Sashe 86
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bata da niyyar tanka masa don haka ta miƙe tana naɗe darduman da tayi sallah a kai. Ya bita da kallo har ta wuce ta je adanawa a yanda ya kamata. Ya samu barci isasshe amma sai da dare ya raba yana yaƙi da zuciyar shi kafin ya samu ta haƙura daga ƙarshe, tunda dai abinda take muradin tana tare da ita yanzu jira kadan kawai zata ƙara, don zai fi son sai Reina ta ɗan sake da shi kafin ya gabatar da kan shi cikin rayuwar ta.
Ganin ya miƙe daga kan darduman shi tayi saurin ƙarasawa ta ɗaga mishi zata ninke. Ya saka hannu ya karba sannan ya jawota jikin shi ya rungume ta a karo na biyu,yana sauƙe boyayyen ajiyar zuciya. ya ji daɗi da yaji ta saka hannu ta zagaye shi a wannan karon.
"Mu koma gado?" Ya tambaya a cikin kunnenta wanda taji maganan har a saman fatar ta. Sai tayi ƙokarin zare kanta daga jikin shi.
Ta girgiza kai tayi "ya ishe ni, wanka zan yi"
"Okay, ki shirya sai mu zaga in nuna miki gidan ki, amma ki sani ana biyan tourist guide kuma ni bani karɓan kuɗi"
Hannu ta naɗe a kirji tace "Da me ake biyan ka kenan?"
"Sai na gama aikin na auna zan sanar da ke" ya amsa idanun shi a kan lips ɗinta.
Ta kare bakin da bayan hannunta "Ka barshi kawai Nagode, zan zaga da kaina"
"Ai daman ba tambayar ki nake ba Umry, sanar da ke nake yi" ya riƙe hannun da take ganin shine zai yi mata kariya ya jawo ta dashi tana ji tana gani ya sake pecking ɗinta. "Yanzu na amshi down payment dole kinga in cika aiki na"
.....
Mariama da Umma ne suka riƙo ta suka fito da Aicha daga ɗakin zuwa mota zasu wuce da ita asibiti jin yanda zazzaɓi ya gama rufeta ga jikinta yayi zafi rauu ga amai da ta kwana tana yi kuma daman babu abin arziƙi a cikinta, duk ta gama galabaita tayi yaushi kaman lawashi. "Auta ɗauko min purse ɗina a sama, sai kace ma mai haƙuri shi da Maama su kai abincin gidan yayanmu"
Sai da ya fara miƙa saƙon ma Sabir dake haɗa abun kari shi da Maama da Suhail sai wasu daga cikin baƙin jama'are dake taya su, kafin yaje ya ɗauko purse ɗin Umman ya shiga gaban mota tare da driver a tafi asibitin da shi.
Suna zuwa aka yi admitting ɗinta aka shiga bata taimakon allurori da drip, sai a lokacin ta samu ta rintsa na dole saboda alluran barci da suka yi mata gashi ana batun jininta yana niman hawa.
Cike da tausayawa Mariama take kallon yanda take sauƙe numfashi a wahalce tana ayyana zafin irin abinda take ji a ranta tunda itama kusan hakan ne ya faru da ita, tana da masoyin ta a rana ɗaya aka rabata da shi aka aura mata mijin yayarta ba tare da an yi shawara da ita ko an bari ta shirya ba. Kuma babu yanda ta iya haka ta haƙura ta zauna tunda ba iya saɓa umarnin iyayenta zata yi ba.
Abinda yafi mata ciwo a nan shine yanda Abdou ya maimaita wannan tarihin a kan ƴar cikin sa. Bai yi duba da irin halin da take ciki tun kafin a sanar da ita ba, yanzu kuma ita yake so ta dubi Aicha ta sanar da ita an ɗaura mata aure kwana biyu da suka wuce da mijin da bata san ko wanene ba.
Gaskiya ba zata iya ba, zata bari duk inda yaje ya dawo yazo yayi mata bayani da kan shi.
.
.
*Yaseer*
Shigowa yayi yana zuba ƙamshi kaman ko yaushe shirye cikin wani yadin maza ruwan madara, ta dakata daga saka ɗan kunnen da take yi tana checking ɗinsa out.
Ya sake mata murmushi tare da kanne mata ido ɗaya "kin yi kyau ƴammata na" yace yana ƙarasowa ya tsaya a bayanta yana kallonta ta cikin madubin. "Ina son irin wannan ɗaurin" yace yana shafa bakin push back ɗin da tayi ta bawa bakin gashin dake kwance a goshinta damar fitowa.
Murmushi tayi tunawa da ɗaurin Zahra buhari ne koyaushe a kan Aicha. "To zaka ɓata min ai" tace tana riƙo hannun shi da take jin yana mata kaman tafiyan tsutsa a goshi.
"Daman ba ma ni aka yi ba?" Ya sunkuya ya daidaita kan shi da nata suna kallon juna a cikin madubin.
"Mun dace da juna sosai, We're a match made in heaven Umry, kowa ya gani ya sani domin Yaseer aka halicce ki" ta saki murmushin jin daɗin kalamin sa.
Shi ya karɓi ɗan kunnen ya saka mata da ƙyar don gani yake yi kaman sakawan da zafi, tunda gashi rami ne a jikin mutum ake saka masa ƙarfe.
Hannun shi da ya samu promotion daga riƙe nata hannun zuwa kunkumin ta suka fito ƙaramin parlon ta mai ɗauke da ɗakuna biyu. Yana haɗe da madaidaicin kitchen da store, daga dining area kuma akwai ƙofar da zai shigar da kai ɓangaren Yaseer kai tsaye wanda ke haɗe da ɗakuna biyu shima amma sun fi na ɓangarenta girma, sai gym da study Room.
