← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 117

Sashe 34

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kewar shekaru goma, shekaru goma cuss sai a yau ya sake ganin wannan abu da ya nima ya rasa, abinda ya gama dubawa amma babu shi a idon kowa bayan ita.

Sake mug ɗin tea ɗin yayi daga yanda yake tsaye sai ƙaran haɗuwan shi da ƙasa yaji, nutsuwar shi yayi jinkiri amma instinct ɗin shi yayi gaggawar sanya hannun shi ya angiza ta kada tafasasshen shayin ya watsu mata ko fasasshen kofin ya ji mata rauni.

Tayi nasarar riƙo hannun shi kafin ta kai ƙasa tana sake kallon cikin idon shi da tsoron da yafi na da. Amma sai gani tayi ya sake ta bamm ta kai ƙasa ta buga bayan ta tana sakin ƙara.

Tana gani ya tsallaka wurin da ya ɓata yayi tafiyar shi ba tare da ya sake waiwayen ta ba.

~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

66

Bayan shi tabi da kallo, ta kasa tantance wani irin tunani zata bari ya shiga kanta har ya fara sauƙa daga matakalar benen a sannu ya ɓace ma ganin ta.

Sai a sannan taci gaba da jin zafin buguwan da tayi, ta dafa bango ta miƙe tana yamutsa fuska. Ta kasa ɗauke idanun ta daga yanda taga ya bi, ta ga Yaseer da idanun ta, hannun ta ya taɓa shi, anya wannan kuwa Yaseer ɗin ne ko dai wani mai kama da shi, a wannan karon kokwanto take yi da gaske.

Saboda ta tabbatar ta ɗingisa ta bi inda taga ya bi.
Idanun ta basu kallon komi har tazo ta wuce daddyn ta a teburin cin abinci tare da Abba da Ummah bata lura da su ba, akalar hancin ta ke janta yanda ƙamshin turaren shi yake fitowa, ƙamshin turaren da take da tabbacin ba yau ta fara jin shi ba, kaman ya daɗe yana tare da ita.

*Yaseer*

Bai san yana riƙe da numfashin shi ba, a ƙoƙarin shi na controlling kan shi kada ya waiwaya koma ƙafafuwan shi su yaudare shi ya koma wurin ta, don yaji zafin sake ta da yayi ta fadi har cikin ran shi. har sai da ya ida shigowa kitchen ɗin ya tsaya yayi dogon ajiyan zuciya.

"Yayan mu ina kwana" Aicha dake wanke-wanken abubuwan da ake ɓatawa a yayin shirya abin karin ta juyo ta gaida shi da murmushi kaman ko yaushe.

Bai iya maida mata murmushin ba, da "Hmm" ya amsa tare da ɗaga mata hannu don idan yace zai yi magana muryar shi rawa zata yi.

"A haɗa maka tea ne?" Sabir ya tambaya ganin ya nemi wuri ya tsaya kaman mai tunani hannun shi a cikin aljihu.

Nan ma girgiza kai kawai yayi, bayi jin zai iya riƙe wani kofin shayin a yanda hannun shi yake rawa.

"Akwai Abinda kake buƙata?" Suhail ya sake tambaya.

Ganin zasu ishe shi da tambayoyi sai kawai ya ƙarasa gaban sink ɗin da Aicha take ya dauko towel yana goge kwanukwan da take wankewa, fatan shi ɗaya kada ya sake fasa wani abun.
Daɗi kaman ya kashe Aicha, Lallai kaman fadar ta yafi na Reina a yanzu, sai zabga murmushi take yi ta shiga jan shi da hiran da yake amsawa da "uhm" ko "uhm uhm".

Shigowa kitchen ɗin tayi a birkice, sauran kaɗan taci karo da Maama dake taya Irfan shirya table. "Ina zaki je haka?" Maaman ta tambaya.

Bata kula ta ba ta kalli mutanen kitchen ɗin ɗaya bayan ɗaya kowa aikin gaban shi yake yi kafin idanun ta suka sauƙa a kan shi daga ƙarshe.

