← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 117

Sashe 5

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta shafa sunan tana jin kaman wata rana zata sake ganinta.

Cikin rasa abin yi Zaheera tace "Sorry. Mu bar aikin mu huta sai muje parlour muyi kallo toh"

Girgiza kai tayi bata sake cewa komai ba ta shiga niman key ɗin da zai buɗe kwaɗon jikin littafin a cikin ƙananun akwatunan. Zaheera da gajiyar aikin da bata saba dashi ba ya kama ta, sai ta ɗibe abubuwan da ta tattara a wurin Reina ta tusa kayan a cikin wardrobe ɗinta Idan masu aiki sun zo zasu gyara mata, sauran kayan shafe-shafe da turare, su hair band da bracelets, kayan kwalliya dai-dai su da abubuwan makaranta kuma ta zuba a kan dressing mirror ɗinta da daman a shaƙe yake da tarukuce amma sai da ta ƙara nima ma wasu wurin zama.

"Sai kin fito Reina" ta fita da gudu kada wani abun ya saka ta kirata ta dawo.

Numfashi ta sauƙe lokacin da Idanun ta ya sauƙa a kan Key holder ɗin na wani ɗan teddy cream colour, gashin jikin shi mai laushin gaske.
Ɗagawa tayi, ƙananun keys iri ɗaya guda biyu suka bayyana suna reto.
Ta jaa numfashi, ta daɗe tana son ganin Abinda ke cikin littafin amma tun bayan rasuwar Aunty yana wurin daddyn ta, sai yanzu ta samu ya shiga hannun ta.

A hankali, da nutsuwar da ya same ta kwanan nan ta zura key ɗin a ramin kwaɗon ta murɗa lokaci ɗaya ya buɗe, sannan ta cire kwaɗon ta ajiye a gefe ta buɗe shafin Farko na littafin.

'Fauzee's Diary'

Shine kawai abinda ke rubuce a shafin, da zanen manya da ƙananun hearts da aka yi da ɓaki, ja, da kuma blue ɗin biro.

Kai tsaye ta wuce shafi na biyu ta fara karantawa.

'Goverment name Fauziyya, a gida Fauzee, ƙawaye na suce Zeezee, abun mamaki duk wanda aka kira sai na juya. Ko suna nawa zan amsa a baki ɗaya rayuwata? Ko nan da shekaru Ashirin ina ina?'

Ɗaga ido Reina tayi ta kalli kwanan watan dake saman shafin ta shiga ƙirge da yatsun hannun ta. Shekaru sha biyar baya kenan tayi wannan rubutun gashi ko ashirin ɗin bata cika ba ta bar duniyar baki ɗayan ta.

Dafe littafin Reina tayi a ƙirjinta, ta kwanta tana mayar da numfashi tare da sumbatu.
"Aunty me yasa kika tafi kika bar mu? Me yasa kika bar ni da daddy da Maama? Mun yi kewar ki Aunty, daddy bayi jin daɗin zama da mu idan babu ke, muma munyi missing ɗinki sosai Aunty don Allah ki dawo, zan bar yin duk abinda bakya so nayi alƙawari."

Taci kukan ta har ta gode ma Allah babu mai rarrashi, daga ƙarshe Barci yayi awon gaba da ita a cikin wannan yanayi.

Zaheera ta shigo dubata lokacin da Hajiya Hauwa ta saka driver yayi musu ordern abincin rana, tunda sun rufe store balle masu aiki su girka musu. Takeaway biyu kawai aka kawo, ɗaya na Zahra ɗaya nata, zasu ci natan ne tare da Reina Amma da ta same ta tana barci sai ta yanke shawarar ci ta bar mata.

Fried rice ne da coleslaw da pepper chicken. Zaheera taci Komai rabi sannan ta bar ma Reina sauran ta rufe ta ajiye a kitchen, sannan ta koma ta ɗauko littafin da take rubutu a ciki ta ƙara ma Reina gudun AC ta jawo mata ƙofar ta cigaba da kwafar note ɗin a parlour domin gobe akwai makaranta, yau ma hutun mother's day aka samu kuma rubutun akwai yawa sosai.

