← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 117

Sashe 90

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alaji Abdou ya ajiye cokalin hannun shi yana kallon ƙwallan dake kwance a idanun Mariama da mamaki, dawowan shi kenan daga tafiyar da yayi tun bayan da ya bada auren Reina a hannun ƙanin Kamal daga jama'are wanda yayi wa Yaseer waliyyi daga can kuma ya wuce ya bada na Aicha duka a ranan. Ya tsaya yayi hidiman kasuwancin shi kafin ya juyo saboda ya sani amsar hukuncin da ya yanke zai yi ma mutane da yawa wahala, shiyasa ya dan bari su huce tukunna amma a iya zaman shi da Mariama fiye da shekaru 15 bata taba tsare shi da magana a lokacin da zai ci abinci ba, koma menene zata jira sai ya gama tukunna amma yau gashi ta fara a kan ƴar da bata tsuguna ta haifa ba.

Mariama takan kwatanta fahimta da bin bayan daidai a kan komai amma banda abinda ya shafi Aicha, ta saba mata da komai take so sai ta samu, kuma ba yau ta fara tauye nata yaran ba a kan Aicha kaman ba duka shine ubansu ba, shiyasa yaga akwai bukatar ya ɗauki mataki da gaggawa kuma ba tare da sanin ta ba, saboda tana daga cikin mutanen da suke ganin kaman har yanzu Yaseer zai iya auren Aicha shiyasa bata ɗaga hankali a kan auren shi da Reina ba.

Tabbas zai iya tunda mijin mace huɗu ne kuma yana da halin riƙe su, amma kuma shi ba zai iya sadaukar da ƴar shi a kan son zuciyarta ba. Tunda har Yaseer ya iya fitowa ya nuna bayi ra'ayin ta gwamma taje inda za'a nuna mata soyayya da kulawar da take buƙata.

"To yaya kike so na yi? In zuba mata ido ta lalace Saboda shirmen banza?"

"Lallacewa? Daddy menene abun lallacewa a nan? Ko yanzu soyayya ya zamo laifi a wurin ka?"

"Ƙwarai kuwa tsananta soyayyar wanda bayi jinka a ran shi laifi ne" yace yana sake daukan cokalin shi ya cika ya kai baki ko idan taga ya riga ya fara zata rabu da shi amma sai ta cigaba da cewa.

"Rayuwar ta ce fa a cikin garari amma hankalin ka kwance, shekaru ashirin da uku kawai amma ta san menene hawan jini. Kuma da ka dawo ko zuwa dubata a asibiti baka yi ba balle ka tausaya mata Daddy, ƴar ka ce fa na cikin ka, ƴarka ta farko a duniya"

Zuwa lokacin da ta dasa aya hawaye na sintiri a kan fuskar ta, ya haɗiye loman abincin bakin shi.

Ya haɗe yatsun shi a ƙasan haɓar shi yana kallon ta na tsawon mintunan da ya ɗauketa ta share hawayen ta daidaita kanta kana ya kira sunan ta "Mariama"

ta sauƙar da idanunta ƙasa bata iya amsawa ba kuma. Ya cigaba da cewa "Hafsatu Umarnin auren Yaseer na bata kuma bata tsaya ko tunani ba kai tsaye ta amince, kafin nan ma ni na yanke hukuncin a haɗa auren saboda zai zamo maslaha ga ƙalubalen da dukka ɓangarorin suke niman fuskanta ba wai soyayya na duba ba, kuma iyayen su suka bani wuƙa da nama in yi yanda nake so saboda suna ganin na isa. Sai a kan ƴar ciki na ne kuma ke da ita zaku gwada min ban isa ba?"

Ta sake sunne kai nauyi da kunya yana daɗa lulluɓeta. Shiru ya ratsa wurin babu wanda ya motsa babu wanda yace komai har sai da ta laluɓo kalmar haƙuri ta ɗaura a kan harshen ta ta furta mishi.

