Sashe 91
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Duk da ka sani ayyuka sun yi min yawa, bani scheduling sessions da patients yanzu"
Ya ɗan ɗaga kafada cikin halin ko in kula "ta musamman ce ita shiyasa"
Dr Fahad kawai ya girgiza kai yana murmushi, bai san garin yaya suka fara mutunci ba, kuma koda ya sani cewa matar shi taso Yaseer a baya amma bayi jin kishin shi shima ya rasa dalili. Ajiye wannan tunanin yayi a gefe sannan ya fara masa bayani "so Yallaɓai YK based on our review muna da yaƙinin abinda Matar ka take fama da shi ana kiransa Post-Traumatic Anxiety Disorder wato (PTSD). Wannan wani yanayi ne da yake bayyana bayan mutum ya fuskanci wani unfortunate event ko wani abin firgici da ya bar masa tabo a kwakwalwa. Sau da yawa wannan yanayin yana kawo mata panic attacks, zamu iya fassara shi da hare-haren firgici, wanda shine ke sa ta fara hyperventilating, wato ta fara shakar iska fiye da ƙima, oxygen da take ja yafi ƙarfin carbon dioxide da take fitarwa, har ta kasa samun isasshen numfashi.”
Yaseer ya sauƙe dogon numfashi tunda duk ya san da wannan abu na gaba da ya kamata ayi mata shine Abinda yake niman sani. Kuma hakan ya furta mishi don haka Dr Fahad ya ɗaura da bayani.
"Trauma-Focused Therapy. Wannan wani irin jinya ne na kwakwalwa wanda yake taimaka wa marasa lafiya su koyi yadda za su fuskanci abin da ya faru da su, ba tare da tsoro ko guje wa tunanin sa ba. A Hausa za mu ce jinya ne da ake yi domin mutum ya koyi yadda zai daina barin abinda ya faru a baya ya cigaba da damun shi a zuciya.
Misali, akwai hanyoyi kamar su:
Cognitive Behavioral Therapy (CBT): wanda yake koyar da mara lafiya yadda zai canza tunani daga negative zuwa positive, kaman daga ‘zan mutu idan na ga wannan abu’ zuwa ‘ina lafiya yanzu, babu sauran hatsari.’
Na biyu Exposure Therapy: inda a hankali ake koya mata ta fuskanci abubuwan da suke tsoratar da ita, har ta saba da su ta daina tsorata idan ta ji ko ta gan su.
Na uku Eye Movement Desensitization and Reprocessing (EMDR): wato wani salo da ake amfani da motsin ido ko wasu dabaru don taimaka mata ta sake sarrafa abubuwan da suka faru ba tare da firgici ba.
Akwai kuma Narrative Therapy, inda za a koyar da ita yadda za ta bada labarinta ba daga bangaren rauni ba, sai daga bangaren ƙarfin hali."
Ya sauƙe kafan ya ɗan zamo a kujeran yana fuskantar Dr bayan ya gama sauraron bayanin da yayi mishi da kunnen basira. "Then for how long kake ganin zata iya samun sauƙi?"
“depending on the depth and gravity na trauma ɗinta ba lallai ace ta warke farat ɗaya ba. Amma idan an hada ta da magunguna da kuma kulawa, in Sha Allah idan muka dace akwai damar samun cikakkiyar lafiya. But akwai buƙatar a canza maganin da take sha zuwa wani daban wanda zai na mata aiki a hankali ba farat ɗaya ba, don wancan dependency kawai yake ƙara mata kuma aka cigaba da tafiya a haka zata koma bata iya rayuwa ba tare da shi ba.”
.
.
.
Dr Fahad shi kaɗai ya koma ɗakin da take ya zauna ya buƙaci ta bashi takardan da tayi rubutun.
Bata yi rubutun da ya wuce layi biyar ba. Shima sunaye ne guda hudu. "Jamal, umman Zahra, Aunty da Yaseer" sai bayanin da ta fara wanda ya fara kama hankalin shi amma bai je ko ina ba ya tsaya.
"Iya abinda zaki iya tunawa kenan?" Ya tambaya yana kallonta.
Ta ɗan jijjiga kai, "ba zan iya rubutawa ba, gwamma in faɗa da baki kawai, zai fi sauƙi".
"Okay to muje daga can sai in ji, and kada ki damu idan baki son kowa ya sani ko mijin ki ba zamu sanar da shi ba, so you can relax and trust me" ta gyaɗa kai sannan ta ƙarasa dogon kujerar ta cire takalmi ta zauna kana ta mike kanta na kallon sama bisa umarnin Dr, a hankali kuma ta lumshe idanunta.
Sai da yayi mata bayanin yanda zata daidaita numfashin ta idan taji ya fara ƙwace mata sannan ya fara mata da tambayoyi har ta shiga mishi bayani dalla-dalla.
.
.
*Yaseer*
Tun daga inda yake zaune a gaban ɗakin dubiyan ya fara jiyo sautin kukan ta, yayi saurin mikewa ya faɗa ciki kafin kiran Dr Fahad ya kaiga shigowa wayan shi.
Kan Reina yayi da ta cure wuri guda idanunta a rufe tana kuka kaman ranta zai fita. Ya saka hannu ya cicciɓeta ya juya zasu fita ba tare da yace ma doctor Fahad komai ba "Idan ba ya gagara bane kada ka bata maganin" cewar Dr Fahad.
