Ya cigaba da cewa "Ki koma sama ki kwanta kawai, I can go from here. Idan an tashi daga juma'a zan bi gidan Umma in gaishe su, akwai abinda kike so in kawo miki?"

Murmushi ya kawo a fuskarta lokaci ɗaya tace "in ɗauko mayafi na toh mu tafi tare?"

"Kin daina jin barcin kenan?"

Ita bata san yaushe ta amsa masa tana jin barci ba amma sai ta gyaɗa kai. "Barin yi sauri in zo".

Ta juya zata haura da saurin ta ya riƙo hannunta ya dawo da ita ta sake tsayawa a gaban shi. "Keda baki da Lafiya Umry, ki bari sai next time"

Narai-narai tayi da idanu, "Please bae, ai na warke babu abinda ba zan iya ba yanzu Allah"

Da bayi son ya tafi da ita a yau ɗin ma, amma kuma babban dalilin shine bayi son taje ta haɗu da Aicha tace zata ɗaga hankalin ta shiyasa shima bai je ya duba ta ba har ta gama kwanciyan ta a asibiti aka sallameta, daɗin daɗawa da ta zamo wanda Bilal zai iya haɗa baki da ita a cutar da Reina da shi da ma iyayen su tunda harda sunan su ne zai ɓaci da ace buƙatar su ya biya.

"I promise, next time Amma yau ki kwanta ki huta. Idan zan dawo ma zan taho da dinner kada kice zaki yi girki"

Ta gyaɗa kai cikin sarewa tunda ba musu, suka taka har jikin mota ya miƙa mata wayanta yana mata tunin shan magani yayi pecking ɗinta a goshi kana ya shiga ya tada motan, itama tayi mishi addu'an Allah ya tsare, saida taga an wangale mishi gate ya cilla hancin motar kan titi, kafin ta koma ciki.

Sai taji gidan yayi mata girma da faɗi gashi ko ina shiru kwata-kwata babu daɗi. Ita yanzu idan ya fara fita office yaya zata yi kenan? Daɗin ta ɗaya itama tana zuwa makaranta.

Komawa parlon shi tayi ta miƙe a dogon kujera tare da ɗaukan remote ta kunna TV zata cigaba da kallon da suke yi tare a Netflix, sannan ta kunna datan wayan ta messages suka fara shigowa.

Status ɗin Friday ta fara sakawa kafin ta koma kan messages daga aunties da cousins ɗinta sai kuma Suhail da yake mata tunin maganan su.

Ita tama manta saboda abinda ya shigo gabanta kwatsam ya sha mata kai. Chat ɗin Safina ta shiga ta yi replying saƙonnin da ta ajiye mata last, suna tafiya taga yayi tick guda biyu alamun tana online don haka bata jira komai ba ta kira ta voice call.

"Ya ne?" Shine abinda Safina tace bayan ta ɗauki kiran da ta bari ya kusan tsinkewa.

"Assalamu alaikum"

"Waalakumussalam, ya ne?" Ta sake maimaitawa.

"Feenah don kin samu na riga da na auri yaya Yaseer kin gama mishi campaign shine zaki fara mun wulaƙanci ko kuma don ƙanin mijina yace yana son ki ina mishi campaign?"

Tsaki ta ja, "kema akwai ki da maida gobe tomorrow Wallahi. Ni ki barni in gama shiryawa yawon juma'a zan tafi yanzu ma zan kashe datan"

"Allah sarki, nikuwa gani ni kaɗai a gidan, mijina sai dare zai dawo hala, ina zaune ni kaɗai kamar mayya gashi ba daman fita ko nan da ƙofa" Ta ƙarashe muryarta yana rawa domin ta san yanzu zata ɗaga mata hankali.

Amsar da ya fito daga bakin Safinan ne ya bata mamaki "Toh ni ina ruwana? Ba haka auren yake ba? Ai zaman ibada kike sai kiyi tayi ma Annabi salati Sallallahu alaihi Wasallam ki samu lada. Ko zaki ganni ma sai wata sati don na gane nufin ki. Bye" ta katse kiran.
.
.
Bedroom ɗin shi ta koma tayi sallan azahar da lokacin ta yayi. Ta idar tana zaune tana addu'o'i wayanta dake bakin gadon ya shiga ruri, ta jawo ganin sunan Safina tayi saurin picking ta ƙara a kunne. "Ya aka yi?" Ta tambaya murya ba karsashi.

Daga ɗaya bangaren tace "Gidan kun dama sai an tuhumi mutum ne kafin a bashi daman shiga? Nan da minti biyu Allah zan yi zuciya in koma."

Zumbur ta miƙe da wawakeken murmushi a kan fuskar ta. Basu wayan dan Allah, tace tana naɗe darduman da ta tashi a kai da hannu ɗaya. Yama ci ace Yaseer ya saka an jona intercom ɗin dake gidan ya fara aiki tunda sun fara samun baƙi.

Da hijabin sallanta ta sauƙa, kafin ta kaiga buɗe ƙofa kuwa Safina har ta iso, tana ganinta ta saka zumbulelen hijabinta ta rungume ta dashi suna tsalle da ihu a wurin.

Safina ce ta fara ɓanɓare Reina daga jikinta da faffaɗan murmushi itama a kan fuskarta take ƙare mata kallo daga sama zuwa ƙasa.

"Iye matar ustaz, wannan hijabi haka Masha Allah"

Dariya Reina tayi tana jawo hannunta ciki tace "da'allah Sallah nayi" tana kwaɓe Hijabin daga kanta da yanzu yake babu ɗankwali, suka samu 3 seater suka zube a kai.

Safinah ta ɗan ɗago ta gyara zama tana mayar da numfashi, "kai samun napep azaba, dama Daddyn Sabrina nace yazo ya kawo ni" tace don taji bakin Reina.

Aikuwa ta amshe da "Amma shine idan na shiga motar Uncle B sai ki dawo Sheikh Assim alhakim ko Omar Suleiman kiyi ta zubo wa'azuzzuka da fatawowi."

Tayi dariya "ba zaki bani ruwa bane sai na roƙa?"

Reina ta harare ta, "ai naga baki san hanyar kitchen ba ko kin makance baki ganin dispenser a can"

"Ai wulaƙanci zaki mun da kika samu na zo? Bismillahi bari ki gani" ta miƙe tana mayar da mayafinta.

Reina ta dauki jakarta ta rungume tana faɗin "sai anjima"

"Kinga ba don muna ganin mutuncin juna ni da yaya Yaseer ba Wallahi sai in danne ki in ƙwata ai ba yau muka fara raba hali ba"

"Kina ganin mutuncin nashi kike wulaƙanta kanin shi? Kin saka bawan Allah yana ta mana sintiri"

Komawa Safina tayi ta zauna tana dafe goshi "na shige su. Yanzu shima ya sani kenan? Wannan mutumi ya gama tagayyara ni a gari"

"Toh wai meyasa ne ba zaki saurare shi ba kawai"

Harara ta watsa mata "ɗan wannan yaron? In banda raini ma ina ni ina yaya Suhail dan Allah? Ko dan yaga ina sake mishi fuska?"
Chapter 92 · 0% Book details