← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 117

Sashe 69

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Reina ta girgiza kai "Yaya Yaseer bai yi min komai ba Feenah, babu abinda zai taɓa zuwa daga gare shi da ya wuce alkhairi, alkhairin da ban cancanta ba" tayi shiru tana ƙoƙarin daidaita numfashinta sannan ta kalli Safina cikin karyewa "Bai taɓa hantara ta ba balle yayi min gori, babu wulaƙanci ko ƙasƙanci a tsakani na dashi duk da duniya ma ta shaida Abinda nayi masa ba iya mu kaɗai ba Feenah. Yaya Yaseer bai taɓa duban idanu na ya tambaye ni meyasa ba? Bai taɓa faɗa min baƙar magana don ya ji daɗi ba, ga daddy na a gidan su kaman wanda suka fito cikin Umma ɗaya da mahaifin shi, da laluran shi da komai amma ko a fuska ban taɓa ganin sun gwada ƙosawa a kan lamarin shi ba.
Ni kuma Feenah ke shaida ce, ke shaida ce a kan irin rayuwar da nayi a gidan Yayan mahaifina jinin shi na shekaru ɗaɗɗaya har bakwai amma ko na rana ɗaya ban taɓa jin daɗin zaman gidan nan ba kafin zuwan Uncle Bilal, ko abinci wannan da zasu bani in ci in ƙoshi ƙyashin sa suke ji. Masu aikin gidan sun fini daraja da ƙima a idanun su, haka na koma baiwar su, boyi-boyin yaran su don kawai in ɗan samu su sarara min, gyaran ɗakin Zahra kyautan ɗan abinda na mallaka ma Zaheera babu wanda ban yi ba amma basu ɗauki nauyin sutura ta ba balle ilimi, harta jami'a da kika ga nake zuwa tare da ke Daddy ya faɗa min yaya Yaseer ne yake biya min, kuɗin transport, handouts, da komai shi yake yi mun tun kafin Allah ya sake haɗa fuskokin mu."

Mamaki ya saka Safina sakin hannun Reina ɗaya ta kai nata hannun baki ta riƙe.

"Yess Feenah bayan duk abinda nayi mishi. Bayan na kalli cikin idanun shi nayi mishi ƙazafi, bayan Daddy na ya wulakanta shi ya wulaƙanta iyayen shi. Yanzu kuma Saboda bani da kunya bani da ta ido saboda Allah ya saaka mishi, ya ɗauƙaka shi kuma sai in shiga inuwar rayuwan da ya tattala ya inganta da gumin shi? Duniya ai sai ta yi min tofin ala tsine."

"La haula wala ƙuwwata illa billa" shine Abinda Safina ta samu ya fito daga bakinta don itama ƙiris ya rage ta shiga taya ta kukan amma ta sani ba shi Reina take buƙata daga wurinta ba a halin yanzu.

"Shigowar Uncle Bilal rayuwata ma ya kawo mun sauyi masu yawa. Ya taimaka min da ikon shi da aljihun shi dukda wasu abun Umman Zahra sun danne amma ya taimake ni a lokacin da nake tsananin bukatar taimako. Ya kula da lafiya ta ba tare da na taɓa biyan shi sisin kwabo ba. Don haka auren shi shine abu mafi ƙaranci da zan iya mishi shi kuma yaya Yaseer ya je ya samu wanda ta fini komai ya aura ya cancanci hakan, soyayyar shi mai sanyin zafin da ba'a samun irin shi nan kusa yayi ma wanda ta cancanta"

"Hmm" Safina ta sauƙe numfashi, ta kawar da kai tana share dan kwallar da ya fara sauƙo mata kana tace "Ni abinda ban fahimta ba a nan Uncle Bilal dama yayi miki wannan ne duk don ki biya shi?"

Sai tayi dariyan da yafi kuka ciwo tana sauƙe ajiyan zuciya. "Ni ɗin a darajar nawa nake da har aure na zai biya shi?"

