← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 117

Sashe 63

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ina wuni" ta gaida ta kai a ƙasa, sai taga ta miƙo mata hannu. Reina ta zura nata hannun cikin na ƴar tsohuwan a hankali, suka yi musabiha kana ta amsa gaisuwar ta.

Ƙwalla ne ya taru cikin idon goggo, yau ga jikar Kamalun ta a gabanta, a cikin ƙasar shi ta haihuwa tazo domin su. Tayi ƙoƙarin dannewa tana tambayar ta "Yaya karatu yaya jikin mahaifin ki?"

Da "alhamdulillah" ta amsa sannan goggo Halime ta sake mata hannu Irfan shima ya miƙo nashi sai ta bige. "Yaseer nace a ina ake gwanjon miji ne in samu in ci tsire?"

Irfan ya amshe da "ina haƙorin cin tsire a nan? Ai sai dai a siya miki yalo ko buredi"

"Wannan haƙorin har ƙashushuwa zasu fasa maka original ne ba na wurin ƴan gwangwan irin na wasu ba, kuma ina bada haya Amma wa mazaje masu cefane."

Ƙanin Abbah ya dawo ɗakin bayan ya saka a kawo musu ruwan sha sannan ya shimfida darduma ya zauna aka sake gaisawa a nitse.

"Ita kuma wannan fah? Ko amaryar ce Allah yayi?" Ya tambaya yana kallon Yaseer.

Reina bata san ta shiga girgiza kai ba da sauri, amma goggo ta riga amsawa da "jikan Kamalu ce, ƴar wurin Ɗahiru"

Ya riƙe baki "Allahu Akbar kabiran. Allah mai iko, yanzu yarinyar wurin Fauziyya ce wannan? Lallai lokaci ya tafi. Allah ya jiƙan mahaifiyar ki ƴar nan wallahi mutuniyar kirki gaba da bai"

Kan ta a ƙasa ƙwalla na son taruwa mata ta amsa da "ameen"

"Kada ka saka ta kuka kuma ka saka mijin mu ya ƙullace ni"

Duk zancen kishi da mijin da ake yi Reina ta ɗauka wasan a kan mijin goggo Halime ne ba wai jikan ta ba, sai ta murmusa wannan karon amma kanta a ƙasa don bata yi zaton ita ƴar rakiya zata fi mai tafiyan muhimmanci a inda zasu je ba.

Yaseer ya buƙaci a shigar da ita tayi sallah ganin mutanen gidan suna ƙara tuttuɗowa ganin su, Musamman da labari ya isa musu Ai ƴar wurin Tahir ne.
Kafin ta dawo kuma an jere musu abubuwa kama daga fura da kindirmo ƴaƴan itatuwa da Reina bata taɓa ganin wasu daga ciki ba, wasu har da kulolin abinci suka kawo.

"Idan kun gama sai ku je gaisuwa ko? kafin dare yayi sosai"

Yaseer ya amsa yana miƙo ma Reina plate ɗin Abinda yake tsammanin zata iya ci, sai taji nauyin karɓa kuma tana jin yunwar. Ganin haka ya miƙa ma yarinyar da ta tashe ta ɗazu daga barci, ya tsiyaya damammen fura a cup ya haɗa mata kana yace a shiga da ita cikin ɗaki taci.

Lokacin da suka fito daga gidan goggo Halime har an fara kiraye-kirayen sallah don haka da suka je gida na farko sai da ta jira Yaseer da irfan suka tafi masallaci itama tayi nata a gidan sannan ta fito ɗauke da sha tara na arziƙi.

Haka duk gidan da suka je sai sun samu wani abu sun bawa Reina, wasu har kuɗi, mai ɗari biyar dubu ɗaya.

"Lallai yau Aunty Reina kin kashe min kasuwa amma ban yarda ba zaki kawo mu raba" cewar Irfan yana riƙe da bakkon da aka zuba mata kaya lokacin da suka iso ƙofar gidan su Abidah Yaseer ya ƙwanƙwasa.

