Sashe 113
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai a lokacin ta tuna da Yaseer ya faɗa mata a tare aka ɗaura auren su, amma ai sai yanzu ake biki, shi cikin daga ina kenan?.
Bata gama tunani ba taji wani amai ya taso mata tayi saurin saka hannunta biyu ta toshe bakinta, sai a lokacin ta lura da saman kan kifin Aicha take. Ta juya da gudu tayi bathroom ɗin dakin, Aicha ta bita da idanu tana murmushi, Allah yasa itama cikin take da shi su sha kunyan a tare, abun ba zai yi mata nauyi sosai ba tunda ba ita kaɗai bane, ai daman mutuwan yawa kaka.
Duk yanda Yaseer yaso yayi hanyar fito da Reina a daren ta dawo ɗakin shi abu ya faskara domin haɗa ta ɗaki aka yi da Ƙanwar Aicha mai binta da kuma Maama, har barci ya ɗauke ta ƙanwar Aicha na faman bada labarai Maama na sauraron ta, idan buƙata ta taso ta ɗan tanka. Oga Yaseer kuwa sai juyi yake yi a gado, kaman da wasa Insomnia da suka yi wata ɗaya da rabi da sallama ya dawo ya same shi, ga gajiyan hanya amma bai samu barci ya zo masa ba sai da ƙarfe biyu ta gifta.
Washegari da yamma za'a fara gabatar da events, don haka kowa ya tashi busy sai aka bata abun karyawan Yaseer ta kai mishi sai tazo ta karɓi nata a wurin Maami.
Jin ta ƙwanƙwasa ƙofa babu response sai ta ajiye tray ɗin a ƙasa ta tura ƙofar ta sake ɗauka ta shiga.
Ya fito daga wanka kenan, daga shi sai boxers yana tsane kan shi, ta ajiye tray ɗin a centre table da ta gani a tsakar dakin tana gaida shi.
Juyowar da zata yi ya rungume ta a ƙirjin shi tana jin tiririn da jikin sa yaje fitarwa na zafin ruwan da ya watsa a jikinta kana ya amsa gaisuwar ta. "Ban iya barci ba jiya Umry, sai kaɗan, kuma tunda na tashi da ketowar alfijir na kasa komawa." Yace yana daɗa shigar da ita jikin shi don ji yake yi kaman na sati ɗaya aka raba su ba kwana ɗaya ba.
"Toh ka kwanta yanzu idan ka tashi sai ka ci abincin, ko abincin zaka fara ci kafin ka kwanta?.
"Kina jin yunwa ne?" Ya tambaye ta.
"Ni naci abinci tun da asuba, ka san gajiyan tafiya na saka yunwa. Amma zuwa anjima zan sake ci."
"Toh shikken" yace yana yunƙurawa ya raba ta da ƙasa sannan yayi hanyar gado da ita.
Ta waro idanu cikin kaɗuwa, "yaya Yaseer gidan mutane muke"
"Barci zamu yi." Yace yana dire ta a saman gadon shima ya hau, ba a son ranta ba itama barcin ya ɗauke ta. Bata tashi fitowa daga ɗakin da tray ɗin abinci ba saida aka kira sallan azahar, fatan ta ɗaya kada Allah ya saka suyi ido huɗu da Umma, sai ta gudu ɗakin Aicha dake ba ƙawaye gare ta ba ita kaɗai tana waya da uban babyn dake shafaffen cikinta.
Ita dai Reina duk inda zata ci karo da abu mai ƙarni kaman nono da kifi guje masa take, Amma dangin mijin Aicha sun jawota cikin su ana ta shagali, duk inda za'a je kuma tana tare da mijinta, yana tabbatar da ya kaita venue ɗin event lafiya ya dawo da ita cikin aminci.
Taƙaita bidirin da za'ayi Rafeeq ya roƙi mahaifiyar sa da ayi, dake Maami ma da iyaye maza sun san halin da ake ciki sai suka goyi bayan hakan, ba'a wahalar da amarya mai juna ba amma ƴan biki sun sha bidirin su har aka yi aka gama aka raka Aicha gidan Rafeeq dake cikin Estate.
Maami da sauran suna kallon yanda take kuka ne kawai da ba zasu ce na menene ba tunda idan sabo ne sun riga da sun saba gashi har da tsaraban alƙawari a tsakanin su, don haka tashin hankali da damuwan da take tunanin zata shiga ranar da za'a raba su ma bata ji ba, ta dai bita da addu'ar alkhairi da Allah ya raba lafiya.
"Maman baby" cewar Rafeeq yana leƙowa cikin mayafinta bayan kowa ya watse, kuma an tura ma Reina kuɗin ƙawancen ta, domin ita ta tsaya mata a babbar ƙawa amma Yaseer yace ba zata zo Abuja ba gida zasu wuce.
Ɗagowa tayi ta harare shi tana turo baki, "I think I like you better when you're not speaking, tunda baka gajiya da tsokana na a kan abinda yake laifin ka ne"
Ya yaye mayafin daga kanta ya ajiye a gefe, yana duban ta cike da so da ƙauna "Ko? Gashi kuwa I'm best at keeping mum. Amma yanzu zamu sake su nafilan ne ko kuma wancan da muka yi ya wadatar?"
109
Shiru tayi kawai tana kallon shi, shima itan yake kallo yana jiran amsa. Sai ta shiga juyawa tana dube-dube.
"Me kike nima?" Ya tambaye ta yana taya ta duba abinda bai san ko menene ba.
