Sashe 98
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Aiki zaki yi mun na tsawon sati guda. Ma'ana zaki ajiye aikin ki da YK & Co ki dawo Bold group a ƙarƙashi na, kinga kenan dole zaki yi abinda nace a lokacin da nace, idan kin yarda zan karɓi 5% har zuwa lokacin da zaku daidaita al'amura sai mu koma normal ko yaya kika ce?"
Ta ja dogon numfashi kawai tana bin shi da ido, yayi nasarar goge duk wani tunani a cikin kanta bayan mamakin shi da ya cigaba da zaunar da ita a wurin.
Anya wannan mutumin ba ɗan iska bane?.
"Zan ɗauki shirun ki a matsayin amincewa, so idan kun shirya ko yanzu sai muje a fitar da takardar yarjejeniya in saka hannu"
Albarkacin Yaseer, albarkacin ɗumbin ma'aikatan dake ƙarƙashin YK & Co. Sannan ta sani ma Yaseer ba zai yarda ba, tunda ba gidan ubanta bane a Abuja kuma duk inda zasu je da sunan aiki tsayawa yake yi a kan lamuran ta har sai sun koma ya miƙa ta a hannun iyayenta cikin ƙoshin lafiya, don haka babu yanda za'a yi su koma Bauchi su barta dukda ma ta ga yazo har da Reina a tafiyan kwana biyu kawai.
"Shikkenan, muje" tace tana ƙoƙarin miƙewa tare da ɗaukan jakar ta.
"Nine shugaban har kin manta? Nine zan dinga bada umarnin kuma nace ki zauna ki cinye abincin gaban ki tukunna"
Sai gashi ta share tsawon lokaci fiye da awa guda har da rabi a ɓangaren Rafeeq domin saida ta jira shi yayi shirin office suka fito a tare amma duk cikin gidan babu mai tunanin sakawa a je a dubo ta, koma su turo yara suyi musu leƙen asiri.
"Toh Jadda na gode zan tafi" tace tana ɗan rage tsayinta.
miƙo mata hannu tayi daga inda take zaune, Aicha da ta fahimci me take nufi ta taka ta kama hannun tana zama a space din gefenta, daman jiran fitowar ta Jadda take yi tuntuni kuma ita ta hana kowa zuwa dubo su.
"A'a keda na ɗauka kuma kin zo kenan?"
Asal ta murmusa tace "banda abinki Jadda a ina kika taɓa ganin amarya ta..." Kallon da Rafeeq ya watsa mata ya saka ta haɗiye sauran kalaman 'kawo kanta ɗaki' dake bakin ta.
"Toh gidajen da nace za'a shiga da ita su gaisa fah? Iye Rafeek?" Ta mayar da dubanta gare shi.
"Nayi lattin office Jadda" shine amsar shi a gare ta.
Aicha ta dafa hannun jadda dake riƙe da nata ɗaya tana ƙara sake fuska don ta samu tsohuwar ta rabu da ita tace "Jadda zan dawo, In sha Allah"
Da ƙyar ta samu ta baro gidan da niƙi-niƙin laida zuwa wurin da tayi parking ɗin motar ta.
Driver ya buɗe ma Rafeeq gidan baya ya shiga shi da sandar shi, motar su ta fara gaba tana biye da su har wurin da suka yi meeting jiya bayan ta kira ta sanar da Yaseer yanda suka yi ya tabbatar mata da zasu riske shi a can.
.......
Tana zaune a gaban screen ɗin laptop ɗin shi dake bayyana fuskar doctor Fahad ta ɗaya ɓangaren, Yaseer ya ƙaraso yana ɗaura necktie "Umry I have to go" yace yana sunkuyawa ya sumbace ta a goshi, ta mayar da dubanta gare shi yanda yake shiri cikin gaggawa tayi ƙokarin miƙewa domin ta taimaka mishi tunda minti 30 ɗin da suka ɗauka har ya kusan cika amma ya dakatar da ita ya saka takalmin shi ya fita riƙe da rigan suit ɗin shi a hannu.