"Babu komai, ki dai sani ba zan cutar da Aicha ba kuma ba zan bari a cutar min da ita ba, kiyi mata addu'an Allah yasa zaɓin da nayi mata ya zamo mata alkhairi, kuma na gode da irin kulawar da kike bata da sauran yaran mu.
ki sani kina da babban matsayi a cikin zuciyata Mariama, ke alheri ce a rayuwata ina matuƙar ƙaunar ki"

Murmushi ne ya suɓuce mata ta ɗago ta dube shi shima murmushin ne a kan fuskar shi yace "Toh yanzu zan iya cin abinci na tunda ina jin yunwa?"

Gyaɗa kai tayi tana daɗa tura mishi sauran abubuwan da ta haɗa mishi, sai can tace "Amma zamu bari sai ta samu lafiya kafin a sanar da ita ko? Kada wani abu ya sake samunta"

Ya kai kofin ruwa mai sanyi baki ya kurɓa ya ajiye kana ya amsa da "babu matsala, nafi so ma sai mun gama da shari'ar masu kuɗin nan don ana buƙatar ta a yunƙurin tseratar da YK & Co, yarinyar kin mai ƙwazo ce ai." Ta sake sakin murmushi tana tsiyaya masa ruwa a cikin kofin da ya riga ya shanye rabi.

"Allah ya basu zaman lafiya, yasa gidan farin ciki da kwanciyar hankali ne"

"Ameen Mariama ta" ya amsa suna sakewa juna murmushi kaman sabon Aure kafin ya sauya akalar hiran tasu yana tambayar lafiyar ta da sauran yara ƴammata guda biyu da suke rayuwa dasu a Nigeria tunda sauran makaratan kwana suke zuwa a Niger shiyasa koda suka san wannan zuwan mai dogon zango ne suka bar su a can saidai idan an yi hutu suke zuwa.
ta amsa da lafiya lau sun wuce makaranta.

~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

102

Washegari

10:38am.

Ganin yanda ta tsura ma takardan ido ya riƙo hannunta cikin nashi, a hankali ta juyo ta dube shi da wani yanayi mai nisa a cikin idanunta, Abinda take tsoro kenan, wannan shine dalilin tambayoyin da take ma kanta kafin ta auri Yaseer, ɗaya daga cikin manyan dalilan da yasa take ganin basu dace da juna ba, kuma bata ishe shi jin daɗin rayuwa ba. Duk yanda tayi yunkurin danne halin da take ciki ta ɓoye rauninta ta gwada son kanta ta hanyar rayuwa kaman kowacce mace mai cikakkiyar daraja tabon cutarwan da aka yi mata ya gagara barinta.

"Umry.. I'm here" yace yana matsa hannunta dake cikin nashi ya tallafo fuskarta da ɗayan. "Ina tare da ke, we'll go through this together okay?, idan kuma baki shirya ba sai mu tafi mu dawo wani lokacin."

Haƙuri take so ta bashi amma kalmar yayi mata nauyi a kan harshe, amfanin mene kalmar zata yi masa a halin yanzu?

"Mu tafi?" Ya sake tambayan ta.

Girgiza kai tayi tana sauƙe numfashi kana ta janye fuskarta daga riƙon shi ta mayar da jikinta ta jingina da nashi ta lumshe idanunta. Gyara mata zaman yayi ya zaga da hannun shi daya ta bayanta ya riƙe ta da kyau yana gyara mata zaman mayafin mint green abaya dake jikinta.

Can kaman an tsikareta ta mike bayan mintocin da basu wuce biyu ba ta ɗauki pountain pen da ya ajiye mata ta fara cika form ɗin da doctor Fahad ya bayar, Ya ɗauke ta kaman minti 15 zuwa ashirin kafin ta samu ta gama Hannunta a ƙirji na Yaseer a bayanta cikin sigar ƙarfafa guiwa.

