← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 117

Sashe 80

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Already gidan Ummi ya cika da mutanen ta, sannan duk abinda baƙi zasu buƙata an tanadar da shi don ba ƙaramin tanadi tayi ba a kan bikin jikallen ta, takwarar ta, ƴa ta farko a wurin Fauzee, don haka da suka zo da nasu suna ta hayya-hayya har da tsayawa a kan abincin kada yara su taɓa da matan da suka yi tunanin na gidan Umma da ake kawowa kullum ne ya zo suma suka je dubawa aka hana su, abun ya so ya ɓata ma Ummi da su Aunty Zeenat rai amma ta share ta bar su da halin su ta kuma hori su aunty Aina kada su bi ta kan su don idan rigima ya tashi sune da asara ma su zasu ɓatawa biki su bar musu abin faɗa.

Haka duk baƙon da ya zo gidan kafin lokacin walima idan aka saka mishi abinci su Hajiya Jummai ma sai su zubo nasu su kawo, baƙi kam barkan su wasu harda takeaway suka yi.

Daga ɗakin da ya kasance na Maama lokacin da take rayuwa a gidan Reina ce zaune a kujerar mai kwalliya ana fyante mata fuska. Sai ƙoƙari take yi wajen ganin ta matse murmushinta na jin daɗin yanda ƴan ɗakin suke zuzuta kyan da tayi tun kafin a ma gama kwalliyar, Saboda ran mai kwalliya ya fara ɓaci har ta ƙare ta fara mitan tana karkata ta.

"Umairah ungo!" Aunty Aina ta miƙo mata abincin da yaji nama a plate ɗin tangaran. Lokaci ɗaya murmushin da mai kwalliya ta sha fama da shi ya ɓace, tun ba yau ba ta san ta shiga uku dama.

"Nikam wai Reinan ta canza suna ne Mama Aina?" Safinah ta tambaya tana dariyar yanda Reina ta hade rai lokaci guda. Tun jiya taji suke ta Umairah-Umairah kuma ta lura da Reina suke yi sannan ita bata so.

"Habibin ta ne ya canza mata kinga muma ba sai mu shiga sahu ba mu kwashi karama?"

Safina ta hau dariya harda buga cinya duk haushi ya cika Reina. "Toh daman sunan da yake kira na dashi naku ne? Kuma A ina Aunty Sajida taji yace Umairah fisabilillahi. Umry ne fah! Yana nufin My Life da larabci."

"Awww.." ƴammatan ɗakin suka saki shewa. Ƴar aunty Zeenat wanda ta girmi Reina da kaɗan tana ƙarawa da "god when?"

"Kema idan yazo rashin kunyan kenan zaki yi?" Aunty Aina ta tambaye ta.

Caraf Reina ta amshe da "wani rashin kunya kuma? Ina abin rashin kunya don kawai na gyara muku suna?"

Aunty Aina ta jinjina kai tana tuna shirin bikinta da Jamal "Yanzu zaki karɓi abincin ne ko kuwa?"

Hannu ta sa ta karɓa don ta tashi musu a kai, zata ajiye a gefe Aunty Aina tace ma mai kwalliya ta dakata sai ta gama ci tukunna.

"Kuma zan dawo in duba, inga ƙwayar shinkafa a saman plate ɗinnan ki gani"

Kaman zata fasa ihu tace "Amma Mama Aina kiga yawan abincin nan fa an shaƙe plate ta ina zan fara cinye shi?"

"Wannan karon babu mitan an baki abinci a rubber kenan?" Maama ta sako bakinta cikin zancen, Safina ta kece da wata muguwar dariya tunda su uku kawai suka san yanda aka yi a wajen, ta juya ta bawa Maama hannu suka sha suka cigaba da ƙyaƙatawa.

4:35pm.