"Sannun ku da zuwa" matar gidan tayi musu maraba sannan ta musu iso "bismillah ku shigo ciki"

"Muje Cherié" ta fara shiga gaba sannan suka biyo ta a baya har ɗan ƙaramin parlon da bai daɗe da shigowa a bisa wani dalilin na daban ba.

"Ai ance tafe kuke da jikan Alhaji ƴar wurin yaya Ɗahiru, kece wannan?"

Ta taɓa ƙafan Reina da ta tankwashe su a wurin tana karewa fuskar ta kallo ita kuma sai murmushin yaƙe take kanta a duƙe cikin jin kunya.

Sallamar wata murya mai zaƙi ta saka ta maida duban ta ga ƙofa lokacin da wata kyakkyawar budurwa fara ƙall ta shigo ɗauke da tray mai jug ɗin ruwa da kofuna sai kuma food flask na farfesun kifi da aka ɗaura kan plate ɗin da yaji duniya ga wasu cokula ma a koɗe ta dire a gaban su sannan tayi zaman tahiya da kunyar da yafi wanda Reina ta samu kanta da shi ta shiga gaida su.

Amsawa suka yi Irfan yana ƙarawa da "Aunty Abidah yau kam ki zo mu koma Bauchi da ke tunda ga ƙawa an sama miki"

_wacece Abidah?_

_auntyn ku mana Reina? Matar da zan aura?_

Ta taryo maganar su da Yaseer a lokacin da ya sanar da ita Uncle B ya dawo da matar shi.

Wannan ita ce Abidan kenan? Reina bata san ta bita da kallon sama da ƙasa ba saida suka yi ido huɗu budurwar ta sake mata wani murmushi mai sanyi tana ƙara gaida ta.

Ƙirjin ta ya doka da tunanin yaya Yaseer ya auri wannan ya daɗa wanke ta ya jiƙa ta da Naira ai sai dai idan zasu je wurinta suna saka niqab.

Innalillahi ta fara yi a zuciyar ta da bata san na menene ba amma tabbas ganin Abidah ya saka mata fargaba.

"Zaki sake cin abinci ne ko mu tafi?" Yaseer ya tambaye ta murya ƙasa-ƙasa tayi saurin dawowa cikin hayyacin ta.

Sai ta girgiza kai harma ta riga shi miƙewa su tafi, Yaseer ya ajiye musu alherin da ya saba shima ya miƙe "Ammi zamu yi tafiyan dare bari muyi mu kama hanya"

Maman Abidah ma ta miƙe ita da tayi tunanin ko ɗan zaure zasu ƙarasa da Abidah su ɗan zanta kafin nan don tunda suka ji labarin isowar shi suke zaman jira amma sai da aka yi Isha ma kafin suka zo.

Itama dubu biyar ta bawa Reina amma firr taƙi amsa sai Yaseer ne ya karɓa mata ya zuba a aljihun shi Tunda sun baro jakan ta a gidan goggo.

Abidah tayi musu rakiya har waje Yaseer yayi mata kyauta itama sannan yace ta koma. Tayi musu sallama tana ɗaga musu hannu Irfan dai ya mayar mata amma Reina kaman bata wurin.

Tun da suka baro gidan kuma Yaseer ya kasa gane kan Hafsatun shi. Duk da ba wani magana take yi ba tun da suka iso Amma idan aka yi tana amsawa da murmushi sai dai yanzu kaman ma bata san a ina take saka ƙafan ta ba. duk tayi laushi sai ya jingina hakan da gajiya don haka koda suka koma gidan goggo basu zauna ba yace zasu wuce Saboda dare.

"Ai na ɗau kwana zaku yi sai gobe ku ɗau hanya"

"Bamu zo da shirin kwanan bane goggo sai dai wani lokacin"

"Toh shikkenan Allah ya kiyaye hanya ya kai ku lafiya, na san dai ka san dalilin kiran kuma ina fatan ba zaka zo ka canza ra'ayi ba bayan mun bawa iyayen yarinya haƙuri."

