← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 117

Sashe 16

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya koma cikin motan da niyyar fiddo da kuɗi amma kafin ya fito tuni na ƙara gaba, sauri nake yi kaman zan ɗiba da gudu, ina ji wata murya daban wanda ba nashi ba yana kiran "ke, ke" amma na saka kai nayi saurin tsallakawa na shiga wani street, ban waiwaya ko na tsaya ba har saida na shiga cikin gidan bikin nan.

Ashe sauƙi na sama wa mahaifin ki.

Bai san lokacin da na shiga cikin tunanin shi ba da ya kai har idan yana lissafa kuɗaɗen shi nake shiga kan shi a irin wannan lokacin, Daga baya yake faɗa min wai har barin kasar yayi don ya manta da tunani na amma ya gagara, sai da ya dawo ya tura a duba mishi gidan da yaga na shiga rannan a tunanin shi gidan mu ne.

Bayi da wani bayani bayan kamanni na don haka ya sha wahalar tantance ni a cikin sauran ƴan biki, har sai da yaje gidan da kanshi aka nuna mishi hotunan biki ɗaya bayan ɗaya yana dubawa.

Cikin Sa'a aka samu nazo wucewa a bayan guda ɗaya na waliman da aka yi ranan. Fuska ta bai fito ba amma ya gane ni da kayan jiki na.

Da yammacin wata Alhamis ina zaune ina assignment duk hannuna yayi tsami da rubutu don full scarf shafi goma zaluncin malamin ya bashi shawarar mu cika kuma rabi kawai nayi gashi gobe za'a yi submitting, aka shigo aka faɗa min ana sallama dani a waje.

Akwai wani saurayin da nake kulawa, mun haɗu a makaranta lokacin ina fresher yana final year gashi yanzu har ya kusan gama service. Da gaske yake yi don har yazo ya gabatar da kanshi ma baba, da ya samu abun yi zai turo a nima mishi aure na, don haka aka bashi damar zuwa gida muna gaisawa lokaci zuwa lokaci.

Na sha mamakin ganin bai shigo ba don bama hira a waje, amma tunda Ummi ta fita unguwa da Sajeedah ni kaɗai ne gwamma mu gaisa a wajen.
Na ɗan goge fuska ta da soson powder na shafa kwalli kana na jawo hijab ɗina daga kan ƙofa na saka na fice.

Ware kansu ƙwayar idanu na suka yi lokacin da suka shiga cikin nashi. Na daskare a wurin ina mishi kallon da ya saka shi murmushi duk abinda yake damun shi saka ni a cikin idanun shi da yayi kawai ya saka sun yaye lokaci guda.

"Ina wuni" ya gaida ni ganin kallon nawa ba mai karewa bane, kaman ina ƙoƙarin hakan ya saka ya ɓace daga gaba na ne.

A maimakon nayi magana ko na amsa shi sai kawai na juya na arci na kare ko ƙofar ban rufo ba sai da na shiga falo tukunna na saka ma ƙofar wurin key da sakata a lokaci guda ina mayar da numfashi.

Kaman hidimar da aka haɗa da aljanu sauƙan da idanu na zasu yi a kan tvn da yake kunne sai a kan fuskar shi da ake gwadawa wurin wani taron buɗe masana'anta da suka yi tare da governor, na karasa da sauri na fisge igiyar tvn daga jikin garu ya mutu.
To hauka ake yi zan ga TK Kingdom a ƙofar gidan mu, sai dai hidimar iskokai wannan.

A ranar ban iya ƙarasa assignment ɗinnan ba, cikin Sa'a aka ɗaga ranar submission zuwa monday.

Nayi tunanin daga nan shikkenan koma aljani ne nayi mishi addu'a Amma a'a, sake ganin da zan yi mishi sai a parlourn Baba ni da shi muna fuskantar juna.

Yakan ce min "Fauzah ke mai tsada ce sosai, nasha wahala sosai kafin na samu ganawa da ke. Kina da tsadar da duk yawan kuɗi basu iya siyan ki sai anyi aiki tuƙuru da mika ƙoƙon bara wurin Allah "
Daga Ranar wani sabon sunan nawa ya shiga kunne na, amma a lokacin bani da sani a kan zan cigaba da amsa shi har ƙarshen rayuwata har sai lokacin da na samu labarin Alhaji Tahir ya bawa saurayi na aiki mai gwaɓin gaske don ya daina kula ni, ƙarshen ta ma bai bar shi a garin ba ya tura shi can kudu ya bashi gida da mota.

Ban iya wulaƙanci ba amma Ummi ta koya min a kan T saboda yayi zuciya ya rabu dani amma abun shin sai ƙara gaba yake yi don bai ƙi a take a daura mana aure ba ma, ya tsufa da shiryawa.

Ummi ta shiga damuwa lokacin sosai, duk da cewa kowace uwa tana so ma ƴarta gidan da zata huta amma ba gidan da hutun zai jawo mata rashin kwanciyar hankali ba, sau ba Sa'ar auren irin su Alhaji Tahir bane, yanzu idan yana cutar musu da ƴa da wani iko zasu yi amfani su ƙwata mata ƴancin ta? Baba ma yaƙi yarda da maganan ganin kaman bani ra'ayin shi, har kira na yayi ya tambaye ni bance komai ba amma nayi ta masa kuka, kuka mai zafi don haka ya gane manufa ta ya sallame ni.