Sai can bayan la'asar kafin Reina ta farka, ta kwana biyu rabon da ta samu barci mai nutsuwa kaman yau da ta rungumi wani ɓangare na rayuwar mahaifiyar ta.

Miƙa tayi tana jin cikin ta kaman anyi mata yasa, amma ganin lokaci a agogon bangon ɗakin ya saka ta faɗa banɗaki ta ɗauro alwala ta gabatar da sallar azahar da la'asar tukunna.

Samun Zaheera tayi har yanzu tana rubutu.

"Zaheera abinci Please" shine abinda tace.

Ɗago kai Zaheera tayi ta dube ta "Har kin tashi?" Ta ajiye biron hannunta ta saka ɗayan hannun tana matsa hannun dama da yayi mata tsami kana ta miƙe daga gaban center table ɗin ta shiga kitchen ta ɗauko ma Reina takeaway ɗin ɗazu har da sauran exotic da ruwa da aka kawo dasu ta dire a gaban ta.

Idanun ta na sauƙa a kan shinkafa ta yamutsa fuska "babu wani abun ne? Ni bani son Rice fa!" Gashi kuma shi taci da safe ma, shinkafa a matsayin breakfast! Har yanzu mamakin kanta take yi.

"Nima shi naci, kinga Umma bata nan, kici da daɗi idan ta dawo sai a baki abinda kike so" ta buɗe mata takeaway ɗin lokacin da wani hamami ya bugi hancin su duka.

Matsawa suka yi daga gaban abincin, sai suka kalli juna Reina na watsa ma Zaheera mugun kallo, wato ruɓaɓɓen abinci zata bata!.

"Umm, cabbage ɗin ne fa da aka rufe shi yayi haka, kinga fridge na kulle babu sanyi a jiki"

Sake kallon abincin Reina tayi taga yanda Zaheera ta gauraye shi duka kuma a cikin takeaway ɗin taci maimakon ta ɗiba a plate idan da gaske ta so rage mata , kuma da ba zata haɗa mayonnaise da baked beans a kan duka salad ɗin ba.

Kaman wani ya sakata ta jawo shi sai ta ture tana turo baki. "Ni ba zanci ba, ki bani wani abun"

"Muje in baki biscuit toh"

"Tuntuni kin san kina da biscuit ɗin shine baki bani ba?" Reina taci gaba da mata kallon sama da kasa.

"Nima yanzu na tuna" ta amsa cikin sanyin murya.

Sai da taci laidan Oreo 3 ta kora da exotic kafin ta jita daidai, sauran abincin dare kuma.

Sai bayan Isha Hajiya Hauwa ta shigo gidan ɗauke da laidojin pizza heaven. A parlour ta riski Zaheera dake rubutu har yanzu da kuma Reina dake zaman jiranta.

Da gudu Zaheera ta ƙarasa ta rungume ta tana zuba mata shagwaɓa.
"Umma shine kika tafi baki faɗamin ba?"

"Ba gashi na dawo ba"
Ta miƙa mata laida ɗaya cikin guda ukun dake hannun ta.

Karɓa tayi ta buɗe "Burger? Ni shawarma nake so"

Karɓan laidan Hajiya Hauwa tayi ta sauya mata da wani sannan ta juya ba tare da godiya ba don haka Reina ma ta ƙarasa ta miƙa mata hannu. "Pizza nake so" tace da iyakar gaskiyan ta.

