Sashe 101
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Idan ta faɗa miki maganan da ba zaki iya amsawa da komai bayan Toh ba ki bani in amsa miki ko Umairah ta?" Ya ƙarashe yana sakin dariya, wani irin sakayau yake jin shi, wannan abu da yake jin ya tokare mishi maƙoshi na shekaru goma a hankali yake jin yana sauƙa tun daren da ya shigo gidan shi yaci karo da Reina a bakin ƙofa a matsayin wacce zata taya shi rayuwa a cikin ta har ƙarshen lokaci.
Amma yau yana jin kaman an ɗauke kaso mai girma a cikinsa lokaci guda.
"Magana ta ƙare tunda kaima ka kama Umairan, sai ka taimaka musu ka yanka min rago ayi suna"
Bai fasa murmushi ba ya ajiye bowl ɗin hannun shi a saman ƙaramin table dake gefen shi Sannan ya mike ya koma bakin gadon yana jawo ta jikin shi ya rungume kana ya raɗa mata wani abu a cikin kunne ya ɗago suka yi ido huɗu ya ɗora da "shiyasa".
Bakin da ta hangame tana kallon shi ya sunkuya ya haɗe da nashi, ta lumshe idanu tana amsar yanayin da take mafarkin tsaye a zahiri. Amma ta sani ba zai tsaya a nata mafarkin kawai ba, sai sun zarce zuwa nashi da yake da girma da falala amma sabo da wuya. domin a wancan daren zata iya cewa suma yayi mata Rana don sai safiyar yau ta fahimci ainihin mai take ciki.
Surrender tayi ta miƙa wuya, domin alhaki ne wuyanta ta cika alƙawarin ƙauna.
.....
*Aicha*
Brush tayi da wanka ta fito tayi Sallan Maghriba sannan ta koma ta kwanta abinta zuwa lokacin Isha ya shiga idan tayi sai ta fita niman Abinda zata ci.
Muhammad ta kira suka tattauna a kan progress na aikin da suka ɗukufa a kai wanda da Bold group sun janye tabbas zasu samu babban tsaiko idan ma aikin bai wargaje gaba ɗaya ba, sai take jin tayi daidai da ta amince da sharaɗin Rafeeq amma hakan ba shi zai saka yayi ta juya ta kaman waina a tandu ba.
Ta ji kaman ta kira Yaseer ta fasa tunda shi da yayi mata sanadin shiga wannan halin bai ji kaman ya ɗaga waya ya kira ta yaji yaya take ba tunda yana tare da Reina matar so.
Wait! Ita da ta amince da hakan kuma mai yasa tun yanzu yake damunta?. Har zata iya ganin laifin Yaseer a kan abinda take ganin yayi mata ba daidai ba?.
Ƙarfe 8 yayi mata a kan darduma ta idar da Sallan isha tana addu'a.
Ta gama subhanallah da alhamdulillah kowanne 33 tana cikin yin Allahu Akbar wayan ta ya shiga ringing. Ko bata duba ba ta san Rafeeq ne amma don ya san zuwa ne ba zata yi ba sai ta jawo wayan tayi rejecting kiran ta cigaba da addu'an ta.
Har ta miƙe bai sake kira ba, amma gabaki ɗaya hankalin ta yana kan wayan domin ta so ya sake kira ta sake rejecting. ta miƙe zuwa inda ta jere kayanta tana duba abinda zata saka ta fita restaurant ɗin cikin hotel ɗin tayi dinner ta sake dawowa ɗaki.
Farin shirt ta cire a jikin hanger ta saka ta haɗe maɓallan ta ɗaura mishi maroon Palazzo, babu hula a kanta ta dauki plain veil maroon tana ruɓa bakin shi yanda zai rufe mata gaban kanta da kyau lokacin da wayanta yayi ƙaran shigowan saƙo.
'I'm coming up' shine abinda message ɗin yace. Agogo kuma na gwada lokaci ƙarfe 8 da rabi dai-dai.
"Coming up ina?" Ta tambayi kanta a bayyane, sai ta ajiye gyalen hannunta ta ɗauki wayan tana danna kiran numbern shi shima yaƙi ɗauka har kiran ya katse ta sake mayar da wani a take.
Saƙon shi ne ya shigo bayan kira na biyu ya tsinke 'ki buɗe mun ƙofa' sai ga knocking guda biyu a jikin ƙofar ɗakin da take.
Gwalalo idanu tayi tana ƙara rikicewa, yaya akayi ya san numbern ɗakin ta? Kaman ta ɗaga waya ta kira daddynta ko Yaseer amma kafin su kai ga riskan ta cutarwan dake bakin ƙofar ta ya fisu kusa.
Idan ta kira police kuma suka zo aka tada hargitsi a hotel mutuncin ta ne zai zube a matsayin ta na ƴa mace da ta kama ɗakin hotel take zama ba tare da muharrami ba.
Idea ne ya faɗo mata ta shiga dube-dube a ɗakin tana niman abinda zata iya amfani da shi a matsayin makami wajen kare kanta. Idanunta suka sauƙa a kan wani glass flower holder dake kan centre table, ta cire flowers ɗin dake ciki ta ruga toilet ta zubar da ruwan sannan ta dawo jikin kofar da take jin ana sake ƙwanƙwasawa.
Har ta murɗa zata buɗe sai kuma ta tuna kanta a buɗe yake ta koma ta ɗauki gyalen ta yafa.
Kaman mara gaskiya ta buɗe ƙofan a hankali ta leƙa idanunta suka sauƙa a kan shi.
"Muje" yace da ita ba yabo ba fallasa.
"Ina?" Ta tambaya tana kiciniyar gyara mayafin da ya zame daga kanta zuwa kafaɗunta da hannu ɗaya saboda ɗaya hannun na riƙe da abun rotse kai dake ɓoye a bayan ta.