Tsarin study room ɗin kusan ɗaya da na gidan Abbah, har da kujeran da take zama idan taje karatu. Da murmushi a kan fuskarta ta karasa ta zauna tana daɗa ƙarewa wurin kallo, "a nan zamu cigaba da karatun mu kenan, ni ina nan kai kana can kaman a gida"
Ya zauna a gefen ta ba tare da ya bar wani space a tsakanin su ba a maimakon yanda a can suke yi daga nesa-nesa "Sai dai idan kin yarda mu canza wani darasi amma tun kina yarinya nake koya miki karatu na gaji"
"Koda zan biya ka?" Tace tana ririta fuska.
"Muji kaman nawa zaki iya biya sai in yi tunani"
Ba zata ci amanar ajin Malama zuwan ta ya tashi a banza ba, kaman yanda Yaseer yake shammatan ta itama haka zata fara masa. Ta ajiye hannunta a matsayin support sannan ta yunkura ta kamo tsayin shi ta ajiye masa quick peck a kunci kana tayi saurin komawa ta zauna tana sunne kai.
Jin shiru ya saka ta ɗago da ɗauka ko mamaki ne ya hana shi magana amma kallon rashin fahimta yake binta da shi. "Shikkenan? Babe ɗinnan kin ɗauki services ɗina for granted"
"Toh ka faɗi nawa kake so sai in biya ka da kuɗi, akwai wanda na tara da sadaki na da aka bani"
"Sadakin da baki ci ba shine zaki kashe?. Kiss me here shikkenan kin biya" yace yana nuni da lips ɗin shi.
Ta kalli tabon nan dake gefen leɓɓen shi na ƙasa tare da miƙa hannu ta taɓa, sannan ta sake yunƙurawa ta sumbace shi a daidai wurin. Kafin ta samu ta janye sai ji tayi ya sunkuce ta ya daura saman cinyar shi sannan ya fara mayar mata da martani fiye da yunƙurin ta, zuciyan ta ya shiga harbawa a ƙirjin ta, ta damƙi rigan shi a cikin hannunta tana ƙokarin amsar saƙonnin da yake aika mata, yayin da lissafin Yaseer ya fara kuncewa yana niman rasa control.
Ƙaran doorbell shi ya dakatar da shi, ya janye hannun shi dake bayan wuyanta yana sauƙe numfashi tare da ƙarewa kyakkyawar fuskar ta kallo, yau dai yayi nasaran shanye jambakin nan.
nata idanun a rufe gamm, itama numfashin take sauƙewa kamar wacce tayi gudu.
A hankali ta buɗe ido ta kalle shi, idanun shi sun sauya launi, jin yana mata dariya tayi saurin cusa kanta a ƙirjin shi.
Yayi gyaran murya don ya samu muryar shi ya fito da kyau yace "Yanzu kin biya ni na tour ne sauran farashin na karatu don yafi wannan"
Sake danna doorbell da aka yi ya tuna mata da tana zaune ne a cinyar shi don haka tayi saurin sauka ta matsa daga gare shi har yanzu ta kasa cewa komai.
Ya ciro Wayan shi da ya shiga ringing a aljihu, ganin sunan Suhail ne mai kira, bai ɗauka ba ya Miƙe yaje buɗe musu ƙofa.
Saida ta dawo cikin nutsuwarta ta koma ɓangarenta ta ɗauko mayafinta ta lulluɓa sannan ta fita main parlor don tarban baƙin da suka yi.
Suhail ne da Maama sai basket din abinci guda biyu suka zo da shi.
Sallama tayi musu tana ƙarasawa cikin parlon zata nufi kujeran da Maama take zaune a kai Yaseer ya kirata ta juyo sannan ya ɗan bubbuga space ɗin dake gefen shi a kan 2 seater da yake zaune.
Kanta a ƙasa ta ƙarasa ta zauna, sannan ta ɗago ta dubi Suhail tana ƙoƙarin daura murmushi a kan fuskar ta.
"Aunty Reina ina kwana, yaya baƙunta" ya riga ta gaida shi. Saida ta ɗan ware idanu saboda mamaki kafin ta amsa, Maama ma ta gaida ta tana ta ƙunshe murmushin ta ganin yanda ƴar uwar nata ta koma wata nutsatstsiya a kwana ɗaya kawai. Lallai aure mai girmar da mutum.
Ta ciro wayanta ta tako ta miƙa mata "wai gashi in ji aunty Feenah"
"Ita ba zata zo bane shine ta baki?" Ta tambaya da damuwa a muryarta tana karɓan wayan.
Maama bata koma ta zauna ba ta ɗauki jakarta ta raɓa tana amsawa da "tace wai sai nan da sati biyu idan ta gama huta gajiya kafin tazo. Muma zamu wuce toh" ta tsaya taga ko Suhail zai tashi amma yana zaune yana danna waya don haka tayi musu sallama ta juya ta kama hanyar ƙofa.
Sai da ta fita Suhail ya ɗago yace "yauwa Aunty Reina dan Allah ina so mu ɗan yi magana"
Ta juya suka yi ido huɗu da Yaseer wanda ya saki murmushi ya juya ya dubi Suhail "wani magana ne ba za'a yi a gaba na ba? Ita wanda baka son taji ɗin ai ta fita"
"Haba yayanmu, Please, sirrine zan yi da aunty na matar yaya na"
"Dake kana niman abu a wurinta ba, ai dole ta dawo Auntyn ka"
Ashe ba ita kaɗai tayi mamakin yanayin Suhail ɗin ba da canzawar shi lokaci guda.