← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 117

Sashe 1

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

41

~~~~~~~~~~
_I try to live in black and white but I'm so Blue_
_I'd like to mean it when I say I'm over you_
~~~~~~~~~~

Idan ƙaddara ce, tafiyar ta take yi babu gargada. Sai dai kai ta jera maka manya-manyan duwatsu a hanyar bin ta bayan tayi maka mamunga, yanda zaka yi ta cin tuntube kana faɗuwa, ka ci da baki ka ji munanan raunuka. kuma dole ne bin hanya guda ɗaya da take buɗewa kowa duk gargadan shi, cikin daɗin rai ko akasin shi dole zaka ci gaba da zabga gudu ne saboda ka samu damar ƙwato numfashin ka daga hannun ta.

A duk lokacin da zasu yi zama irin wannan toh babu alkhairi a cikin ta. Domin idan alherin ne yazo ma ɗayan su ɓoyewa yake yi ma ɗan uwan shi saboda ya amfana shi kaɗai, amma idan sharri ne aka samu sai an haɗu an kasa ma kowa rabon sa.

"Yaya Kalabu kaga kaine babba, a yanzu kaine mahaifin mu baki ɗaya a nan, sabila da haka kai yafi kamata ka ɗauki nauyin yaran Tahir ko ɗaya daga cikin mu a bayan sa"

Jinjina kai suka yi alaman gamsuwa da zancen Hajiya Lubabatu, sai shi kalabun dake kallon ta baki sake yana mamakin sai idan hidiman son zuciya ya iso suke tunawa da wai yana da matsayi a gare su, amma ai da Tahir ɗin ne suke girmamawa fiye da kowa saboda abin hannun shi.

"Ni da girma ya fara kama ni a yanzu jikoki nake fama da su ina zan iya ɗawainiyar yarinyar shekara 11 zuwa 12? Duk yarana na gama aurar da su da waye zata zauna a gidan kenan? Wa zai iya ɗawainiyar ta a cikin tsofaffin mata na?. Kema ai kaman uwan su kike tunda banbancin mu kaɗan ne!"
Ya mayar mata da tayin da tayi mishi.

Da hanzari ta amshe da "Ni da Tahir ya raba gaari da ni saboda Hafsatu? Har Allah ya isa fa yaja mun shine don bayi nan za'a ce in riƙe ta aci amanar shi?"

Tana zaune ne ta lungun kujerar shigowa parlourn, ƙafafuwan ta a kalmashe ta ɗaura hannayen ta saman cinyoyinta ta ƙura musu Idanu. A zahiri dukkan nutsuwar ta na gare su amma hoto ɗaya ne ke yawo a ganin ta tun kwanaki takwas baya har zuwa yau, Ranar da ƙaddara ta gaji da binta da take yi a baya ta juyo ta tsinka mata marin da ya sanya dole ta dakata.
Bata ganin komai a yanzu, bata gane komai, bata kuma jin zafin marin zai bar ta a kwanan nan, sannan bata san yaya zata yi ta rage raɗaɗin ba.

sama-sama kunnen ta ke jiyo mata musayyan da suka cigaba a tsakaninsu.

"...Jummai kinga kina da yara sa'o'inta da zata ji daɗin zama da su, kawai ki ɗauke ta ki haɗa su Allah ya biya"

Dafe ƙirji da hannu bibbiyu Hajiya Jummai tayi tace "A kan Maama har rana mai kaman ta yau Tahir bai sake duban hanyar da nabi ba balle ku haɗa ni da sarauniyar zuciyar shi. Ina Salisu? Ba kai kafi kusa dashi ba? Kuma ma yarinya a wurin baffanen ta ya kamata ta zauna don muma a ƙarƙashin wasu muke, zamu kai musu yara ne ba tare da amincewar su ba?"

Rayuwa kenan, Rayuwa juyi-juyi, Rayuwa mai abun mamaki. Wai yarinyar da aka ƙare duk wani tanadi ma rayuwar ta tun tana ciki, yarinyar da idan gata ne yara ƙadan ne suke da da irin nata a faɗin garin Bauchi baki ɗaya, kaii a Nigeria ma basu da yawa.
Amma wai yau ita ce sai anyi muhawara kafin a samu wanda zai bata abinci da wurin kwana.

Alhaji Salisu ke fadin "Nima zargi na yake yi da kawo wanda ya lalata mishi yarinya har cikin gida na, ba don an kama Yaron nan Yaseer ba to da ɗana ne yanzu a matsayin shi..."

Da sauri ta ɗaura duban ta a kan shi jin ya ambaci sunan Yaseer, wanda a karo na farko kenan da duban ta ya haɗe da hankali da nutsuwar ta a wuri guda, ƙwaƙwalwar ta kuma ya shiga ɗauko mata tunanin ta na shekaru uku da suka wuce.

....
Sai bayan an tafi da Yaseer, bayan ta tabbatar da ta cece shi daga mutuwar da aka yi mata alƙawari, kana ta shiga niman Auntyn ta ko tana cikin ƙoshin lafiya.

Ta rasa taron me ake yi a gidan su, amma duk cikin ƴan taron bata ga Aunty ba. Gashi daddyn ta yana riƙe da hannun ta a dakin shi yaƙi barin ta taje ta nemo Auntyn.

Shima Alhaji Tahir ya gagara komawa wurin gaisuwar, domin bayi jin zai iya jurewa gaisuwar da ake masa Saboda rashin Fauziyya a tare da shi.

Har sai da kwanaki biyu suka ja kafin Reina ta fahimci da gaske mutuwar da Umman Jamal ta yi alƙawari ma Aunty ne ya ɗauke ta.
Bata gama fahimtar menene mutuwa ba amma tana da tabbacin aunty kuma ta tafi kenan ba zata sake ganin ta ba.

