← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 117

Sashe 15

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suka zauna aka shiga bubbuɗe gifts ana gani, yawanci daga wanda aka ɓaro musu manyan wayoyi da laptop sai masu wasu kayan kuɗin.
Itama kwalin da baba ya bata waya ne a ciki, ba wata mai tsada bace amma tayi murna sosai, yau ɗinnan zata sake gwada kiran wannan numbern.
A Tsawon shekaru biyar ba zata iya ƙirga sau nawa ta kira ba, ta saci wayan Zahra, Zaheera, hajiya Hauwa, har wayan Alhaji Salisu ta taɓa sata ta kira, kuma a duk lokacin ta taje gidan Ummi haka zata wuni ta kwana tana trying, su kuwa basu gajiya da sanar da ita cewa yana kashe.

Bata gama murnar ba Safina ta miƙo mata wasu gifts din.
"Gashi inji mummy da Daddy" sai tayi saurin yage wrapping ɗin ƙaramin kwalin ta fiddo da sabon iPhone 12 pro max ta haɗa da kwalin nata wanda suke iri ɗaya sakk, ga sim anyi musu register da komai.
"Kinga anyi mana ankooo" ta jijjiga jiki cikin jin daɗi, ita kuwa Reina mamaki ne ya kama ta, ta karɓi wayan duka biyu a hannunta tana kallo baki sake.

"Feenah kuma ma ni suka ce ki bayar?"

Ta harareta "idan baki so bani na haɗa"

"Allah Sarki Feenah mai yasa ke da iyayen ki kuke sona bayan abinda na dinga miki a baya? Feenah na gode" tana hawaye amma dariya take yi. Kullum Safina tayi mata wani abu taji daɗi sai ta maimaita mata wannan maganar ita har ta gaji da ji.

Saboda tana matse a socket ɗin ajin ta saka cajin nata wayan na wurin baban Safina, ta bawa Safina ta ajiye mata na wurin kakanta, suka cigaba da duba sauran kayayyakin.
Ɗayan kwalin kuma Saudi abaya ce mai kyau mai tsada a kwalin ta.

Wasu daga cikin mazan ajin su ma sun kawo musu gifts ita da Safina kuma anyi rabon chocolate da kayan zaƙi masu yawa har cake Reina ta cishi kaman ba gobe Ranan, basu ankara ba sai ji suka yi ana kiran sallan la'asar.

Suna dawowa daga masallaci tazo ta kunna wayar don yanzu an fara zuwa ɗaukan sauran yaran sai hayaniyar bankwana ake yi. Bata damu da hakan ba tunda ta san layin ba tafiya zai yi ba ta rubuta numbobin da garin hadda har tabo suka yi mata a ƙwaƙwalwa, ta ƙara a kunnen ta tana jiran taji 'the number you're trying to call is kindly switched off' amma a maimakon muryar computer sai ƙaran ringing ya shiga kunnen ta.

Tayi saurin ɗago wayar ta duba ko tayi kuskure wurin saka numbern ne, amma kuma ko daga barci ta tashi aka ce ta maimaita sau ɗari zata iya.
Numfashin ta bai ɗauke ba saida taga an ɗauki kiran ya fara reading. Mayar dashi tayi jikin kunnenta ta furta "Hello" da sanyin murya, tunanin hayaniyan ƴan class ɗin ya hana ta jin muryar wanda ta kira ya saka ta mikewa ta fita a guje kada kiran ya tsinke.

Numfashi ta sauƙe ganin har yanzu call ɗin yana reading ta mayar kunnen ta tayi sallama amma ba amsa.

"Hello" ta furta ba amsa.

"Hello" ta ƙara kaman zata fashe da kuka still ba amsa kuma kiran bai katse ba.

Tana tsoron ta katse ta sake kira kuma ko network ne ta jishi a kashe.

"Yaya Yaseer?"

