Sashe 82
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sun sake waya da yaya Yaseer bayan dare ya fara rabawa amma kaman yanda ya faɗa mata ne bayan ta bashi hakuri, ya haƙura, don haka bai sake ɗago zancen ba koda suke magana.
Tambayar ta dai yayi ko akwai abinda take buƙata a karan kanta tunda su Safina dai ya haɗa su da Muhammad duk abinda ke akwai ta same shi. Ta amsa mishi da babu don kafin ta buƙaci komai ake mata.
Ya dai cigaba da mata tambayoyi ɗaya bayan ɗaya a kan abubuwa ko akwai abinda ta manta tana dai amsa shi da eh ko A'a gabaki ɗaya jikinta babu karsashi.
"Yaya Yaseer yanzu baka jin wani iri?" Ta kare dai ta tambaye shi.
Yayi wani irin murmushi mai taushi a cikin kunnenta sannan yace "wani iri kaman yaya sarauniyar zuciya ta?"
"Wallahi ina jina ne kaman ba ni ba, kaman mafarki nake yi, wai nine gobe zan zamo matar aure! Ya rabbi."
Ya sake murmusawa don tun farkon wayan su ya so harbo jirginta amma sai yayi tunanin ko abinda ya faru ɗazu ne ya dame ta shiyasa yayi ta janta da hira don ta fahimci shi ya wuce a wurin shi, ashe dai bai kuskure ba fargaban ce.
"Nima haka nake ji Umry, amma farin ciki da ɗoki duk ya shanye su. kema ki kwantar da hankali ki babu wani abu a ciki, just rayuwa zamu yi kaman na can gida amma wannan akwai extra ƙauna da soyayya a ciki, shine kawai"
Ta yi ƙokarin kwantar da hankalin ta bayan ya faɗa mata hakan sai gashi sun yi Sallama tun 11 amma ƙarfe biyu yayi mata idanun ta a buɗe. Sai ta ɗan taɓa waya ta kalli hotunan da akayi mata jiya da yau tabi ta ajiye taci gaba da juyi amma idanunta a soye kaman gyaɗa. Daga karshe ne taga asaran zai yi mata yawa ta tashi ta ɗauro alwala tayi nafila ta ɗauko qur'ani a cikin side drawer tana karantawa har sai da taji idanun ta sun fara nauyi sannan ta ajiye, sai kuma ta rasa wani kalan addu'a zata yi, mai zata roƙi Allah a game da aurenta da Yaseer?.
Sai tabi bakin mutane ta roƙa musu zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba, kuma Allah yasa wata rana ya yafe musu abinda suka mishi ita da daddynta. A kan darduman barci yayi awon gaba da ita wuraren karfe 4, da aka kira asuba aka tashe ta tayi sallah shine ta koma gado yanzu kuma Aunty Sajida ta sake tashin ta.
Lokacin da ta dawo daga tunanin, Aunty Sajida bata tsaye a kanta don haka ta sake komawa ta kwanta zata cigaba da barcin ta.
"Mu je na haɗa miki ruwan, na ƙaramin bokitin ne mai turaruka, kiyi ki fito in shirya ki in koma bakin murhu in same su"
Sai gashi har taran ta wuce bata samu shiryawan ba Saboda shirirta har masu girki suka gama kayan su suka shigo suyi wanka suma, Aunty Sajida tana ta fama da Reina wai naman da aka bata da bauri.
"Ba dole yayi bauri ba tunda na magani ne?"
"Toh ke kici mana?" Tace da abokiyar wasanta tana watsa mata harara.
"Nawa daban ai, wannan na Yaseer ne. Na ɗauka yanda kike ɗokin nan ma sai kin buƙaci ƙari"
Ita bata san mai ya saka suka saka ta a gaba ba ko kuma so suke yi ta ƙunsu a ɗaki tayi ta ƙunci saboda za'a yi mata aure, auren ma da yaya Yaseer?.
Haka suka saka ta a gaba da maganganu, wanda zata iya tankawa ta tanka wanda yafi ƙarfinta tace musu hmm, har ta saka undies ɗinta aunty Sajida ta gyara mata fuska kafin safina ta ƙaraso da laidan rigan Reina wanda tayi ƙanin kwana tana gyara bead work ɗin jiki wai wanda aka yi daga farkon bai yi musu kyau ba aka karɓa aka yi kabbasan shi da VIP kabbasa set na Bakhoor by Seemah sannan aka taya ta sakawa. su kuma baƙi Ɗaya bayan ɗaya suka dinga tashi suna wanka su shirya su dawo.
Rigan jikinta ta ɗaga ana ɗaura mata zani matar ɗazu ta sake cewa. "Yanzu bayan bikin shi Yaseer ɗin ne zai dinga ɗaura miki zani Aunty na tunda baki iya ba?"
"Ya ɗaura min zani kuma? Yayan nawa? Mai kuka ɗauke shi?"
"Tohh?? uhmm." ta taɓe baki kana tace "wanduna kenan zaki yi ta saka mishi ki ɗame yayi ta kallon cinyoyin? Kinga zani kam bayi da amfani idan haka ne."
"Nifa kunga ya ishe ku. Bawan Allah mumini uztazi kuna ta mishi sharri, idan Allah ya tsayar da ku ranar ƙiyama kuyi bayani ni babu ruwana"
"Ƙarewar ta ma limamin makka ya haihu balle local ustaz ɗin ki" wata daban ta amshe zancen. "Ko ba zaku haihu bane da yaya Yaseer din kin?"