Kiran doctor Fahad Yaseer yayi sai gashi ya turo nurse ta zo ta ɗauka, ta sanar da shi zasu jira kaɗan kafin Dr ya kira su ciki. Tana gama bayani ta wuce don hankalin shi yana ga matar shi dukda kunnuwan shi sun jiyo masa abinda tace.

Ta sake mayar da idanunta ta rufe tana ajiyan zuciya bayan nurse ɗin ta fita. Ga wayan shi dake silent sai vibration yake yi, ya ciro daga aljihun wandon shi da niyyan ya saka shi a DND sai kuma ya ga saƙo ne mai muhimmanci daga Muhammad bayan missed calls biyu da ya ajiye mishi bai ɗauka ba, don haka ya shiga typing reply da hannu ɗaya bayan ya karanta.

Sun ɗauki lokaci a haka har ya fara tunanin ko barci Reina tayi kafin nurse ɗin ta dawo tace zasu iya shiga consulting room ɗin, sai yaga ta miƙe kafin ya tashe ta.

Ya ɗauki baƙin jakar ta da laidan maganin da aka basu bayan an yi mata allurar da taƙi jiya sannan suka shiga.

Ɗakin yafi kama da office ɗin wani ma'aikata a kan ɗakin duba marasa lafiya, sai dai yana da haske sosai ga manyan shukoki da ake iya ajiyan su a cikin gida ana kula dasu, sai kuma paintings da aka lanƙaya su suka ƙawata bangon ɗakin.
Dogon kujeran da majinyaci zai miƙe ya amsa tambayoyin likita dake a tsakiyan ɗakin shine kawai zai fahimtar da kai ainihin abinda ake yi a cikin ta.

Kujeran zaman mutum biyu Dr Fahad ya fara basu suka zauna, ya sake tambayan Reina yanda take jin jikinta ta amsa da sauƙi sannan ya fara karanto mata wasu daga cikin amsoshin da ta tanadar a kan takardan da ya bata ɗazu.

Da ƙwarin guiwar da ta tattaro ta gyaɗa kai don tabbatar da kowanne. Sai ya ajiye mata wani takardan daban, a kan table mai ruwan ƙasa dake gaban su, ta ɗaga ta duba amma babu komai a jiki, plain sheet ne.

Ganin kallon rashin fahimta da take masa yace "Labarin Abinda ya faru zaki rubuta min. Duk abinda zaki iya tunawa kada ki bar komai daga ciki"

Sai ta juyo ta dubi Yaseer, "ko zamu je mu dawo ne?" Ta tambaye ta hannunta cikin nashi. Shi ba gaggawa yake yi ba, zai jira.

Girgiza kai tayi "zan ƙoƙarta" ta amsa domin idan suka je suka dawo ɗin ma abinda aka yi yau shi za'a maimaita.

Dr Fahad ya miƙe, "zamu baki wuri idan kin gama zan dawo" sannan ya dubi Yaseer "Yallaɓai ko zan iya ganinka a ofishi na?"

Fita suka yi suka barta ita kaɗai da takarda a gabanta. Dr Fahad ya tura ƙofan office ɗin da aka rubuta sunan shi da golden ink ya shiga kafin yayi ma Yaseer iso suka samu wuri suka zauna suna fuskantar juna.

"Ai ban ɗauka wuri na zaka kawo ta ba"

Yaseer ya jingina bayan shi a jikin kujeran yana ɗaura ƙafar shi ɗaya bisa ɗaya "Saboda meyasa?"

"Saboda overtaking kayi ma siriki na"

Ya ɗan yi murmushin gefen baki don har ya manta da wani Bilal tunda ya samu duniya ta shaida Hafsatu da zama tashi. "I thought kun yi rantsuwan zaku kare lafiyan kowanni majinyaci ba tare da bambanci ba, so ni wurin likitan da na yarda da ƙwarewar shi na kawo matata"
Chapter 90 · 0% Book details