Sashe 12
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suka shiga da Reina changing room ta saka mata kayan ta fito wani duguzum-duguzum ta yafa gyalen a kan kitson ta da ya gama tsufa, sai yaga bata yi kyau ba.
"Armm.. Please baku da ɗan lipstick ɗinnan ne ku ɗan shafa mata? A ɗan wanke mata fuskar ma" har yanzu wurin da ta mari kanta yana nan jawur sai ya fara danasanin sakata da yayi, da ya bari sai sun dawo.
Matar mai wurin da kanta tazo ta jata toilet aka wanke mata fuska da ƙafa ta ɗauko mata wani takalmi mai kyau ta bata wani paper bag tace ta saka wanda ta cire, sannan ta zaunar da Reina a kan kujera, ta fara kwantar mata da gashin goshinta da gel kana ta ɗibo office pins tayi mata ɗaurin turban da gyalen, bakin lace ɗin jiki ya fito ta shafe ɗin V da ɗaurin ya bada ga sumanta da ya kwanta luff kaman ba kamɓorin datti bane a jikin shi.
Powder ta ɗauko daga cikin jakarta ta shafa mata ya kuwa amshi fatarta tunda itama tana da haske sosai, ta saka mata lip oil da ya bawa bakinta kalan pink kaɗan sannan ta saka brush ta taje mata gira ta gyara shi, ta fesa mata turare sai ga Reina ta fito cancaras.
Uncle B yayi mamaki da ya ganta kaman ba itace wacce suka shigo shagon a tare ba.
Bayan ya biya kuɗin kaya da takalmin kafarta saida yayi alkhairi wa matan don yaji daɗi, kuma yace su bawa Reina sabon loopers ta yarda na cikin jakar nan yayi mishi ƙazanta.
Suka shiga mota tana ta zabga murmushi, shima cikin jin daɗin ganin farin cikin ta suka isa hall ɗin dinner sannan yaja hannunta zuwa ciki.
Su Hajiya Hauwa suna kallo suka shigo suka ratsa mutane suka wuce, Bai ajeta wurin kowa ba ya ƙarasa table ɗin abokai da ita ya saka ta zauna a kujeran shi ya jawo wani ya zauna a gefenta.
Gabaki ɗaya sai ta tsorata kada ta sake yin wani abun kuma ga snacks da drinks da aka shaƙe table ɗin dasu kala-kala tana tsoron taɓawa, har sai da ya jawo Plate ɗin samosa da goran pulpy orange ya tura mata gabanta kafin ta ɗauka ta fara ci, sauran abokan suna ta tsokanarta amma sai ta ƙoshi tukunna zata kula su.
Ganin zata ɓata jikinta Uncle B ya kawar da plate ɗin naman kaza da wani aboki ya ajiye mata don yana jin daɗin kallon yanda take ciye-ciye kaman bata da wani damuwa a duniya. ya zaari tissue a kwali ya riƙo hannun ta yana goge mata, sai ta dubi baturen gefen ta da yasha babban riga shima tace "you look handsome"
"Thank you kiddo" ya amsa da murmushi ya miƙo hannu su gaisa, sai ta ƙwace nata daga na Uncle B ta mika mishi suka yi handshake. Haka ta shiga bawa kowa hannu suna gaisawa a table ɗin tana faɗa musu sunyi kyau suma suna cewa ta fisu kyau ai har da musu Reina kam, tana fayyace musu abinda keda kyau a fuskar su. Da abintan ya ishi uncle B ne ya kamo hannunta wai suje suyi manni.
Tsayin ta ba zai kai ba don haka ya yunƙura ya ɗauke ta don ta zuba ma su Meesha bundle ɗin sabbin kuɗin da ya fasa ya bata, ta shiga zaran su ɗaya bayan ɗaya kuwa ta saka ma amarya ta saka ma ango, aka shiga ɗaukan su a hoto don sunyi kyau sosai gashi rigan yayi ɗass ma Reina, Zaheera tana tsaye tana kallon su da tuƙuƙin baƙin cikin jin dama itace ake mata haka. Su da Uncle B har tsoron zuwa jikin shi suke yi amma ji yadda yake yi da Reina.