"Yaya Yaseer!" Ta kira idanun ta a bayan wanda take da yaƙinin ƙirar Yaseer ba zai zama haka ba.

Lokaci ɗaya kowa ya juyo suka zuba mata idanu banda shi Yaseer ɗin da nata idanun yake a kan shi.

"Yaya Yaseer?!" Ta sake kira yaƙinin ta yana daɗa gushewa.

Cikin dakiya da ƙarfin hali ya juyo ya dube ta, zuciyar ta tayi wani irin dokawa a ƙirjin ta, ya tabbata shi ɗin ne kenan?.

"Na'am, yaya aka yi?" Ya tambaya cikin kalmomin da ya samu haɗa kan su da ƙyar.

Tsaki Suhail ya ja yaci gaba da abinda yake yi. A wannan karon Yaseer ya sakankance yana ƙare mata kallo kaman yanda take ƙare masa itama.

Ta canza.
Ya canza.

Kowa a cikin su karanto kalan sauyin da ya hango a jikin ɗan uwan shi yake yi a cikin ransa. Duk da cewa shi Yaseer abun bai zo masa a bazata ba amma wannan ne karo na farko da ya saki ran sa idan yana kusa da ita, ba tare da tsoron zai fallasa kan shi ba.

Suna kallon juna Aicha na kallon su duka biyun, sai kawai gani tayi Reina ta fashe da kuka sannan ta ɗibo a guje, kafin suyi wani yunƙuri ta ƙaraso ta shige jikin Yaseer wanda ya ja wani gauron numfashi a take, ta ruƙunƙume shi. "Yaya Yaseer, nayi kewar ka yaya Yaseer ɗina"'

Firgigit Aicha tayi ta dawo daga mafarkin tsayen da ta lula, ta shiga girgiza kai tana dariyar da babu nishaɗi a cikin sa "Inaa, Impossible" sannan ta koma gaban Yaseer ɗin ta tsaya tayi masa shamaki da Reina, amma ratan tsayin dake tsakanin su ya saka bata rage komai ba daga kallon da suke ma juna ba, Yaseer ne yayi ƙoƙarin fara ɗauke kan shi ya juya mata baya, a maimakon yaci gaba da goge kwanukan da aka wanke sai gashi yana saka farin towel ƙarr a jikin abubuwa masu datti.

A hankali maiƙo ya fara taruwa cikin idanuwan Reina, Aicha ta ware hannunta ta gama shirin tareta, ganin ta baya ma zata rungume shi kenan yanda ba zai ma sani ba balle ya kare kan shi.

"Bani hanya" Suhail dake ɗauke da tray yace da ita fuska a tamke, dakatawa da tara hawayen tayi sai ta tsaya duba space ɗin dake tsakanin ta da ƙofar kitchen ɗin, ba tray ba ko teburi yazo wucewa dashi zai samu hanya. Amma gudun fitina sai ta matsa masa, hakan ma kaman zai bangaje ta saida ta sake matsawa ta mannu da bango kafin ya wuce yana ciccin magani.

Aicha da ta gaji da jiran isowar ta sai ita ta taka ta ƙaraso inda take, kaman bata lura da hawayen da suka fara bin fuskar Reina ɗin ba ta rungume ta sama-sama tana dariyar yaƙe. "Yaya kike, yaya baƙunta?" Ta saka karfi ta juyar da Reina zasu fita daga kitchen ɗin bata bar dariyan yaƙen ba.

Reina ta gwada Yaseer tana ƙokarin magana amma Aicha taƙi bata dama sai tambayoyi take jero mata har suka ƙarasa dining ɗin ta ja mata kujera ta dungurata sannan ta shiga zuba mata abinci duk don kada ta bata daman tashi.
.
.
Sai da Yaseer ya ga fitan su ya ja dogon numfashi ya furzar, sai kuma ya tsargu da kan shi, yaya haka? Kwarjini ne Reinan take dashi ko me da ya gagara fuskantar ta? Shi da yake shirya koya mata wasu darussan da ba a mata a makaranta? Ai ba zallan Alhaji Tahir da su Jamal bane suka yi mishi laifi, Reina itace ummul aba'isin duk wata masifa da ya shiga, kuma ya ɗau niyyar koya ma kowa hankali a cikin su daidai da laifin shi, idan haka ne kuwa dole ya sake shiri a kan Reina.