"Haka kika ɗauki kan ki ko haka yake gwada miki?. Ko zaki iya faɗa min menene baki da shi? Asali? Addini? Ilimi? Kyau? Ko mutuncin ki kika zubar a titi ba tare da sani na ba?. Idan duka wa'innan sun cika me yasa zaki sauƙe farashi?"

"Nayi mishi rantsuwa da alƙawarin zan aure ahi Feenah "

"Sai ki faro azumin kaffara daga gobe. Sai me kuma?"

Babban damuwan ta bai wuce yanda Uncle B zai ɗauki abun ba idan ta sanar da shi Yaseer ta zaɓa a kan shi. Amma ta sani Safinah ba ganewa zata yi ba sai tace
"Ko da ace ban dace da yaya Yaseer ba na ƙi auren shi idan ban auri uncle Bilal ɗin ba sai waye nake da shi? Menene aibun auren nashi tunda yana so na? Na san na fi ƙarfin ci da sha harda sutura a ƙarƙashin sa"

Tagumi Safina ta saka yanzun nan ta gama bata tausayi har zata koma bata haushi. "Sai kuma aka ce miki ci da sha da sutura sune kawai matsalar aure idan an kawar da su babu sauran matsala? Idan haka ne meyasa ake samun rashin daidaito a gidajen masu rufin asiri da masu wadata? Ai da sun fi kowa zaman lafiya"

Ta shiga nazarin kalaman Safina tunowa da Abinda ya raba Auntyn ta da daddyn ta kaman yanda ta karanta, ita ce, ƴar cikin ta. Ina ga Uncle B mai wasu yaran? Mai wata matar? Mai hali daban da na daddyn ta?.

Ta kalli Safinan da idanun roƙo ta daina ƙara mata firgici don already tsoron tafiyar da yake gaban ta ya fara shigan ta. musamman ma da a yanzu yaya Yaseer yake haska mata hanya ta hango gargadan da yake cikin ta wanda ko ido a bude ta bi kai sai ta fuskanci ƙalubale balle ita da take da niyyar tafiyan ido a rufe.

Fahimtar ma'anar kallon ya saka Safina cewa "ba hana ki auren Bilal zan yi ba ko ince sai kin auri yaya Yaseer dole amma wanda ya soka da alkhairi a lokacin da yake ƙin ka baka da haufi a kan alkhairin soyayyar shi. Amma ki ƙara tunani Reina, ina miki fatan alkhairi"

Da haka ta jawo ɗaya daga cikin handouts ɗin ta shiga karantawa don ta san kafiyan Reina, idan ta biye mata zasu wuni tana kawo hujjojin da zai saka taji a karan kanta Abinda ta yanke shine dai-dai tunda ita mutum ne mara ɗaukan shawara komai kyan ta sai ta fahimci Allah guda ɗaya yake tukunna.

Sun ɗan taɓa karatun kuma har Reina ta tashi barin gidan basu sake sako zancen ba, suna yin la'asar tayi ma mummyn Safina sallama zata tafi, Safina kuma ta nemi izinin mata rakiya suka fita daga gidan.

Takawa suke yi zuwa babban titi saboda iwar haka zirga-zirgan abun hawa da sauƙi a layin.

"Kin san mahaifi na ya ji zafin Abinda kike mun lokacin da muke primary? gashi babu yanda ya iya koda cire ni a makarantar ne saboda yana tsoron ɓacin ran Alhaji Tahir. Mummy ma ta ƙullace ki a lokacin sosai idan kika ga ta bari na ji suna musanyar yawu a tsakanin su toh a dalilin ki ne saboda mummy tace bata haifo miki jaka da zaki dinga duka kinawa ƙwace ba Daddy kuma yace hanyar samun abincin sa yake tsoro mu ƙara haƙuri zai wuce"

Reina ta ja ta tsaya jin basu taɓa magana makamancin wannan ba Amma ganin Safinan ta wuce ta cigaba da tafiya ya saka itama ta cigaba da takawa yanayin nadama da yanzu take yawan shiga yana zuwa ya lulluɓe ta.

