← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 117

Sashe 45

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ni ina page 2 ne ma" ya ɗago ya nuna mata shafin ta gani da idanun ta na biyu ne amma kaman ba a handout ɗin yake ciro tambayoyin ba baki ɗaya.

Ɗan turo baki tayi cike da shagwaɓar da bata san ya zo mata ba, ita dai in zai barta ta tafi ta kwanta shikkenan "toh yayanmu in je in kwanta gobe sai in zo maka da answers ɗin?"

Babu wani tunani zuciyar shi ta amsa tayin ta, idanun shi suka mace a kan abinda bai taɓa ganin yayi wa wata mace kyau ba sai yau.
Idan Aicha tayi kai tsaye yake sanar da ita bayi mata kyau amma yau ƙwaƙwalwar shi ta susuce.

"Ba zaki je ba" bakin shi ya yaudari Sauran sassan jikin shi. "Ki koma ki sake duba abinda nace miki, yau muna nan tare duk dare sai kin cika sharuɗa na kafin in sallame ki".

Kaman zata yi kuka haka ta koma ɗin, ta sake fara karatun daga farko don takaicin shi ya saka ta wartsakewa.

"Amma dan Allah CGPA ɗin ki ya kai nawa? Aicha ta tsomo bakin ta tana dariyar rainin hankali"

Ci kanki Reina bata ce mata ba, ba don bata da raddin mayar mata ba sai domin da gaske take yi da tace babu abinda ya haɗa su, ita yanzu magana ma idan ba ya zamo dole ba tunda ba a kanta take zaune ba ba zata dinga mata ba.
.
.

Table ɗin da ya kifa kan shi ta ƙwanƙwasa tana sake kiran sunan shi. "Yaya Yaseer gashi na gama fah" wato ita ya hana ta rintsawa shi ya kwanta hankali a kwance yana minshari.

Tashi zaune yayi yana murtsuka idanu. "Barci nayi?" Ya tambaya da mamaki sanin babu abinda ya sha.

"Eh mana, har baya na nake jin ciwo saboda gajiya Allah"

"Ina Darling?" Sai da ta ƙara turo baki sannan tace "tun 10:40 ta tafi kuma idon ka biyu lokacin"

Agogon hannun shi ya duba ya waro ido ganin sha biyu har da kusan rabi.

"Tuntuni ɗinnan barci nake yi?"

Eh manan da ya sake zuwa bakinta yayi kalar rashin kunya sai ta gyara shi da "Eh fah"
Ta miƙa mishi handout ɗin yayi ya mata tambayoyi ita ta ƙara gaba.

"Ina sauran?"

"Kullum ɗaya zan dinga yi, zai fi shiga mun"

"Better for you" ya shiga sake karanto mata tambayoyi, aka ci Sa'a ta amsa masu yawa, wasu kuma sai ya canza approach ɗin tambayan kafin ta gane ta bada amsar da ya dace.

Ya jinjina kai cikin gamsuwa sannan ya mayar mata d handout ɗin yana faɗin "Allah ya tashe mu Lafiya"

Ta tattare sauran tarukucen ta tayi mishi sai da safe.

Wannan wartsakewan da yayi da ƙyar ya samu ya sake rintsawa kusan asuba, shima sai da ya saka tunanin lokacin da take shagwaɓar nan a cikin kan shi kafin nutsuwa ta sauƙa mishi, tsananin bugun zuciyar shi ya ragu, idanun shi suka yi nauyi.

Ita kuwa sai 6 ta iya miƙewa tayi sallan asuba shima sai da ran Maama ya ɓaci tana faɗin yanzu kam idan bata tashi ba bazata sake ɗaga ta ba.

Da tayi sallan ma komawa tayi ta ƙara kwanciya kuma Allah ya gani yau ta so ayi shirin abun karyawa da ita, Amma bata farka ba sai 7:28, kafin tayi wanka ta shirya ma har 8 ta gifta.

Haka tazo tayi breakfast a gurguje yau ma Yaseer ya sake bata kuɗi kafin su wuce, bayan sun gama lectures ɗin 11 to 1 suka siya abinci mai Lafiya suka zauna ci. Reina ta shiga bawa Safina labarin daren jiya ita kuwa dariya take yi sosai cike da jin daɗin yanda Yaseer ɗin ya ƙular da Reina kuma yayi kaman bai sani ba.

A hankali da masu ganin saiɓin lokaci da masu ganin saurin ta, Reina ta cika sati guda curr a gidan su Yaseer cikin farin cikin kasancewa kusa da mahaifinta da kuma amincin protection da ta samu yanda take da tabbacin abu mai cutarwa sai dai ƙudira ta Ubangiji ya saka ya riske ta a wannan gida.

Amma fa akwai takurawar yaya Yaseer. Ya kasa ya tsare a kan komai da ya shafe ta, tun su Abbah suna zuba mishi ido har umma ta ƙare tace ya ɗan rage takurawar nan albarkacin idanun mahaifin ta kada yaga kaman iko suke musu don sun taimake su.