Ita kuma ganin pillow yayi mata nisa sai ta ɗauki gyalen ta da ya ajiye a wurin ta tukuikuye shi sannan ta wurge shi da shi, yayi saurin caɓewa yana dariya. "Ni fa tambaya kawai nayi"
Ƙwabe fuska tayi kaman zata yi kuka "Idan baka bari ba Allah gida zan koma" tace tana murje-murje.
Ya riƙo kafaɗun ta yana ƙoƙarin tsayar da dariyar shi. "Sorry na bari Maman baby na."
"Kuma ka daina ce min Maman baby"
"Toh na bari mai ciki"
Ta ƙara saka bori tana ƙoƙarin ƙwacewa daga riƙon shi. "Ni kawai ka maida ni gida idan na haifi abinka sai in kawo maka"
"Wani gida? Gidan da muka samu baby? Kinga daman ya fi nan sirri"
Ta kwanto da kanta a kafaɗan shi a tunanin shi ta sadaƙar ne, ya saki ƙara ba shiri jin zafin cizon da ta gallara masa. Ta ɗago ta kalle shi tana huci. "Mai juna biyu shi kuma babyn naman Daddy zai fara ci?"
Ta sake ranƙwafowa zata ƙara mishi yayi saurin tare ta. "Sorry, muje ki ci abinci, sai mu huta ko in gaisa da baby tunda yanzu an yi biki" sai kawai ta koma baya ta kwanta kanta na kallon ceiling domin yanzu kam ta sadaƙar.
......
"Nayi missing ɗin ɗakin nan bae" cewar Reina tana shiga ƙasan duvet ɗin da Yaseer yake ciki. Ya gyara mata rufuwa yana zagaye ta da hannun shi don har barci ya fara kama shi, "nima haka" ya amsa cikin ƙasa da murya bakin shi a saitin kunnenta, sai yanzu yake jin zai sauƙe gajiya mai gabaki ɗaya.
"Shikkenan yanzu har an yi biki an gama sauran na ƴan baya, ko su waye next?, da Feenah zata yarda ne kaga nan ba da daɗewa ba za'a sake wani gagarumin bikin, Maama ma tana nisa a University zaka ji an fara zancen aurenta"
Ɗan darawa yayi "Tunda kin yi aure kowa ma yayi ko?"
Murmushi tayi tana juyowa ta fuskance shi. "Ina musu sha'awar samun yaya Yaseer ɗin su ne duk da na san it's impossible amma ina musu fatan samun dacewa da kwatankwacin shi, mu kuma mu sha biki ga karɓan kuɗin ƙawance ma akwai daɗi ashe"
Ya ja lallausan kumatun ta "kullum ƙara min kyau kike Umry, My beautiful forever"
Ta ɗaga gira tare da fari da ido, duk daɗi ya cika ta.
"Yauwa kafin in manta Ina son sanar da ke gobe za'a yi reopening case ɗin mu NDLEA sun yi approving order of production da court ta tura kuma sun bada handover ɗin shi, kuma na faɗa miki ne ba don ki daga hankalin ki ba sai don bani son ki fara ji a wani wurin. But idan kina son faranta mun kada kice zaki shiga Reina please, ki barni nayi handling mana komai Saboda zan iya"
Saida tayi shiru na ɗan lokaci tana kallon fuskar shi tana ayyana dalilin da zata musa ko kuma uzurin da ya kamata ta bayar, amma komai yazo kanta bayi iya sauƙa kan harshen ta.
"Toh" ta amsa mishi kawai.
"Allah yayi miki albarka" ya sumbaci goshinta, ta amsa da Ameen jiki ba ƙwari.
Washegari ya kasance mata ranar da zata fara girki don haka tana sallar asuba ta shiga ta wanko ban ɗakin su tare da wanka ta shirya sannan ta sauƙo tunda Yaseer sammakon fita zai yi, bayan ɗan lokaci ta tattare ko ina ta baje gidan da ƙamshi sannan ta shiga haɗa ma mijinta abun karyawa.
Saabo da aiki cikin tashin hankali, gaggawa da matsi wajen sarrafa abinci a rayuwar ta na baya ya saka girki ya zamo cikin abubuwan da suka fi mata komai sauƙi a lokacin da take cikin nutsuwar ta. Kuma tana son girki saboda yana saka ta farin ciki haka kawai tare da kawar da tunani da damuwa daga cikin kanta.
Shigowa kitchen ɗin Yaseer yayi goma ta wuce. lokacin ta gama zuba komai a cikin sabbin warmers tana jera su a kan sabon tray ɗinta. "Subhanallah wannan ƙamshi haka chef Wifey"
Ɗagowa tayi ta dube shi, yana cikin ɗanyen shadda fara ƙall da hula wanda duk kyan da za'a ce ya taɓa yi wa wani namiji to yau yaya Yaseer ɗinta yayi cancelling ya kafa sabon record.
Ta kwaɓe fuska, "kai da zaka zauna a kawo maka me yasa ka shigo?"
"I want to know if you need any help?"
"Da farin kayan?"
"Zaki sha mamakin idan nayi miki dishes da shi kuma babu abinda ya taɓa shi"
"Wow" ta amsa tana ɗauko gorunan ruwa a fridge ta juyo zata saka a kan tray ɗin sai ganin shi tayi yayi hanyan fita ɗauke da shi don haka ta bishi a baya riƙe da gorunan, suka sama ma komai wurin zama a saman dining, tana zuba masa abincin yana taya ta saka ma kan shi peppersoup sannan ya zauna ya ɗauki cokali da bismillah sai ya kalli yanda ta saka tagumi da hannunta biyu a saman table din ta zuba mishi idanu.
Murmushi yayi ya kai loman farko baki, ya tauna ɗaya biyu sai ya tsaya yana kallonta.
"Menene? Gishiri yayi yawa ko? Ko yaji? Ko mai?"