← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 117

Sashe 23

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"In sha Allah"

Da haka suka yi sallama Safina ta maida mata wayar, itama Sallama suka yi saboda ya sanar da ita yana jin yunwa.

Bata sauƙe hannun ta daga wurin katse kiran ba Safina ta fara faɗin "daman Uncle ɗin Zaheera ne? Mai yara biyu?"

Reina ta juya ido "yap, da wa kike tsammani?"

Ta taɓe baki kawai domin maganar dake bakinta ba lallai taji daɗin shi ba.

Sauya akalar zancen tayi tana tambayar "Gidan Ummi zaki koma ne?"

Da can ɗin zai fi mata amma handouts ɗinta da sauran kayan karatun ta duk suna gidan Hajiya Hauwa kuma gobe ma suna da exams da rana.
"No, can gidan zan koma"

"Toh ki zo a kira su a faɗa musu kina nan inji mummy, don Daddy yace sai ya dawo zai maida ki"

Cike da jin nauyi tace "A'a fa zan iya shiga napep, na warke ai"

Safina ta harareta tare da miƙewa da nufin barin ɗakin "Sai ki kira Daddyn ki faɗa masa haka tunda ni ƴar aika ce"

....

Sabir ne miƙe saman kujera mai zaman mutum uku da remote ɗin Tv a hannun shi, Irfan da Suhail suna kan kujerar mai zaman mutum biyu. Hira suke sama-sama Suhail yana basu labarin ƴammatan shi, suna jiran lokacin da za'a haska wasan ball ɗin da suke son gani ya cika.

"Bros yaya kaga wannan babe ɗin?" Ma Sabir yake gwada fuskar wayan Amma Irfan sai leƙe yake yi.

"Yaya mu gani" ya karɓe wayan a hannun shi yana ƙarewa hoton budurwar kallon.
"Masha Allah ta haɗu" yace yana washe baki.

Sai da Suhail ya dungure mishi ƙeya kafin ya amshi wayar. "Kai me ka sani" ya miƙe ya koma kujeran da Sabir ke kwance tunda shi ya damu sai ya gani, ya ture ƙafar shi ƙasa ya zauna yana gwada mishi kaman dole.

Irfan ma ɗaya gefen yazo ya zauna suka saka Sabir a tsakiya, bayi da zaɓin da ya wuce ya maida hankalin shi a kan wayan shima.

"Tayi kyau" yace a taƙaice.

"Yaya sunan ta yaya?" Irfan ya tambaya.

"Muguwa nayi-nayi da ita taƙi faɗa min, username ɗinta a IG wai 'H angel' so da angel ɗin kawai nayi saving numbern ta, Amma barin sake gwada Sa'a na tunda naga tana online"
Ya ɗaura daga yanda suka tsaya a hirar su yanda zai sake mata tambayar a moment ɗin da ya dace.

"Toh kai ma sai kace dole, kana kai kan ka ana maka wulaƙanci"

"Barta ta ja ajin ta Please, sanin darajar kai ne"

Sabir ya taɓe baki, ya maida hankalin shi kan TV Irfan har ya tashi ya koma gefen Suhail an mayar dashi gefe an matse shi, shi da aka same shi a wurin amma bai iya mita ba da yayi musu tunda duk girman parlon kasa musu yayi.

"Yauwa gashi tana typing" Suhail ya bubbuga cinyar Sabir dole shima ya mayar da hankalin shi kan wayar.

'Hafsat' shine abinda ta rubuto, tare da hotunan da ya kwana biyu yana roƙon ta turo mishi, kuma a take suka yi downloading kansu suka sauƙa a kan wayar.

Suka haɗa baki Wurin faɗin "Kan uban can" Sabir ya ƙara da " yi maza ka danna mata block sannan ka goge number ƴar banza, har da hotunan ma"

Hannu na rawa ya shiga yayi blocking number tare da deleting chat ɗin su na Whatsapp baki ɗaya, sannan ya fita ya shiga contacts ya goge layin ta yana sauƙe numfashi.

