← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 117

Sashe 93

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya Reina take yi sosai daman ta sani dalilin kenan, don Safina akwai raina maza tafi son wanda ya bata shekaru goma ko fi idan da hali ma sha biyar.
Saida ta daidaita kanta ta dubi safina da ta cika ta tumbatsa tace "To ai shima ya girme ki da wurin shekaru 6 nake ji, ai kinga akwai tazara ko? Kuma kinga dogo ne zaku dace"

"Wallahi kada ki saka in zage ki, in banda son kai ke gaki kin samu wanda yayi daidai da ke ni kenan sai in zo a matsayin matar ƙanin mijinki kune manya kafin mu? Allah ya sawake."

"Daman ban girme ki bane?"

"Da wata biyu ba?"

"Ko da minti biyu ne dai na girme ki ehe"

Safina ta taɓe baki ta miƙe tana ɗaukar hanyar kitchen, can sai gata ta haɗo ma kanta kayan motsa baki ta nemi wuri a saman lallausan ottoman carpet ɗin ta zauna ta fara tanada ma cikinta.

"Gwamma dai mu fito a matan abokai abun zai fi mutunci Suhail kuma yaje ya nemi sa'ar shi nama cire yayan tunda kalmar ne ke ruɗan shi"

Reina ma ta sauƙo ta same ta don saida taga tana ci abubuwan suka bata sha'awa ta saka hannu suna ci tare tace "nikam ba kece kike min huɗuban auren mai mata ba?" Reina ta tambaya da ba'a.

Ɗage gira Safina tayi tace "maƙaryancin mai mata ba? Ai ba dan Uncle Bilal ya sako ƙarya a cikin lamuran sa ba kema kin san babu abinda zai saka in yi adawa da tarayyar ku. Amma kinga yaya Muhammad bai zo mun da ƙarya ba"

Reina ta jinjina kai "ai shikkenan" daga nan suka shiga wasu hirarrakin domin ta san matsa ma Safina ba shi zai saka ta canza ra'ayi ba.

Sai da ta bari ta shiga alwalan la'asar a banɗakin daya daga cikin ɗakunan baƙi dake ƙasa sannan tayi sauri ta kira Suhail ta sanar da shi zuwan Safina sai yazo ya ritsa ta suyi ta da bajewa a tsakanin su.

Sun idar da Sallah ba da daɗewa ba sun koma suna kallon a tare sai gashi ana knocking ɗin ƙofa. Dake Reina ta riga da ta san waye mayar da hijabinta tayi ta miƙe ta nufi ƙofan zata buɗe.

"Waye?" Safina ta tambaya gudun kada mijinta ne ya dawo.

"Ina ga abinci aka kawo mun" ta amsa tana murɗa handle ɗin ƙofar ta buɗe shi, cikin Sa'a kuwa Suhail na riƙe da babban basket ɗin abinci.

"Yau kai aka ɗago yaya Suhail? Bismillahi" Reina ta ɗaga murya yanda Safina zata jiyo su, ai kuwa tsugul ta mike zata gudu saidai ya riga da ya ida shigowa ciki.

"Sannu Feenah" yace lokacin da suka yi ido huɗu tayi wuri-wuri kaman wacce aka kamata tayi sata.

Murmushin karfin hali tayi tana gyara tsayuwarta kana ta amsa da "sannu yaya Suhail" ta dubi Reina dake dariya ƙasa-ƙasa ta watsa mata harara.

"Ni barin wuce da abincin sama. Feenah ki taimake ni ki ɗan bashi ruwa" bata tsaya jin ta cewar ta ba ta wuce ta bar su tsaye a wurin.

"Yanzu Babu Maama da zaki turo mun ki samu daman guduwa, Please ki zauna muyi magana"

Zaman tayi tunda bata da ta cewa.

Shima ya sama ma kan shi matsuguni sannan ya shiga tambayan ta yaya makaranta da zafi saboda ta ɗan sake kafin su kai ga gundarin abinda ya kawo shi.

"Zafi akwai, makaranta kuma muna hutu"

"Yayi kyau, Allah ya taimaka, sai kuma laifin da nayi miki fa? Kin huce?"

"Wani laifi ka yi min ni kuwa?"

"Laifin cewa ina son ki mana?"

"Hmm" kawai tace ta mayar da duban ta gefe.

Ya ɗaura da cewa "ban ce sai kin so ni dole ba Feenah, ban ce sai kin rabu da Muhammad ko wani saurayin ki kin kula ni ba, kawai dama nake so ki bani ɗan kaɗan kuma ki daina gudu na don Allah, ni ba dodo bane, ki bani dama komin kashin sa idan abu ya gagara sai in haƙura in rabu da ke, amma kin sani wulaƙanci babu kyau kuma wannan ba halin ki bane"

Ta ɗan yatsina fuska, Ba halinta ba a ina ya san halinta? Amma sai tace "shikkenan, in sha Allah "

Yace "toh kiyi unblocking ɗina yanzu."

"Ni yaushe nayi blocking ɗin ka?"

Ɗaga wayan shi yayi ya danna mata kira ya saka a speaker, kafin ta kai ga dauƙo wayan da ta bar shi a kan kujerar da ta tashi ɗazu taji har ya tsinke ba tare da kiran ya shiga ba, kuma shima yaga wayan a kunne, gidan kuma da network.

A kunyace ta ɗauko wayan tayi ƴan danne-danne sannan ta ɗago tace "na cire, ashe na saka ban sani ba"

Sai ya murmusa yana ƙare mata kallo.