Iska mai ɗan ƙarfi ya shiga kaɗawa a wurin, ganyen bishiyoyi suna kaɗawa suna bada sautin shuu amma babu komai daga cikin wayar.

"Yaya Yaseer!" Ta sake ambata sannan ta durƙusa a wurin ta shiga rera kuka har saida Safina ta ƙaraso wurin ta sameta.

"Reina Lafiya?" Ta tambaya cike da damuwa ta ƙaraso ta tsuguna a gabanta tana ƙoƙarin ɗago kanta amma kuka take yi kaman Allah ne ya aiko ta don haka Safina ta ƙwace wayar sai dai kafin ta kai kunnen ta tayi magana an kashe.

Da ƙyar Safina ta samu ta rarrashe ta, duk yanda tayi kuma ta biyosu su sauƙe ta a gida taƙi, haka ta haɗa mata kayan ta a jaka ta shiga napep ya kaita gidan Uncle Salisu, a yanayin da take ciki gwamma taje wurin da babu wanda ya damu da damuwar ta don bata da amsar bawa su Ummi idan suka dameta, ta biya da ɗari biyun jikin bouquet ɗinta da suka zauna suka warware, duk yanda Safina tayi da ita ta karɓi na dollars ɗin taƙi, ita yanda zata samo canjin su ma shine aiki.

Zahra ta fara haɗuwa da ita a parlourn, tana ganinta ta saki murmushi. Reina bata gama tunanin wani bala'in ta jefa kanta a ciki ba taji sauƙar bulala a gadon bayan ta. Taurin rai har yanzu saidai abinda ya ƙaru amma dake a kusa take sai ta saki kukan azaban jiki da na zuciya. Hajiya Hauwa bata barta ba saida ta tabbatar tayi mata irin dukan da tayi niyya Sannan ta shiga karanto mata laifukan ta wanda ko kalma ɗaya bata ji ba.

Ta wuwuro jakar bayanta ta zazzage kayan ciki a ƙasa nan kwalin abayan nan ya faɗo tare da waya. Zahra tayi kan abayan da gudu ta ɗaga tana dubawa "wallahi ita ta sata kuwa, ki gani har ta kashe"

Bata bi ta kan Zahra ba ta rarrafa wurin Hajiya Hauwa dake riƙe da wayan tana jujjuyawa. "Wallahi Daddyn Safina ne ya siya mana ni da ita, idan baki yarda ba ma a kira shi wallahi, dan Allah kiyi haƙuri ki bani Umman Zahra"

Hankaɗeta tayi ta faɗi ta juya da wayar da kwalin shi a hannun ta Reina ta sake rarrafawa ta riƙi ƙafar ta. "Dan girman Allah ko zallan sim ɗin ki cire ki bani na roƙe ki"

Ta kashe mata gargaɗin dukan da tayi mata ba komai bane idan bata sake ta ba sannan tayi gaba ta barta a wurin ta ƙaraci kukan ta Zahra kuma ta shiga ɗaki gwada abayar ko zai yi mata.
.
.
Tana kwance magashiyyan ta ƙura ma ceiling idanu Zaheera ta turo ɗakin da yanzu Reina kaɗai ke kwana a ciki Zaheera an bata sabon ɗaki nata na kanta. Jakar makarantar Reina da ta tattaro ta ajiye mata kana ta zauna a bakin gadon "Reina kizo muyi dinner"

"Bani jin yunwa." Ta amsa can ƙasan maƙoshi ta juya mata baya.

"Toh ga waya na ki karɓa sai ince Abbah ya siya min wani"

"Bani s..." Sai tayi saurin juyowa ta karɓi wayan, iPhone 11 ne shima ance sai tayi candy za'a siya mata iPhone 16 gashi wai har Reina ta rigata riƙe iPhone 12 koda na kwana ɗaya ne kuwa, shiyasa yanzu tazo ta bata sauran ta.