"Toh ai sai ki ƙwata uwata." Ta buge hannun sannan ta juya wurin Zaheera da ta samu wuri a gaban TV tace "Idan kinci kin ƙoshi ki rage mata"

Idanun ta na kan channel ɗin da take ƙoƙarin canzawa ta amsa da "Toh umma. Reina kizo mu ci"

Maƙe kafaɗa tayi "Ni Wallahi pizzan zaki bani"

Hajiya hauwa ta jinjina kai kana ta raɓa ta gefen ta kawai ta wuce.
Sai Reina ta rasa yaya zata yi, rikici ɗazu bai bata abinda take so ba haka ma tsayayya a yanzu. Sai tabi Hajiya Hauwa daƙi, ba tare da ta kwanƙwasa ba ta tura ƙofar ta shiga, Hajiya Hauwa da ta kwaɓe dogon rigan jikin ta tana ƙoƙarin cire brezzier tayi saurin dakatawa hannun ta riƙe da hook ɗin da riga ta balle su, Reina ta fara tsorata ta.

"Ke wacce irin jarababbiyar yarinya ce haka don Allah! Haba!"

"Umman Zahra kiyi haƙuri don Allah ki bani pizza ɗin"

"Na shiga uku" tace tana ɗago ɗankwalin ta daga saman gadon ta kare kirjinta don yanda ta zuba mata idanu kaman zata cinye ta, sannan ta nufo ta gadan-gadan koda Reina zata tsorata, amma tana tsaye ƙeƙam idanun su a cikin na juna.

"Dan ubanki ba zaki ɓace min daga gani ba?" Tace tana zare mata idanu.

Don tsorata ta tsorata amma biyan buƙatar tumbin ta yafi gaban komai a yanzu. Bata jin idan bata ci pizza ɗinnan ba zata iya kai gobe.

Hajiya Hauwa ta ɗaga hannu a harzuƙe sai a karo na farko a rayuwar ta, daga wannan lokacin a cikin wannan ɗakin ta shiga sabuwar duniyar da bata taɓa sanin akwai irinta ba tunda Aunty ta haife ta.
Saboda wawan mari Hajiya Hauwa ta kwashe ta da ita, wanda sai da ta samu makanta na wucin gadi domin ganinta komawa yayi kaman na TVn zamanin da Idan aka kunna shi babu signal, hakama signal ɗin radio ɗin kunnen ta shima ya ɗauke sai sautin Shuushuu take ji tare da ƙaran da yake biyo bayan karafuna guda biyu idan sunyi karo da juna.

Ba don nauyin jikin ta ba da tabbas sai ta kai ƙasa amma yanzun ma jingine take da wardrobe ɗin Hajiya Hauwa, har zuwa lokacin da duniyar zai dawo mata dai-dai.

"Ki ɓace min da gani nace!" Ta hankaɗa ta waje tsanar ta na daɗa ruruwa a cikin zuciyar ta, itace ta lalata ma ɗanta rayuwa. gashi yanzu rabon da ta saka shi a idanun ta shekaru 3 kenan tunda suna tsoron dawowar shi ya iya bankaɗo da sirrin da rufe shi bai zamo musu da sauki ba.

Bata san yaya ake kukan mari ba gwamma ma duka shikam ta sha a wurin Aunty, don haka idanun ta suna bushe banda kaɗawan da sukayi suka yi jaa, sai ta miƙe ta gyara zaman rigan jikin ta tana jin wani azababben zogi a kan fuskar ta, sannan ta juya ta ɗauki hanyar waje. Har yanzu kunnen ta bai samu signal ɗin sauraron kiran da Zaheera take mata ba har sai da ta buɗe ƙofar parlorn ta fita waje.

Ko takalma babu a ƙafafuwar ta haka ta nufi gate ganin haka Zaheera ta shiga sanar da Hajiya Hauwa.

"Hajiya ƙarama ina zaki je?" Cewar security dake haske ta da toci duk da hasken wuta da ya wadaci wurin.

Runtse idanunta tayi saboda karfin hasken, kana ta buɗe bakin da motsa shi ke ƙara tunzura mata raɗaɗin marin tace "ku buɗe min, gida zan je"

Sai tausayin shi ya kamata tunda babu wanda bai san abinda ya faru da mahaifinta ba.
"Kinga dare yayi Hajiya ƙarama, kiyi haƙuri ki koma ciki gobe idan gari ya waye sai a kai ki."
Chapter 5 · 0% Book details