Sashe 26
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tunanin ko sanyin ƙanƙaran ke mata ciwo ya saka ya ɗaga tare da mayar mata ƙafar a ƙasa ya ajiye. Sai a lokacin ya furta kalmar "sannu" yana kallon fuskar ta da yayi caɓa-caɓa.
Murmushi yayi don ya kan manta da Aicha ƙaramar yarinya ce sosai saboda yanda take acting, dabi'un ta sun girmi shekarun ta, tana da juriya da jajircewa, ba kasafai take gwada raunin dake tuna mishi shekaru goma ne a tsakanin su ba.
"Dariya kake mun ko?" ta kwabe fuska zata cigaba da kukan yace
"ke da'alla shagwaɓa ba kyau yake miki ba" ya juya wurin Irfan da ya dame su da sannu yace "ɗauko min First aid box a kitchen in shafa mata magani. Daga nan kuma ku wuce ku yi alwalan isha mu wuce masallaci"
.
.
.
Wani asabar ɗin bai sake dawowa ya riske su a Nigeria ba. Shaƙar iskan Niamey yayi ya furzar yana jin ɗan sauƙin da zuciyar shi ke samu a duk lokacin da ya nisanta da matsalolin shi, Babban cikin su wanda ita ce Reina da a yanzu da ya saba da saka ta a cikin idanun shi, da ita zuciyar ke kwana yake tashi, yanzu zuciyar sai ta huta tunda yayi mata nisa.
Da fara'a Mariama da sauran kannen Aicha suka tarbe su, aka bazu a parlour ana gaisawa da ban gajiya.
"Darling kinka tafi kinka maƙale wurin ƴan uwan ki ko? Kin bar ɗan tsoho Daddy da aiki shi kaɗai" Mariama ta tsokane ta.
"Kai Maami kada ki haɗa mu"
Aicha ta tashi daga gefen Mariama ta koma gefen Alaji Abdou dake murmushi ta shige jikin shi.
"Daddy aiki fah nake koya a wurin yayan mu yanda zan na maka amfani sosai"
Lakatan hancin ta yayi "babu wanin nan kin dai fi son ƴan uwan ki a kai na"
Dariya suka yi ya shafa kanta yana saka mata albarka.
Kallon su kowa yake yi cikin burgewa, a wannan yanayin zuciyar da ya gama yiwa faɗa ɗazu ya tuno mishi da ita, da nata mahaifin.
"Yaya mai jikin Kuma Alhaji?" Kamal ya tambaya.
"Ahh jiki da sauƙi sosai, bai ma daɗe da komawa barci ba bayan ya ci abinci ya sha magani"
Miƙewa kamal yayi yana faɗin "toh bari mu duba jikin nashi"
Yaseer da Sabir suka miƙe zasu bi bayan shi, Suhail na kame a kujera, Irfan kuma cacan baki suke yi da ƙanwar Aicha, first born ɗin Mariama.
Basu tilasta musu su biyo su ba suka murɗa ƙofar ɗakin ya buɗe ya bayyana Alhaji Tahir dake kwance idanun shi a rufe, Injin dake ƙara a ɗakin na shaida bugun zuciyar shi.
Kusa da shi suka ƙarasa kawai suna kallon shi. Amma fuskar ta ke yi mishi yawo a kwanya. Yaya zata ji idan ta san mahaifin ta na raye? Wani irin farin ciki zata shiga?.
Basu daɗe ba suka fito don kar su tada shi a barci.
"Lallai jiki yayi kyau naga har kumari ya ƙara" cewar Kamal bayan sun dawo parlourn.
"Sannu a hankali wata rana har zai koma kan ƙafafuwan shi idan Allah yaso"
"Allah ya nufa, amma zamu wuce da shi maradi ku samu ku huta, ɗawainiyar da yawa"
"Bana tunanin akwai bukatar komawa da shi maradi, domin Lokaci ya ƙarato da zamu fara motsi a kan lamarin shi, idan bamu yi mun yi wani yunƙuri ba lokaci zai iya ƙure mana. Sannan babu sirrin dake rufuwa har Abada, idan bamu bayyana shi da kan mu ba muka bari wani ya fara ganewa to komai zai suɓuce mana"
Yaseer ya jinjina kai "Ƴar shi ma tana buƙatar kasancewa a kusa da shi, idan har za'a bayyana mata yana raye a shekarun da take yanzu yafi dacewa kafin rayuwar ta ya ɗauki hanyar da ba zai yi mata da kyau ba".
"Ka je wurin ta ne?" Sai yanzu Saudat ta sako baki.
Shiru yayi dan bai san wani amsa zai bayar ba. Idan yace ya je wurin ta ƙarya ne, haka idan yace bai je ba ma yayi ƙarya, Yana dai hangen ta daga nesa.
"Umma har abinci ya taɓa siya mata, Darling tace wai kar mu faɗa muku" Wa kuwa idan ba Irfan ba?.
"Ita ce mai rabin YK fa, abinci da kuɗin ta na siya mata ba wani abu ba"
Wani mugun kallo Saudat ta watsa mishi don bata taɓa tsammanin ko hanyar da Reina tabi Yaseer zai kalla ba ballantana.
Murmushi Alaji Abdou yayi ganin yanda Yaseer ɗin ya sunne kai "Ni na yarje mishi ya shiga lamarin ta Hajiya fatan ban yi laifi ba"
Da sauri ta girgiza kai tana sake fuska "A'a wallahi, tunda kai ne babu komai"
"Ban ga amfanin ayi ta tara mata dukiya tana can tana shan wahalan rayuwa ba shiyasa, ƴa mace ce, idan wahalar rayuwa yayi mata yawa zata iya shiga wani hali"
Maganar Alaji Abdou gaskiya ne, ita ma uwa ce ta kuma san zafin da iyaye suke ji a kan wahalar yaran su.