Amma shi yana komai ne da zuciyar shi ɗaya, idan bai karfafa ma Reina guiwa ya gogar da zuciyar ta ya tsayar da ita da ƙafafunta ba bai ma ɗauki darasi a kan abinda ya faru a baya ba kenan?.

~~~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

74

~~~~~~~~~~
_J'étais prêt à graver tou image_
_(I was ready to engrave your image)_
_A l'aucre noire sous mes paupieres_
_(With black ink under my eyelids)_
~~~~~~~~~~

Daga Ranar da Reina da Alhaji Tahir suka samu kwanciyar hankali Hajiya Hauwa da Alhaji Salisu suka rasa nasu, duk jigilar da suke yi ko samun ganin Jamal basu yi ba, an ƙi bawa kowa daman ganin shi kasancewar sa high profile criminal, domin cartel ɗin da ake zargin yake aiki a ƙarƙashin su sun yi ƙaurin suna don haka case ɗin ma ba na nan bane headquater za'a tura shi a Abuja.

Duk gidan sun fice a hayyacin su, yaran basu gane komai don haka Zahra ta samu free pass na yawon ta yanda taga dama, Zaheera kuma ita ke raka Hajiya Hauwa fafutukar yanda za'a yi, har south Africa sai da suka je gaida wata matar kawun ƙawar ta wanda take a matsayin kishiyar surkuwar first lady, haka suka dawo babu wani cigaba., ga bala'in Alhaji Salisu dake ɗaura laifin komai ma Hajiya Hauwa tunda ita da ubanta suka saka Jamal ya dawo bayan yayi iya ƙoƙarin shi wajen ɓoye shi na tsawon lokaci a kan kuskuren da suka yi daga farko, ta sake ƙara ma ƙwaben sa ruwa saboda ƙaramin tunani irin nata.

Sun yi ƙoƙarin bin ƙafa ko bada cin hanci abu yaci tura, duk wanda suka nemi taimakon su daga sama kuma sai dai su ce suyi haƙuri amma abun ya fi ƙarfin su, haka ga kuɗin su sun zuba ana ci Amma babu biyan buƙata.

.....

Yau ta kasance asabar, ƙaryan babu makaranta tayi ma Yaseer ta zauna a gida saboda lectures ɗaya kawai suke da shi, kuma a gaskiya ba zata tashi daga nan har gubi a kan lecture ɗaya da sai ka isa ma a iya cancelling ɗin shi ba ko lecturer ya ƙi zuwa.

Kasancewar babu mai fitan wuri a gidan har ta sauƙo kitchen ɗin ƙasa karfe 7:18 babu kowa, kuma bata san mai za'a haɗa na karyawan ba don haka sai kawai ta buɗe fridge ta firfito da kayayyakin da take da tabbacin za'a yi amfani da su, kaman su kayan miya, nama, kifi, sausages da kayan lambu. Ta fitar da minced meat da kaji guda biyu daga freezer ta ajiye su a sink su sake, kana ta shiga wanke kayan miyan tayi blending ta ajiye ta yi dicing onions ta ajiye shima sannan ta koma kan veggies, ta yi yanka mai kyau ma rabin carrot ɗin da ta fito da su bayan ta wanke, kana ta yi grating sauran.

Tana yanka cabbage Mai haƙuri ya shigo. "Ah-ah kece yau a kitchen ɗin?" Yayi maganar fuska ba yabo ba fallasa .

"Da murmushi Reina ta yi mishi barka da safiya, Ya amsa yana duba abinda take yi ɗin ya ɗan jinjina kai sannan ya wuce jikin coffee machine ya kunna ya saka mug a bakin shi ya zauna a ɗan ƙaramin dining ɗin wurin yana jiran ya gama tsiyaya.

Ba'a fi minti biyu ba sai ga Irfan. Ya gaida Sabir Amma kaman bai ga Reina ba ya wuce ya buɗe fridge na biyu ya ɗauki goran ruwa.
"Barka da safiya Autah" tace don bata ga dalilin da zata ce masa ina kwana yana ƙanin bayan ta ba, ko Sabir ma dan girman jiki da tsayin ƙafar shi ya hana ta gane kan su ɗaya ne.

A maimakon ya amsa sai yace "Amma kin san idan kika yi ba dai-dai ba Ummah zata yi mana faɗa ko?"

"Sai ka faɗa mata ni nayi ai kaga ma ni kaɗai zata yi"

Ƙwafa yayi ya karasa jikin kitchen island ɗin yana kallon yanda ta shirya komai yanda cikin ƙanƙanin lokaci zasu fara girkin su gama ga shi yankan da tayi ko a ido yayi kyau.

"Yau fa ba za'a yi amfani da beef ba, chicken peper soup Umma tace a yi" yace yana yatsina fuska a kan naman da take yankawa.

"Sai in mayar da shi freezer ɗin idan na gama yankawa ai bai ɓaci ba, kaga zai fi sauƙin aiki ma gaba."

"Toh darling bata cin cucumber idan aka yi mishi irin wannan yankan"

"Autah ya isa! Ka bar wurin nan" Sabir ya tsawatar masa.

Da ta bar maganan da a wurin zai mutu Amma ba zata iya ba. Sai tace "Ai ba ma ita na yanka ba, bani da lokacin fidda ficen ta, zata iya sake yanka wani ko kuma ta tsine ta ajiye a gefe idan bata ci"

Kama baki Irfan yayi yana kallon ta kaman wanda tayi wani saɓo, "Kutt... Kika zagi darling?"

....

*Yaseer*

Daga fitowan shi daga ɗaki ya haura upstairs domin shan Tea ɗin shi na safiya. Tun da ta dawo gidan kullum yazo wuce ƙofar ɗakin su sai wannan Ranar da suka fara saka idanun su cikin na juna ya dawo mishi, yanzu ma ya san ba zai wuce tana ciki tana bacci ba.

ƙarasawa kitchen ɗin dake saman yayi ya tari tafasasshen ruwa a mug ya saka ƙaramin cokali biyu na zuma sannan ya dawo jikin cabinet ya jawo ɗaya daga cikin drawers ɗin shi ya ciro wani ƙaramin akwati wanda ke ɗauke da kalolin ganyen shayin shi na musamman ya buɗe sai dai mene, wayam ya gani babu komai a ciki.
Chapter 45 · 0% Book details