Lokaci daya jikinta yayi sanyi don ita ta cire wannan a cikin lissafin ta. Ko ajin malama da take zuwa da wa'azuzzukan da take ji ɗaukan wannan part ɗin take yi kacokam ta ajiye shi a gefe don ba zata iya harsaso ita da yaya Yaseer ta haɗa su da wannan yanayin ba samm. Amma kuma yaya zancen haihuwa kuma? Tunda ta san dai ba a ruwa ake sha ba, kuma zata so ta haifa ma yaya Yaseer yara masu yawa masu kama da shi da ita.
Taɓdijam.
Aunty Zeenat tace "kinga, idan wasan yaya da ƙanwa zaku je yi ki faɗa min sauran mintuna 30 za'a iya dakatar da abin nan. Sai kici gaba da zama a ƙanwar shi kuyi wasan da tushe, idan ba haka ba kuma zuwa wata shekara iwar haka muke son dawowa sunan ƴan biyu ko uku"
Ta kalli Aunty Zeenat a karo na farko bakinta yayi nauyi da fitar da amsar da taso bayarwa. Suka samu nasarar rufe bakinta ta nutsu musu suka ƙarasa shirya ta.
Ana cikin ɗaura mata ɗankwali ƙanwar Ummi ta shigo da guɗa Ayyiriri "Alhamdulillah An Daura!"
Ƙirjin Reina ya doka dumm.
"Shikkenan kin zama ɗauko riga, kin zama ɗauko hula kin zama matar Yaseer."
Ta sunkuyar da kai sai ga ƙwalla mai sanyi yana bin idanunta ɗaya. Shikkenan ta zama matar Yaseer, Ta maimaita abinda suke faɗa a cikin zuciyarta.
Yanzu jiki, zuciya da ruhinta duka nashi ne.
Aunty Aina da itama shigowarta kenan ta dubeta "wai kuka kike yi a maimakon tsalle da murna? Mu bamu son munafurci"
......
*Yaseer*
Ko gonar auduga ya gan shi zai jinjina ma murmushin da yake yi yayin da jama'a ke miƙa masa hannu suna taya shi murnar cikan burin shi. Ganin yanda mutane suka yi dafififi saboda shi ga mutanen shi daga ƙasashe da dama sun riƙe zumunci.
Aka shiga ɗaukan hotuna ana ta gyara zaman babban riga, da ba zai ce ga iya yawan mutanen da suka shiga aka ɗauka da su ba. Wasu ma bai san su ba, wasu kuma an yi shekara da shekaru rabon shi da ganin su.
Hotunan da Suhail yayi mishi a wayan shi ya ɗan samu sararin ɗaurawa a shafukan shi na sada zumunta domin ya shaida ma duniya ya zama mijin aure.
_"Alhamdulillah… after all the storms, I found my calm in her smile.
Reina ta zama tawa, Hafsatu ta zama uwargida na.
Duniya, ku shaida, na samu wadda zuciyata ta daɗe tana jira."_ ... Shine caption ɗin shi na Instagram feed.
Ya shiga X (Twitter) wanda bayi saka wani abu personal a can musamman da Aicha tayi mishi shirme wancan lokacin sai ya daɗa janye jiki da shi amma a yau da hannun shi ya rubuta musu.
_"Alhamdulillahi rabbil alameen. Finally na samu abinda zuciyata ta daɗe tana nema.
My crown, my comfort, my Hafsatu Reina
The only one. She's now Mrs Yaseer 💍"_
Jawo shi da Muhammad ya zo yayi ya hana shi ziyartan sauran shafukan don yau alƙawari ne ya ɗauka sai duniya ta shaida irin farin cikin da yake ciki.
Ana gamawa da nan aka wuce grand reception da ya haɗa daga nan kuma aka wuce gidan su amarya don ya saka matar shi a idanu.
Suna shiga gidan mata suka kicime da guɗa, bai san cewa akwai wani sirrin daɗi a cikin guda ga wanda ake masa ba sai yau. Ya luma hannu cikin aljihun shi da bai yarda ya shigo da su babu nauyi ba ya fara fito da abinda yake ciki.
Miƙawa kawai yake yi, duk inda ya tsuguna gaisuwa sai ya ajiye yara ma saida suka samu rabon su don yana bukatar addu'ar su suma, kana aka musu iso parlon baba inda zai gana da amaryar shi a ɗauke su hotuna.
He has always been a confident person amma yau dai gashi he's almost anxious, ɗan jiran mintuna 10 zuwa 15 da suka yi kafin ta samu fitowa sai yake ji yayi masa tsayi sosai.
Idanun shi a kan ƙofa lokacin da aunty Aina ta shigo da guɗan ta sannan Aunty Zeenat dake riƙe da hannun Matar shi kanta a lulluɓe tana takawa a sannu biye da ƴammatan amarya cikin ankon su wanda yayi mamakin ganin su Zahra da Zaheera da shi amma ba ta su yake ba.
Kusa shi aka ƙaraso da ita kafin Aunty Zeenat ta fara kiciniyar cire hannun Reina da take jin yanda yayi sanyi yana karkarwa daga nata, Amma haka ta rike ta gamm da ƙyar ta samu ta fincike ta koma gefe.
"Assalamu alaikum Matata" yace cikin ƙasa da murya daidai kunnenta.
"Ango banda fuskar amaryar ne za'a ɗauka?" Cewar mai hoto.
Sai yayi taku ɗaya ya tsaya a gabanta ya saka hannu da bismillah sannan ya ɗaga mayafin daga fuskarta ta gyara mata zaman shi a kanta, duk yanda yaso su haɗa ido a yayin haka kuwa ta ƙi.