"Kin yi kyau" shine kalma na gaba da ya fito daga bakin shi. Sai ta shiga gyaran mayafi ta lulluɓa da kyau kana ta amsa da "Nagode"

A haka kaman da wasa ya jata suka ɗan taɓa hira,Reina kuma ta mayar da kallon ta parlon Yaseer bayan sun yi waya da shi ya sanar da ita yana maghriba zai taso saboda saida yabi office kafin ya wuce gidan su, ya bata wayan suka gaisa da Umma, Maihakuri da Auta, bata tambaye su jikin Aicha ba saboda bata san bata da lafiya ba. Maama kuma da safe Ummi ta haɗa su sun gaisa dukda Maaman bata so ba, a cewar ta bata da abinda zata ce mata.

Ƙarfe 6 daidai kiran safina na 7 ya shigo wayan ta, sai a lokacin taga daman komawa ta same su yanda Safinan zata samu hanyan guduwa, iya tunzura kam ta san ta gama tunzura.

"Na barku ku kaɗai" tace tana ƙarasowa, Safina ji take kaman ta shaƙe ta dan haka tayi saurin miƙewa tana saɓa jakarta.

"Zan wuce Maghriba ta kusa, na san yanzu mummy zata fara nima na" ta faɗi saƙon ma Suhail ne Amma idanunta suna kan Reina tana jifan ta da mugun kallo.

Kafin Reinan ta kai ga buɗe baki Suhail yace "nima kuwa unguwan zani wurin wani friend ɗina, muje in ajiye ki saboda samun abun hawa da wahala a unguwar nan"

"Kaman ka san da complain ɗin shi tazo a bakin ta kuwa ƙani na, mun gode. ai ba ma sai nayi muku rakiya ba don yayan ku yana hanya zan shirya masa abinci" tace tana juyawa tare da daga hannu ma Safina wanda ta dau alwashin ba zata sake dawowa gidan ba.
.
.
*Yaseer*

"Yaya jiki"

Cikin murya mai rauni Aicha ta amsa masa da "da sauƙi" tana kallon kaman ya ƙara haske da murmurewa, yana cikin kwanciyar hankali yana can suna shan romon amarci da soyayya tare da Reina shiyasa ashe bai tashi zuwa duba ta ba sai bayan kwana huɗu, bayan tana da tabbacin ya san a kan shi ta shiga wannan halin.

"Allah ya ƙara sauƙi" yace cikin alhini, sai kuma yayi shiru bukatar da ya kawo shi gareta yana mishi nauyi ganin tana halin jinya amma yake niman fifita son zuciyan shi.

"Idan kika warware akwai inda zaki je ki ƙare hutun ki ne ko kuma a nan zaki zauna?" Yayi mata tambayar a sigar da ya san ita zata ɗauki damin ta ɗora a kanta kuma amfanin ciki nasa ne.

"Akwai abinda kake so ne in yi maka?" Tayi masa kalan tambayar da yayi tsammani daga gare ta.

"Kawai tafiyan da zan yi ɗinnan ne zan fi so ace tare muka je saboda kin fini ƙwarewa a fagen negotiation, mutanen nan will need a lot of convincing kafin su yarda su janye ƙudurin su domin ba da sauƙi muka samu suka yi investing ba da farko. Muna buƙatar bold group Aicha kuma muna buƙatar ki a wannan deal ɗin"

Murmushi ne ya suɓuce mata, daɗi ya baibaye zuciyar ta, sai taji kaman ma ta riga da ta warke. Tace "mun yi magana da Muhammad ya sanar da ni komai in sha Allah Monday tare da ni za'a tafi, amma..."

"Amma me?"

Ta ɗago ta dubi yanayin shi, kafin ta sake sunne kai, "yayanmu kayi haƙuri ka yafe min Abinda ya faru dan Allah, Wallahi tun kafin in aikata nake nadama kuma na ji daɗi da plan ɗin shi bai yi aiki ba"

Ya kalli agogon hannun shi yana miƙewa jin an fara kiraye-kirayen sallah. "That's a topic for another day, yanzu yamma yayi ina buƙatar komawa gida"

Tayi saurin miƙewa itama dukda jiri-jiri da take ji. "Dan Allah yaya Yaseer, Wallahi ba tare da Bilal ba ko a karan kaina nayi alƙawarin ba zan sake yunkurin cutar da Reina ba, zan zauna lafiya da ita, kuma a shirye nake in yi mata bayani in bata haƙuri"

"Amma meyasa tun farko kika yi yunƙurin ɗora mata laifin yanda zan ga baƙinta a lokacin da muke daff da zama ma'aurata? Kin san na sani Reina bata da tunanin da zata shirya haka da kanta, ɗaukan wayanta ki tura min text ba zai isheni hujjan da zan kama ta da laifi ba. But save your explanations to yourself, komai ya riga da ya wuce saidai a gyara dan gaba, Allah ya baki lafiya" ya juya ya bar parlon yana haɗa benen bibbiyu yana sauƙa zuwa parlon ƙasa jin har ana niman shiga Sallah.

Saida ya shiga gidan yayi musu Sallama bayan ya dawo daga masallaci duk suka bada saƙon gaisuwa a bawa Reina sannan ya fita ya ɗauki hanyar gidan shi cikin nishaɗi da ɗokin ganin sanyin idaniyan shi.

~~~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

103

Ƙamshin turaren wuta haɗe da air wick da ya gauraye parlon ya saka shi sakin murmushi kafin ta ƙaraso da gudu ta shige jikin shi, kayan hannun shi ya sake a ƙasa ya daga ta yana juyi da ita a tsakar wurin.

Saida ya ga zata fara jin jiri kafin ya sauƙe ta suna ƙyalƙyala dariya. "Kin yi kewa ta ko Umry? Gaskiya idan kina gida waje babu daɗi"

Tayi murmushi tana karya kai "welcome back Babe, I was dying to set my eyes on you again"
Chapter 93 · 0% Book details