Ya samu Alhaji Tahir ya bashi haƙuri kan ya fita hanyata kawai nan ne fa rikici ya fara. Yana yi da dangin shi ni da iyaye na muna yi da ƴan uwan su, dan ɗaya bayan ɗaya yake bi yana siye su, ga sintiri da yake mana a unguwa, zai zo ya jira koda ba za'a barshi ya shigo ɗan akurkin gidan mu ba balle a bashi daman ganawa da ni don bani so, nima ina tsoron gaba, nakan zauna in yi tunanin irin rayuwar da zan yi a ƙarƙashin shi, gashi bani jin zan iya sakewa da shi don ratar dake tsakani na dashi yayi min yawa da irin mijin da nake son aure.

magana ya girmama ya dawo ƙato a ɓangare biyun, har wata ƴar uwar shi Zuwairah tazo ta ci ma su Ummi mutunci suka daɗa ɗaukan zafi shikuwa T ya raba gari da ita.

A kan Daddyn ki har so aka yi ayi min aure da wani cousin ɗina don kawai ya rabu dani.
Sai dai ance matar mutum kabarin shi, sannan ƙaddarar kowannen mu a rubuce yake tun kafin muzo duniya, don haka na wayi gari a gidan Tahir a matsayin matar shi, a cikin wata duniyar da ban taɓa mafarkin samun kaina a makusancin shi ba.

Abu daya da yayi matuƙar faranta min rai shine canjin rayuwar da iyaye na suka samu. Ya siya ma mahaifina sabon gida amma baba yace shi ba zai tashi a unguwar mu ba don haka ya sayi gidan maƙwaftar mu aka haɗa aka tada mana sabon gini ya siya ma baba mota ya bawa yayu na aiki.

Tahir yana sona, tsananin soyayyar da bayi iya ɓoyewa a gaban kowa, a saboda haka na kwantar da hankali na har nima ya fara shiga rai na, a sannu muke gabatar da rayuwa har ya samu na sadaukar mishi jiki da ruhi na, amma Allah bai kawo mana rabo ba har sai bayan shekara biyu kafin ya azurta mu da falalar da babu wani mai bayarwa bayan shi.

Na riƙe ki a kan ƙirji na Hafsatu, zuciyata ta koma bugawa domin ki.'

Shikkenan kuma an wuce daɗin, daga nan za'a cigaba daga inda ta dawo matsala a cikin rayuwar wannan kyakkyawar halitta.

Yanda ta zamo sanadi na farko da Tahir yayi fushi da Fauziyya, suka ɓata, ya sake ta, duk a kanta, bayan irin wahalhalun da taji ta sha a sanadin ciki da rainon ta.

Kuka take yi kaman ko yaushe ta kifa kanta a jikin littafin hawayen ta na cigaba da goge rubutun. "Kiyi haƙuri don Allah Aunty, ki yafe ni ko zan ga daidai a rayuwa ta."

Ta tsallaka wasu shafuka masu yawa ta tafi na ƙarshe.

Yanda ko kwanan wata Fauziyya bata rubuta a kan shafin ba amma wannan Rana ba zai taɓa gogewa daga cikin kwanyar ta ba.

Numbern waya ne a layin farko na shafin.
A ƙasan numbern ta rubuta 'Yaseer Kamal'

Sai ta saki layi biyu kafin ta rubuta. 'ban so in ajiye kowacce irin shaida na wannan baƙin babi na rayuwa ta ba, zuciyata tana tsiyayar jini saboda Hafsatu, ko mafarki ne wannan idan na farka ba zan sake komawa cikin sauƙi ba.

Reina ki yafe ni, na gaza wurin riƙe amanar ki da Allah ya bani, ban cancanci zama uwa ba, Allah ya wadaran mai hali iri na, wanda zata cutar da ƴar cikin ta da kanta, domin koda wani na da laifi a baya na yake, ni na haifi Hafsah ba kowa ba, she's my responsibility ba na Yaseer ko na Ummi ba.

Ina fatan shi yana da masaniya a kan abinda yake faruwa da ke.
Jiki na bayi bani yana da hannu a cikin abinda ke faruwa saboda yaro ne mai nagarta tabbas, kuma iyayen shi nagartattu ne.

Amma ina tsananin fatan harsashe na ya zama gaskiya.'

Layin ƙarshe kenan a cikin littafin daga kan shi babu ƙari.

"Ina miki albishir a karo na babu adadi, babu komai a tsakanin ki da Yaya Yaseer bayan alkhairi, bai yi miki komai ba Aunty bayan alkhairi, kuma zan cigaba da niman shi ba zan taɓa dakatawa ba sai ya yafe min"

.....

"Feenah kina da pad a gida ne?" Reina ta tambaya bayan sun tashi a Hadda jin yanda kasan cikin ta yake murɗawa ta san daga anjima zuwa gobe period ɗinta na hanya.

Lokacin da ta fara tana da shekaru 14 bata ciwo ko kaɗan amma tana daɗa girma yana wahalar da ita.

Sai da tabi gidan su Safina ta bata laidan pad guda biyu da Ibuprofen kafin ta ɗauki hanyar gida da ƙafa koda zata ji daɗin jikin ta, tana da kudin abin hawa baba ya bata amma bata son shan maganin idan ba ya zama dole ba, don haka lokacin da ta shiga gidan Hajiya Hauwa har an fara kiraye-kirayen Sallar magriba.

Mutane ta gani a parlour maza, ta gaida su zata wuce ɗaya a cikin su yace "Hafsatu Tahir Kamal ko?"

Juyowa tayi tana amsawa da "Eh nice"

Ya miƙe ya miƙo mata manilla envelope.

"Gashi admission letter ɗin ki ne, an riga anyi miki registration da komai, ana resuming sabon session zaki iya fara zuwa."
Chapter 16 · 0% Book details