Ya riga su Aicha isowa tunda ya fisu kusa da wurin, kuma ya sani dama zata iya daidata komai don bayi da ko kwana ɗaya da zai iya ƙarawa a Abuja, shiyasa yake fatan komai ya tafi mishi a yanda ya tsara yana addu'an Allah yasa kada a samu tangarɗa ta kowace hanya.
Takardar yarjejeniya aka buga babu ɓata lokaci Yaseer da Rafeeq suka saka hannu a yanda aka bukata kana suka miƙe suka yi musabiha kaman yanda yake a al'adar yarjejeniya.
Rafeeq na sakin hannun Yaseer kuma ya miƙa ma Aicha.
Ta kalle shi ta kalli hannun dake jiran kusancin nata sai kuma ta dubi Yaseer tana jiran ya bawa Rafeeq uzuri ya karɓa mata gaisuwan kaman yanda yake yi koda yaushe kuma a ko ina idan hakan ta faru don ita daga farko ta so tana bayarwa shi ya hana ta.
Amma sai taga Yaseer ɗin kaman bai gani ba ma, hankalin shi yana kan wayan da yake rubuta text.
Hannunta ta daga ta manna a kirji sannan ta dan sauƙe idanu alamun girmamawa amma ko da ta ɗago bai ɗauke hannun shi ba.
"Bani shaking hannu da maza, Sorry"
"I need to feel your sincerity kafin mu fara aiki tare, ko har kin sake mantawa? Har yanzu naga dama zan iya janyewa"
Itama ganin hannun ta kawai tayi a cikin nashi, bai jijjiga ba sai ya ɗan matsa taushin hannun na shigan shi, babbar yatsan shi yana yawo a bayan hannunta hakan yasa tayi saurin janyewa saboda bata son baƙon yanayin da take ji, ta shiga nanata istigfari a ƙasan maƙoshi tunda sun riga sun yi.
Mayar da wayan shi aljihun suit ɗin shi Yaseer yayi sannan ya maido da hankalin shi gare su yana faɗin "So ni da daddare jirgin mu zai ɗaga zuwa Turkey, I'll leave her in your care" sannan ya juyo wurin Aicha da bakinta ya kusan taɓa ƙasa saboda kaɗuwa. "Make sure kina kiran gida a kai a kai, kada ki bari su shiga damuwar rashin ji daga gare ki"
Daga haka sai gani tayi bayi cikin meeting room ɗin, bata ma san lokacin da ya fita ba.
"An bar ki da dodo ko?" Rafeeq ya tambaye ta sai ta dawo da duban shi gare ta hawaye na kwanciya a idanun ta. Da gaske yanzu kam babu sauran hope a tsakanin ta da Yaseer tunda har zai iya tafiya ya barta ƴa mace budurwa da namijin da babu abinda ya haɗa su bayan hidima ta cinikayya kuma yayi tafiyar sa ba tare da damuwan komai ba.
"Trust me Darling, you're safe with me"
"Darling? A ina yasan sunan ta darling?"
.....
*Reina*
A yau ta ɗau aniyar gane inda matsalar take, idan ma Yaseer gajiya yayi da ita ko wani abun ne daban. Domin ganin Zahra a cikin yanayin da ta ganta ya saka ta daɗa godewa Allah da irin ni'imar da yayi mata, ya karrama ta ya haɗa ta da abokin rayuwa na gari, saboda haka zata ajiye kunya da tsoro ta fuskanci Yaseer idan har hakan shi zai zamo musu maslaha da sai gani sai hange da suka dawo yi a tsakanin su.
Zauna take a bakin gadon suna video call da Safina. "...ƴar rainin hankali sai dai in ji labarin tafiya ba sallama, har kin fara juya min baya kenan?"