Daga nan babu wanda ya sake ɗago zancen Reina ko Alhaji Tahir suka cigaba da hiran Duniya suka ci suka sha kowa ya shiga hutawa banda Yaseer da fita ya kama shi daman jiran shi ake yi. Aicha kuwa da ta kama Irfan sai da ya sha zafafan ranƙwashi, ya ɗauki fushi da ita yana fadin gaba ko fuskar ta zata ƙona ba zai damu ba sai ma ya kawo man zafi a shafa mata.
....
Kallon agogo yayi ƙarfe 10 da 40 na dare, idanun shi har yaji suke mishi amma yafi awa guda yana juye-juye a kan gado barci yaƙi zuwa.
Wayan shi ya ɗaga ya danna numbern Aicha dake na huɗu a cikin favourites ɗin shi.
"Yayan mu?" Muryar ta mai haɗe da barci ya kira ta ɗaya layin.
Ba barci take yi ba saboda tayi barcin sosai da rana, so dai take yi yaji abinda take ji a kan nashi muryar barcin, yaji wani abu ya tsarga mishi amma shi bai ji komai ba.
"Darling ina magani na?" Ya tambaya kai tsaye.
Sai da tayi wani nishi irin tayi miƙa ɗin nan kana da amsa da "ya ƙare sai gobe zan karɓo maka"
"Gora biyu na bar miki, kin zo kin haɗa da wanda yake wuri na zaki ce min ya kare a ina? Ina jiranki ki kawo min yanzu kafin ran ki ya ɓaci" da haka ya katse kiran.
Ko na awa uku ne ya samu ya rage barcin sai ya samu faragar fama da kewar da ta fara cin shi tun yanzu.
Kallon layukan dake favourites ɗin yayi, duk layukan Niger ne ita ƙadai ce mai +234, layin wayan da ya siya mata lokacin graduation ɗin su ya bawa Daddyn Safina ya bata.
Layin shi ƙadai ne zai iya kiran tsohon layin shi na Nigeria koda bayi ƙasar. Saboda ita ya bar layin a cikin wayan shi har yanzu, kuma tunda ta kira shi sau ɗaya bata sake ba, a lokacin ma yayi mamakin ganin ta kira ɗin sosai.
Bayan minti 5 aka ƙwanƙwasa ƙofar shi, ya sauƙa daga gadon ya zura fararen takalmi a kafar shi yana tafiya yana haɗe sauran botirin rigan barcin shi kafin ya buɗe ƙofar yanda Aicha ke tsaye a cikin hijabi ta san idan tazo da pyjamas ɗin dake jikinta faɗa zata sha.
Hannu ya miƙa mata ta saka mishi maganin ya furta kalmar "Thank you" tare da juyawa ya rufo ƙofar shi kafin ta fara mishi sharhi a kan lafiyar shi.
~~~~~~~
Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.
*Seemahwrites ✨*
60
~~~~~~~~~
_But they could say the same bout you_
_Born blameless_
~~~~~~~~~~
Satin Yaseer ɗaya ya koma makaranta a China, yana ajin shi na ƙarshe kuma cikin ƙasa da watanni 8 yake saka ran kammala degree a karo na farko.
Bayan sati Uku itama Reina hutun ta ya ƙare, a wannan karon su Ummi sun yi yunƙurin biya mata kuɗin makaranta, ana buɗe registration suka je da yayan Fauziyya sai dai anyi ta saka numbern ta yana gwadawa babu a ita a cikin system. gashi kuma taga sakamakon ta na zagayen farko da zagaye na biyu na aji ɗaya, kuma tana da student portal ma, sun shiga a wurin amma duk yanda suka yi ayi generating remita ya ƙi, ƙarshe suka tura su DICT. Basu daɗe a wurin ba aka sanar da su suje gida kawai an riga da an yi mata registration.
Abun ya so ya ɗaga hankalin su wannan karon har da ita Reina ɗin, Ummi ne tayi tunanin ko masu sadaqatul jariya ne da basu son a san su wani a ciki ya tausaya wa marainiya.
A wannan karon ma Alaji Abdou yayi musu siyayya sosai ita da Maama wanda zata shiga ss1, a shawarar Alhaji Tahir aka tura kayan ta hannun Ummi, kuma aika ya isa yanda ya kamata daga kalan murnar da yaji a muryar yaran lokacin da aka kira a mishi Godiya. Alhaji Tahir da har yanzu sai an ɗaga an kwantar yana sauraron su yana ta sharar ƙwalla.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya sannu a hankali ga mai jira, da sauri ga mai buri, da gudu ga rayayye.
.....
*Bayan watanni Takwas*
Tsaye take a gaban tukunyar dake ɓararraka tana fasa maggi da hannunta tana zubawa, wanda yayi mata tauri da yawa ta saka a baki ta fasa da haƙori.
Yau ran ta a ɓace yake sosai don sun samu saɓani da uncle B tun jiya da safe gashi har almuru ta gabato bai kira ya bata haƙuri ba, bata taɓa tsammanin zai iya awa ashirin da huɗu bai ji muryar ta ba gashi har sun zarce hakan, shine umman Zahran nan zata wani ce tayi abinci za'a yi baƙo.
Ƙwafa take faman yi tana ayyana abinda zata faɗa ma Uncle B duk lokacin da ya kira, idan ma taga dama ta ɗauka kenan, idan tayi niyya sai dai ya kira ta wayan Hajiya Hauwa shima sai taga dama ta karɓa, zai gane yau ya taɓo ta ne.