"Idan muka je zaki gani" yace yana ɗauke idanun shi daga baƙin gashin kanta wuluk mai santsi dake tufke cikin farin scrunchie.
"Toh bari na ɗauko waya na" tace tana garƙame ƙofan ta koma ciki tana sauƙe numfashi. Ita yanzu koda ace attack ya kawo mata ta san ba iya rotse shi zata yi ba tunda ƙarfin ba ɗaya ba. Kuma ma ba ciki zai shigo ba don haka dole ta canza plan.
Sama-sama ta yane gyalen a kanta sannan ta ɗauko farin designer side bag ɗinta ta mayar da atm cards ɗinta da ID ta saka wayanta a ciki ta saka takalmi sannan ta fita da niyyan ba zata dawo ɗakin ba domin saitan hanya zata yi ta gudu, sauran kayayyakin ta dake ciki kuma ta haƙura da su tunda basu kai darajar rayuwa da mutuncin ta ba.
Ta buɗe ƙofar ta fito a ɗarare sai ya taso daga jinginen da yake a jikin garu yana danna waya ya kalleta daga sama har ƙasa.
"Na san dai nace kiyi kwalliya kiyi kyau, Amma zan ajiye request ɗin zuwa gaba for now mu tafi" ya juya ya fara takawa ta bi bayan shi don bata son su jera a samu wanda suka san shi suyi mata mummunan fahimta.
Kaman ta tambaye shi ina sandan ɗazun amma luguden da zuciyanta yake ciki yafi ƙarfin haka. Motar shi aka kawo mishi mashigar hotel ɗin, parking valet ya miƙa mishi keys ɗin ya gaishe su yayi gaba. Rafeeq ya riƙo hannunta ya buɗe mata seat ɗin gaba ya saka ta ya mayar da kofa ya rufe kaman ya harsaso niyyan ta.
Sai taga ya zaga ya shiga seat ɗin driver yayi ma mota key. Zai iya driving shine ya barta ta tuƙa shi ɗazu? Bata gama tunani ba sai gani tayi sun bar haraban hotel ɗin.
Tunanin yanda zata yi ta bar garin idan ta samu damar escaping ya saka ta ciro wayan ta daga jaka ta karkata tana duba Flight ɗin da zai tashi daga Abuja zuwa Bauchi koma Niamey don gwamma taje inda samunta zai yi mishi wuya.
Juyowan da zai yi ya dubeta ya hango reflection ɗin abinda take yi ta window sai yayi murmushi kafin yace "Mahaifiyata ƴar Sarkin Agadez ce, kuma a halin yanzu tana auren Sarkin Damagaram So samun ki a Niger sai yafi mun sauƙi"
Ta tsaya da abinda take yi, tana kallon Flight ɗin Niamey da tayi booking wanda zai tashi ƙarfe 12 na dare domin na bauchi sai gobe da safe.
Kallon mamakin da ta bishi da shi ya saka yayi mata nuni da window ɗin ɓangaren ta. Ta juya taga ashe da ma juyo mishi da fuskar wayan tayi da yafi mata sauƙi.
Sauƙe wayan tayi cikin ta na kara ɗura ruwa tace "ban san wani irin kallo kake mun ba amma ka sani ni ba mutuniyar banza bace"
Ya furzar da numfashi "Na sani, shiyasa na zaɓe ki"
"Sannan kayi min abinda bai dace ba mahaifina ba zai barka ba"
Parking yayi a gaban wani coffee house. Sannan ya dube ta "Idan nayi miki abinda bai dace ba na yarda ki kai ƙara na wurin shi ya ɗauki mataki." Ya sake mata murmushi yana ɗaukan manilla envelope a kan dashboard ya buɗe ƙofa ya fita ya zago ya buɗe mata.
Sai da ta gansu suna duba takardun office bayan sun ci sun sha tukunna taji kaman tayi ta dungurin kanta, garin yaya zata kawo wancan tunanin kanta ita da take aiki da workaholic da babu komai a cikin kan sa bayan aiki.
A ɓangaren Rafeeq kuma dinner date yaso fito da ita, tunda ba isasshen lokaci yake da shi a hannun shi ba ya kamata yayi aiki da sati ɗayan nan ya bayyana mata ra'ayin shi a kanta idan ya samu hankalin ta ya kwanta da shi akwai yiwuwar ta san matsayin shi a gare ta, ta san da igiyoyin shi guda uku a kanta wanda yake da niyyan riƙe su da kyau har zuwa lokacin da mutuwa zata raba su.
Amma ya ɓige da sauya sheƙa Tunda waswasi ya fara kama ta, kuma takardun ma sun kasance a wurin ne saboda bai daɗe da karɓan su ba, kuma bayi da niyyan fara aiki a kan su sai satin gaba amma sai ga su har ƙarfe 10:30 suna ƙoƙarin gamawa da ƙididdigan su, Sauran turawa department na gaba da zasu yi aiki a kan shi.
"Aysh. Mu huta haka nan" yace yana kallon biron da ta soka a jikin kunnenta ta cikin gyalenta ga nashi ta karɓa tana rubutu da shi. Kan teburin yayi kaca-kaca da takardun da ta yage ta kudundune saboda lissafin da ta fara a kansu bai ɓulle mata ba.
Itama ta gaji daman amma kunyan sake fuskantar shi ya saka ta cigaba saboda kada ta lura da wucewar lokaci har su gama su tashi ya maida ta.
"Okay" ta ajiye pen ɗin hannunta amma ta manta da na kunnenta don haka ya miƙa hannu zai cire mata tayi saurin ja da baya tana kallon shi.