Kullum sai tayi kuka, ba zallan kukan ba zata sake ganin auntyn ta ba harda na cewa ita ce sanadin mutuwar Auntyn, kuma tana tsoron faɗawa daddynta ta rasa shi shima.

Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci daga ita har mahaifin ta suke fice daga hayyacin su, gashi babu nutsuwa a jikin shi, hatta aikin office ma ajiye shi yayi a gefe, Ya maida hankali wajen ganin ya galabaitar da Yaseer da iyayen shi kafin yayi masa ɗaurin da zai lalata rayuwar shi har abada ya mayar dashi mara amfani.

Bata fahimci cewa tayi kuskure ba har sai da suka je dubo Maama ita da uban a gidan Ummi tana zazzaɓi.

Duk rashin jituwar su Reina sai da ta tausaya mata ganin yanda take a wahalce, a nan ne bayan Alhaji Tahir ya tafi ya barta a gidan take tambayar Ummi ko itama Maama mutuwa zata yi, ko an faɗa abinda ba'a faɗa ne yasa take ciwo zata mutu?.
Ummi ta ɗau tausayi ne na ƴan uwantaka da kuma basu daɗe da rashin mahaifiya ba yasa tayi mata bayanin mutuwa da kyau yanda mai shekarun ta zai fahimta.
Baka mutuwa don an faɗa maka wani abu kuma baka mutuwa sai lokacin da Allah yaga dama.
Hakan na nufin Umman Jamal ƙarya take yi? Hakan na nufin abinda ta faɗa ma yaya Yaseer umman Jamal tace Ya faɗa ma Auntyn ta ba shi yasa Auntyn ta mutu ba? Hakan na nufin ƙaryar da tayi ba shi ya ceci yaya Yaseer ba?.

"Ummi dan Allah kira min Daddy na a waya yanzu" ta buƙata hawaye na cika idanun ta da sauƙowa a lokaci guda, ga yanda ta fara rawan matsuwa kaman mai jin fitsari.

Tambayar ta abinda yake faruwa Ummi tayi amma sai girgiza mata kai take yi tana kukan a kira mata daddyn ta.
Suna haka Aina'u tayi Sallama ta shigo gidan. Alhaji Tahir ne ya turo ta da driver su dauko ta domin a yanzu ko driver ɗin da yayi shekara da shekaru yana masa aiki bai yarda da shi ba a kan Reina, bai yarda da kowa ba ma a kanta bayan kanshi.

Tun a hanya take kuka har suka Isa gida, ko parking ba'a gama ba ta ɓalle marfin motan ta fita da gudu har tana niman kifawa.

Bata tsaya ko ina ba, sai study room ɗin Alhaji Tahir.
Yana zaune da takardu a gaban shi yana amsa waya.

"Daddy.... Daddy Wallahi ba yaya Yaseer bane, ƙarya nayi Daddy... Yaya Jamal ne wallahi, shi yake kira na ɗakin shi ya rufe ƙofa yayi ta taɓa ni, don Allah kace su sake yaya Yaseer ba shi bane."

Sauƙe wayar Alhaji Tahir yayi daga kunnen shi ba tare da ya katse ba. Sunan 'Yaya Salisu' ne ke yawo a saman screen ɗin, da shi suke magana ta shigo, lokacin kira na ƙirga mintuna Arba'in da ɗaya da sakwannin dake kan gudu....

"Ke Hafsatu!"

Firgigit tayi ta ɗaga duban ta daga kan Alhaji Salisu ta mayar kan Alhaji Kalabu.

"Zaki bi goggon ki Zuwairah Abuja, ina zaki iya zama a can?"
Reina dai kallon shi take yi kawai ba don tana fahimtar abinda yake faɗa ba, kaman an kwashe ƙwaƙwalwa a ciki ƙoƙon kanta haka take jin ta kwanan nan.
"Ko dayake ma meyasa nake wani tambayar ki kaman kina da zaɓi?"

Ya juya wurin Zuwairan dake son tabbatar da wai ita yake nufi ba wata daban mai irin sunan ta ba.
"Ko a mota ne sai ki saka ta goben tunda baku yi shirin tafiyar da ita ba. Kinga kafin ta iso har kun yi shirin tarbar ta ko Zuwairah?!"

"Wa? Ni?! Yaya Kalabu ka ganni a auren Tahir? Ka ganni nazo barkar haihuwar yaran shi?, Ni da Tahir yace min ko ƙofar gidan shi nazo ba za'a barni na shiga ba? Bai bani ko yarana katin gayyatar bikin shi ba kuma ko a cikin list ɗin baƙi babu ni. Idan ba mutuwa ba an faɗa muku zaku taɓa gani na a hidimar Tahir ne balle har kuce ni zan riƙe mishi ƴa?! Allah ya sawaƙe" ta saɓa jakar ta a kafaɗa tare da miƙewa tana yafa gyalen ta.

"Kunga tafiya ta, saduwan alkhairi."
Bata sake sauraron kowa ba ta bar wurin don yanda take jin tsanar Fauziyya da faƙiran dangin ta haka taƙi jinin ƴar ta Hafsatu, kuma ko me zai faru bata jin zata taɓa son ta.

Sai suka fara kallon-kallo kowa yana son ya zame jiki shima ya tsere ma ɗawainiya, wanda babu ribar komai a cikin ta bayan wahala, kalan sauran bashin da ake bin Tahir ɗin ma a maƙala maka dole ka biya tunda ƴar shi tana hannun ka.
Sun gode ma Allah ma da dangin matan shi suka dage sai sun amshi Maama lokacin da zahirin lamari bai bayyana ba, suna ganin tarin dukiya yaran zasu samu har suka so hana su da ƙarfi.
Chapter 1 · 0% Book details