Murmushin kan fuskar Meesha ne ya ɓace lokacin da ta gane kamannin Reina.
"Uncle B!" Ta Kira shi kaman zata saka ihu tana matsawa baya, Doctor Fahad ya riƙeta kada tayi tuntuɓe da ƙasan bayan gown ɗinta.
"Lafiya?" Ya tambaya ganin tsoron dake cikin idanunta.
"Itace fa yarinyar, yarinyar da ta saka aka rufe Yaseer...."
49
Sammako yayan Fauziyya yayi zuwa gidan gidan Hajiya Hauwa ɗaukan Reina taje tayi ma Ummi weekend, sun yi da ita a kan duk karshen wata zata dinga zuwa tana yi musu kwana biyu amma tun shekaran jiya yake sintiri ana ce musu sun je biki duka gidan.
Ummi taso ta bari weekend ɗin gaba a ɗauko Reinan tunda yanzu lokaci ya tafi har Lahadi amma rainin hankali ne ai bata kai wanda zasu faɗa mata halinda ake ciki ba, kuma tana da tabbacin masu gadi zasu sanar da ita sintirin da suke yi a gidan, bata kuma iya ɗaga waya ta kira ta bada haƙuri ba. Shiyasa tace a ɗauko tan ikon da suke taƙama dashi a kanta suma suna dashi, duk talaucin su dai Reina jinin su ne ƴar cikinta ta tsuguna tayi naƙudan ta.
Ba'a yi mishi iso cikin gidan ba haka ya tsaya a waje yana jiran ta fito. A cikin jakar makarantarta ta haɗa abinda take tunanin zata buƙata Zaheera ta taya ta kimtsawa dan daɗi take ji yau ba za'a tafi da Reina wurin buɗan kai ba balle Uncle B ya sake bata kayan da yafi nasu kyau irin na jiya.
Da gudu tazo ta ɗale shi tana murna, yayi ƙasa da wuya ya sauke ta jin tana niman karya shi.
"Wai baki san kina da nauyi bane Hajiyar mu? A hakan ma naga rashin lafiya ya ɗan sace ki" ya riƙe hannunta yana juyar da ita tare da duba jikinta, ga dai kaya ta saka amma bata yi fasali ba kaman wata bogaza, ba kaman lokacin da Fauziyya take shiryata ta fito abin sha'awa ba, ko Alhaji Tahir ma yana kamantawa a bayan ranta.
Ita kuwa Reina tunaninta ne ya tafi kan abinda ya faɗa, Tana da nauyi? Amma shine Uncle B ya iya ɗaukan ta na tsawon lokaci a daren jiya? Lallai Uncle B yana da ƙarfi.
Tunawa da abinda Meesha ta faɗa mishi tayi, 'itace yarinyar da ta saka aka rufe Yaseer, itace tayi mishi sharrin da ya lalata mishi rayuwa'.
Kuka ta fashe dashi a lokacin saboda tashin hankali, Meesha ma kukan take yi don haka Uncle B ba tare da yace da ita komai ba ya juyo da Reina suka bar hall din, bai ajiyeta a ƙasa ba saida suka fito waje.
Hajiya Hauwa ta biyo su a baya itama nata hankalin a tashe, Bilal dai ba zai huta ba sai ya since mata zani a kasuwa tunda gashi nan asirin su yana rufe tsawon shekaru 3 an birne zancen nan amma zuwan shi sati ɗaya kacal yana ƙokarin bankaɗo shi.