Daɗi ya ziyarce shi sosai ganin goggo ta bashi goyon baya ba tare da ya sha wahala ba.
"In sha Allah babu canji Goggo, na gode sosai Allah ya ƙara lafiya da tsawon rai mai albarka"

Ganin yanda ya gagara ɓoye farin cikin shi ya saka ta jinjina kai "Lallai wannan kishiyar ta ƙwace min fada" ta ƙarasa tana kallon Reina da ita hankalin ta ma bayi wurin, tunani take yi da yaya Yaseer ya auri Abidah ai kaman gwara Darling.

Sai da suka koma mota ta ciro wayar ta da Yaseer ya mayar cikin jaka tun zuwan su.

Missed calls ɗin Umma ta gani har guda 23 na Abbah guda 10 sai Safina 16 ga na Uncle B ma guda 5. Ta shiga call logs ɗinta tana salati, ta gani tun wuraren shida suka fara jero mata kiran, na ƙarshe kuma ko minti biyu bai wuce ba. Sai ta tuna ta saka wayan a DND lokacin da barci ya fara daukan ta a mota hala shiyasa ba wanda ya ji ko a gidan goggo balle a miƙo mata.

"Lafiya?" Yaseer da Irfan suka juyo suna tambayan ta jin innalillahi da take ƙara maimaitawa.

"Su umma basu kira ka ba yaya Yaseer? Missed calls ɗinta da na abbah na gani rututu, Allah yasa dai lafiya."

Kashe engine motar yayi ya ciro nashi wayan amma babu missed call ko ɗaya daga wurin su sai abun ya ɗaure mishi kai.

"Kira su muji" yace da ita da tunanin ko network ne ya hana su samun shi.

Umma ta fara kira kuma yana fara ringing Yaseer ya amshe wayan ya saka a nashi kunnen kada ta ji Abinda zai ɗaga mata hankali.

Bugu biyu aka ɗaga yayi saurin sallama yana ɗorawa da "Umma Lafiya?"

"Yaseer ina Hafsah? Mai ya same ta?" Ta tambaya cikin gunjin kuka.

"Gata nan Lafiya ƙalau muna tare, ki taimaka ki faɗa mun menene ya faru?"

"Kuna tare a ina? Allah yasa ba asibiti ba, don duk inda muke tunanin zata je mun kira mun tambaya har gidan da ta zauna ma Abban ku na hanyar zuwa ko tabi ta wurin ne suka cutar da ita"

Kallon Irfan Yaseer yayi fuska a tamke yace "baka faɗa mata bane kafin ka fito?"

A tsorace Irfan da ya fahimci abinda yake faruwa cikin ƙoƙarin kare kan shi yace "Na shiga na samu tana banɗaki ne shine na bari idan mun dawo a faɗa mata ban ɗauka zamu yi dare haka ba"

"You're very stupid!" Yaseer ya daka mishi tsawan da har Reina saida ta jishi a ƙirjin ta.
"Jama'are unguwa ne da zaka ce sai mun dawo zaka faɗa mata? Me yasa baka faɗa mun a lokacin ba mun jira ta fito ko a fasa tafiyan?!" Ya ja dogon tsaki kana ya mayar da wayan kunnen shi Saudat dake jiran ba'asi bata kashe ba tukunna.

"Umma Wallahi muna Jama'are, kuma na faɗa ma Irfan ya faɗa miki"

Irin ihun da ya yiwa irfan ɗin shi ta shiga masa.
"Baka da hankali ne zaka ɗauki yarinya budurwa ku bar gari ba tare da sanin kowa ba? Hauka kake yi Yaseer?..." Shi dai an barshi da huci da bada haƙuri Irfan na ta kuka ita kuma Reina ta maƙure a gefe ɗaya kaman zaka cemata kyatt ta zura a guje.
Chapter 63 · 0% Book details