"Bani son African time, Wallahi naƙi jinin African time a rayuwa ta. Ita Hafsatun me take yi a ciki har yanzu an tara mutane a wurin walima ita kawai ake jira? Ba ance tun 3 da rabi suka gama wahalalliyar kwalliyar ba? Yanzu ai yaci ace sun gama shiryawa ko?" Ummi ke wannan sababin tana ratsa tsakanin su Hajiya Hauwa da su kaɗai suka rage a parlo suna zaune jungum-jungum da yaran su wai su zasu wuce da amarya.

Ta ƙarasa ɗakin da amaren suke. Bata sha wahalan dube-dube ba idanunta suka sauƙa a kan Reina dake tsaye tana rangwaɗa da juyi a gaban cameran mai kwalliya, sauran ƴammatan ma sun saita ta da wayoyin su basu ma lura da shigowar Ummi ba.

"Oh ni Hafsatu." Ummi ta riƙe baki. Sannan ta ɗaga murya yanda Reina zata jiyo ta tace "Kin san Allah zan saka uwar ki Saudatu tazo ta tafi dake tun yau don ba zan iya ba! Yanzu yaron nan ya turo muku motoci tuntuni ina tunanin matuƙan su a unguwar nan suka yi sallar la'asar amma kun shanya su kusan awa guda?!"

Jin yanda Ummi ke sababi mai kwalliya tayi saurin mayar da cameran ta jakar shi ta shiga since ring light bayan ta kashe kafin Ummi ta gama ta dawo kanta tunda ta lura ba son kwalliyan take ba dama, tayi mita kaman ta ari baki jin yawan kuɗin da ake biya na kwalliya wanda bai kai ko rabin kudin da aka biya ta bama.

Ummi bata bar ɗakin ba sai da ta angiza ƙeyar su ta rufo ƙofa.
Salati ne ya kuɓce wa Inna larai (tsohuwar mai aikin Hajiya Lubabatu) wanda isowar su kenan da tawagar ta zuwa bikin ƴar Fauziyya da Yaseer ɗin Umman Yaseer.
A yayin da kusan ashar kala guda ne kuɓuce ma su Hajiya Jummai da ƴan uwanta da yaran su ganin yanda Reina ta fito kaman tauraruwa a sararin samaniya.

Mutanen Inna larai suka shiga sakin guɗa Reina sai washe baki take kaman gonan auduga bata lura da Zahra da take fuska fayau kaman wanda zata je gaisuwar mutuwa ga zazzaɓin da ya rufe ta don harda agogon likitan ta a hannu ko kuma Zaheera dake binta da kallon ƙyashi ranta na ƙuna ba ta wuce wurin su Inna larai sannan ta ɗan durƙusa ta gaida su. Inna larai sai shimata albarka take tana aikawa mahaifiyar ta addu'ar samun rahama a wurin ubangiji.

Ummi ne ta sake musu tinin masu jira sai ma suka juya a tare kawai, su Hajiya Hauwa basu yi ƙasa a guiwa ba suka rufa musu baya.

A motar Muhammad aka saka Reina Maama ta shiga gefen ta Safina ta shiga gaba. Sauran ƙawayen guda huɗu suma suka samu mota kowa ta shiga gaba muƙarraban inna larai suka cika bayan aka kama hanyar wurin walima biye da jelar su na dole.

Tun ana wa'azi Reina tana murmushi da ɗaga ma mutane hannu har ta ƙare ta koma yaƙe kawai don abinda ake faɗa ya fara shiga jikinta, yanda ake tuna mata girman aure da girman miji ya saka ta fara kokwanton ko dai ta ɗauko dala ba gammo?.

Lokacin da aka gama wa'azi duk tayi luƙus, ita dai ta san ana jan ta daga nan zuwa can kuma hasken flash har ya gama kashe mata idanu amma tunanin ta bai wuce cewa nan da awanni 15 ta zama mallakin Yaseer all in all ba.
Ya ilahi.

