Sashe 72
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ni daman na san za'a yi haka Hafsah daman na sani haba! Ba aka ce some-somen hauka zubda yawu ba? Na daɗe da gane nufin su a kan ki, amma ke kin bani mamaki wlh don ban yi tsammanin zaki iya juya min baya cikin sauƙi haka ba, na ɗauka koda an so shiga tsakanin mu sai inda ƙarfin ki ya ƙare"
Ɗago idanunta da sune kaɗai abinda kake iya gani ta cikin niqab ɗin tayi ta dube shi "Da iyaye na kake so in yi faɗa kenan?"
"Iyayen naki ba a kan ɓata suke ba? Ko duk inda suka ja ki kema bin su zaki yi idanu a rufe? An ci moriyar ganga an yada koren ta ko? Hafsah da a shekarun baya ne kin isa ki sake hannu na?" Wannan karon Safina dake zaune a gefen su ne ta ɗago ta dube shi da mamaki, itama rabin fuskar ta rufe yake da takunkumi. Tana da abin faɗa, tana da raddin mayar ma Uncle B dai-dai da tambayar shi yawun ɓatawa ne dai a kan shi ne da bata dashi don haka tayi ƙwafa tana mayar da idanun ta kan wayar ta.
Dukda yayi kaman bai lura da ita ba amma yayi ƙoƙarin sassauta fushin sa da harshen shi tunda ya lura ƴan black stomach ɗin suna da yawa idan ba haka ba ai Safina ma mai tsaya mishi ne tunda ita shaida ce a kan abubuwan da yayi ma Reina tunda suna tare tun tale-tale, amma ya daɗe da lura da itama ba son shi take yi ba.
"Hafsah yanzu kin yi min adalci idan kika min haka?" Ya miƙo hannu zai riƙe hannunta da ta ajiye a kan teburin tayi saurin ɗagawa.
"Ka mayar da Mummyn Mufid baka sanar da ni ba. Kuma...."
"Amma ban haɗa ku har gaisawa kun yi ba?" Ya katse ta kafin ta ƙara a kai.
"Bayan tana da cikin da ta haife shi da safiyar jiya? Ko wata biyu ban yi da sani ba fa Uncle Bilal, da ace Yaya Yaseer bai faɗa mun ba da sai an ɗaura mana aure kawai in je in ganta."
"Anzo wurin" ya murmusa sosai kaman ta faɗa mishi wani abun dariya "daman na san duk inda aka je nan za'a dawo, na san zaki sanar da ni shine ya shirya miki duka wannan, harsashe na a kan shi ba zai zama ƙarya ba, Mutumin da yayi zaman gidan kaso kuma?.
Amma Hafsah nayi miki alƙawarin ba zan mayar da uwar ƴaƴa na bane kokuma nayi miki alƙawarin bayan ke babu ƙari? Shi Yaseer ɗin da zaki aura a yanzu faɗa miki yayi da ke kaɗai zai zauna har karshen rayuwar shi?"
"A'a, amma bai ƙaryata akasin haka don ya ruɗe ni ba." Ta amsa cikin rashin jin daɗin abinda ya faɗa a kan Yaseer bayan yana sane da laifin waye kuma gata nan zaune a gaban shi.
"Saboda ke na yarda na miƙa ragamar rayuwata ma general ko shi idan ya ga daman ƙara min aure dole zan karɓa saboda abinda na amince da shi kenan kafin ya yarda ya nima min auren ki. Shi ya dawo da Afifa ba ni ba. Hafsah idan kika ji dalilin rabuwa na da matar nan zaki yi mamaki, babu abinda ban yi mata ba amma saboda na roƙi alfarmar ta sadaukar min da wani abu da da take ganin yana da muhimmanci ta zaɓi ta haƙura da ni da yara na ta tafi tayi irin rayuwar da take so, ta dubi idona ta faɗa min she doesn't love me anymore, da nayi ƙoƙarin sake bata dama na ƙi rabuwa da ita sai gamu a gaban alƙali saboda tonon asiri. Ban yi niyyan sake zama da ita ba believe me amma yaya zanyi da general Hafsah, bai yarda ya saka an kama Jamal kuma ya cire hannu a kan lamarin Aunty Hauwa ba ya biya maƙudan kuɗaɗen da research Centre ɗinnan suka cini tara ba sai da na yarje mishi, kuma duk saboda ke"
Gani yayi jikinta yayi sanyi cikin ƙwarin guiwar cin nasara ya matso gaba ya ɗaura guiwowin hannun shi a kan teburin sannan ya daɗa sauƙe murya. "Doll ni ke nake so zallan ke ba tare da komai ba. Afifa surkuwan general ce wanda zai nunata ma duniya saboda cimma wata manufar shi a duniyar Daula da siyasa, zama na da ita hoto ne kawai na ruɗan duniya amma kece matata mai ɗaki na, zan sirrinta ki a duniyata babu ruwan general ko Aunty Hauwa ko mummy M ko Ameesha ko Afifa dake domin bata ma san ki ba kuma ba zata sani ba!. ni kaɗai keda ke, zuciyata taki ce doll dan Allah kada ki bari a rusa kyakkyawan tanadin da nayi mana."
Tayi shiru tana jin wani yanayi mara daɗi. Don kyautawa bata kyauta ma Uncle B ba Amma kenan shi yayi biyayya ma mahaifin shi ita zai hana ta yiwa nata?.
Miƙewa Safina tayi tana raɓa jakar ta a kafaɗa "Muje lokaci ya cika" ta wuce gaba kafin Reina ta tsaya ɓata mata lokaci.
Daman da ƙyar ta yarda ta rako ta kuma minti talatin ta yanka mata ba ragi ba ƙari.
