← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 117

Sashe 44

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari drivern gida na kai Irfan da Maama makaranta ya dawo don ya ɗauke ta ya kaita har gubi bisa umarnin Yaseer don ba zai samu nutsuwa da tafiyar ta ita kaɗai ba bayan abinda ya faru.

Kafin su tafi shima ya fito cikin shirin shi na tafiya aiki, yayi kyau cikin suit ruwan ƙasa ga kuma farin side bag ɗin ta na jiya da ya riƙo ya ƙara ma adon nasa kyau.
Ƙoƙarin gimtse dariyar ta tayi lokacin da ya iso ta ya miƙa mata jakan.

"Cikin dokoki na, idan naga kina abinda bai dace ba da wayar nan zan ƙwace!"

Karɓa tayi kai a ƙasa kafin yace tayi mishi kallon banza zai maida ta gidan Umman Zahra.

Saida ya ga fitar su kafin ya shiga tashi motar nashi drivern ya ja suka ɗau hanya.

Daga nesa ta saka aka sauƙe su ita da Safina da suka ɗauketa a Bus stop ganin kalan motar zai jawo mata attention idan aka sauƙe su a idon mutane, ita kuwa Safina ta so su ci wuri tunda ba a kan kowa suke ba, amma saida aka samu wa'inda suka zo har seat ɗin da take suna tambayar ta wai motar da aka sauƙe ta na mijinta ne? Don sun ji labarin tayi aure ga kuma dressing ɗinta da ya canza lokaci ɗaya kana ganinta kaga amarya.

~~~~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

73

Ɗagowa tayi daga kan wayar da tun a mota take ta dubawa ko zata ga missed call ko saƙon Uncle B ko guda ɗaya ne Amma wayam. Sai ta jingina hakan da rashin sanin kan iPhone da bata yi ba taci gaba da shige-shige tunda ta kira shi har ya ɗauka ta ji muryar shi kuma basu samu daman zantawa ba kiran ya katse, ya kamata ace ya maido da kira.

To ko yaya Yaseer ne ya ɗauki kiran tunda jakan ta ya kwana a wurin shi kuma wayan yana ciki? Ga kuma gargaɗin da yayi mata ɗazu.

Kallon ƴammatan tayi su uku ne clique ɗin su daman kuma babu wanda suka taɓa magana da ita a cikin su, don yanda suke jin kan su itama haka take kare mutuncin kanta.

"Sai in yi aure kuma ban sanar da ku ba?"

Magana ta faɗa musu kuma sun gane amma dake suna son shigewa jikinta sai na biyun tace "muka sani ko kin manta? Dan wasu ana tare Amma idan suka tashi aure sai dai ka ga biki a IG"

Safina da ta ƙaraso wurin da baƙin laida a hannunta tayi magana ma na ukun su ta matsa mata a hanya, ta koma wurinta ta zauna sannan ta dire laidan a saman desk tana faɗin "yanzu tunda kun tuna mana kunga ba zamu manta ba"

"Hmm Allah yasa ba wasa da hankalin mu kuke ba, don nikam har katin auren ta na gani a status"

"Kika sani ko wata mai sunan ta ne? Idan aure tayi ai zata yi ciki ta haihu ko? Sai ku cigaba da zuba idanu mu gani"

Haka suka ƙaraci damuwan su Reina bata ƙara cewa uffan ba, tana ta kwokwanton ta sake kiran Uncle B ne ko ta haƙura? Ya kamata ace ta fahimci saƙon, bayi buƙatar ta ya rufe babin ta amma zuciyar ta tana son tayi mishi uzuri, wataƙil wani abun ne ya hana shi samun minti goma zuwa talatin cikin awanni ashirin da huɗu na tsawon sati biyu shiyasa bai kira ba.

"Hajiya mun dame ki ko? Shine kika bar mu da P.A ɗin ki" cewar na biyun su.

"Ai bani jin zan taɓa yin arziƙin da zan iya hiring P.A mai bakin Feenah, ni ɗin ne bani da amsar baku shiyasa"

Da suka ƙaraci gulman su dai suka tafi. Feenah ta cire biscuit Fab ta fara ci kana ta tura laidan Sauran gaban Reina.
"Ki saka wani abu a cikin ki kinga yau lectures har 6"

"In sake kiran shi ko sau ɗaya Feenah? Sau ɗaya kawai"

"Idan na hana ki hanuwa zaki yi ne?"

"Idan ba Lafiya bane ba fah? Ko halin da yake ciki a can yafi wanda na shiga muni? Idan ban tuntuɓe shi ba ban kyauta ba tunda shi haka yake tsayin daka a kan lamari na"

Sai da Safina ta kora da chapman tace "idan kina tunanin haka ki kira shi amma ba shawara nake baki ba"

"Ah-ah, to wanne zan yi?"

"Wanda zuciyar ki ta raya miki mana kalan in baki shawarar kiran shi ya saka ki kuka a barni da share hawaye da dakon magani ko kuma in hana ki kiran shi daga baya kuzo ku ɗinke ku haɗa kai ku zage ni! So babu ruwan Feenah kin gani, kada in yi abinda idan an zo auren ni mai gayyata ma ba za'a gayyace ni ba"

Ajiye wayan tayi ta fara cin biscuit ɗin da niyyan zata kira shi idan ta koma gida ta samu nutsuwa sai ta daidaici lokacin da shima take da tabbacin yana hutawa koda aiki ne ya sha masa kai tun Safiya ɗin.