Umma ita ta jata ta saka ta a mota ganin masu ɗaukan hoto ba masu gamawan yanzu bane kuma har an fara kiraye-kirayen sallah. Maama daman ta daɗe da dawowa cikin motar don duk sun ƙarar mata da energy ɗin da ta tanada na bikin tun yau, sai dai rashin dawowar Safina motar ya saka Muhammad neman afuwan Reina da su ɗan ƙara jiran ta.

Ita bata ma ji shi ba tayi shiru ta zurfafa cikin tunani, tunanin girman matsayin Yaseer da kuma yanda rayuwar su zai kasance daga gobe.

Zata iya kula da shi yanda ya kamata?
Zata iya mishi biyayyar da ake buƙata?

Ta sauƙe numfashi lokacin da Safina ta buɗe gidan gaba ta shiga tana basu haƙuri, Muhammad ya kunna motar suka fara tafiya.
"Na tsaya tabbatar da souvenir ɗin ƙawaye ya shiga hannun su ne don gida zan wuce yanzu, akwai abinda zan yi idan ba Sa'a ba ma in kwana".

"Ki kwana kuma? Ni da na faɗa miki abinda zamu yi cikin dare shine kuma kike wannan maganar?" Ta faɗa kaman zata fasa ihu. Kukan da ta jure bata yi shi a wurin walima bane take niman dalilin yin shi a yanzu.

"Ai shi ɗin zan je miki hajiya ni bani son sakalci ni ba yaya Yaseer bane"

Ta ƙunsa amma dai tayi shiru don ta san tayi kuka tsokana zata sha. Cikin ƙanƙanin lokaci suka koma tunda daman ba nisa wurin yake da shi sosai ba. Ta cire takalman ƙafarta tun daga ƙofar shiga safina ta sunkuya ta tattara mata Maama kuma na riƙe da purse ɗinta da laidan souvenirs ɗin su.

Kaya ta fara tuɓewa tayi sallar maghriba Sannan ta shiga duba messages ɗin Yaseer tana zaune saman darduman. Tun shekaran jiya rabon da su samu faragan yin waya yanda ya kamata, yayi busy itama haka sai dai su yi ta ajiye ma juna saƙo.

Tana shirin reply sai ga kiran Uncle B. yau ma sai da gaban ta ya tsinke kafin tayi ta maza ta ɗauka tana masa sallama tare da ayyana a ranta daga daren yau dai shikkenan gobe bayi da hurumin magana da ita don haka blocking ɗin shi zata yi suna gama wayan.

"D.. Hafsah. Yaya kike yaya hidima?"

"Ina wuni uncle Bilal"

"Lafiya ƙlau, yaya jikin ki, kin sha maganin ki yanda nace ina babu abinda ya faru tunda aka fara hidiman?" Yayi maganan yana fatan jin akasin abinda ya tambaye ta yanda zai samu daman da zata fito daga gidan zuwa asibiti a daren don daren yau ne dama na ƙarshe da yake da shi.

"Eh na sha, kuma ban ji komai ba tunda na sha ɗin, Nagode."

Aicha bata canza mata maganin ba kenan? Ya ayyana a ransa.

"Okay Masha Allah. Daman maganan Doctor ɗinnan ne da nayi miki wanda zai duba ƙafan daddyn ki. ya shigo yau ɗin yayi wani surgery kuma zuwa ƙarfe 12 jirgin shi zai tashi ya koma."

Da sauri tace "dan Allah uncle Bilal?"

"Ba nayi miki alƙawari ba Hafsah? So na dai yi mishi bayani yace in sha Allah mahaifin ki zai sake takawa Amma akwai buƙatar ki gana da shi ki roƙe shi kema ya san da gaske muke yi don samun ganin shi ba abu ne mai sauƙi ba".
Plan B ɗin shi kenan, wanda ko da taimakon Aicha ko babu idan ya samu Reina ta fito daga gidan shikkenan an gama.

"Toh bari nayi Isha sai in tambayi Ummi mu zo da Maama tunda Safina har ta tafi"
Chapter 80 · 0% Book details