"Sauran hotunan" Sabir ya tunasar dashi.

A rikice ya shiga cikin gallery ɗin shi ya hau kan hoton farko da niyyar gogewa lokacin da suka ji ƙaran tsayuwar mota a waje.

Irfan ya tashi da sauri ya ƙarasa window yana leƙawa sai ga Yaseer ya fito daga motar da aka buɗe mishi, babu ɓata lokaci kuma ya ɗauki hanyar shigowa parlorn riƙe da briefcase ɗin shi Muhammad na biye dashi da wasu takardun da basu samu shiga ciki ba.

Irfan ya juyo ya dube su cikin tashin hankali "Wallahi gashi nan shigowa"

"Shi wa?!" Sanin wanda ake magana a kai ya saka su tambayar ba wai don suna neman tabbaci ba.

"Yayan mu mana!" Yaji kaman yaje ya rufe su da duka, a yanda suke yin nan ma ai har zai riske su.

A maimakon Suhail ya Ida goge hoton sai ya cilla ma Sabir wayan. Yanda kasan ya ajiye masa garwashi ko riƙe wayar da kyau Sabir ya gagara, hannun shi yana karkarwa ya samu ya miƙe ya wulla ma Irfan wayar ai kuwa ya sake ta a kasa ya bita da ƙafa ya take jin an murɗa handle ɗin kofar an buɗe shi.

A tunanin shi ya hallaka wayar don haka ya ranƙwafa ya ɗauko sai dai babu lalacewar screen balle na waya baki ɗayan ta don haka ya koma da wayan kawai ya ajiye ta ya zauna a kai.

Haka Yaseer ya ƙaraso ciki ya same su jere su uku bi da bi, kallo ɗaya zai tabbatar maka basu da gaskiya, sai wulli-wulli suke yi da idanu.

"Sannu da dawowa yayan mu"

Yamutsa fuska yayi yana musu kallon tuhuma "ko arziƙin karɓan jaka yau ba zan samu ba?"

Aikin Irfan ne tunda shine ƙarami amma a halin yanzu shi ke zaune a kan wayar don haka tsugul Suhail ya miƙe zai karɓi briefcase ɗin Yaseer ya matsar baya yana kallon yanda suka haɗa gumi, ya kai duba ga AC dake tsaye a duk kusurwar parlon babu wanda bayi aiki.

"Da wata matsala ne?"

Dukkan su suka shiga girgiza kai, Suhail ya amsa da "Babu komai fa" yana murmushin yaƙe.

Ya ɗaure fuska "Toh menene kuka wani jeru kaman masu karɓan gaisuwa"

"Mu.. mu... Muna hira ne kawai"

Yana da tabbacin gulmar shi suke yi ya kusa kama su "Hmm, munafurci dai babu kyau" yayi shigewar shi ciki domin a gajiye yake tun fitar safiya gashi babu komai a cikin sa.

Sai da suka tabbatar ya ƙule ciki suka fito da wayar suna goge hotunan. "Ƴar banza zata jefa mu cikin matsala wai Hafsat. Yau da yayan mu ya ji sunan nan da mun kaɗe"

Muhammad dake fitowa ya jiyo su saboda ajiye masa takardun kawai yayi a study room ya juyo zai tafi nashi gidan.

Sun tsorata da ganin shi amma sai yayi murmushi kawai ya wuce. Suna ɗaga hankalin su a kan mai suna Hafsah bayan shi ogan daga wurin ainihin Hafsan yake, domin basu bar ƙofar gidan Alhaji Salisu ba sai da suka ga motar baban Safina ya shigar da ita ya fito.

......
*Yaseer*

Yayi iya ƙoƙarin shi wajen ganin bai sake duba ta ba tsawon sati guda domin ya samu maida hankali a kan ayyukan gaban shi kafin ta shanye tunanin shi baki ɗaya.