Reina tayi fari da idanu "ba fushi kike ba? Kin huce kenan."
"Hmm" Safina tayi ƙwafa "ai ba'a taɓa min yaudara irin wannan ba Amma babu komai, gwamma ma da na daina guje-guje ya gane ba tsoron shi nake yi ba"
"Toh daman wa yace kina tsoron shi? Ko tsarguwa?"
Share zancen tayi tana tambayar "Yanzu daga Abuja sai ina? Yaya Suhail yace mun wai honeymoon zaku bazama har Umrah zaku bi kafin ku dawo, Allahu Akbar Reina Allah yayi kira"
Ba don abinda ta sanar da ita yayi shocking ɗinta ba da tsokanarta zata yi jin cewa a bakin Suhail ta ji zancen tafiyan.
"Feenah da gaske?"
Ta rufe baki da hannunta "kar dai na ɓata ma yaya Yaseer surprise ɗin shi? Toh gaskiya yaya Suhail ne ya fallasa ba ni ba tunda ban ce ya faɗa min ba balle ki ji."
Haka suka ƙarasa wayan rabin hankalin Reina na ga abinda Safina ta sanar da ita, daga ƙarshe suka yi sallama ta tura mata hotunan abincin da suka ci da daren jiya, gabaki ɗaya ɗoki ya cikata ita kaɗai sai tayi ta murmushi, kuma ba zata gwada ma yaya Yaseer ta sani ba zata tsaya ne taga gudun ruwan shi.
Kuma ta gani ɗin, ruwan ya bi hanyar da bata taɓa tsammani ba domin a yammacin ranar sai gashi suna shiri jirgin su zai ɗaga nan da ƴan awanni.
9:30pm
Hannun shi riƙe da nata suka shiga jirgi har suite ɗin su dake First class. Bayan addu'a, hira, ci da sha, kallo da kuma barci tafiyan awanni shida ya sauƙe su a Ankara Esenboga airport, Garin Ankara Babban birnin ƙasar Turkiyya.
Lokacin har Masallatai sun riga da sun fito daga Sallah don haka suke wuce hotel ɗin da yayi booking musu, ya jasu Sallah.
Tana gama azhkar ɗinta na safiya ta miƙe a wurin domin ta cika sauran barcinta, ta bar Yaseer yana karatun Alqur'ani.
Ɗago ta yayi ya kwantar da kanta bisa cinyar shi har saida ya gama sannan ya ɗauke ta ya kwantar a kan gado shima ya bita ya rufa musu duvet.
Ƙarfe 10:02 sautin muryar shi yana magana ƙasa-ƙasa ya tashe ta, ta buɗe ido a hankali suka shiga cikin nashi dake zaune a can ƙuryar katafaren ɗakin hotel ɗin yana amsa waya idanun shi a kanta.
Ya sake mata murmushin da ya ƙawata annurin fuskar shi, ga wani kyau da yayi mata na musamman cikin farin wando da baƙin button up shirt yayi stocking, maɓallan wuyan rigan a buɗe abinda ke ɗaukan hankalinta a duk lokacin tayi arba da shi yana mata Hi ta karaso ta kwanta a jikin shi. Ya fito kaman wani black American.
Miƙewa tayi ta zauna da kyau tana ɗaga idanunta daga ƙirjin shi ta mayar fuskar shi. Ko minti ɗaya bai ƙara ba yayi Sallama da wanda yake ɗaya ɓangaren sannan ya miƙe ya tunkaro ta. "Good morning sweetheart"
"Morning bae" ta mayar masa tana ɗan dafa gaban kanta da taji ya riƙe mata.
"Lafiya?" Ya tambaya yana zama a gefenta ya ɗaura nashi hannun a goshinta sai kuma ya sauƙo da shi wuyanta domin ya ji ko jikinta akwai zazzaɓi amma noƙewan da tayi harda saurin matsawa daga jikin shi ya bashi mamaki.