Ya ji amma bai amsa ba, ya ɗauki abinda yake nata suka bar asibitin yana ɗauke da ita idanun jama'a na musu rakiya, ta boye fuskar ta a ƙirjin shi don gani take yi kaman duka duniya yanzu kallonta suke yi da Abinda ta gama sanar da Dr, ƙamshin turaren mijinta shi kawai ke tuna mata da akwai wanda ya sani kuma bai gujeta ba.
Tun daga nesa ya danna makullin motar shi ya buɗe Sannan yayi yunƙurin ajiyeta a ɓangaren mai zaman banza saidai taƙi sakin shi, kuma har yanzu idanunta a rufe.
Tsugunawa Yaseer yayi a wurin ga riƙon da tayi ma farin button down shirt ɗin dake jikin shi kaman wanda yayi mata sata.
Addu'a ya shiga tofa mata jin ta fara cisgan numfashi, ya ɗauki lokaci har sai da yaji numfashin ya fara sauƙa Ya riƙo hannun da ta riƙe shi da su.
"Umry, kalle ni"
Ta buɗe idanun da suke ambaliyar hawaye bakinta na karkarwa kaman mai jin sanyi, har haƙwaran ta suna karo da juna.
"Ba laifin ki bane abinda ya faru da mu, ke aka yiwa laifi kuma ba zan bari ya tafi a banza ba nayi miki alƙawari. So ki kwantar da hankalin ki babu wanda yake ganin laifin ki, ni kuma ina kaunar ki a duk yanayin da na same ki, balle kin riga kin zama nutsuwata"
Ya ɗan dakata yana karantan yanyin ta ganin ta rage karkarwan numfashinta ya fara daidaita, gashi ta zuba mishi na mujiya. Ya ɗan saki murmushi ya shafo fuskar ta yace "kin bani farin ciki Ya rawhaty, kin tabbatar da kyawawan mafarkai na, ɓarin zuciyata ta haɗe da ɗaya bangaren ta, yanzu ta cika Hafsatu Reina, although kin tsorata ni Amma ba zan taɓa mantawa da ranar da kika kwaɗaita min rayuwa sannan kika tunasar da ni mutuwa ba"
Dariya ne ya kwace mata shima ya ɗan murmusa "ka ji tsoron in mayar da kai bazawari ko?" tace cikin shaƙaƙƙiyar murya.
"No naji tsoron mu mutu dai bamu ajiye masu mana addu'a ba, cos da an duba jini na a lokacin ya haura Dubu ɗaya" ta cigaba da dariya sauran hawayen na ƙarasa gangaro mata.
"Ina son in yi rayuwa mai tsayi da kai yaya Yaseer, Allah ya ara min tsawon rai in kasance a tare da kai na tsawon lokaci ina saka maka da alkharin soyayyar da kace kana mun saboda shi. Ina sonka fiye da yanda nake son kaina mijina"
Yayi pecking ɗinta a lips ɗinta sannan ya haura goshinta. "Muje gida ki huta" yace yana saka mata seat belt, ya zaga ya shiga ya kunna motar suka bar asibitin.
Saida ya hango wani babban pharmacy a ɗaya hannun yayi parking a tsallake, ya dubi Reina da barci yayi awon gaba da ita sannan ya buɗe motar ya fita ya turo ƙofar a hankali kada ya ɗaga ta, ya jingina da jiki yana amsa kiran Muhammad ya addabe shi.
"Amma na faɗa maka ina asibiti ko?" Yace yana zura hannu ɗaya a cikin aljihu.
"Bold group ma sun yi cancelling contract ɗinsu YK. Na san lokacin iyalin ka yana da muhimmanci amma at this point muna daff da rasa komai, matuƙar manya-manyan investors zasu cigaba da janyewa toh fa zamu rasa kowa. Don haka kayi haƙuri ka dawo bakin aiki koda zuwa mu magance matsalar nan ne, in yaso sai ka sake ɗaukan hutu ka kasance da madam amma babu kai babu Darling ban san yaya zamu yi handling komai mu kaɗai ba, bamu so matsalar nan ta kai har ta taɓa mu a Niger "
Murza goshin shi yayi yana furzar da numfashi. Tare da juyawa ya dubi Reina dake barcinta har yanzu. "Shikkenan, ka bani ko sati ɗaya, akwai abu mai muhimmanci da nake yi amma ni da Aicha duk zamu dawo"
Sai da suka yi sallama ya tsallaka ya siyo maganin ya dawo ya shiga motar dake a kunne suka kama hanyan gida wani zuciyan na faɗa mishi kaman ya kaita gidan Umma saidai bai biye mishi ba tunda ya san zai iya kula da ita da kan shi.
.
.
.
Bayan kwana Uku.
Tsaye take a gaban full length mirror dake staircase wanda zaka iya kallon kanka tun daga sama har ƙasa a cikin sa, da waya a hannunta tana ɗaukan hotunan kanta yayin da take jiran fitowar Yaseer wanda har sun fito tare yace yayi mantuwa ta jira shi.
Tana jin sautin zaratan takun shi har ya ƙaraso ya sako kai bata samu ta ɗauki hoton da ya hana ta juyawa ta dube shi ba.
Ya rungumo ta ta baya tare da zaga hannun shi ɗaya ya ajiye a ƙasan wuyan ta, ya ɗan ranƙwafo ta ɗauke su hoton a tare.
Har gobe bata daina jin gudun zuciyar ta yana ƙaruwa idan suka samu kusanci irin haka ba.