Numbern ɗazu tayi saurin jerawa ta danna kira ta ƙara a kunne zuciyar ta yana bugu da yaƙinin yanzu ma zai yi ringing kuma za'a ɗaga. Muryar computer na shiga kunnenta ta katse ta wulla ma Zaheera wayar ta "Bani so" ta juya ta cigaba da kwanciyar ta, har Zaheera ta ƙarashe iyayinta ta bar mata ɗakin kafin ta tashi taje ta saka ma ƙofar lock ta dawo.

Jakar ta buɗe, babu abayar shima sun rabata dashi. Chocolate ɗin ciki ma an ɗiba wasu an bar mata ƙanana, ta duba kuɗin da ta saka a ƙaramin zip shima babu. Sunyi ma kansu ƙananun mutane kawai, taja tsaki sannan ta dauko diaryn Aunty da har ya koɗe tsaban karantawa, tayi bitan shi dungu to dungu har ta haddace wasu wuraren, babu abinda yafi burgeta a ciki kamar soyayyar Aunty da daddy, yana ɗebe mata kewa sosai.

~~~~~~~
Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

52

'komai ya fara ne da safiyar wata Juma'a, na sauƙa daga bus ɗin makaranta a GRA kasancewar akwai bikin wasu ƴan uwan Ummi a ranar, sai dai wani lecturer ya saka mana test shiyasa na fara zuwa na rubuta tukunna. Ɗaga kaina nayi na kalli hadirin dake sama, an sheƙa ruwa ɗazu kuma da alamu wani ma yana kan hanyar zuwa don har an fara yayyafi.
Na buɗe leman hannu na a kai na, na gyara zaman jakar baya na ga logbook ɗin da na karɓo ma Aunty Zeenat ya hana shi rufuwa ina tafiya sai kallo na ɗaiɗaikun mutane dake wurin suke yi.

A hankali nake tafiya kaina a ƙasa ina ƙoƙarin tuna ko na rubuta abun arziƙi a test ɗin ɗazun, lokacin da moticin sa suka fito daga gidan gwamnati suka zo wucewa, suka samu nasarar watsa min ruwan dake kwance a kan titin a jikin kaya na mai kyau na ado duk da ba gudu suke surfawa ba. Ihu na saki domin sun shammace ni gashi nutsuwa ta bayi jiki na, na ƙanƙame hannun leman nan tamau kaman wani ke niman ƙwace min.

Har sun yi nisa idanu na suna musu rakiya sai naga sun tsaya, kafin a hankali motocin guda biyu suka fara reverse har inda nake tsaye. Ganin kaman fitowa na cikin motar zasu yi tsoro ya saka nayi saurin ɗaga kafa na zan bar wurin.

"Baiwar Allah" ƙaddara ta ya kira ni.

Kwarjinin dake cikin muryar ya saka ni juyowa ba tare da na shirya ba.

"Hafsatu na kinji yanda Allah ya fara haɗa fuska ta da na Mahaifin ki." '

Reina ta karanta layin karshen a bayyane yanda zai shiga kunnen ta kana ta saki dariya. "Kai Labarin soyayya akwai daɗi"

Ta buɗe shafin gaba duk da cewa zata iya kawo abinda ya faru a wurin da kayi.

'Juyowa nayi na dube shi, babba ne domin daga gani ya girmi babban yayan mu. Yace "kiyi haƙuri Please" Idanun shi a kan ruwan da ya jika ƙasan kayan jiki na.

"Ba...ba komai, kayi haƙuri dan Allah" meyasa na bashi haƙuri bayan ni aka yiwa ba daidai ba.

Sai ya saki murmushi duk da yasan yana yiwa mutane kwarjini amma yasan wannan yarinyar matsoraciya ce don jiki na da muryata rawa suke yi a lokacin abinka da introvert.

"To bari na bada kuɗin wanki ko"
Chapter 15 · 0% Book details