"Bilal lafiya dai? Ina kuma zaku sake zuwa?" Ta ƙare maganar haɗe da haɗiyar miyau. Tana yafato Reina da hannu ta dawo jikinta amma ta maƙale a gefen Uncle B tana riƙe da babban rigan jikin shi gamm kaman shi zai bata kariya.
sauƙe hannun shi yayi daga kan Goshinsa kana ya juyo ya dubeta ɗaya hannun shi a cikin aljihu.
"Zaki faɗa min abinda yake faruwa ne Addah Hauwa ko inje in bincika da kaina? General yana nima na kuma ba zan tafi ban gama fahimtar gaskiyar lamarin nan ba"
Ambatar general kawai da yayi saida ya saka cikinta ya hautsina, yo ai gwara duka duniya su san da wannan lamari a kan ya shiga kunnen general, bata da haufin idan ya cireta daga cikin yaran shi yayi mata da sauƙi.
"Wallahi duk munafurci ne da sharri"
"Na san da hakan shiyasa ke nake son ki faɗa min gaskiya, nasan kin sani yanayin ki ya gwada"
Zata iya cewa tunda ta haifi Zahra bata taɓa faranta mata ba kaman a lokacin da ta fito riƙe da hannun Zaheera dake tirjewa domin yanzu ma ta fara cashewa, shine za'ace wai zasu tafi gida.
"Umma gamu nan" ta katse mata tseren da tunaninta ya tafi na nemo kalaman da suka cancanta ta kare kanta dasu a cikin ƙwaƙwalwarta.
"Reina zo mu tafi gida, Bilal ka bar maganar nan zuwa wayewar gari yara suna jin barci" ta manta rabon da ta kira wannan laƙani mai ban haushi, har a gaban ita takwarar tata ma yanzu Hafsatu take kiran ta.
Kallon 'Are you kidding me?' Yayi mata. Yace "shikkenan, saida safe zan samu ita Ameeshar tayi min bayanin komai daman ni naƙi sauraron ta a da ɗin ma, yanzu kuma a shirye nake"
Saboda tsananin tsoro har suka isa gidan bata iya ce ƙala ma Reina ba har yau da safen kuwa, jiran kiran general kawai take yi domin babu abinda zai hana Meesha sanar da Bilal.
Sai gashi kuma wai anzo ɗaukan ta, ita su tafi da ita har abada ma tunda bakin alƙalami ya kusa bushewa, bata ga amfanin riƙeta da zasu cigaba da yi ba.
Ba yanda Ummi batayi da Maama tayi fashin Islamiyya na yau kawai su gana da ƴar uwarta ba amma taƙi harda kuka wai za'a mata bulala, to ta zauna tayi mata mene?.
Ita kanta Ummi da taga yanda Reina ta dawo cikin wata guda kawai saida tayi salati, yarinya kaman tana rayuwa a cikin jeji tare da dabbobi?.
Abin karyawa suka fara bata sannan ta zaunar da ita tace a miƙo mata kifiya da reza. babu ɓata lokaci ta warware mata kitson da tun barinta gidan aka yi mata shi ta yanke mata ƙumbunan da suka yi zuƙa-zuƙa, na ƙafanta ma yafi muni tunda na hannun da baki take cinyewa.
Ta ɗuma ruwa ta tsugunar da ita a bakin rariya ta wanke mata kai, saida tayi kumfa uku da shampoo haɗe da ruwan karkashi kafin taga hasken kan ta saka mata conditioner aka ɗauraye.
Zuwa yamma ita karan kanta idan ka tambaye ta zata faɗa taji daɗin jikin ta, Ummi ta tura ta makwafta an zizara mata sabbin kitso, ga wani hutu da ta samu tayi barcin da ta daɗe bata yi irin shi ba amma duk lokacin da zuciyar ta ya tuna da Maganar Meesha na jiya sai ta farka.
"Ummi" ta kira tana juya shinkafa da miyar da aka saka mata harda nama da salad yaji mayonnaise da ƙoyi tunda sun san tana son haɗe-haɗen bature.