Har an shiga sallan maghriba kafin suka shigo gida, don haka driver na parking ya wuce masallaci itama ta shige daƙin ta don sauƙe farali.

Miƙewa kwance tayi a saman sallayar saboda yanda jikinta yake amsawa tunda ta daɗe bata je tayi wunin makaranta ba, wai don ma kaita aka yi aka dawo da ita da bin kwaraɓaɓɓun buses ɗinnan da samun ka siya seat su iso su ɗauki mutane ma aiki ne, ai da yanda ta shigo ɗinnan har abincin dare ta haƙura da shi.

Ana kiran Isha ta daure ta miƙe ta gabatar da shi Sannan ta sauƙa downstairs cin abinci.

Kowa na nan banda mahaifin ta Alhaji Tahir kuma daman ya faɗa musu ita da Maama zai koma cin nashi abincin a ɗakin shi domin yafi sakewa kuma suma masu gidan ya barsu su sake, amma su suci gaba da zama tare da su.

Sannu da gida tayi ma Umma da Abbah, sai da ta zauna ta fahimci a saitin Yaseer take suna fuskantar juna amma kaman bai san da halittar ta a wurin ba ya ƙarasa cin abincin shi yana duba wayan hannun shi yana yiwa Aicha tambayoyi sama-sama ita kuma ta zage sai bayani take kaman mai bada rahoto a gidan talabijin.

Bayan sun gama ya miƙe sannan ya dubeta ba tare da ya tantance sunan ta ba kaman yanda ta fara sabawa daga gare shi yace. "Idan kin gama ki ɗauko takardunki ki same ni a study room."

Da kai ta amsa don bakinta a cike yake lokacin. Bata ƙara ɓata lokaci ba kuma taje ta ɗauko sabbin handouts ɗinta wanda ta siya da kuɗin da ya saka mata a cikin jakarta da safe.

Da sallama ta shiga bayan tayi knocking, yana zaune a kujeran bayan babban teburin kaman shekaran jiya yau ma da gilashin da yake ƙara masa kyau a idanun shi, sai kuma idanun ta suka sauƙa a kan Aicha dake zaune a kujeran da yayi mata izini ta zauna ranan, itama ta saka wasu files a gaba da abin rubutu a hannun ta.

"Gani Yayanmu" ta mayar da hankalin ta gare shi.

Sai da ya dasa aya a laptop ɗin da yake typing kana ya ɗago ya dubeta yana miƙo hannu.

Ta gane abinda yake nufi tayi saurin miƙa mishi handouts ɗin ya shiga duba su ɗaya bayan ɗaya.

"Iyakacin su kenan?"

"Ehm.. akwai wasu na da a jaka, wannan sune na siya yau, yawancin last part ɗin kuma sai an fara test zasu sake.

"Okay, so yaya kike tsara karatun ki? Kina taɓa su kaɗan-kaɗan ne ko kuma idan kika fara ɗaya sai kin dire?"

Murya can ƙasa irin na masu laifi da sanin su tace "Duk wanda Safina ta zaɓa mana shi muke yi ko wanda zamu rubuta test ɗin shi."

Ya ɗage gira ɗaya yana dubanta "Okay saboda Safina ita ta saka ki a makaranta? Ko ƙwaƙwalwar ku kala ɗaya ne hala?"

Shiru tayi tana kallon wani wurin yanda ba zasu haɗa ido ba. Ya nuna mata wani couch daga gefe.

"Zauna daga can ki fayyace wani tsari zai fi zama miki ki fara gwadawa kuma kullum kafin mu tashi akwai gwaji, idan kika faɗi akwai hukunci" da haka yayi mata alama da hannu da ta tashi masa a kayi.

Ta ƙarasa wurin da ya nuna matan ta ɗauki handout ɗin dake sama tana masa karatun jarida ba'a je ko ina ba ta fara gyangyaɗi.

"Ina kallon ki fa" yace daga inda yake zaune.

Firgigit tayi tana kalle-kalle har sai da ta saka Aicha murmusawa amma shi hankalin shi na ga abinda yake yi, toh ido yake da shi a ƙeya?.

Sai ta koma tana karatun tana jan layi a duk inda take ganin yana da muhimmanci idan taji barci na son kama ta kuma ta canza da wani darasin daban.

Ƙarshe ma miƙewa tayi ta shiga zagaye amma karatun kaman zubawa take yi a kwando sai ta gama ta dawo baya taga kaman bata taɓa karantawa ba.

Suna a haka har agogo ya gwada ƙarfe goma bata ga wani a cikin su yana da niyyan zuwa yayi shirin kwanciya ba.

"Yayan mu... Yaya Yaseer"

"Menene?" Ya amsa kira na biyun don Allah ya gani yana jin daɗin yanda take fitar da sunan shi a kan harshen ta.

"Lokacin kwanciya na yayi, barci nake ji kuma ina da class ɗin 9 gobe"

Gyara zama yayi da kyau ya jingina yana miƙar da bayan shi "Kawo abinda kika yi mu gani."

Da ɗan Hanzarinta ta ɗauko handouts ɗin da ta karanta shafukan farko a cikin su har guda uku ta ajiye masa.

Ɗagawa yayi yana ganin yanda ko ina ta ta zane shi da biro.

"Sabon handout kika yiwa wannan ta'asar Reina? Yanzu duk inda kika ja layin nan kin haddace?"

Da kwarin guiwarta ta gyaɗa kai, su da suka saba yiwa jarabawa ma karatun sha ka zubar kuma ka rubuta ka ci balle ɗan tambayoyin yaya Yaseer?.

Ai kuwa yana fara jero mata tambayoyi ta rikice, da ƙyar ta iya amsa ɗaya. "Yaya Yaseer ban yi nisa ba fa, kowanne a page 5 na tsaya"
Chapter 44 · 0% Book details