Zuciyar shi ta shiga taryo mishi ɗan ɗingishin da yaga ta fita tana yi sai yaji ba daɗin saketa da yayi, duk da ma faɗuwan ba tun daga sama tayi ba da nan ne zata yi ɗingishin gaskiya.
.
.
"Ina yayan mu?" Saudat ta tambaya ganin kowa ya samu wurin zama har an fara karyawa banda shi.

"Na barshi a jikin sink, ko ya tsaya ƙarasa ɗauraye sauran dishes ɗin ne?" Aicha ta amsa tana miƙewa da nufin taje ta dubo shi, Reina ma tsugul ta miƙe zata bi bayan ta.

Sai gashi ya fito yana sauƙe hannun Farin long sleeve Tee ɗin dake jikin shi, a wannan karon ba fuskar shi ba, a ƙirjin shi idanun ta suka sauƙa, ta haɗiyi miyau muƙut, ta ina wai za'a ce mata wannan yaya Yaseer ne?, wannan mini giant ɗin!

"Zauna mu karya" cewar Kamal, sannan yayi hannu ma Aicha da Reina da su zauna suma.

"Emergency ya taso mun Abbah, zan je inyi shirin office, in yaso na karya a can"

"Emergency ranan Lahadi Yaseer? Wani irin emergency kenan?"

Laɓɓan bakin shi na ƙasa ya ɗan ciza yana sosa ƙeya, ya fara tunanin wani ƙarya zai haɗo Abban ya bar shi ya tafi?. Shi matsalar ko ƙaryan yace zai yi gano shi ake yi.

Abinda yayin da kuma tabon da Reina ta gani a gefen leɓɓen shi ya tuna mata da wancan Ranar, Ranar da tayi mishi ƙazafi, tana tuna yanda ya ciza bakin har sai da ta fitar da jini a yanda ya bar masa tabo yanzu.
Ya tabbata shi ne.

"Zauna kaci abinci, koma menene ya jira" Umma ta furta cikin bada umarni, sai ya haɗiyi miyau, ya janyo kujerar da babu kowa a tsakanin Mai haƙuri da Alhaji Tahir ya zauna.

Yana jin kaman babu kowa a teburin bayan ita, presence ɗinta duk ya cika wurin ga idanunta da yake jin su a jikin sa kaman zasu mishi rami.

Haɗiye miyau yayi bayan an zuba mishi abincin ya ɗauki fork a hannun shi sannan ya ɗaga idanun shi.
A saitin Aicha yake amma tana zaune ne a gefen ta, kusan fuskantar juna suke yi. Haka dai yayi ƙoƙari bai kalle ta ba ya fara cin abincin a hankali gudun kada ya ƙware, bai yi nisa ba Alhaji Tahir yace "yau babu shayin ne Yaseer?"

Tunawa yayi da mug ɗin da ya fasa ɗazun, ya miƙe cikin jin daɗin ya samu escape.

"Nayi ɓari upstairs ɗazu, bari naje nayi cleaning ɗin shi up"

"Irfan ya goge, zauna kaci abinci" cewan Saudat ba tare da ta dube shi ba, domin ta fara fahimtar inda ya dosa.

Haka ya koma ya zauna, amma bai taɓa ganin karyawan da yayi masa tsayin wannan ba, kafin mutum na farko ya miƙe wanda Irfan ne da zai tafi islamiyya sai yaga kaman sun fi awa biyu suna zaman kuma bayi son ya zama farkon tashi ya sake bada kan shi.
Chapter 34 · 0% Book details