Ganin da gaske tafiya zata yi Reina tayi saurin mikewa itama ta ɗagawa Uncle B hannu sannan ta fice ta bar shi a wurin. Ko mata rakiyar idanu bai yi ba domin ya san ba wannan ne haɗuwan su na ƙarshe ba, zai bawa Reina lokaci tayi yadda taso amma da sannu zata shiga hannun sa.
.
.
.
"...Wallahi this should be the first and the last! Reina Wannan ya zamo karo na farko kuma na ƙarshe da zaki saka ni biyo ki wurin wannan tsamin. Idan ba haka ba hmmm"
A cikin adaidaita Safina take sauƙe mata wannan tijaran, matar da take gefen su ta saki baki tana jiran kanun labarai aka ci Sa'a Reina bata tanka ba.
Sai da ta tabbatar Safina ta gama hucewa lokacin har sun yanko layin gidan su ta riƙo hannunta a cikin nata dake cikin safa tace "haba bestie, Mrs YK ne fa kikewa fushi, kin san yaya Yaseer bayi son ana mun faɗa ko?"
Wangalelen murmushi Safina ta saki saida ta saka Reina murmusawa itama tace "ko zamu wuce kasuwa mu cire ashoben ne kawai ya wuce mana?"
"Ki dai yi haƙuri mu zana jarabawan goben babban ƙawar amarya, ko rana ma fa ba'a saka ba" ta amsa tana dariya.
"Idan aka tashi sakawan ma zai fi wata ne ko sati biyu? abinka da masu yi?!"
"Haba-haba sati biyu? Sai kace wanda ake niman kai da ni?"
"Idan dai yaya Yaseer ne niman kan muke". Ta sauƙa lokacin da aka tsaya a ƙofar gidan su ta ciro kuɗin mai napep ta bashi lokacin da Reina ke sauƙowa itama.
Matar nan dai ji tayi da ita ce za'a fara sauƙewa fasawa zata yi sai ta bisu ta ji ƙarshen zancen nan gashi ko fuskar amaryar bata gani ba balle ta san wanene Yaseer ɗin labarin ya ƙara armashi.
Cikin jin daɗi Safina ta riƙo hannun Reina suka shiga ciki tana gwada mata samples na ashobe da tayi screenshot a Instagram.
"Kinga wannan last week aka yi bikin kuma ba karamin kyau yayi ba, sai mu samu muyi tun yana hannun yaran Abuja kafin ayi mai arhan shi a kasuwan kano ya karaɗe garin Bauchi."
Reina dai cire niƙab da hijab ɗinta tayi bayan sun shiga parlo da babu kowa mummyn Safina ta je bikin ƴar ƙawarta, ta miƙe a kujera AC na ratsa ta don babu karya waje akwai rana.
"Ga wani ma ki gani" safina ta zauna a ƙasa a gaban kujeran ta kawo mata wayan fuskarta tana ƙarawa da cewa "kinga ma sai muyi order din shi daga nan, tunda da tsada kuma sai yaya Yaseer ya biya ko?"
Reina ta harare ta "sannu ko? Wahalar min da shi zan bari kuyi ko shi zai saka muku ankon?"
"Wayyoo Inama ace na kunna recording kafin kiyi maganan nan in tura mishi ya ji in ga yaya zaki yi! Amma ko kiran ki yayi haka zaki koma kamar kazan da aka zuba ma ruwan zafi kina simi-simi da murya kamar kyanwa."
Reina ta juya idanu bata ce komai ba Safina taci gaba da scrolling a cikin wayan ta. Can kaman an tsikareta ta juyo ta ɗaka ma Reina duka a cinya sai da ta saki ƙara ta miƙe zaune babu shiri.
"Ke banza albishirin ki!. Ina ranan birthday ɗin ki da muka je sabon restaurant ɗinnan? Kin san waye ya biya mana kuɗin abinci ya siya miki cake da tarukucen abubuwan nan?"
Ba don ta daina jin zafin dukan ba ta gyaɗa kai cikin kaguwa.
"Wallahi Yaya Yaseer ne. Haba na ga na san fuskar amma na rasa a ina? Ashe kuwa ga inda na san shi"
Ta juyo ma Reina fuskar wayanta dake nuna shafin Yaseer na Instagram.
"Ashe tun 2023 nake following ɗin shi amma na daɗe ban ziyarci shafin ba gaskiya kuma shima posting ba a kai-a kai yake yi ba yafi saka story shima na tallen abubuwan su"
Ganin Kallon bayi mata a haka ta karɓi wayan a hannunta tana dubawa ga followers ɗin shi sun doshi million.
Safina ta dawo gefenta ta zauna suna kalla a tare.
"Dan Allah ki kalli mijin da Allah ya darje ya baki, Wallahi Hafsatu Tahir ke mai Sa'a ce ki gode ma Allah ki sake gode masa".
Ita dai hankalin ta yana kan comment ɗin da ƴammata suka mishi a kan wani post na hoton shi da navy blue kaftan yafi shekara ma da ɗaurawa. Ga dubbannin likes comments kuma rabi da kwatan su ƴammata ne sun ajiye kunyar su na ƴaƴa mata suna ta yaba haɗuwan shi wasu harda mishi tallen kan su.
"Wallahi wasu matan dai babu har babun ga" ta nuna ma Safina tana jan tsaki.
Safina tace "baki ga komai ba ma tunda wa'innan a haka suna jin kansu, wani abu sai kin je tiktok"
Ta fito daga wurin kafin zuciyarta ya buga taci gaba da scrolling ga hotunan Aicha kaca-kaca da suka ɗauka a wuraren taro kaman dama shafin na haɗin guiwa ne.