"Kuma ya wuce ɗin, kin rasa gatan ki mahaifi na kuma ya rasa aikin sa bayan faɗuwar TK kingdom. Mahaifin Aicha shi ya ɗago daddy na saboda alaƙar da Allah ya ƙulla a tsakanin mu, don tausayin ki nake ji kuma da kika fara komawa mai kirki sai na fara jin ki a raina. Ya ɗauke shi ya bashi aiki don kawai ki samu kulawa ta wani wurin ko yaya ne, Mummy ta fara maraba da ke har tana bada irin abinda take bani in kai miki . Amma yaya Yaseer shi ya zo har gidan nan ya durƙusa ya nema miki yafiyan su a kan laifin da bayi da hannu a aikatawan da kika yi, kuma yace nima a bani haƙuri, in taimaka in zauna tare da ke kada in rabu da ke koda kin ɓata mun" sai a lokacin ta tsaya da tafiya ta juyo ta dube ta, ga masu adaidaita har sun fara rage gudu don su saka musu hannu su tsayar dasu su ɗauke su amma ba ta su Reina take ba tukun.

"Saboda su biyu alaƙar mu ta kai har yanzu Reina, domin da iyaye na sun daɗe da datse shi da yanzu babu Safina a rayuwar ki don haka ina roƙon ki a matsayin aminiyar ki tun yarinta don Allah Reina kada sakarcin ki ya saka nayi dana sanin kasancewa da ke. Ki yi ƙokari wannan ya zamo karo na ƙarshe da zaki kawo min kukan ki, kema kiyi farin ciki in samu hankali na ya kwanta"

Safina ta saka hannu tsayar da wani empty napep sannan ta faɗa mishi unguwan da ze kai Reina ta biya shi.

"Allah ya kiyaye, sai mun haɗu a school jibi" tace tana ɗaga mata hannu da murmushi har suka bar wurin.

Ita kam ta shiga uku, Safina ƙara ɗaure ta da jijiyoyin ta tayi. Tayi zuru tana kallon hanya don ta rasa wani irin tunani zata yi, ta faɗawa mai napep adireshin gidan Ummi ya juya da ita yace mata zata ƙaro kuɗi tace babu matsala don ji tayi ba zata iya komawa gidan su yaseer ba.

Gidan Ummi dai ya dawo busy tun Ranar da suka yi ma Reina aikin souvenir da Yaseer ya bata ɗinnan shikkenan orders suke shigo musu wasu daga su yaseer ɗinne wasu kuma daga mutanen da suka yaba da aikin su a dalilin sa.

Dalilin haka mata da yawa dake taɓa wa Ummi da ƙanwar ta aikin da suka raba a tsakanin su ma sun samu hanyar samu ba zallan su ɗin ba. Ummi ita take yin hidiman su kaji da su abinci ita kuma kanwar ta tana hidiman gashe-gashe da soye-soye.

Damuwa gami da sakalci suka saka ta kwanciyar a cinyar Ummin ta rufe idanu tana jan numfashi a hankali. Sai Ummi ta zame ɗankwalin ta don ta duba ko tana da buƙatar kitso ko wankin kai ayi mata kafin ta tafi Amma kanta a wanke a kitse yake tass, har gida Wanda take zuwa tayi ma Umma da Aicha take yi mata har da Maama ma idan tana nan.

Ummi tayi murmushi tana ƙara yiwa Yaseer da mahaifan shi addu'a ta shiga shafa mata kan a hankali.

Can har Ummi tayi tsammanin ta fara barci ta ji ta kira ta "Ummi"
Chapter 69 · 0% Book details