Haɗuwar yau kam ƙaddara ce, bai shirya mata ba, sabida haka ganinta yayi kamar a mafarki, irin mafarkin da idan yana yi bai damu da sai ya farka ba.

Suka shigo cikin restaurant ɗin hannun su cikin na juna, manganaɗisun ta dake manne a idanun shi ya tilasta mishi bin ta da kallo.
Tana cikin wata Egyptian abaya Navy blue, fuskar ta da matsakaicin kwalliya, wanda yake da tabbacin kwalliya baki ɗayan ta saboda fuskar ta aka ƙirƙira, domin haka duk kyan da zai yi ma wata ƴa mace a bayan ta ne.

Wani waiter ne ya ƙarasa yayi musu iso zuwa seats ɗin da babu kowa, sai a yanzu ya fahimci dalilin su na riƙe hannun juna kaman za'a raba su domin Safina ke jan ta ciki gabaki ɗaya a ɗarare take.

Kujeran da Waiter ya fara ja Safina ta zaunar da ita sannan ta zaga ɗaya bangaren ta ja ma kanta wani ta zauna, waiter ya basu damar duba menu kafin ya je ya juyo suka yi mishi godiya.

Ganin ya ƙura ma wuri guda idanu ya saka su Sabir juyawa su ga me yake kallo amma gefen fuskar ƴammatan biyu bai isa ya shaida musu kamannin su ba, basu da tabbacin hankalin shi a wurin ma yake.

"Lafiya yayan mu?" Suka tambaye shi ganin binciken su bai bada result ba.

Ya janyo Pacing cap ɗin kan shi gaba tare da maida hankali kan abincin gaban shi.

"Lafiya lau" ya amsa a taƙaice.

~~~~~~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

58

"Zaɓa wanda kike so a ciki" Safina ta faɗa bayan ta baje rigunan guda biyu a saman gado yanda Reina zata tantance da kyau.

Murmushin fuskar ta ya gagara ɓoyuwa ta nuna navy blue ɗin abayar mai adon baƙaken beads da flowers a jiki.
Ɗaukar rigan Safina tayi ta damƙa mata, "ki naɗe mu saka a jaka ko laida, sai mun je gidan kwalliya an gama mana kafin mu saka.

Reina ta waro idanu "Kwalliya mai tsadan nan?" Ita bata taɓa yin heavy make-up a fuskar ta ba, ko biki za'a yi a family sai dai ayi ma su Zaheera banda ita, tunda bata da mai biya mata.

"Eh, kuma wanda zata mana ta iya sosai" Safina ta riƙo hannun ta suna dirin murna.

"Amma to kuɗin zai isa mana? Ni a bar kwalliyan kawai mu shafa powder muje wurin nan, ina son zuwa wallahi"

"Kada ki damu, saurayin ki mai yara biyun nan ya turo kuɗi ɗazu, amma monday zamu je a buɗe miki account kema kafin ku maida ni ƴar aikan ku"

Matse baki tayi a ƙoƙarin ta na haɗiye murmushin ta kada ta ƙular da Safina domin ta lura ba son ta da Uncle B take yi ba. Ba don ita Safinar bace ba ma sai tace Hassada take mata, domin bata tunanin akwai wacce tayi sa'ar masoyi kaman ta.

Iya zama kam Reina ta zaunu a kwalliya har saida ta ji ba daɗi tana sakawa a ranta bata sakewa amma lokacin da taga kanta a madubi sai taji ko yanzu aka ce ta sake zaman babu musu zata sake.

Da alwalar su ta azahar don haka suka kabbara la'asar suka sallame suka zura rigunan su kana mai kwalliyan tayi musu rolling gyalen abayar suka fito kaman wasu ƴammatan larabawa.
Chapter 23 · 0% Book details